← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 117

Sashe 110

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da cewa haqarsa bai cimma ruwa ba,amma a ranar yayi yadda yaga dama,ta luguiguita sosai a hannunsa,wannan din ya rage masa zafi fiye da kima,saidai ita din ta rabauta da ciwon mara,wanda sai daga bisani ta samu relief,ta kuma gudu daki yana fita sallar asuba.

A abun salla ta sake samun jawahir,suna hada idanu tayi turus,sabida bata zaci a dakin zata kwana ba,ga kayan jikinta gaba daya a yamutse,wanda duk wanda ya kalla ya tabbatar akwai ayar tambaya akai.

Dauke kai jawahir din tayi,tayi kamar bata gani ba,sum sum sum ta shige bandaki,ta sakarwa kanta shower bayan ta daidaita duminsa.

Ƙarfe biyu na rana dai dai motar da suke ciki ita da samir,da kuma spare wadda tayi musu rakiya ta tsaya cikin garin dinya,qofar gidan malam amadu.

A nutse ta bude qofar ta tura,sai kuma ta tsaya turus tana kallon qofar gidan nasu,maida kallonta tayi ga gidajen dae hagunsu da damansu,duk sune dai gidajen data sani,duk da su din ma kamaninsu sun jirkice da shafen suminta da kuma fenti daya haska gidajen gaba daya.

Waiwayowa tayi ga samir,sai taga ita ya zubawa idanu gaba daya,yana jingine da bayansa a owners corner,tun asubahin jiya ya zama wani me sanyi maras laka a jikinsa,duk motsin da xatayi idanuwansa na kanta

"Anya su ummanmu basu tashi ba?" Tayi maganar cikin taraddadi,saboda batasan amsar da zata samu ba.

Batasan ya iso inda take ba,sai maganarsa taji cikin kunnenta

"Ummanmu tana ciki,tana dakon isowarki.....maza ki shiga ki sameta.....amma ina nan ina jiranki kizo muyi sallama,kada a manta dani" wani qawataccen murmushi ya subuce mata,ta ritsashi da idanu tana son karantar wani abu tattare dashi,zuciyarta na gaya mata yayi halin da ya saba duk yadda akayi,sai taji gaba daya zumudi ya cikata,don haka cikin wani irin hanzari.....ko duba da high hill din dake qafarta ba ta zuro qafafunta waje.

Dai dai sanda ta doshi qofar gidan nasu wata mata dauke da qullin kaya saman kanta tazo zata gifta kaltum din,babu abinda yake tashi a jikinta illa tsami hade da wari,sai maganganu take kai kace wata zararriya ce,fuu ta wuce ta gefan kaltum din,bisa dukkan alamu bata gane wace ba.

Daukin shiga gidan ya sanya bata tsaya wani dogon tunani akan wasilan ba tayi cikin gidan,daga ciki ta tsaya tana shawarar inda zata shiga,saboda gidan ya zama kala biyu,daya sashen gini ne na musamman akayi kai bazakace a qauyen bane,daya sashen kuma an masa kwaskwarima,babu laifi.....

Yaran da suka fito daga ainihin sashensu riqe da robar man quli suka bita da kallo,ta ganesu dukansu,saidai suma da alama basu shaidata ba

"Nan ne wajen umman bilalu?" Ta tambayesu

"Eh nan ne" suka hada baki wajen bata amsa,kana suka bita da kallo sanda take wucewa sashen nasu a gaggauce.

Tana tsaye ta bawa qofa baya,sanye da atamfa ABC ja me kwalliyar korayen ganye,idan ka duba wajen qafafunta da hannayenta da kake iya ganowa ta baya lalle ne ja shar,hakanan jelar gashinta ta nuna sabintar kitso dan hannu biyu dake kanta.

Muryarta kawai taji ta tabbatar ummanta ce,magana take da wata dake daya daga cikin dakunan da aka qawata da window da qofofin zamani,batasan dawa take magana ba,amma muryarta kawai zata gaya maka cikin farinciki da walwala take.

Da sauri ta matsa ta rungumeta ta baya sannan ta saki kuka tana dora kanta saman kafadarta,qawataccen murmushi ya subuce daga fuskar umman

"Alhamdulillah" ta ambata tun kafin ta waiwayo ga diyar tata,kaltum dinta,wadda ta kwashe watanni da kwanaki masu tsaho bata bacci,ta kwashe lokaci me tsaho tana begen ganinta....tana taraddadin a wanne hali take ciki?,wacce rayuwa take?,a hannun wa ta fada?.

