← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 117

Sashe 16

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkaninsu suka miqe kowanne fuskarsa na nuna tsantsar farinciki,daya daga cikin matasan yammatan nan wadda da alama batakai shekarun daya ba ita ta tako da sauri zuwa inda professor yake
"Abba.....sannu da dawowa"ta fada da 'yar siga ta shagwaba,da alama kuma hakan habit dinta ne,tana dora kanta saman kafadarsa,kamar marayan daya samu tallafi,murmushi ya saka yadan dora kansa saman kanta
"barka kadai auta....na sameku lafiya?"
"lafiya qalau abba,saidai munyi missing dinka"murmushin yakuma saki
"gani na dawo ai jauhar,duk wata kewa ta qare ko?"kai ta gyada,sai dayar itama ta matso,tasa hannu kadan tana gyara eye glasses dinta,fuskarta itama murmushinne kwance
"barka da zuwa abba"
"barka kadai lelen abba.....na sameku lafiya?"
"lafiya lau abba ya hanya?"
"alhmdlh,ya karatu?"saida ta saki wani ni'imtacce murmushi,tana jin wani dadi na ratsata,ta daga idanun a hankali ta maida gashi,samir.......wanda har yanzu yake tsaye a bayan abban nasu tamkar wani dogari,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon dukkan abinda ke faruwa, inside him yana jin tsaiwarsa a wajen cikin abubuwan da suke gundurarsa nan da nan,ya qagu duka a gama wadan nan gaishe gaishen.

dauke idanunta tayi ta maida kan abban,a duniya tana jin dadi tana alfahari abban nasu ya tambayeta karatunta,tana jin wani qwarin gwiwa yana shigarta aduk sanda ya tambayeta wani abu daya danganci karatunta,takanji burinta kwadayinta da qwarim gwiwarta yana daduwa
"alhmdlh abba....komai lafiya"
"ma sha Allah"ya fada yana maida dubansa xuwa gareta,har yanzu bata matsa daga inda take tsaye ba,amma hankalinta idanuwanta da hankalinta dukka yana kansu
"sarautar mata.......yada tsaiwa a nan?"murmushi ta saki
"to ai naga hankalinka duka yana kan yaranka,kaga gwara na barku ku gama tukunna.....barka da dawowa"
"barka kadai.....na sameku lafiya?"
"alhmdlh"ta fada taba jifansa da wani murmushin,saita tako a hankali ta raba ta gefansa,idanunta saman fuskar samir,suna hada idanu ya kauda kansa ya miqa mata jakar professor dake riqe a hannunsa,hannu ta miqa zata amsa tana cewa
"ka kyauta samir"ya fahimci abinda take nufi,saiya saki qaramin murmushi yana juyawa kadan zai fita
"ya da haka son...ka bari daddy ya kintsa muci abincin rana tare mana"ta furta cikin nuna zallar kulawa,kansa ya girgiza yana sosa kan mashi da tsinin key din mota,shida yakeson tsallakewa fadan professor,yayi imanin idan ya zauna suci abin tare zai tono laifin da shi yaketa qoqarin bunnewa ne
"akwai abubuwa da yawa dana bari,zanje na rage wasu,bazan jima yau a waje ba zan dawo gida" sanda yake maganar shima professor ya nufi hanyar da zata sadashi da sassansa da suka qunshi bedrooms manya guda biyu,da.katafaren falo guda daya
"da zaki daina wahalar da kanki wajen tsaidashi,ki barshi ya tafi kawai, saboda haka yakeso,hakan ya tsarawa kansa kamar ko yaushe" sarai samir yasan magana ce mai harshen damo yayi masa,sai data waiwayo ya kalli samir
"ohk....saika dawo,Allah ya tsare" kansa ya gyada sannan ya juya zai fice,itama ta rufawa professor baya.

"ya saraki"kiran da aka masa shine abu na biyu daya shiga kunnensa daga hirar professor da matarshi,sai yaja tunga ya tsaya sannan ya waiwayo a hankali sanda take tasowa a shagwabe ta riskeshi.

Idanuwan najwa tar bisa fuskar jawahir sanda take nufar yayan nasu,saita sanya hannunta ta cire airpiece guda daya cikin biyun dake maqale a kunneta,tana jin wani abu na tokare zuciyarta,ta tsani taga tana magana dashi sam,tana son taji yanzun me zatace da shi ne.

