← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 117

Sashe 25

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bugu biyu umar din ya daga,saiya tsaida tafiyarsa,ya jingina da qarafunan barander da yake tsaye akai,sannan ya goya hannunsa guda daya a qirjinsa,daya kuma yana riqe da wayar yana amsa wayar.

Cikin nutsuwa irin tashi yayi sallama,cike da matuqar girmamawa umar ya amsa,sannan ya gaidashi,ya dora da bayanin dalilin kiran
"Na bincika yallabai,kuma dukkan abinda kaji suna tattaunawa gaskiya ne,yanzu haka ma a gobe yake tunanin maida musu kudin qurensu,hakanan gobe ne rana ta qarshe ta biyan kudin registration din kamar yadda kaji ya fada" Sauke hannun nasa dake harde a qirjinsa yayi bayan yaji bayanan umar na qarshe,kansa a qasa yana ci gana da sauraren sauran bayanan da Umar din yake masa,yasa qafarsa guda daya yana tona fararen duwatsun da aka yiwa qasan harabar varender ado dashi,yana jin zuciyarsa na masa wani nauyi kadan kadan.

Har saida umar din ya kammala bayanansa tsaf sannan ya sauke ajiyae zuciya,cikin sanyi yace
"Ka duba account dinka,zan turo maka da saqo,ayi dukkan abinda ya dace,inason ka gama da matsalarsa a gobe....."
"In sha Allahu sir"
"Yauwa"ya fada sannan ya sauke wayar daga kunnensa.

Muryar jawahir da yaji daga bayansa ya sanyashi tsaiwa daga latsa wayar da yakeyi,ya waiwaya ya dubeta,tana takowa inda yake tsayen,hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando,daya daga cikin abinda yake iya hangowa a ciki flask na tea,wanda yake da yaqinin favourite tea dinsa ne a ciki.

D/Z
13

*Zafafa biyar na kudi ne,ki siya ki karanta naki cikin aminci ba tare da kin shiga haqqin kowa ba*

Ku tuntubi wadan nan numbers din
08184017082
Ko kuma
09134848107

"Yaya....abincinka ya xama ready"jawahir ta fada da yanayin shagwabar nan tata,kai kace har yanzu bata rufa shekaru goma bama,da qaramin murmushi ya saki,akwai abinda yakeson sani amma ta hanyarta,don haka yace
"Thank you autar momy...muje ki hadamin,saiki koma cikin gida"
"An gama yaya"ta fada tana dariya,ya jinjina kai ya soma takawa tabi bayansa.

Baiyi taku biyar cikakke ba wayar tasa ta sakeyin qara,saiya dagata yana duban waye kuma ke sake kira,Hajiya hafsatu ce wadda suke kira da hajiya qarama,qanwa ga Professor rashid azare,qanwa 'yar gaban goshi wadda yakeji da ita qwarai da gaske,kasancewarta diya mace qwaya daya kaf a fadin dakinsu da mahaifiyarsu ta haifa,har ta koma ga mahaliccinta,sai qanwarta mahaifiyarsu me suna karimatu da suke kira ya dikko da a yanzu suke kalla a madadin mahaifiyar tasu,wadda ke zaune a azare cikin ainihin gidan gadonsu da ayanzu professor ya qawata mata shi,babu yadda baiyi ta zauna kusa dasu ba amma sam taqi,tace tafison qasarta,tafison ta rasu a inda aka haifeta,amma halan baisa sunyi watsi da ita ba,lokaci zuwa lokaci suna ziyartarta,hakanan dukka yaransu suna daukarta kamar kakarsu ce wadda ta haifa iyayensu.

Hakan na mata dadi ba kadan ba,yadda yaran yayarta suka maisheta uwa,saboda dama yaro daya tal Allah ya bata,ya rasu yabar nashi yaron guda daya shima,wanda a yanzu suke tare dashi cikin gidanta,ita dinma tunda can macace mai kirki qwarai,ta hadasu ta rungume duka,saika rantse da Allah yaranta ne.

"Hajiya qarama?"ya fada qasa qasa murmushi na fita saman fuskarsa,babu abinda ya fado masa sai drama dinta,mutum ce mai rigimar tsiya,idan ta gaddame kan abu babu mai saukar da ita,idan bashi ba da Allah ya hada jininsu qwarai,ya kuma sanya mata qaunarsa saiko daddynsu,don ko yaranta idan ta hutsance musu saidai su nemi agaji a wajensu.

