Sashe 30
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Karba tayi ta irga,saita dubi bilal
"Nawane kudin aikin naku?'
"Dubu biyu ne" ya bata amsa,ta sake waiwayawa ga kudin,ta irga dunu biyun,ta linke dubu daya ta miqawa umar
"Mun dauka iya kudinsa,ga canjinku"
"Ku riqe gaba daya"kaita kada
"Bamaso,haka aka biya sauran abokan aikinsa,shima haka za'a biyashi" sosai umar ya cika da mamakinta,ya tsammaci tun a karon farko zata karbi kudin cikin murna da farinciki,ba tare data tsaya neman musaya da tsaffin kudi ba,bare ta tsaya ta irga iya haqqinsu.
Kafin ya ankara tuni ta juya taja hannun bilal sun fara barin wajen
"Oga yace a gaya muku....idan kika ci gaba da zuwa nan wajen,to qaninkin xai rasa aikinsa" cak ta tsaya sannan ta waiwayo,sai data watsa masa wani kallo sannan tace
"Ko da baka fada bama bilal bazai sake aiki a nan wajen ba,tunda babu amfani yin aiki qarqashin mutanen da basa da adalci" daga haka taci gaba da jan hannun bilal suka bar wajen,yayin da tabar umar yana binta da kallo,cike taf da mamakin daya cika masa zuciya.
"Ka gani ko mai gida,dama bata da kunya,duka 'yan gidansu ma,ana xargin qanin nata ma barawo ne" musbahu ya fadi haka,cike da fatan bilal din ya sake nisa gaba daya da wajen aikin,ta yadda shi zai samu ya dinga aikin mutum biyu yana karbar kudin,kallonsa kawai umar yayi,saboda ya shiga shakku ga zaton da suke mata,saiya jiya ba tare da yace komai ba ya koma wajen da saraki ke zaune.
Dakatar da umar din yayi yayi kafin ya gama bashi labarin abinda ya faru,yace yaje kawa yaci gaba da duba abinda za'a qara saman kayan aikin dake wajen.
Suna isa gida ta tattara sauran kararen dake ajjiye kusa da bayan gidansu ta kunna wuta ta dora ruwan zafi,tas ta gasawa bilal jikinsa,tana yi tana baqin rai ita kadai tana mita harta gama sannan ta dubeshi
"Idan na sake ganinka wajen daga yau nida kaine wallahi,tunda kai bakasan dadin jikinka ba bare ciwon kanka,kuma zan koma,duk wanda kake vi bashi a cikinsu saisun hada maka kudinka" hada masa sauran ruwan ya shiga bayan gida yin wanka,daidai sanda umma ta fito daga dakinta,tashinta kenan a bacci,tana dabarun yadda zata miqe saboda yanayin qafarta ta jiyo mitar kaltum din
"Wai lafiyarki kuwa....ke kaltum keda waye?,ga wankin ma har yanzu baki gamashi ba,garin yaya?" Tas ta gayawa umman komai,shuru tayi umman ta sanya buta a gabanta zata daura alwala,shurun na umman ya tabbatarwa kaltum akwai inda tayi kuskure kenan,duk da ita bataga wajen da tayi ba dai dai ba
"Yanzun kin kyauta kenan kaltume?,ki tafi cikin maza kina fada kina babatu?,tarbiyyar dana baki kenan?ina kunyar dana sanki da ita?,shine har kike cewa zaki koma?,to idan kece da kanki ki koma din" daga haka umman taja butar da kaltum din ta xuba mata ruwa taha daura alwala.
Sosai jikinta yayi sanyi,sai a sanna ta gane rashin kyautawarta,saidai ranta ne ya riga daya baci a sannan din,takai maqura kan abinda akewa bilal din,tunda ba yaune na farko ba da hakan take faruwa ba.
A sanyaye taci gaba da aikinta,da zummar idan umman tasu ta huce zata je ta lallabata ta bata haquri.
Bayan sallar isha'i sanda tasan umman nata na zama su danyi hira,tayi amfani da wannan damar ta bata haquri,kamar kowanne lokaci umman na yawan mata uzuri,wannan karonma uzurin tayi mata,tayi mata nasiha
"Kiyi koyi da haquri kaltum,babu abinda yafi haquri riba,duk wanda kikaga yayi haquri baici ribarsa ba,to ba shakka ba ainihin haqurin yayi ba" kai ta jinjinawa umman tasu,saidai cikin ranta tana juya kalmar umman ta haquri,wa shin wanne haqurin umman takeso tayi baya ga wanda sukeyi a yanxu?,ko so take a daga hannu a dagesu,a zagesu,a dalla musu mari su tsugunna su baiwa mutum haquri harda tukuici ma?,to idan ba irin wannan haqurin ba batasan wanne umman takeso suyi ba.
Suna nan zaune umman tana basu labarqi na rayuwa da zai amfanesu,ya kuma zame musu izina saiga sallamar suwaiba,sosai kaltum tayi mamakin hakan,saboda ta manta rabon da suwaiban tazo gidansu,harda bikin habiba,wanda har akaci aka cinye babu ita babu dalilinta,duk kuwa da takawar da tayi taje gidansu,ta kuma sake roqarta tazo din,tun daga wannan lokacin itama kaltum din taji haushin hakan,ta kuma janye jikinta daga suwaiban,dama ita ba gwanar tara qawaye bace,gaisuwa dai ta mutunci tana yi da sauran sa'anninta,an kuma san junq,amma ba qawance irin nata da suwaiba ba.
Wannan dalilin bai sanya kaltum sakar mata fuska ba,ta kuma bata wajen zama.
