← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 117

Sashe 29

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda ta shiga bata samu inna ba,sai ummansu dake zaune,suna hada idanu umman ta kauda kanta taci gaba da abinda take,tasan ummanta sarai,ta santa ciki da bai,tasan yadda zata saukar da ita,don haka saita zame takalmanta ta isa gabanta ta duqa
"Don girman Allah,don manzan Allah ummanmu kiyi haquri idan kinji haushi,wallahi ummanmu bazan iya bata bane" shuru ne ya ratsa kamar umman ba zatayi magana ba,sai kuma tace
"Idan ba zaki iya bata ba kuma saiki gaya mata maganganu kamar sa'arki?,idam farincikina kike nema to bai samu ba,tunda daga qarshe akaina koma meye ya qare"
"Kiyi haquri ummanmu,kinyafemin" shuru ta sakeyi,kafin daga bisani ta fidda wata ajiyar zuciya
"Allah ya shiryamin ke kulsum" don ta fahimci kaltum din ba zata taba sauyawa ba,saidai addu'ar
"Amin" ta amsa murmush na subuce mata na ganin nasarar data samu ta sauke umman nasu.

D/Z
15

*Littafin kudi ne,guji daukan nauyin haqqin wasu,ki biya ki karanta cikin aminci*

Ku tuntubemu ta wannan numbers din
08184017082
Ko kuma
09134848107

*_ka/ki gujeta!!!_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*_Dabi'ar da zata iya sanya ubangiji yayi maka kaca kaca!,RIQO QULLACI KO KWANA DA WANI DAN ADAM_*

*_Me yiwuwa wanna bawan da kake kwana dashi cikin ranka koka qullata,ubangiji na sonshi fiye dakai,ya fika matsayi a wajen ubangijinka,kaga qullatarshi ko gaba/ko kwana dashi a rai daidai yake da SHIRYA YIN YAQI DA UBANGIJI NE_*

*_Allah ya haskaka mana zukatanmu_*🤲🏽🤲🏽🤲🏽

******Rana ce sosai akeyi a ranar ta lahadi,wadda tun safiya dama ta qwalle sosai da zafinta,kusan indai ba lalura ba da wadanda ta kama dole,kowa ya samu mafaka yana shan iska,tare da jiran ranar ta danyi sanyi kafin ya wuce yaci gaba da aikinsa.

Ita daya ce qwal a tsakar gidan nasu,tsit gidan yake,babu motsin kowa,sai waqe waqen baba laure dake tashi tsakanin babban tsakar gidan nasu zuwa sassanta,tana aikace aikacenta,da alama duniya tayi mata dadi.

A duqe kaltum take tana wanki kayan ummansu da nata dana bilal,ranar ce ke dukan gadon bayanta,duk da zafin da ranar keda ita hakan bai wani dadata da qasa ba,qunci ne fal zuciyarta,wadda babu abinda take mata sai zafi da quna,musamman idan ta tuna da irin tijarar da mahaifinta ya tsiyaye musu tas ita da mahaifiyarta a dazun kafin ya fita,a kullum idan yana irin wadan nan halayen mamaki kamata yakeyi,kai bazaka ce shine ya haifesu ba,ba zaka taba dauka mahaifinsu ne da suka fita ta tsatsonsa ba.

Ta gama matse wasu tana shanya ta soma jiyo dan qaramin kuka da nishi,saita dora sauran kayan dake hannunta saman igiyar tana waiwayawa bayanta da sauri,bilal ne ke shigowa yana dingishi,yayi futu futu dashi da qasa sai kace wanda yayi wanka da gari.

Sakin abinda takeyi din tayi,ta nufoshi da sauri tana kallonshi,fuskarsa daga gefe ta kuje,hancinsa kuma da alamun jini daa hade da qasa,dafashi tayi tana kallon fuskarsa cikin tashin hankali
"Kai....lafiya bilal...meye haka?,waye yayi maka haka?"
Cikin haki dake nuna zallar kukan da yasha yake magana
"Su musbahu ne...."sosai ranta ya baci fiye da tunaji,batasan me yasa suke masa haka ba,sun maidashi kamar wani jakinsu,ko yaya yayi musu abu saisu kamashi suyita duka,bayan duka duka ba wani girme masa sukayi ba,kusan sa'anninsa ne
"Me kayi musu?"ta fara da tambayarsa duk da fushin da take ji yana cinta
"Ban musu komai ba wallahi,wai don kawai am bamu kudin aikinmu yace na ranta masa zai siya sabuwar waya,saina hanashi,saboda wancan karanma da suka ranta basu biya ni ba" wani fushi taji ya taso mata,wannan ba shine karon farko da suka fara dukansa ba,kuma a yau din bata jin zata qyalesu,rashin gatan nasu da galihu baikai har haka ba,don haka tace dashi
"Ina zuwa"saita shige daki.