Sallama ya soma yi mata sannan ya dora da cewa
"Mamana..,maganin kuka na"
"Eh....kace haka mana,tunda ko ranar da zan dawo ma baka riqe ba?"murmushi mai dan sauti ya saka
"Kiyimin afuwa don girman Allah,wallahi abubuwa ne masu yawa suka sha kaina"
"Nayi maka,ka shigo gobe inason ganinka" saida fargaba tadan kamashi,saboda sanin halinta,ba kasafai take masa irin wannan kiran na gaggawa su qarketa ta dadin rai ba,dama ko kafij ta tafin akwai tsumammiya a tsakaninsu,amma don duka ya wanke kansa sai yace
"Ina nan zuwa in sha Allah hajiya"
"Allah ya kawoka lafiya,kafin ka tafi,kaje wajen babanka ka karbarmin man zafin nan a wajensa,don da ciwon qafa na dawo"
"To hajiya,babu damuwa"daga haka dukka suka gimtse layin,ya sauke wayar yana sauk ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da najwa dai dai sanda take ajjiye kwandon hannunta a qasan makeken lallausa carpet din dake shimfide a falon,wanda kusan kaf gidan nan ne kawai babu tiles,dariya take tana fadin
"Ho hajiya qarama,don Allah yaya idan xaka goben na shirya na rakaka". Girarsa ya dage sama yana neman wajen zama,sannan ya girgiza kansa alamar a'ah
"Ba zaki bina ki kwabamin al'amura ba"dariya ta saki sosai ta samu waje ta zauna ta fara zuba masa abincin,sannan kuma tana bashi labarin wasu dramomi da suka sha da hajiya qaraman,yanata murmushi yana saurarenta.

Bai katseta ba,haka baice da ita komai ba,yana cin abincin tana ci gaba da yiasa hira,wanda ta dauke masa kewa sosai.

Kusan dukka cikin gidan yafi kowa fahmtar jawahir,zahiri tana da surutu sosai,saidai kuma akwai hankali nutsuwa da sanin ya kamata,fiye dana 'yar uwarta,tana da sauqin kai da tausayi fiye dana najwa,ta wannan fannin kam ta mata fintinkau,sabanin najwan dake da shegen daukan kai da fadin rai,da kuma miskilanci idan taso,harda na banza da wofi ma.

Sai daya tabbatar labarinta ya qare sannan ya dubeta
"Akwai wani abune da bansanshi ba?"ya mata tambayar data je mata a baibai,don bata gane abinda yake nufi ba,duk da dama tasan halayyar yayan nasu,gwanine wajen magana da kalmomi masu harshen damo
"Me kenan yaya?"ta tambaya kai tsaye,sai daya gyara zamansa sosai sannan yace
"Meya kawo sauyawar najwa fiye da yadda take a baya ne?" Take alhini ya bayyana sama fuskar jawahir,ita kanta abun yana damunta,sannan yana bata mamaki,duk da dama najwam ba kirki ta cika ba,amma a ya zu abun nata yana qara gaba ne,tamkar wani tunzuri,tsahom wasu sakanni tana tadi da zuciyarta da tunanun amsar da zata bashi,shi kuma tsahon wannan lokacin yana karantar fuskarta,yana kuma karanto amsar tambayarta ba tare data furta ba
"Ban sani ba yaya,nima abin yana ta banu.mamaki" ta bashi exactly irin amsar da yake sanya ran dama ita zata bashi,saiya dauke idonsa daga kanta yana jinjina kai gami da sauke numfashi
"Ohkey...ohkey....shikenan to"
"Amma yaya kona tambayeta,ko kumw na bincika?"ta fada har yanzu yanayin alhini baibar saman fuskarta ba,hannu ya daga mata yana fadin
"No auta....barshi,zan aiwatar da komai da kaina"saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,da alama itama abun na ci mata rai
"Shikenan yaya"....

*******. ******. ********

Idan banda qamshin daddadan turare babu abinda jikinsa yake fitarwa a yammacin,wanda dukkan wanda ke kusa dashi idan ua shaqi qamshinsa gamida sassanyar iska mai dadi dake kadawa,babu abinda xai haifarwa zuciyarsa sai wani yanayi na farincikin da baisan daga wace nahiya ya taho ba.

