← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 117

Sashe 106

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yes yaya" ta fada tana dariya,saiya maza ya katse wayar,karon farko hawaye na sulmiyo masa,yasa yatsansa ya dauke,wannan wanne irin son zuciya ne da zaiyi nasarar cusa baqinciki a rayuwar wanda baiji ba bai gani ba?.

61

Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya gidan ya canza ya koma wani iri,tamkar gidan da ake zaman makoki,duk da wani ɓarayi na farinciki da ya samu cikin zukatansu,to amma mummy ta bar musu babban tabo a rayuwarsu.

Mummy tana kwance a asibiti,ta samu mummuna yanka wanda ta illata qodarta,najwa na hannun 'yan sanda,saboda asibiti da suka qi amsar mummy lokacin da aka kaita,suka dage kai da fata sai an nemo 'yan sanda,drivern gidan professor da yaga zai shiga ciki bayan bashi yayi aika aika ba yayi musu bayanin komai,take suka garzaya,suka kuma damqe najwa sukayi ram da ita,baiwar Allah jawahir na azare tana ta tambayar kanta abinda ya faru amma bataji komai ba hakanan bata ga komai ba,don haka sai tadan kwantar da hankalinta,sukaci gaba da zama da tsohuwa yadikko tana kula da ita da ciwon suger dinta daya tashi,ta ta'allaqa zuwan nata ma da ciwon nata da ya motsa.

Ta gefen dadday gaba daya tunda al'amarin ya faru yana dakinsa ya kulle kansa,babu wanda yake bari ya shiga kamar yadda shima baya fitowa,yayi kuka yayi kuka har baisan adadinsa,yayi nadamar da yace baiga amfaninta ba,yaji gaba daua siyasa ta fice masa fit a ka,ya tabbatar abinda ya sake kawo wannan matsalolin da gidansa ya fuskanta shine rashin samun wadataccen lokacin zama da iyalinsa da ya fara samu sanadin siyasa,ya tuna yadda rayuwar gidansa take a baya,ya tuna irin soyayya qauna da kulawa da yake samu daga raihana,yayi kukan da tunda mahaifiyarsa ta haifeshi bai taba irinsa ba,har sai da idanunsa suka soma rauni.

yayin da saraki ya duqufa wajen ganin an duba lafiyar mommansa an tabbatar da ingancinta.

Cikin hikima da isa irin ta ubangiji treatment kadam take da buqata,sai kuma idanunta da ya samu raunin gani saboda zama a duhu data jima tana yi,so ko yaya ta shiga haske sai yayita damunta,wannan dalilin ya sanya aka yi mata glass da zata dinga amfaji dashi sanda zafa fita ga haske har zuwa sanda ganinta zai dai daita.

Sai da yaga yadda jikinta ya fara kyau,ta fara dawowa cikin hayyacinta sannan ya karkata zuwa ga gyaran dukkan abubuwan da suka wakana.

Da farko bai sanya an kama bala ba,saboda bisa dukkan binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa tursasashi akayi ya aikata abinda yayi din,saidai kuma ta yaya zaka yarda kaci amanar mutumin daka jima kana aiki qarqashinsa yana hidimta maka?,wannan shike nuna babu aminta ko kadan tattare dashi,wannan dalilin yasa ya sallami bala daga bakin aiki,abunda ya sanyashi cikin tashin hankali da baqinciki me yawa,haka nan ya kori fawwwaz shima,sa'an nan yana jiran samun lafiyar mummy ya hada ita da hajiya shuwa ya shigar da qara akansu,saboda lallai ba shakka akwai abinda yasa hajiya shuwa yin wannab tonon sililin,ya tabbatar ba banza ba,da ita kuma da mummy shi a wajensa dukka masu laifi ne,laifinsu daya.

Abu na gaba ya sanya an tattarewa mummy dukka wasu kaya da suka shafeta an kai Warehouse na kamfaninsa an jibge,bayan ya samu Tex daga daddyn kan ya aiwatar da hakan,saidai abu daya ya kasa tabawa ya kuma kasa magana akai shine najwa,sosai jikinsa ke sanyi idan ya tuna waye mahaifinta?,meta aikata?,don jawahir ko sama da qasa zasu hadu baya jin zai bari sunanta ko rayuwarta su baci,kuma bayajin zai bari ta kufce daga hannunsa ko a cire mata sunan 'yar uwa kuma autarsu,saidai kuma ta yaya zai binne abun?,bayan idan ta dawo zata tambayi mahaifiyarta da 'yaruwarta?,ba shakka yaqi ne babba a gabansu.

