← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 117

Sashe 8

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba'a rufa minti uku ba taga sunyi sallama ya juya ya nufi cikin gari,ita kuma kaltume ta nufo inda umman ke tsimayenta
"Waye wannan ne?" Umman ta jefawa kaltume tambayar sanda suke ci gaba da tafiyar,murmushi kaltume tayi
"Umma baki ganeshi ba?,yusufa ne fa dan gidan huwailan malam baffa"
"Af...af,saikuma da kika fada naga kamarshi da mahaifinsa....ai ban shaida shi ba,na kwana biyu ban ganshi ba"
"Eh....legas yake zuwa ya dawo,bai fiya zama garin na ba"
"Ma sha Allah,Allah ya taimaka....." Ta fada tana son jin qarin haske game da tsaida kaltume da yayi,kamar tasan meke kai kawo a zuciyar ummantata saita ce
"Nifa nan babbar yaya ce,bakiga yadda yake gaidani ba cikin girmamawa" ta fada tana dariya,har hasken haqoranta na bayyana,wanda hasken rana suka qara masu sheqi,dan murmushi umman tayi
"Babbar yaya kamar yaya?"saida tadanyi dariya mai sauti sannan tace
"Habiba fa yakeso,wai don Allah na masa hanya ya sameta" shuru umman tayi tana dan qaramin nazari,a nata lissafin kaltume ce gaba,ita zata fara aurarwa kafin habiba,ko kum duka ta hada ta aurar dasu gaba daya,wala'alla walwalar da suka rasa cikin rayuwarsu su sameta a gidajen mazajensu,don bataga alfanun zamansu ba,dukkansu sun tasa,a karkarar sun isa aure,don an aurar ma da wadanda basu kaisu ba,to amma ita kaltume sam maganar aurenma kamar bai gabanta,har gwara jiya da abun nan ya faru taji tayi zancan nasiru.

"Ummanmu.....bakice komai ba,ko baiyi miki bane?" Kaltume ta fada da alamun sanyin jiki,sai umman ta sauke ajiyar zuciya
"Ba wanda bansan iyalan gidan malam baffa ba,yarane nutsatstsu duk da kuwa kusan duka yaransa maza ne,abu daya zuwa biyu kawai nakeso......banason ya fara neman habiba kansa tsaye,ya fara neman izini daga wajen mahaifinku sannan su gana,abu na biyu,kema inason ki shaidawa nasiru.....indai da gaske yake karya qara tsaiwa dake saiya nema izini wajen mahaifinku,saboda gujewa sake faruwar abinda ya faru a jiya" maganar umman tasu tana hanya,amma jin zafin abinda mahaifin nasu keyi ya sanyata ta zunbura baki
"Ni ummanmu baba mamaki yake bani,irin abubuwan da yakeyi umma kamar ba shine ubanmu ba,jarrabar yau daban ta gobe daban,anya kuwa shine ya haif....." Faf! Taji an doke mata baki,wanda ba kowa bane illa umman tasu,cikin bacin rai take kallonta bayan ta dakata da tafiyar
"Kina cikin hankalin ku kuwa kaltume?.....sau nawa nake ja miki kunne akan irin wannan maganganun ne?,to bari kiji...." Ta fada tana nunata da yatsa
"Yau ya zamana itace rana ta qarshe da zan sake jin magana makamanciyar wannan ta fito daga bakinki,idan ba haka ba ranki zaiyi bacin da baki taba tsammani ba" saita juya zata ci gaba da tafiya tana qoqarin maida qwallar dake taso mata,da sauri kaltum ta cafki hannunta ta zagayo gabanta,itakam tunu qwallar ta soma zuba
"Kiyi haquri ummanmu,in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba,na miki alqawari" ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,bata iya dogon fushi dasu,musamman kaltum din,dukkansu suna bakin qoqarinsu wajwn yi mata biyayya da kyautata mata,ta sani cewa a irin halin rayuwar da suka tsinci kansu dole akwai tarin bacin rai fushi da saqe saqe marasa ma'ana da zasuyi ta dawafi a qwaqwalwarsu,hakanan tarin damuwa zata yi musu yawa,idan tace zatayi fushi dasu me tsayi dukan saiya musu yawa su rasa na tarewa,amma hakan ba yana nufin zata sanya musu idanu tana gani su kauce hanya ba
"Ya wuce amma kada ki qara,saboda ke din kece babba a cikinsu,dukkan abinda kikayi zaya zame musu mudubi ne kuma abun koyi,dukkan wani tsanani yana tare da sauqi,hakanan kowanne yanayi bawa ya tsinci kansa me wuce wane,kuyita addu'a kuyita jurewa,Allah yayi miki albarka keda sauran 'yan uwanki.