Juyowa tayi ta rungumeta sosai cikin jikinta itama,muryarta na bayyana tsantsar farinciki da take ciki

"Ahaf.....daga shigowa kuma sai kuka?" Tayi mata maganar itama tana qoqarin hana kanta kukan dakeson qwace mata

"Ummanmu....ummanmu" ta tsinkayi muryar habiba daga cikin daki,da hanzari kaltum ta daga kafadar umman,saidai kuma tana riqe da hannayenta da qarfi ta qwalla sunan

"Habi ta" kan kace kwabo saiga habiban tsaye a qofar daki,aka shiga kallon kallo,kafin dukkaninsu su barke da kuka suka nufi juna suka rungume.

"Wai lafiya naketa jin koke koke?" Muryar inna laure ta ratsa kunnuwansu,wanda dama kusan yanzu aikinta kenan,bata iya zama,ko yaya taji wani motsi daga sashen,tun daga sanda ta bude idanu taga sauyin rayuwa ya fara saukarwa zuwairan,shikenan bata iya wani cikakken bacci da idanu biyu,kullum cikin fargaba take,musamman da asiya ta fara haduwa da gwagwarmayar rayuwa daga gidan alhajin data aura,yau fari gobe tsumma,kullum cikin nuqu nuqu da qoqarin boye halin da suke ciki take.

"Ah....baquwa kukayi ne?......tofa....ikon Allah,wannan fuskar kamar na taba ganinta" inna lauren ta fada bayan ta zagayo saitin fuskar kaltum

"Eh,'yarku ce kaltume,tazo ganin gida gaidamu" ummanmu ta fada,dai dai sanda yara suka fara shigowa da kaya suna jibgewa a tsakar gidan daga gefe daya

"Kal wa?....kai haba zuwaira....ina kattume zata samu kyau da zatin wannan?,kigs fuska luwai luwai,jiki lukui lukui....jiki sai tahin qanhi yake.....ke bakiga kayan jikinta bama,anya kuwa zuwaira akwai Allah a ranki?" Inna laure ta fada tana kama baki,rabi da rabin hankalinta kuma akan kayan da yaran ke jibgewa,wanda sun fara cinye bakin qofar gaba daya.

Murmushin yadda hassada ta fito sosai muraran saman fuskar inna lauren ummanmu tayi

"Kayya,amma abu baiyi dadi ba da uwa ta kasa gane diyarta,matsa dai da kyau ki sake dubawa" koda inna lauren ta matsa ta tabbatar kaltum din ce,saita juya sumi sumi ta bace daga sashen,yayin da kaltum ta bita da kallon mamaki,gaba daya ta lalace,tsufa ya keto mata,idan suka jera da ummanmu sai ka dauka umma diyar inna laure ce.

Falon da aka qawata kuma aka kira da falon ummanta take bi da kallo,sanda habiba ke feshe shi da freshener samir zai shigo,qamshin freshener din ya cakude da qamshin sabon gini da kuma sabon fenti,ita har yanzu gani take idanunta nayi mata gizo ne,idan ta kalli qawataccen gidan da sunan gidan mahaifanta,kamar ba'a karkarar ba,ko ina tiles da tiles,ga ruwan famfo ga wutar solar inverter,fankoki kota ina?,fakadeden tsakar gida da yasha tiles aka qawatashi da shuke shuke,ga yalwataccen kitchen irin na zamani,ga dan qaramin gas,abun kamar a mafarki?,bayan maka makan dakuna dake tsakar gidan,duk da bata bude ba batasan meye a ciki ba,kai koda a cikin garin ba kowa zai dace da irin wannan gidan ba.

Har samir ya shigo suka gama gaisawa da ummansu tana cikin duniyar tunanin wanda ya yiwa rayuwar ummansu wannan baban aikin,umman tasu ta qara qiba tayi wani shar da ita,idan ta hada umman data bari lokacin aurenta data yanzu sai kace uwace da 'yarta,babu wani gami ko kadan.