Baiyi qasa a gwiwa ba wajen sawa a cafko dukka ma'aikatan da mummy tayi amfani dasu wajen tsarewa da cutar da momma,daga nan aka miqa su kotu aka kuma fara shari'a dasu,bayan ya dora umar kan case din,cikin qaramin lokaci saiga batun ya yadu,cikin manyan shafukan jarida,labarai na gidan radio da television,kafofin sada zumunta,ko ina ka leqa zancan ake tattaunawa
"MATAR BABBAN SIYASA KUMA DAN KASUWA PROFESSOR RASHID AZARE TA BAYYANA A GIDAN MASU TABIN HANKALI,BAYAN DA ABOKIYAR ZAMANTA KUMA 'YAR AIKINTA DATA AURE MATA MIJI TAYI MATA QULUMBOTO TA BADDA ITA TSAHON SHEKARU ASHIRIN DA DORIYA SABODA KISHI KAWAI" topic ne daya dauki hankula matuqa da gaske,aka dinga tattaunashi ana yamadidi dashi.

Koda batun yakai kunnen samir sai yaji dadi da ya karbi wayar jawahir babbar ya hadata da keypad kan zai sauya mata wata,gidan yadikko kuwa ba wani kallo ta cikayi ba,yasan ba lallai labarin yakai kunneta ba,idan ba takanas wani zaiyi ya gaya mata ba.

Cikin qanqanin lokaci al'umma da dangi makusanta suka fara tururuwar zuwa yiwa momma barka da fitowa da kuma jajen abinda ya faru,abinda ya sanya samir ya bada umarnin duk wanda yazo ace momma din bata gidan,badon komai ba,sai don yana buqatar ta samu hutun daya dace,ta sake komawa hayyacinta,don har a sannan tana samun kulawar lafiya daga wajen qwararren likita da samir din yayo haya takanas aka ware daki guda ya zuba duk abinda ya kamata kamar dakin asibiti yake kula da ita.

Cikon sati na uku momma ta fara komawa nutsuwarta,da taimakon bibi da kuma kaltum da take qoqari wajen girka dukka kalar abincin da tasan zai maida ma momman lafiyarta cikin sauri,takan dafa mata dawa kamar shinkafa,tasa mata manja da gishiri,kuma momm din bata qi,tana amsa taci,hakan tasa qashinta ya fara samun qwari nan da nan,kuzarinta ya dawo,abinda zai baka mamaki,tamkar ba itace ta rayu tsahon wannan lokacin tana azabtuwa a rufe ba,saidai idan kayi duba da kasancewarta mace mai tsananun ruqo da ibada tun da can ba abun mamaki bane,to sai kuma zamanta a wancan wajen ya sake sawa ta kusanta kanta da Allah sosai,yawan ambaton Allahnta yafi na baya kafin wannan musibar ta sameta,lalllai ba shakka ambaton Allah kat ne!,dashi kadai kuma zukata suke samun nutsuwa.

Amiru shine ya ankarar da samir rashin fitowar daddy kwata kwata,sanda yaje gareshi ba yadda baiyi ya fito din ba amma daddyn yace yayi tafiyarsa,ya shiga damuwa samir,saboda yasan abinda daddyn ke dubawa da abinda ke damunsa,saidai yadda ya roqeshin ya tafin hakanan ya tafin kamar yadda ya buqata.

Wata sabuwa......sanda yake gayawa momma matakin da daddyn ya daukarwa kansa saita kauda kai

"Ka rabu dashi,qila wannan shine abinda yafi dacewa da shi,saidai a gobe inason ka hadani dashi,ina buqatar takardar sakina,don inason nan da rana ita yau na wuce gaban dangina,wadanda basu da labarin fitowa ta" kai samir ya daga,fuskarsa cike fal da damuwa gami da tarin fargaba,da gaske momma take tafiya zata sakeyi a karo na biyu ta barsu?,idan ta tafin to ya zasuyi su rayu?,waye zai zauna dasu?,wacce rayuwa daddyn zai fuskanta a nan gaba?.