"ya saraki.....please,alqawarinmu fa" ajiyar zuciya yayi hade da lumshe idanu,lokaci guda kuma ya furzar da iska daga bakinsa,baice komai ba saiya cusa hannunsa cikin aljihunsa ya fiddo sabbin 'yan dari biyar biyar masu dama ya miqa mata,wani dan tsalle ta saki bayan ta amshu kudin
"thank you so much,am proud of you my yaya"murmushi kawai ya bita dashi sannan ya taka ya fice.

kudin na hannunta tana juyasu,fuskarta a wadace da murmushi ta koma kujerar data tashi akai ta zauna,duk abun nan da ake idanun najwa a kanta,tana binta da wani kallo da zai nuna maka zallar tkaici da haushinta daya cika mata zuciya,sam jawahir batasa me take ba tana irga kudinta hankali kwance,ganin cewa da gaske jawahir batasan tana yi ba,lissafin kudinta kawai take,saita miqa hannu ta fusge kudin a tare tana furta
"banza"da qarfi,hakan yaja mata hankalin jawahir din yadda takeso,dubanta take baki bude
"me na miki ya najwa"
"banza"ta sake maimaitawa tana hararta,idanuwanta kamar zasu fado akan jawahir din
"wai me na miki?"
"ke wai.me yasa baki da zuciya,kuma baki da kishin kanki?,na meye zaki tambayesa kudi,momi ba zata baki bane da ba zaki tambayeta ba?"sosai jawahir ta bata fuska tana kallon najwan,ranta a dan bace
"amma shi da momyn ai duk daya ne ko?,kuma ko ita ai taga ina tambayarsa,kuma bata ce komai ba"baki najwa ta tabe
'bakya ganewa,kuma ba zaki taba ganewa ba....."
"nidai koma meye bani kudina"ta furta tana miqa mata hannu
"naqi na bayar din"najwa ta fada tana cusa kudin a gefan cinyarta,sai jawahir din ta sake gimtse fuska sosai
"kinga ki bani kudina ya najwa,ko momy tace ki daina shiga harkata ko?"
"idan kina da qarfi ki danne ni ki qwata,sarai dai kinsan babu abinda zanyi da kudin nan.....".

A hankali ta buda qofa ta dawo ta cikin falon,idauwanta ya sauka a kansu sanda jawahir ke sake maimaita wa najwan ta bata kudinta
"lafiyanku?"momyn ta jefa musu tambayarsu,wanda banda tayi magana babu wanda yaga fitowarta cikinsu
"momy....ya saraki na tambaya kudin ankon yasmin tun rannan,to ya bani shine ya najwa ta karba ta hanani,tana masifar wai don me zan tambaya ya saraki"jawahir tayi caraf ta gaya mata,sai data tabbatar ta aikawa jawahir saqon harara sannan ta maida dubanta ga mony da nufun yin nata bayanin
"momy wai ba....."wani kallo momyn ta aika mata,sannan ta daga hannunta kawai ba tare da tabi takan qorafin da takeso. sako.mata ba tace
"bata kudinta"fuska ta bata
"momy...."
"nace ki bata kudinta ha'an...?"ta fada da dan zafi zafi yanzun a muryarta,fuskar najwa a cunkuse,ta zaro kudin ta jefawa jawahir,ya fada saman cinyarta,bata damu ba ta dauki kudinta taci gaba da irgawa,momyn ta kalleta
"ajjiye kudin nan kizo kitchen ki hadama daddynku drink"
"to momy"ta amsa mata tana miqewa da kudinta a hannu tabi bayanta,yayin da najwa ta bita da harara,tana jin kamar ta shaqeta,saita gyara glass din fuskarta,ta kuma gyara zaman qaton littafin dake ken cinyarta taci gaba da dubawa,can qasan ranta abubuwa da yawa na mata yawo,inda tana da qarfin iko da sai ta canza abubuwa da dama cikin gidan nasu,abubuwa masu tarin yawa da basuyi rayuwarta yadda takeso ba,basu zauna kuma a gurbi da muhallin da takeson ganinsu ba.