********
Tafiyar mintina talatin a qasa suka qaraso gidan tsohuwar wato inna,tun kafin sukai ga shiga zauren gidan ran kaltum ya gama baci,idan tana qaunar mutuwarta to tabbas tana son shiga cikin gidan,a duniya babu abinda ta tsana irin zuwanta gidan,saidai don bata da yadda zatayi ne,ba yadda ta iya,haka tabi bayan ummanmu suka sanya kai cikin gidan.

Filin tsakar gida ne babba kamar nasu,saidai su nasu wannan malale yake da sumunti,a share yake fes saboda badai tsafta ba tsohuwar,daga hagunka madafa ce wadda da bandaki daga kusa da ita,wanda akillace suke a gyare ba kamar na sauran al'ummar karkara ba,da yawancinsu a bude suke,hakanan zaka samu tarin turbaya,daga daya gefan hannun damanka dakuna ne a jere,ginin bulo,wanda aka yi musu rumfa gaba daya gaban dakunan,saboda kare rana da kuma zama saboda shan iska,da kuma zama yayin saukar ruwan sama da sauransu.

A qasan rumfar kuwa tabarma ce babba a malale,sai filo daga bayan tsohuwar wadda ke zaune riqe da mafici tana firfita,daga gabanta danta ne zaune wato qani ga mahaifiyar kaltum wanda suke kira da kawu ado,kusa dashi yaransa ne maza guda biyu,bisa dukkan alamu zuwa sukayi dubata,sai jikokinta guda biyu yaran kawu sama'ila suma,kusan sa'anni suke da kaltum,duk da cewa tadan girme musu da watannin da basu wuce hudu ba.

Sallamarsu ce dukka taja hankalinsu,suka amsa musu kafin su gama fahimtar su waye,tashin farko fuskar innar ta sauya sanda suke qarasowa saman tabarmar don yiwa kansu masauki,cikin qanqanin lokaci walwalarta ta ragu,sai kawu ado ne ke maraba da zuwan umman,fuskarsa a sake yana matsar da yaransa gefe don ta samu wajen zama
"Yanzu nake shirin yin maganarki yaaya,tunda nake zuwa ban taba samunki ba,duk sanda nazo kuma inason qarasawa wajenki,sai hira tayi hira nida inna lokaci saiya quracemin,hakanan nake juyawa na koma" fuskar umman a washe,cike da jin dadi yadda har kwanan gobe ado na daya daga cikin jama'ar dake girmamata,gami da ganin mutunci martaba da qimarta,kafin ta bashi amsa innar ta magantu,cikin sautin dake nuna zafinta
"Yo me zakaje kayi mata?,me xaka ce mata ma?,yau gashi tunda akwai rabo kun hadu" duka sai suka kalleta,hatta da jikokin nata fatsima da kubra sai da suka waiwaya suka dubeta,amma ba wanda yace komai,tunda halin innar bawai sabon abu bane a wajensu,hakanan wannan ba baquwar dabi'a bace,don haka umma ta maida hankalinta kan innar tana matsawa kusa da ita,muryarta cike da ladabi ta ambaci
"Ina yini inna?"
"Lafiya" ta amsa a gajarce
"Ya qarfin jikin naki kuma?"
"Mun godewa Allah" ta sake fada a dake,maficinta yana hannu tana kadashi a hankali,ta lanqwasa qafarta ta dama ta dorata saman gwiwar qafar hagu,idanunta kuwa ko sashen da umman ke zaune bata duba ba,duk da haka umman saita dora
"Ban sani ba inna,sai da salisu yazo maqwafta sannan ya shigo ya gayamin,kusan sati inna amma ba'a aiko an gayamin ba?" Wani banzan kallo ta watsa mata
"Idan an aiko mikin me zaki tsinanawa mutane,zuwanki da rashinsa duk daya fa zuwaira" sunkui da kanta kawai umman tayi,tana ji ranta yana mata suya,yayin da kaltume ke gefe tana qoqarin tausar zuciyarta,kada ta furta wa inna maganar da tasan umman ba zataji dadinta ba,shuru ne ya dan wanzu kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa,muryar kaltum tana gaida kawu ado ita ta katse shurun,fuska a sake ya amsa mata ya dora da cewa
"Ku dinma kaltume ba'a ganinku?,kuda umman naku duk kunqi zumunci,idan ita batazo ba aiki kwazo ko?"
"A'ah ado.....dakata,banason kwashe kwashe,na meye sai sunzo gidanka sun matsanta maka kaida iyalinka sun dora maka nauyi,ni banason irin haka"
"Inna naga...."
"Kaga me?,kar na sake jin bakinka,mara kunyar yarinyar,data shigo ma kaga ta gaisheni ne?" Tasan da wannan zata fake dama,don haka tayi wuf ta gaisheta,sai data gama sheqar iska sannan ta amsa mata,daga daya itama kaltum din bata qara ba,saita waiwaya suka soma magana dasu fatsime,inna kuma sukaci gaba da hirarsu da ado,duk da jefi jefi yana sanyo umman,saidai bata fiya tankawa ba,sau tari saidai tayi murmushi kawai,daga bisani saita ja daya daga cikin yaran adon ta soma hira dasu.

