Sashe 46
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru suka danyi dukansu,shi yana jin yadda tsawar ta ratso har cikin wayar da sukeyi
"Yaaya" jawahir ta fada a shagwabe,ranta kuma a dan bace
"Bata wayar" yace da ita kai tsaye,yanajin sanda ta miqa mata wayar ta amsa
"Yaya....barka da asuba" baibi takan gaisuwarta ba,don bayau ta fara irin wannan dabi'ar ba idan suna waya,yana iya jin yadda takan hantari jawahir din
"Kiyi dukka iya tunanin da zakiyi,ki samu abun fada min randa na qaraso gida kan dalilin da yasa kikewa auta haka…...bata wayar" cikin tsorata da sanyin jiki ta bude baki da niyyar baiwa kanta kariya,cikin tsawa tsawa yace
"Shut your mouth.....ki bata waya nace" hakanan badon taso ba ta miqawa jawahir wayar tana jifanta da harara,qasa qasa yadda bazaiji ba tace
"Munafukar Allah" batabi ta kanta ba ta amsa wayar tana maidawa kunnenta,daga can inda yake ya daga wayar daga kunnensa yana kallon screen din jin alamun kira yana shigowa,sai yaga salisu ne still,don haka yace da ita
"Auta....i will call you in the evening in sha Allan"
"Ok yaya" ta fadi tana katse kiran,yayin dashi kuma ya daga kiran salisun.
"Banza kawai asararriya,wallahi duk abinda kika sanya yayimin a kanki zan huceshi,kuma aishi din ba Allah bane,sai yazo din,idan yaso ya kulleni a kurkukun bayan duniya ya jefa maqullin teku,ko kuma ya zaremin raina" ta fadi zancan cikin son nuna bata damu ba,duk kuwa da yadda ranta ke cike da fargaba,don sunfi kowa sanin waye saraki idan ransa ya baci,jawahir bata ce komai da ita ba sai data miqe tsaye ta saita hanyar daki
"Oho dai,ke kika jiyo kuma,ni ba matsalata bace" da hanzari najwa ta yunqura zatabi bayan jawahir data qara wuta ta shige dakinta tana shirin kulle qofa,saidai kaifafan idanuwan mummy suka maidata suka zaunar,mummyn ta qaraso wajen,ba tare data zauna ba ta dubeta
"Ki dinga yawan tunawa da cewa,'yar uwarki ce da baki da kamarta kaf fadin duniya"
Ran najwa a bace tace
"Momy kina gani fa,yasa ta soma rainani" saida mommyn ta fara tafiya ta bata amsa
"Ke kika ja,tunda kika kasa riqe sandata domin ta yimiki jagorancin da bazaki fada kwata ba bare rami" shuru najwa tayi tana jujjuya zancan momy a ranta,saita miqe zumbur tabi bayanta,dai dai sanda daya daga cikin ma'aikatan gidan ta fito dauke da farantin data shiryo kayan ciye ciye a kai
"Ranki ya dade gashi an kawo"
"Koma dasu kitchen" najwan ta bata umarni tana ci gaba da tafiya sauri sauri zuwa dakin mommyn ba tare da tako juyo ya kalleta ba,saifa girgiza kai tana juyawa da uban farantin zuwa inda tasha wahalar shiryo kayan da sai da iyayenta suka zagu kamin ta gama lissafa mata dame dame takeso.
Cike da girmamawa ya gaidashi,sannan ya fara shigar masa da dalilin kiran,baqi gareshi,'yan qasar china dakeson zama dashi,an masa saqo ta email dinsa saidai basu samu respond ba,sai a sannan ya tuna cewa yabar system dinsa a gida wancan zuwan da yayi
"Am on my way jibi in sha Allah,ku shirya dukkan abinda ya dace,daga wannan karon ina saka ran zuwa daya xanyi na gama zuwa,zan bar ragowar aikin a hannun mutanen da aka amince dasu na dawo muci gaba da aiki,but....kada ka shaidawa kowa ranar dawowata"
"Yes sir,in sha Allah" daga haka sukayi sallama,dai dai lokacin daya ji muryar hannafi daga bakin qofa yana neman izinin shigowa.
Izinin yayi masa,hannafin ya shigo ya samu waje ya zauna yana gaidashi cikin girmamawa,ya amsa masa,suka dan tattauna kan batun gini,da abubuwan da za'a qara siyowa na kayan aiki,kusan komai akwai,langa langa kawai za'a dado bandir daya,suka lissafa abinda zai isa,ya bashi harda dori,saboda kusan da wuya yayi aike ya baiwa mutum kudin kai da kai.