*_9:30 am_*

*_DARMANAWA HOUSING ESTATE_*

*_PROFESSOR RASHID USMAN AZARE RESIDENT_*

Daya ne daga cikin jerin qawatattun gidaje dake gine cikin unguwar,,wanda suka qawatu aka kuma ginasu bisa basira da kuma kyakkyawan tsari.

Gini ne na alfarma mai cike da qayatarwa da ban sha'awa,kamar yadda akasan ire iren gidajen masu sukuni suke da kuma unguwaninsu.

A hankali momy ta daga kanta,fuskarta na fidda wani irin murmushi mai haske tunda ta jiyo sautin muryarsa,tun gabanin ma ya iso inda suke din,yayin da ta tsaida dukkan abinda takeyi,ciki harda cin abincinta,da kuma hira da take da 'yammatan dake gefanta su uku,najwa jawahir da kuma ramla da take 'yar ruqo a wajenta.

Dukkaninsu sunsan meye ta baiwa hankalinta haka gaba daya,ba wacce bata saba da ganin tarin kulawa da qauna daga gareta ba zuwa ga samir,wadda ta banbamta da ta kowanne da dake cikin gidan.

Kallo daya professor yayi mata yaci gaba da cin abincinsa a nutse,don shi din ma hakan ba baqon al'amari bane a wajensa,illa dai ya kada kansa sannan ya maida hankalinsa ga farantin gabansa.

Cikin sakanni da basu kai goma ba ya bayyana cikin falon dab dasu,matashin saurayi muhammad samir me laqabin saraki,ma'abocin tsaho,wanda murjewar jikinsa ta hana bayyanuwar tsayin da Allah yayi masa yadda za'a fahimta,ya mallaki kalar fatar da hausawa suke kira da wankan tarwada amma irin wankan tarwadan nan dake da haske,taqi kadan zai dada ka kirayeshi da farar fata,matsakaicin kyau gareshi,saidai abubuwa guda biyu sun taru sun qarawa siffarsa kyau da cikar haiba KWARJINI da yake dashi,da kuma wasu lumsassun idanuwa masu kama da na me jin bacci.

Yana da sanyin murya,irin sanyin da bai hana bayyanar cikar mazantakarsa gami da jarumtarsa ba,sam ba miskili bane,kamar yadda wasu mutane da yawa suke masa kallon haka,abubuwa ne guda biyu suka sanya suke masa wannan kallon,baya shiga sabgar da bata shafeshi ba,bashi da shishshigi sam,hakanan bai fiya magana kan abinda yasan yana da qarancin muhimmanci,koma kwata kwata bashi da muhimmancin,yana da kamewa da wata irin nutsuwa mai jan hankali,yana da zurfin ciki a yawancin lokuta,komai nasa bisa tsari da dacewa yake tafiya,shi yasa wasu ke ganin abune mai wuyar gaske iya zama dashi,abunda basu sani ba shine,zama dashi din wani abune mai dadi ga duk wanda ya soma mu'amala dashi.

Akwai boyayyun halayyensa da ba kowanne ya sanshi dasu ba,ciki kuwa harda makusantansa,yana da tausayi yana da taimako,a wasu abubuwan ba zaka taba tsammanin cewa ya fito daga gidan girma da arziqi irin wannan ba,rayuwa sassauqa da yakan gudanar....saidai,matuqar kazo lokacin da yake kan tsininsa,zaka dauka baida kirki ko kadan.

Muhammad samir,da namiji guda daya tilo da Allah ya mallakawa professor rashid usman azare,wanda tarin banbamce babancen halaye da zabi na rayuwa yaso ya zama babban shinge tsakaninsa da mahaifinsa da samun dukkan wata yarda da qauna tashi.

"welcome son.....na tsammaci yau ba zaka fita ba?,naji shurun yayi yawa,duk da na kira wayarka taqi shiga....saina zabi na barka ba tare dana aika ba,wala'alla kana bacci ne kada a katse maka shi" hajiya jidda wadda auke kira da mommy ta fada,dukkan kulawarta tana tare da samir din,fuskarta na fidda wani kalar murmushi dake nuna farincikin dake tattare da ita na ganin fitowar samir din,kamar yaune lokaci na farko data fara ganinsa,ko kuma wani gari yayi tafiya mai nisan zango ya dawo a yau din.
Chapter 16 · 0% Book details