Daga gefan tabarmar ta zauna kamar wadda take a darare,ta gaida umman,sai umma ta tashi ta basu waje,sai bayan barin umman sannan suwaiba ta kalli kaltum
"Kwana da yawa" murmushi kadan kaltum din tayi
"Ke za'a cewa haka,harna zaci ma ko batan kai kikayi,ba gidan nan kikayi niyyar shigowa ba" murmusawa ta danyi kadan sannan ta tabe baki
"Nikam ai ana ganina,kece dai,daga ke jar nasuru kunyi batan dabo"
"To me zan fita nayi a waje suwaiba" kaita jinjina
"Nasiru fa?"sai data kalli suwaiban sannan tace
"Baya nan,yana cikin gari,yacemin jarrabawa sukeyi a makaranta,sai kuma sun gama zai dawo" yanayin fuskar suwaiban ne ya canza,sai tace
"Allah sarki,Allah ya bada sa'a....."tayi furucin tana miqewa tsaye
"Bari na wuce"
"Da wuri haka?"kaltum ta fada tana dubanta,baki ta sake tabewa
"Eh....dandali zani,kuma nasan ke ba zuwa zakiyi ba"
"Gaskiya kam"ta amsa a gajarce,cikin nuna halin ko in kula tace
"Su lantana ma sun bani saqo,sunce suna jiran sabuwar waqar dandali da kika musu alqawari....naga sai wani kulawa take da lamarin,ban sani ba ko sabom qawance kuka qulla ba" Murmushi kaltum tayi,lantana tana da kirki,hakanan duk wani abu daya shafeta tana shiga ciki,saidai ita qawance bata daukeshi wani abu ba,ummanta a yanzu itace babbar qawarta
"Koda yake idama hakanne ba laifi,sai anjima" Cewar suwaiba tanayin gaba,sai kaltum din ta bita da kallo kawai,kullum mamaki ke qara kamata kan silar canzawar halaye da dabi'un suwaiban,wanda batasan daga inda ya samo tushe ko kuma asali ba.
Tana tsaka da wannan tunanin ummansu ta fito daga daki
"Harta tafi kenan suwaiban" tana gyara zama ta bata amsa
"Eh umma,tace wai dandali zata" kan kujera 'yar tsuguno ta zauna tana miqe qafarta yadda zatafi jin dadin zaman
"Bansan me yasa sam yanzu bakison fita kiga mata 'yan uwanki ba,ba hanaki fita nayi ba kaltume,kawai dare ne banaso kinayi sosai a can" dan murmusawa tayi
"Inason zuwa ummanmu,zan leqa wani lokaci".
Umman bata sake bi takan wancan zancan ba ta sako mata wani
"Kinga daxu fatsima tazo,lokacin bacci ya daukeki bata tasheki ba,inna bata jin dadi,ni kuma ga yanayin qafata data matsamin,gobe idan kin gama abinda kikeyi ki shirya kije ki dubomin ita"
"Toh" ta amsa qasa qasa alamun batason zuwa dai,sai umman ta share bata bi takan sauyawar yanayinta ba.
D/Z
16
*MIERAH'S DUKKAH is ur plug!!!*
*_Muna siyarda kaya kala kala kamar_*
*jaka da takalmi kamfanin* *lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers 'yan yayi dominku da yaranku*
*Muna order kaya daga kasashe daban-daban na duniya*
*Muna siyarda da kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr suratti*
*Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria*
*Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi*
*_ku tuntube mu awannan number kamar haka_*
07039773001
*Muna turawa ko Ina a fadin Nigeria da wasu kasashen ketare*
_LOCATION_= Kano ND gusau
*NAGARTA DA INGANCI SHINE TAKENMU*
*MIERAH'A DUKKHAN farincikin customers dinmu shine namu*🤞🏽🤞🏽🤞🏽
________________________________
Karfe biyu na rana ra gama duk abinda tasan umman nasu na buqata ayi mata,ta shirya tsaf cikin atamfarta wadda tasha wanki,fes da ita,ta sanya hijabinta wanda bata da kamarshi,tunda a qalla kala biyu gareta kwata kwata hijaban data mallaka kenan,duk da cewa su fatsima da yaran kawu ado suna basu suttura ita da habiba,amma nasa samun isowa garesu,inna tana amshewa ne ta saida,kota bada kyauta ga wadansu bayan su gasu a zaune,cikin lefan habiba kuma babu yadda batayi da ita ta dauki guda daya cikin kala biyar din da akayi mata ba amma sam taqiya.
A idanu fes take,saidai kayan sun nuna kodewarsu matuqa,wanda ga duk mai kallo yana gani yasan cewa anajin rayuwa yadda ya kamata.
Gaban ummansu ta tsugunna tayi mata sallama
"Saikin dawo,don Allah idan kin tadda aiki,kada kice ba zakiyi mata ba saboda bana wajen..,kinji ko?"umman tafada,saboda tasan halin kaltum din sarai,kaita jinjina
"In sha Allah" ta furta tana kallon qafar umman,da alama yau din tana mata radadi sosai fiye da kullum,tsabar haquri irin nata ya sanya bata furta ba bare ma ayi mata sannu,da wannan tunanin ta fice daga gidan,ta yanki hanyar unguwarsu inna.
Tana kashingide baya fitar kaltum din da minti goma malam amadu ya shigo,riqe da jakar buhu da muke kira da bacco,miqewa tayi da hanzari ta zauna tana masa sannu da zuwa,gabanta na faduwa,saboda yanayin data ga fuskarsa,ba shakka akwai wani abu,daga sanda tayi masa maraba kuma bai amsa ba ta tabbatar da zarginta.