Sosai yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,wadda koda ba'a gaya maka ba kasan cewa sabuwa ce,hakanan bata qananun kudi bace,saidai duk da tsadarta hakan bai hana ayi mata dinkin zamani ba wanda ya dace sosai da mamallakim shaddar,ya bayyanar da sunan na nasa na THE GIANT SARAKI wanda mafi yawan abokai ke kiransa tun ba yau ba.

Ainihin ginin gidan ya nufa,yana tafe yana daura gogo tare da amsa waya da zakayi tsammanin surutansa kawai yake shi kadai,saboda baka hangi ta inda wayar da yake magana da ita take ba,saika lura da kyau sannan zakaga abinda ya maqala cikin ramin kunnensa.

Koda yayi sallama cin falon ma ya kusa kashe minti uku yana wayar,da alama bayanin sa ake masa ta cikin wayar mai tsaho ne,amma ganin fitowar mommy saiya ginmtse wayar ta hanyar cewa zai kira,ya daga kai yana dubanta sanda take isowa,fuskarta kamar kowanne lokaci dauke da murmushin dake bayyanawa duk wanda ya mu'amalanceta koda na minti biyu ne bare wanda ya zauna tare da ita tsananin kirkinta
"Daka qarasa wayar son ai" kai ya girgiza yana sakin qaramin murmushi
"Umar ne,zan kirashi later....za fita ne nace bari na shigo na gaya miki.....zanje gurin hajiya qarama,ta dawo jiya" yayi maganar ne sanda yake sanya links din hannunsa guda daya da bai qarasa sanyawa ba,baima kula ba sai yanzu.

Da sauri ta gimtse abinda ke tasowa saman fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi,muryarta a tsananin washe tace
"Ma sha Allah,amma hafsatu ta dawo babu wanda ta shaidawa cikin gidan nan saikai?,bana jin ko daddynku ma yasan da dawowarta,don inda ya sani zai shaida min"
"Ayyah...bansani ba,da nasan bai sani ba dana gaya masan" murmushi ta kuma yi
"Wala'alla har yanzun fushi dai take ci gaba dayi dashi.....idanma hakanne mu ba zamuyi fushi da ita ba ai,bari na baka saqo ka kai mata,duk da babu yawa,bansan da dawowarta ba"tayi zancan a lokacin da take gab da shiga kitchen.

Daga baki bakin qofa ta tsaya,ta riqe dukka hannayenta a qugunta,idanunta na yaw cikin kitchen din,ta zuqo iska daga hunhunta ta fesar,sannan ta sauke hannayenta ta taka zuwa ciki,sai a sannan kuma mutanen ciki suka ankara da shogowarta.

Katafaren kitchen ne wanda ya hada dukkan wani abu na buqata da kitchen ke da buqatarsa,masu aiki ne har mutum uku a ciki,kowa da abinda yakeyi.

Cikin nuna tsantsar girmamawa ta matakin farko kowa ke mata barka da shigowa,bayan kowa ya dakata da abinda yakeyi don jiran me zatace
"Zuwaira..."
"Hajjaju"ta amsa a ladabce
"Hada abinci maza ki miqawa samir yana falo zaici fita zaiyi,ki tabbatq kome kin zuba masa a tsaftataccen mazubi"
"Angama" ta fada da hanzari tana ajjiye abunda ke hannunta ta nufi aikin da aka sanyata
"Lami" ta sake kiran daya daga ciki
"Gani hajiya" tana matsowa dab da mommyn,duk da ta bada 'yar rata a tsakaninsu
"Ina kilishin nan da aka kawomin jiya?"
"Yana inda kikaje na ajjiyeshi" saita jinjina kai
"Deboshi ki kawomin shi nan"
"Duka hajiya?" Ta tambaya a mamakance,saboda bata manta yadda tayita jaddda mata tayi masa ajiyar mutunci ba,don ma'abociyar son kilishi ce
"Gaba dayansa"ta fada mata yadda zatafi fahimta,da sauri itama ta wuce,minti daya bata rufa ba ta dawo dauke da leda,wanda ko a ido idan ka kalla zakasan yana da yawa basai ka duba ba,hannu tasa ta karba,sannan ta juya ta fice daga kitchen din,su kuma suka ci gaba da abinda sukeyi.
Chapter 25 · 0% Book details