← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 117

Sashe 77

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_Shin kinsan cewa,duk sanda jini ya dauke miki,minti biyar kafin rana ta fadi saikin RAMA SALLAR AZAHAR DA LA'ASAR?_*

*_Idan ya dauke miki minti biyar kafin alfijir ya keto,saikin rama sallar magariba da isha'i ta jiya?_*

*_idan ya rage saura minti uku alfijir ya keto ko biyu ko daya,ba zaki RAMA MAGRIBA BA AMMA ZAKI RAMA ISHA'I tana nan a kanki_*

*_idan ya rage saura minti daya rana ta hudo to SALLAR ASUBA TANA KANKI SAI KIN RAMA TA_*

_wadan nan wajibi ne ki riqe ki kuma ramasu,idan ba haka ba zaki tashi a littafin ayyukanki baabu su_

*_YAYA KIKE QARA KWANAKIN AL'ADA IDAN KIKA LURA DA QARIN KWANAKIN DA JINI YAKE MIKI KAFIN DAUKEWARSA???_*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

45

*_KIJI TSORON ALLAH,ki biya ki karanta cikin aminci,ba tare da kin taba haqqin kowa ba_*

08184017082
Ko
09134848107
_______________________________

Ana gama sallar magaribar daga masallacin layin gidan hajiya qaramar gidan yayo,a qasa yake tattakowa cikin nutsuwarsa har ya kawo gidan.

Sanda yayi sallama falon dukkaninsu ke qoqarin amsa mishi sallamar,amma banda mubina da tayi suman xaune,tana jin jinin jikinta kamar ya daskare ne waje daya ya dauna zagayawa yadda ya kamata.

Babu wanda ya fahimta halin da take ciki,shima duba daya yayi mata ya ganeta,amma bataga alamar haka ba,saiya samu waje ya zauna yana duba hajiya qarama da jiki,yayin da jawahir ke masa sannu da xuwa,gami da yunqurin miqewa da gaggawa tayi ciki itama don tayi sauri tayi sallar kafin yace su fito su tafi,don tasan bayason jira.

Da wata shaqaqqiyar murya mubinan ta gaidashi,tana jin wani iri babu dadi da ganinsa qalau da tayi,don ta gwada kiran wayarsa yafi a qirga amma baya dagawa,ta rasa wacce irin rashin sa'a ce irin wannan,ta mallaki number dinsa cike da fata da burin samun soyayarsa,sai kuma ya datse hanyar da take fata da burin tabbatuwar hakan.

Ganin babu kowa a falon sai ita ya sanya dole itama ta miqe tabi bayansu,saidai dukka wanda ya kalleta yasan jikinta a matuqar sanyaye yake

"Kicewa kalsum tazo ta bawa yayansu abinci....yauma dai ita ta ciyar damu,wadan nan iyayen qyuyar ba abinda suka iya sai abincin bature mara inganci bare qara lafiya" hajiya qarama tace da mubina tana kuma yiwa samir bayani,gami da yunqurin miqewa itama don taje tayi salla.

Sanda take gayawa kaltum din taje takai abincin sai jawahir ta bi mubinan da kallo ganin yadda lokaci daya tayi laushi sosai,yanayinta ya canza.

Miqewa kaltum tayi daga saman abun sallar data kafu a kai tana addu'o'i,kwanakin nan kawai daurewa takeyi tana mazewa,amma ranta damuwa ce fal,tayi kewar gida kamar hauka amma babu wanda ta nunawa,bata kuma da yadda zatayi,kullum da tunaninsu take kwana take kuma tashi,uwa uba kuma ita din asalan da wuya kaga bata kwana gida kusa da ummansu ba,bako ina take zuwa ta tarda ta kwana ba,sai gashi yau wani qaddara ta kawo silar rugujewar zamansi,ta nesantata da gida zuwa wani waje me nisan da tunaninta bai taba dauko mata wannan ba.

Daga nan dakin kitchen din kawai ta wuce ta hado kayan abincin dai da yadda ya dace,don tasan qila samir dinne ya iso.

Tun kafin ta qarasa ta hangeshi yana amsa waya,sai tayi qas da kanta tana takawa a hankali zuwa inda yake zaunen.