Har hannafin ya miqe saiya tuna
"Nace a garin nan akwai teloli?" Murmushi hannafi yayi
"Yallabai akwaisu,amma kamar ba zasu dace da tsarinka ba" baibi takan zancansa ba yace
"Hijabai nakeso guda uku,daga nan zuwa anjima,zan samu?" Kai hannafi ya gyada
"Zaka samu sosai,yau kasuwar mafara take ci,ko a can saina gangara na siyo maka"
Baice komai ba,ya zaro wasu kudin ya miqa masa,hannafi yasa hannu biyu ya dafe sanna ya fice yana masa sallama.
A iya qaramin karatunta da tayi,da kuma dan wayewar data samu game da yanayin yadda karatu yake daga bakin nasuru,da kuma sanin data yiwa makarantar garin nasu,bata taba jin inda suka diba daliban J.s 3 aka tafi kaisu wani waje ba,koda na wuni daya bama bare akai ga kwana,sai gashi ita asiyan ta qirqiro qaryarta tayi mata fenti,iyayenta sun sanya hannu bibbiyu sun amsa.
"Allah ya kyauta" ta furta cikin zuciyarta,tare da tattare duk wani abu daya shafesu ya watsar gefe,abinda ta sani kawai shine,wanda baiji bari ba zaiji hoho.
Abu na farko data lura dashi kallo da wani lokaci akr binta dashi,idan ta hadu da wasu mutanen
"Akwai wata kenan" ta gayawa kanta,tasan dabi'a da halayen mutan qauyensu kaf,mutanene da basu raina abun magana,sun iya gila gutsiri tsoma da yanyana magana,don haka saita qara kama kanta,har ta isa gidan habiba.
Ta samu habiban jikinnnata da sauqi,laulayin nata ba wani mai zafi bane,kamar ta dauki kaltum ta goya,saboda ba qaramar sa'a bace zuwan kaltum gidanta,ta karba dambun tana murna,ta dibawa surukarta takai mata,baban ta amsa kuwa tana ta godiya,surukar arziqi kenan,wadda ta dauka habiba kamar 'yar cikinta.
Sanda kaltum din tayi yunqurin tafiya hanata habiba tayi,ta tareta da hira,duk a yunqurinta na qata ragewa kaltum damuwa da debe kewa,don ganin farko tayi mata taga ta rame,hakanan babu zafin nan data santa dashi.
Duk da haka saida kaltum din ta yakice tace gida zata,ba hala habiba taso ba,amma bata sake matsa mata ba sukayi sallama,baya ta dauki hijabi guda biyu ta bata,hijabin da sai da akasha dambarwa kafin ta karba,har sai da babar yusufa tasaka baki,ta fita babar yusufan tana binta da kallo,cike da tausayinta,lallai inda ace tana da wani yaron bayan yusufanta,da sai ta sanyashi auren kaltum din,tana bata tausayi qwarai.
Kan hanyarta ta komawa gida ta yake shawarar leqawa gidansu lantana,a jikinta takejin akwai wata matsalar kuma,bata kuma fatan wata matsalar ta sake tunkarota a yadda take,tasan ba zata rasa jin abinda ke faruwa daga bakin lantana ba.
Ta tarar lantanar bata nan,innarta ta aiketa gidan yayarta,tace amma ta jima,don haka tana gab da dawowa,tayi tayi kaltum din ta jira amma tace a'ah zata gida,idan tazo a gaya mata.