Bayan sun gama gaisawa umman ta qwalawa muntasir da shigowarsa gidan kenan kira,murna da mamakin ganin kaltum din ya cikashi,ta bashi key

"Ka bude masa dakin can hanyar soro,yadan huta kafin su wuce,ai baya juyawa ba daga zuwansu" ummanmu ta fada bayan ta yiwa samir magana ya dakata da zancan tafiya tun yanzu,muntasir ya karbi muqullin cikin murna ya fice.

Nannauyar ajiyar zuciya kaltum ta saki,tabi habi da kallo wadda ke ajjiye fulasan abinci masu kyau a gabanta da batasan inda suka samo fulasai masu kyau haka ba,habi din tata ta cika ta zama babbar mace,tayi qiba sosai,kamar ba 'yqr ficikar habi din data tafi ta bari ba,tayi adonta cikin wani lace mai kyau,da alama tana samun kulawa daga wajen mijinta yadda ya kamata.

"Ina dana ko 'yata da ban sansu ba?" Kaltum ta jefawa habi tambayar,saita dago kai,suka hada idanu,suka sakarwa juna murmushin dake cike da qauna irin ta 'yan uwantaka

"Yaya kaltume,ki fara sallamar dan aljannar mijinki din nan tukunna,yau kwanan hira zamuyi" saita dan dubeta

"Ki baro yusufan a gida?"

"Baya nan ma,ya tafi Lagos,kuma koda ya nan shi da kansa zaice nazo na kwana din"

"Lallai yusufa,likkafa ce taci gaba haka?"

"Duk ya sanadin mijinki ne ai,arziqinku muke ci" ta amsawa kaltum,duk da maganar ta daure mata kai amma haka ta duqa ta dauki kwandon,sannan ta fice tabar su ummanmu suna binta da kallo,kowa zuciyarsa fes qal,suna mamakin yadda kaltumen ta sauya gaba daya,kai baka ce ita bace.

Zata fita taci karo da wata mata na shigowa,idanu jage jage da hawaye tana sharbar qwalla,sai taja da baya don bata hanya,saboda ganinta riqe da yaro ga kaya ga kuma tsohon ciki.

Data sake dubawa sai taga ashe asiya ce,mamaki sosai ya kasheta,asiyan ce haka?,yarkace yarkace cikin tsumma?,itama asiyan idanu ta zuba mata,amma sam zuciyarta taqi yarda cewa kaltum din ce,don haka ta gwada kiran sunanta,jin ta amsa saita zabura,sannan da sauri ta qara gaba zuwa sashensu tana waigenta tare da qoqarin boye hawayenta.

Mamaki ya cikata sanda take ajjiye kayan abincin data jiyo muryar samir a qofar gidan tare da muryoyin jama'a,ko data leqa,sai taga qofar gidan nasu cike yake da al'umma,samir na cikinsu,daga gefe daya kuma wasu kaya ne aka sauke,da alamu kuma wannan al'ummar za'a rabawa,don kowa ka kalli fuskarsa cike yake da farinciki.

Idaunta ta maida kan samir,ta zuba mishi idanu tana masa kallon qurilla,irin kallon da bata iya masa matuqar yana tsaye a waje gata gashi,yadda yake ta haba haba da mutanen kawai zai alamta maka he's so simple man,bashi da qyamata,hakanan bai dauki duniya da fadi ba,kuma yadda suke gaisawan kadai xai gaya maka sabo sukayi,ba iya na yau ba kadai.

Ci gaba tayi da morewa kallonsa,duk inda ya matsa idanunta suna biye dashi,daga bisani ma saita zauna saman wata 'yar kujera stool dab da window din tana bibiyar duka motsinsa da idanunta,murmushi na qwace mata lokaci zuwa lokaci,har zuwa sanda taga sun fara rabon kayan,yana miqa wani abu a envelope da tafi kyautata zaton kudi ne,ana dorawa kowa saman kayan.

Komai da yakeyi yana yinsa ne cikin nutsuwa,cikar haiba da kamala,zuciyarta ta dinga qara gudu saboda yadda yake sake burgeta da shiga ranta,ganin bai qyamaci al'ummarta ba.

Hayaniya ce ta tashi daga can baya,harta qaraso inda samir yake tsaye,da alama kuma duka akan rabon abincin ne,matar da suketa tarewa ta qaraso,data duba da kyau sai taga wasilarta ce data shige dazu,wasilar da ayanzu tafi kama da mahaukaciya tuburan.
Chapter 110 · 0% Book details