"Barka da yamma" ta fada cikin wani yanayi fa batasan yadda akayi tayi magana a hakan ba,wala'alla kodon idanunsa daya zuba mata ne da sukayi mata nauyi?.

Zare idanun nasa yayi daga kanta,don baima san yana kallon nata ba,saiya amsa mata daka yana ci gaba da amsa wayarsa,shida jauhar ne,a yanzun tana jinta kamar tafi kowacce mace sa'a a duniya,ta fara sarewa daga samun samir din kwata kwata,duk kuwa da yadda yayi mata,saiga albishir kwatsam na dukkan dama ta samun mallakar tasa,wannan dalili yasa ta buse wutar mallakar zuciyarsa babu qaqqautawa.

Yadda taga jawahir na masa,saita duqa tayi serving dinsa,bayan ta gama ta yunqura zata miqe sai ya dakatar da ita da hannu yana ci gaba da amsa wayarsa,hakanan ta koma gefe ta zauna tana,ta takure waje daya tana wasa da yatsun hannunta,jinta take wani iri,saboda babu kowa a falon daga ita saishi,sai take ganin kamar ya cika falon shi kadai.

Batasan me yasa a duk sanda zasu kebe daga ita saishi ba saita dinga jin wani nauyinsa,tana auna hakan a ma'aunin girma da nauyin alkhairin da yake shigowa dashi a rayuwarta.

A hankali kunnuwanta ke dauko mata wasu daga cikin wayar da yakeyi,ta fuskanci da mace ne,haka kawai sai takejin wani abu mara dadi a qirjinta,amma tafi ta'allaqa hakan da ajjiyeta da yayi tana suraran sirrinsa,saita qara tsumewa a waje daya,tana ta faman murza yatsunta kamar wadda aka baiwa wannan aikin.

Shi da kansa ya gimtse hirar ta hanyar daukar excuse din zaici abinci,saboda bayajin wani dandano nata ko armashi,ya sauke wayar idanuwansa na sauka kan zara zaran yatsunta wanda ke nuna dukkan alamu na laushin da fatarta keda ita.

Sai da yayi bismilla alamun fara cin abincin sannan ta farga ya gama,a hankali ta gyara zamanta ba tare data iya kallonshi ba.

Hankali kwance yake cin abincinsa,tare da mamakin yadda girkin yayi dadi,dama can ta iya girki ne ko zuwanta ta koya,tunda tazo basu taba wata doguwar hira tsakaninsa da ita ba,saiya jefa mata tambayar

"Ya akayi kika iya girki?"
Ka ta jinjina masa sannan ta bude baki da 'yar qamar muryarta ta amsa masa da eh

"Waya koya miki?"

"Ummana ce" ta amsa masa

"Madalla da umma,tayi qoqari sosai" maganarshi ta sanyata daga kai ta dubeshi,sannan murmushi ya qwace saman fuskarta.

Karo na farko da yaga wadataccen murmushinta irin haka,fuskarta ta qawatu matuqa,ta sadda kai murmushin taci gaba da wanzuwa kan fuskarta

"Na gode" ta fada tana jin dadin yadda ya yabi ummanta,sama sama yake kallonta,yana kuma karantar farincikin dake zuciyarsa dangane da yabon mahaifiyarta da akayi,sa yaji wani abu yana taba ransa sosai akan hakan,harma yaji ya qoshi,duk da dadin da abincin yayi masa,don bazai iya tuna yaushe yaci irin wannan tuwon ba,gidan hajiya qaraman yake samu dama,to ita kanta kwana biyu daya zamana yau lafiya gobe babu sai ta sakarwa masu aikin girkin duka,su kuma bason tuwo suke ba,kamar yadda ya fuskanci mummy bata sonsa,hakan ya sanya ba'ayinsa sam a gidan.

"Tunda kike baki taba period ba dama?" Ya tambayeta kansa tsaye,tadan daga ido ta kalleshi,sai tayi saurin sakewa,nauyi da kunya suka cikata,saita cure waje daya kamar mejin sanyi,ta kasa amsa masa tambayar,murmushin gefan baki ya saki,sabida ganin yadda tayi daga yi mata tambayar,saiya tuna sanda take bala'i lokacin da zata amsa haqqin dan uwanta,duk yadda suke hasashen bata da kunya ashe ba haka bane,abu daya ne zuwa biyu kawai,ita din bata bari a danne haqqinta indai tana da ikon karba,sai kuma zamantowar mutum me qaunar mahaifiyarta da yan uwanta.