Tun hirar batayi nisa ba fatsime tace da kaltum
"Don Allah ranar saukata kuje da wuri keda habiba,sai kuyita dari dari ku kam,kamar bakuson shiga mutane?" Duban fatsime tayi da mamaki saman fuskarta,don su kam sam basusan da wani batun sauka ba,kafin tace wani abu innar ta rigata
"A'ahhhhhhh....fatsima?,suje da wuri suyi miki me?,wai ni don Allah don annabi sai yaushe zakuyi hankali?,kuyita kalan dangi kuna jajibowa kanku nauyi?,wai meye alaqarku dasu kattume ne?,mantawa kukeyi iyayenku uwa kawai suka hada dasu basu hada uba ba?,kunga wannan...." Saita nuna kawu ado da yatsa
"Shine shida yaransa dolenku,sune suka hada uwa da uba da uwarku,sune abokan yin zumuncinku...."
"Haba inna....haba inna,don Allah ki daina irin wannan abun,baifa kamata ba,ina cewa dukkanmu 'ya'yanki ne,daga cikinki muka fito?,su kuma duka jikokinki ne tunda ke kika haifa iyayensu,kowanne mutum a rayuwa da kalar rayuwar da Allah ya nufata xaiyi,hakanan kowanne da irin arziqinsa,don Allah don annabi inna ki daina,abun bayamin dadi"
"To ubana,idan ka gama wa'azin saika gayamin" tace tana tsareshi da ido,ransa ya baci don haka kawai ya miqe tsaye yana laluba aljihunsa tare da umartar yaran nasa dasu tashi,kudi ya ciro masu yawa ya duqa ya ajjiyewa innar a saman filon dake ajjiye a gefanta
"Gashi,a qarasa siyan abinda babu" caraf ta dafe kudin,bakinta har kunne,kai kace ba itace ke zabga bala'i ba yanzu,tahau godiya da sanya masa albarka kamar zata maidashi cikinta,saita soma cewa yaran su wuce susa takalmansu,shima ya shige ya tafi sanda taga yana maida hannunsa aljihunsa,da alama wasu kudin yake lalubowa.

Ilai ashe kuwa ta fahimci abinda yakeson yi,su fatsima ya miqawa kudin yana cewa
"Gashi kwayi kudin mota" sai tabi kudin kawai da kallo ba tare da tace komai ba,saboda ta sani cewa suma tana morar uwarsu,ya sake dauko wasu ya miqa saitin inda umma da kaltum ke zaune yana cewa
"Yaaya,gashi wannan ba yawa....." Kafin ya qarasa inna ta yunquro zata cafkesu,tuni kaltum ta fuskanci nufin innar,don haka kafin ta kai ga qarasawa ita nata hannun yakai,ta amshe tana fadin
"An gode kawu ado" yayin da inna ta cafki iska,shima ya fahimta abinda yaso faruwar,kuma hakan da kaltum tayi yayi masa dadi,don haka yayi gaba yana sanya takalmansa,yayin da innar ta tsiri mitar babu gaira babu dalili
"Yanzu kai ado saboda rashin sanin ciwon kai,wannan uban kudin haka ka dauka ka baiwa zuwaira?,yarinyar da zuciyarya ta riga ta mutu?" Baice komai ba illa
"Inna Allah ya baki haquri,sai anjima,Allah ya qara lafiya" ya juya ya fice abinsa.
Chapter 8 · 0% Book details