Ko zanin jikinta bata sauya ba,ta zaro hijabinta dake cikin kayan datti ta saqala,ta tabbatar ummansu bacci take,ba zataji fitar ta ko dawowarta ba,hakan kuma yayi mata,don haka ta warci hannun bilal suka fice daga gidan,tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta isa wajen.

Sauri take falfalawa kamar zata tashi samq,cikin mintina qalilan suka isa wajen,ko ina ma'aikata ne birjik,sai tarin was ada duwatsu na aikin ginin makarantar,iya kayan aikin da aka zube kawai ya isa kasan cewa aikine za'ayo tuquru babu wasa,sai taja ta tsaya tana wulga idanunta inda zataga su musbahu.

Daga can ta hangosu,sunata daukan kwababben sumunti cikin kwanon sarki zuwa cikin sabon foundation din makarantar da aka fitar aka kuma soma sanya bulo.

Tsaiwa tayi ganin isyaku na dosowa inda suke,shine abokin bilal da tasu tafi zuwa daya,ci gaba tayo da dakonsa har yazo gab dasu
"Isiyaku"ta kirasa ganin bai gansu ba,ya waiwayo sannan ya taho inda suke
"Isyaku.....me ya faru tsakanin bilal dasu musbahu?" Sak yadda bilal din ya gaya masa hala shima isyaku,sannan ya dora da cewa
"Saida nace ya daina bawa kowa bashi amma yaqi ji,ni ya gani aiba wanda nake bawa,shima kuma dukkansu babu wanda yake iya ranta masa naira biyar,amma shi duk wanda yace bilalu aramin kaza,ko ragowar kudinsa duka saiya dauka ya basu,kuma yawansu ba biyansa suke ba,idan sukaci sunci kenan" Duban bilal tayi,kamar ta mangareshi haka takeji,saidai yanayin yadda yaji jiki a hannunsu musbahu yasa ta daga masa qafa,kuma tunda Allah yasa taji zata yiwa tufakr hanci,maida dubanta tayi ga isyaku
"Yanzu dawa dawa yake bin bashi a wajen nan" Dukansu isyaku ya lissafa mata,daga inda take tana iya hangosu da idanu,sai daya gama sannan tace
"Muje wajen nasu" tayi gana cike da qarfin hali da qwarin gwiwa,duk da cewa musbahu ya girmesu bama su ba har ita,amma batajin koda tazarar shekara nawa ya bata zata qyaleshi.

Tun kafin su qarasa musbahun yaga tahowarsu,saiya tsaya da abinda yakeyi ya riqe qugu yana jiran isowarsu.

A gabansa ta tsaya tana kallonsa ido cikin ido
"Kudin bilalu nazo karba"
"Na qarfi ne,idan kina dashi saiki amsar masa"
"Bana qarfi bane,kuma nwzan qwata ba,kuma dole ka bashi"
"Bazan bayar ba,duk wanda zaki kira ya karbar masa ki kira" sosai ranta ya baci,hakan ya tunzurata ta fara magana cikin daga murya,cikin masifa da tada jijiyar wuya tana nuna musbahun tare da jaddada masa ba zata bar wajen ba sai ya bada wannan kudin.

Daga can gefe daya dukka cikin sansanin da ake gabatar da ginin makarantar,qarqashin wata qaramar rumfa da akayi da ciyawar bunu,zaune yake saman wata kujera mahadi da teburin dake gabansa,saman teburin lemo ne da cup sai ruwan roba,gefe daya kuma kwamfutar tafi da gidanka ce ta laptop,duk da haka jarida ce a hannunsa yake dubawa shafi bayan shafi,jikinsa na sanye da jeans da shirt wadanda sukayi qura saboda qasar dake wajen,sai rigar ma'aikatan kamfaninsu mai kama da apron daya dora saman kayan nashi.

Hutun minti talatin ya tafi a yanzu yanzu daga filin da ma'aikata suke,wanda kusan duk wani aiki da ale gabatarwa a kowanne qauye indai yana nan yalan shiga yaga yadda yanayin aikin nasu yake,daga irin nashi experience din ya musu gyara a inda yake ganin yana da buqatar gyaran,ya dauki jaridar kasuwanci ne yana duba yanayin hawa da saukan hannuwan jari dollar da sauransu.