"Ki dauko takalminki muje,yanzu zamu dawo,ki gayawa jawahir ta zauna" bata iya tambayarsa ba,sai kawai ta miqe kamar zata harde ta nufi daki,binta yayi da kallo kafin ya janye idanuwansa,yana tuna ganin da yayi mata a dandali ne,a sannan halayyarta ce ta gaskiya kenan?,kansa ya shafa yana ture tunanin gefe guda tare da duban hajiya qarama dake dawowa falon.

"bazan boye miki ba,sonsa nake kuma yayimin.......zaki iya taimakamin?" Wadannan ne kalaman da suka shiga kunne kaltum sanda take shiga dakin,duka sai suka juyo suka kalleta,kanta ta dauke tana nufar inda ta ajjiye takalmanta,ba tare data sak dubansu ba tace

"Yaya yace ki jirashi,zamuje mu dawo"ta fadi mata tana nufar qofa

"Ok,saikun dawo" ta amsa mata tare da maida hankalinta ga mubina,wadda gaba daya ta koma kalar tausayi,bisa kuma dukkan alamu zuciyarta a karye take sosai.

Ta cikin hasken gidan yake hangota yana zaune daga cikin motarsa sanda take fitowa,ya fuskanci bata da wani zafi ko kadan,komai nata tana yinsa ne cikin sanyi,saiya buda gida gaba kafin ta qaraso,ya kuma janye idanunsa ya maida ga wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo.

Sai data zauna sosai sannan ta rufe qofar,ya ajjiye wayar gefansa ya tayar da motar sannu a hankali suka fice daga gidan.

Tafiyar mintuna ashirin suka iso wani guri da tun daga waje yafi mata kama da asibiti,da suka shiga ciki ta daga kanta tana duba rubutun dake maqale a qololuwar ginin wajen,a nan ta tabbatarwa kanta a sibiti ne,tana jin sanda yayi waya da alama da wanda sukazo wajensa yake,kana ya bata umarni suka fito,yana gaba tana biye dashi har cikin asibitin.

Kai tsaye reception suka tsaya,wanda ke dauke da files na marasa lpy a tsare cikin wata kanta,sai tarin computers da suke amfani dasu wajen karbar kudi da bada receipt.

Da mutane a wajen don haka suka dan tsaya daga baya,hankalin samir na ga wayarshi yana qarasa duba saqon da ya samu dazun,daya hannun nasa kuma riqe da key na mota yana dan kadashi.

Tunda suka shigo wajen hankalinta ya dauko a kansa,ta juyo ta kalleshi yafi sau shurin masaki,saidai shi baisan abinda ke faruwa bama.

Kaltum kuwa duk abinda ke faruwa tana kallo,har zuwa sanda tadan matsa kusa dashi,da wata maqalalliyar muryarta dake nuna gayunta tace

"Hi" sai a sannan ya daga kanshi ya dubeta

"Hi" ya mayar mata yana qoqarin maida kansa ga wayarsa,ta yunqura zata sake magana muryar receptionist din ta katsesu

"Sir.....kaine muhammad samir?" Kai ya gyada mata

"Sorry sir.....Dr labaran yace ka shiga office dinsa ka zauna,zaka ha sama ne,daga hannun damanka daki na qarshe a nan zaka samu office dinsa"

"Thanks" yafada yana yin gaba,kaltum tabi bayansa,saidai koda bayan sun gota ta din sai data waiwaya ta kalleta,itama su take kallo,ta sakarwa kaltum murmushi tare da daga mata hannu,saita dayke kanta tana tabe baki,itakam koda a karkararsu tana ganin baiken irin wannan zub da kan,ashe har a nan ma da ake ganin matansu sun waye suma suna irin wannan dabi'ar?.

Tana biye dashi tana mamakin me ya kawosu asibiti?,waye baida lafiya?,kuma.taji ana zancan dr,koshi za'a duba?,duka bata da amsa,saita haqura taci gaba da binsa tana zubawa sarautar Allah ido.
Chapter 77 · 0% Book details