Saidai tana fita qofar gida sukayi kacibus da lantana tana dawowa,fuskarta cike da fara'a da kuma ganin kaltum din agidansu tace da ita
"Wai....batan kai kikayi ko umma ce ta aikoki?"murmushi kaltum tayi da busashshiyar fuskarta
"Wajenki nazo kuma ban sameki ba" lantana tana qarasowa waje tace
"To ai gani na dawo,da tafiya zakiyi kenan ba zaki jira na dawo ba?" Ta fadi tana kama hannun kaltum zuwa cikin gidan
"Sauri nake wallahi,ban cewa ummanmu zan biyo ba"
"Idan kika ce mata nan kika biyo ba zata ce komai ba,ummanku da innata qawayene,inna laure ce tasa babanku yayi silar daina zuwansu gidajen juna da shegen kitsa gulma da munafuncinta.....inna na dawo" ta hade maganar tata da shaidawa innar tata dawowarta,tana jawa kaltum abun zama
"Yauwa....ashema kun hadu,yanzu nake shirin shaida miki ai tazo" inna data leqo daga daki ta fada
"Eh wallahi inna,a qofar gida mukayi karo" lantana ta amsa mata tana daukar kofin silba,ta ciko ruwa a randa tasha,sannan ta sake debo wani ta ajjiye gaban kaltum din sannan ta zauna tana dubanta
*_Assalamu alaikum masoya 'yan cikin gidanmu na zafafa,fatan alkhairi a gareku tare da fatan dimbin nasara a rayuwarku,ina mai shaida muku cewa in sha Allahu nawa hutun xai kasance juma'a da asabar,saboda nawa jadawalin rayuwar nafi buqatar hutun juma'ar saboda shine nake da issue da ita😁😁,nasan in sha Allah hakan ba matsala bane,kunga zai kasance ranar washegarin randa 'yan uwana zasu je hutu xaku samu guda daya da zai tayaku zama,ina fatan muna cikin wadanda xami rabauta da juma'ar,MUN GODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR_*
#TEAM ZAFAFABIYAR
ANA TARE✌🏾✌🏾✌🏾
27
D/Z
https://youtu.be/tymhRI5zfbQ
👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽
*Kada dai ku gaji,ga tashar dan uwanku,danku kuma qaninku SUDAIS tana buqatar gudunmawarku,shiga kawai zakuyi,ku dannan maballin SUBSCRIBE,ku kuma kunnawa yara 'yan uwansa dake gida su dinga saurara don zaburar dasu suma*
*Jazakumullah bi ahsanil jazaaa*👏🏽👏🏽👏🏽
Tana zaune a tsakar gidansu,yamma ne liqis tana bin gashinta layi layi tana shafa ruwan danyan karkashi data jiqa,hanya ce da take bi wajen gyaran gashinta,yana qarawa lallausan gashin nata baqi,da kuma hanashi zubewa.
Tana aikin tana tuna abubuwan da suka faru kwanakin da suka shude cikin rayuwarta,har yanxu har kuma kwanan gobe walwala da sakewarta bata dawo ba,tana jin tamkar an bude sasari ko kuma mari an sanya hannu da qafafunta,ta tuna irin nacin aiken daya ringa yi mata a jiya kan ta fito ta saurareshi,saidai gana daya lokaci guda,tunda abun ya faru taji kamar am zareshi fit daga ranta baki daya.
"Ka jirani,ina zuwa.....ai bance bazan baka ba,yanzu zan fito" ta tsinci muryar bilal yana fada,tun kafin ya qaraso sashen nasu muryarsa ta rigashi qarasowa,kasancewarsa mutum me murya.
Idanunta kan qofar har ya shigo,hannunsa dauke da wata baqar leda da baka iya ganin abinda ke ciki
"Kaida waye,me kuma zaka bashin kake fadin ya jiraka?" Tayi masa tambayar tana taje kanta da santsin karkashi ya sanya tsahonsa sake daduwa
Dan qaramin turminsu da suke amfani dashi ya janyo kusa da ita ya zauna yana amsa mata
"Dan ladi ne yake neman rancen kudi" wani kallo ta watsa masa mai kama da harara
"Kai din har yaushe kayi kudin da zaka dinga bada bashi,bana hanaka basu bama?,nawa kake binsu amma shuru babu wanda yake da niyyar biyanka?kai sun taba baka aron kudi saboda kana da buqata?,idan fa ka tambayesu kowa cewa yake bashi dashi a cikinsu"
"Kiyi haquri yaya a basu,meye a ciki?,ai na fisu lada har a wajen Allah ko?,yanxu baga irinta ba,saboda Allah yaga zuciyarmu,hijabi aka bani akace na kawo miki" ya fada yana ajjiye mata ledar,ta bita kuwa da kallo bayan ta tsaya da tazar kan da takeyi
"Waye ya baka?,ince dai ba nasuru bane?"
"Haba yaya,ni ko kallonsa yanxu banayi....mutumin nan da yace zai sakani a makaranta ne,bansan ma ya akayi yasan hijabinki ya yage ba"
"Ina fatan na roqarsa kayi ba?" Da sauri ya girgiza kai
"Haba yaya,kin manta ummanmu tace babu kyau roqo?" Hannu ta miqa ta janyo ledar bayan ta dauke idanunta daga kanshi,ta zazzage hijaban dake ciki.