"Momma....idan kika tafi kuma?....." Hannu ta daga masa
"Bance kace komai ba" sai yayi shuru yana sadda kansa,kafin ya miqe a hankali,yana jin maqogoransa a bushe,don haka yayi hanyar kitchen don ya samu ruwan da xai sanya masa ko xai dawo dai dai.

Tarin ganyayyaki ne gefe guda a kitchen din,wanda dukka tayi amfani dasu,wasu cikin girkin da a yanzu takewa momma din,wasu kuma ta zuba cikun kunun ganye data kammala ta sauke,tana ta kiciniyar bude flask don xubawa a ciki kada ya huce.

Daga bakin qofar kitchen din ya dakata,duk kuwa da tarin qishirwar daya kwaso,ya zuba mata idanu yadda taketa bata fuska da yarfa hannu saboda yadda murfin flask din yayi mata tauri yaqi buduwa,sake gwadawa tayi still yaqi,sai ta sake yamutsa fuska taja ta zauna kan kujerar plastic din dake kitchen din tana tura baki,kamar wani ne yayi mata laifin.

Idanunsa ya lumshe a hankali,murmushin da baiyi zato ba ya kufce masa,yana jin wata qauna da soyayyarta mai qarfi tana zarmewa gami da kwarara cikin zuciyarsa,tana hawa kuma wani mataki da matsayi mafi qololuwar daraja cikin ransa,matsayin da mahaifiyarsa kadai yakejin ta wuce nan.

Bai taba zato ku tunanin yarinyar tana da dakiyar da zata aikata abinda ta aikata din ba,bai taba kawowa tsayayyar zuciyarta takai haka ba,abu mafi burgewa tattare da ita tausayi da imani irin nata,da son tsage gaskiya komai dacinta.....wanda dama wannan halayyarta ce tun dadewa.

Sake dubanta yayi,ta dan fada ita kanta,tunda momma ta shigo gidan bata huta ba itama,bayan ta gama dawainiya da lalurar daddy,shikam a duniya me zaiyi mata ya saka mata?,bayan tsaftatacciyar soyayyarsa da yakejin kaf duniya babu matar data cancanci ta mallaketa irin ita?,UMMANTA ta fado masa a rai,dukka jiki da zuciyarsa sun masa amannar cewa za'a samar da mace kuma uwa ta gari a wajen,haqiqa ta canci dukkan wata soyayya da qauna gami da kulawa.

Hannayensa ya sauke ya saka kai zuwa cikin kitchen din ahankali,idanunsa na akanta,cinyoyinta sun fito sosai ta cikin wandon rigar baccin jikinta,hakan ya bawa hips dinta damae fitowa sosai,sai ya maida hankalinsa ga qirjinta,wajen da akoda yaushe yake tsole masa ido .

Sun fita sosai sun kuma tsaya car a jikinta,hakan ya sake baiwa structure na jikinta fita,yabi santala santala hannayenta da a baya suka cika sirantaka,wanda a yanzu sun cika sosai.

Gab da zai isa gareta ta miqe,ta dan qara gaba kadan zuwa gaban famfo ta tara,ta kunna ta tara saman flask din,wai ko saukar ruwan zai sa flask din ya saki ta samu damar budeshi.

Ba zato taji an kama dukka qugunta an riqe,amma sai qamshin turarensa ya bata amsar waye,take jikinta ya amsa gaba daya sanda yake sake matso da ita cikin jikinsa,rungumeta yayi sosai sannan ya miqa dogayen hannuwansa ya gefe da gefanta ya jawo flask din yaa bude mata shi,ya daurayeshi sosai sannan ya ajjiye a gabanta

"Gashi nan,me aka dafa mana ne?,saboda rowa gaba daya mu ba'a taba yi mana tayi ba ko?"

"Subhanallah" ta fada cikin zuciyarta tana qanqame jikinta waje daya,saboda yayi maganar cikin kunneta,hucin numfashinsa da na bakinsa wanda ke bada qamshin mint ya shige kunnenta,ya tada duk wata tsiga ta jikinta,yayin da shi kuma yaci gaba da sansanar wuyanta,sassanyan qamshin turaren data shafa daren jiya na shiga hancinsa,yana aikawa da wani rikitaccen saqo zuwa qwaqwalwarsa,a nutse ya shinfide tafukan hannayensa saman mararta,idanunsa a rufe yana ci gaba da sansanar wuyanta zuwa gashinta dake qamshin man kitson da tayi oiling dashi.
Chapter 106 · 0% Book details