Kadan kadan hayaniya daga can gefansa ta soma shiga kunnuwansa,tana kuma rarraba masa tunani,saiya cira kansa a hankali ya waiwaya gefan nasa.

Tana tsaye tsakiyar ma'aikatan maza,sanye da duqunqunen nan hijabi wanda habarda ta koma gefen kuncinta,tsingilallen zani wanda ya tsaya iya qaurinta,da wasu sudaddun silifas,fuskarta sai shining take cikin hasken rana,sakamakon baqar fatarta da kuma gumin da take saboda zafin rana.

Sosai ya zuba mata idanu yana kallon yadda take wulwulga hannu,gamida motsa bakinta da sauri da sauri,duk da baya iya jin muryarta sosai amma ya tabbatar rashin kunya take,dubda da yadda na bayanta keta mata magana,amma batajin me suke fada ma bare tabar abinda takeyi din.

Ranshi yadam baci,donshi mutum ne da baison rashin kunya ko qanqan,shi yasa yake respecting duk mutumin dake sama dashi a shekaru,koda kuwa qasa yake dashi a muqami,daya daga cikin abinda yasa ya tsani SIYASA kenan,saboda yadda dan qanqanin yaro zai iya tsaiwa gaban sa'an kakanshi bama babansa ba,ya danna masa zagi,rashin mutunci ko cin fuska yadda zuciyarsa ta raya masa,saboda kawai ya fishi wani abun duniya,muqami ko matsayi ko kuma kudi ko fada aji.

Ajjiye jaridar hannunsa yayi,saiya kiqe tsaye yana sanya hannayensa cikin aljihun wandonsa,kana ya taka zuwa bakin rumfar ya tsaya yana ci gaba da kallon abinda ke faruwa.

Tsahon wasu mintuna ya hangi umar na nufo rumfar da yake tsaye din,sai yasa hannu ya fitoshi,ya qaraso wajen cikin girmamawa
"Me yake faruwa a can wajen?" Yayi masa nuni da idanuwansa,saida umar din ya kalla wajen sannan ya dawo da kansa wajen samir din
"Nima dai naxo na tadda abun na faruwa....dana tambaya sai yaron yacemin,kudin aikin da aka basu ne babu canji ba'a bawa yaron nashi ba,shine yaje yacewa yayar tasa an hanashi,shine tazo karbar masa,tanata zaginsa yana qoqarin yi mata bayani amma taqi saurarsa" Tsaki yaja yaa ci gaba da sauraren umar
"To nidai ban mata magana ba,saboda kasan halin wasu yaran qauyen nan ba tarbiyya garesu ba,yanzu 'yar cikinka saita qunduma maka ashar" komawa yayi da baya ya zauna kujerar daya tashi din,ya zura hannunsa aljihun wandonsa ya fiddo kudi,'yan dari biyar biyar ne sababbi guda shida,ya miqawa umar
"Ka kai mata,tayi qoqari tabar wajen nan yanzun nan,banason hayaniya" karbar kudin umar yayi,har yayi gaba samir dake murza goshinsa yace
"Ka gaya mata,indai taci gaba da zuwa wajen nan,to qaninta zaibar aikin da yakeyi a wajen,saboda ba wajen zuwansu bane"
"Ok sir" umar ya fada yanayin gaba.

"Kinga madam,kiyi haquri,karbi kudin aikinku da Allah" umar ya fada yana shan gabanta,saida ta yima umar din wani irin kallo sannan ta saka hannu ta karbi kudin,ta kallesu sosai ganinsu sababbi a miqe,idanun musbahu qur akan kudin,ji yake a ransa dama shi aka baiwasu,saboda yana ganin yawansu yasan sun wuce adadin da aka basu din na ainihi,daya sani ma ya biyashi kudinsa,da bai samu wannan garabasar ba,ga mamakinsa saita maidawa umar kudin
"Da irin kudin da aka biya kowanne ma'aikaci za'a biyashi haqqinsa,bama huqatar sabon kudi ko wani abu daban" duban mamaki umar yayi mata,ganin kamar tazo da sabuwar tsirfa,amma kuma daya tuna nau'in muhallin da take rayuwa,sai mamakin nasa ya ragu,ya kuma danganta hakan da qila zallar qaunyanci ne ya sanyata aikata hakan,akwai wasu kudaden a aljihunsa,don haka ya laluba ya irgo 'yan dari biyar biyar guda shida kamar yadda suke a sababbin.
Chapter 29 · 0% Book details