← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 117

Sashe 33

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai waqar ta tuna mata lokacin daya shude,ta tuna mata da qanwarta habi da takan riqo hannunta su taho nan din,hakan yasa ta tashi daga jinginar da tayi daga jikin yankakken dabinon,ta fara tafa hannayenta a hankali itama tana murmushi,kamar yadda saura 'yammatan ke tafa hannuwansu.

Shadda ce a jikinsa wadda ta dace da yanayin yawancin jama'ar qauyen,a yanayin shigar da yayin ba zaka kalleshi kace ya mallaki dubu hamsin ta kanshi ba,jikin shaddar ya koma kamar atamfa saboda tadan kwana biyu,babu qyalli ko maiqon sabunta ko kadan.

A nutse yake kewaye filin yana nazari da duban sana'o'in da jama'ar waje ke gudanarwa,wanda da alama itace rayuwarsu,sun kuma ta'allaqa jin dadinsu kacokam a wannan wajen,hannafi wanda ya zama shine idonsu cikin garin yana biye dashi a baya,gefansa kuma umar ne da yasha jeans da shirt,ya zuba kyau shi kam,kuma yaci gaba da tafiya cikin dandalin yana daukar hankalin yammata da yawa,hanafin shike musu jangora a duk wani abu da suka shiga duhu game dashi,tun bayan saukar saraki a wani kebantaccen gida na musamman da aka bashi ya sauka,bayan ya nuna sha'awar zamansa a wajen,ya gudanar da hutun daya rubutawa kansa da kansa zaiyi na sati uku,wanda hakanan ya tsiri hutun saboda target dinsa.

Duk inda ya kewaya yana lura da abinda ke faruwa,wani abun ya bashi mamaki,wani ya bashi sha'awa,wani ya bashi mamaki,bazaice basu da qauye ba,suna dashi,amma ba irin wannan ba,ba irin wadan nan jama'ar bane kuma a ciki ba,wannan qauyen yasha banban da nasu nesa ba kusa ba,akwai abubuwa da yawa da yake gani masu tarin ban mamaki da al'ajabi,basusan duk wani abu najin dadi ko more rayuwa ba,yana mamakin yadda mutum xai rayu kamar haka.

"Ga tacan haka,ko zaka leqa kaga fasahar 'yammatan qauyen ɗinya?"murmushin gefan baki ya saki,cikin nutsuwar nan tasa yace
"Me zai hana,muje mana,ka sani kona samo mata a ciki ma" dariya sosai hannafi ya saki,don gani yake yadda aljanna ta haramta ga kafiri,haka yallabai saraki ya haramta ga duk wata mace wadda ba 'yar gayu irinsa ba,inda ace da gaske sarakin zaiyi muradin hakan,da babu shakka sai inda qarfinsa ya qare wajen bashi qanwarsa 'yar uwarsa ramatu,da wannan tunanin nasa suka qarasa inda samarin qauyen ke zaune,sun yiwa filin qawanya daga bangare daya,daya bangaren kuma.mata ne matasansu da yaransu,saiya kutsa a hankali ya isa daga gaba,inda idanunsa zasu fi ganin komai.

A hankali yake zagayawa da idanunsa wajen yana ganin abinda ke faruwa,tsayin wasu mintuna kafin ya janye idanun nasa ya lumshesu,kana ya budesu gami da sakin numfashi,yaga abubuwan burgewa da yawa,yaga kuma gyarararraki daya kamata ace an gyara din,saiya sake bude idanun nasa don maidasu cikin filin.

Wannan karon a kanta suka fada,tana tsaye daga gefe daya tana tafa hannuwanta,karon farko daya soma ganinta bata fada,bata kuma rashin kunya
"Ka ganta can dan dali,har yanzu bata tafi ba,don Allah ka gayamin yadda zan tunkareta,kwarjininta yayi yawa wallahi,ta hadu kaf yammatan karkarar nan Allah ta tsere musu,ta musamman ce" kalaman da yaji wasu samari dake gefansa suna fadi kenan,hakan yaja hankakinsa,yadan waiwaya don ganin su waye.

Samarine guda biyu,daya yana riqe da kafadar dayan,da alama shike maganar,gaba daya hankalinsu kacokam sun azashi kan kaltum daketa tafi batasan ma wainar da ake toyawa ba,hakanan saiya samu kansa da maida hankalinsa kan fuskarta,yaci sa'a kuwa wutar wajen ta hasketa sosai,baqar fuskarta sai shining take da maiqo da baisan na meye ba a hasken wutar,mayafinta a nade yake har yanzu yayi spring spring saboda rashin guga,alhali wanda ya qerashi yayi rayuwarsa ta tabbta bisa kyaune tare da taimakon gugar,rashin samun hakanne ya sanyashi nannadewa,kanta a daure yake tamau,kwamae wadda ta boye quli quli a ciki,ya sauko ga kayan jikinta,tsingilallen zani wanda bai qarasa ko idanun sawunta ba,wanda ta daurashi saman rigar jikinta,hakan ya taimaka wajen fitowar shafaffen qugunta da bashi da wani shape,sai zallar sirantaka data cikata tako ina,don hatta qirjinta shikam bai hango komai ba,duk da cewa ta cukuikuye mayafinta sosai ta wajen,da alama sirranta wajen takeyi wanda hakan yaso bashi dariya,don baiga abun boyewar ba,daga qasa kuma qafafunta na sanye da wasu sidaddun silifas,wanda idan ka kallesu a tsanake zakaga ba kala daya bane,da alama wari da wari ne,uwa uba kuma sunwa siririyar qafarta yawa,dukka wannan nazarin ya qarashe shi ne cikin wasu taqaitattun daqiqu,sai kalaman saurayin ya fado masa
"Ta hadu ne......kwarjininta yayi yawa" dariya ce taso subuce masa,saiya dan dake tare da qoqarin maidata,ya furta
"Astagfirullah" qasan ransa,indai har tafi duka yammatan karkarar haduwa toba shakka baisan wanne irin gari bane wannan,yana tunanin dai kawai soyayya ce ta rufe masa idanu,amma gashi wanda baqar mace sam bata burgeshi,ya hangi 'yammatan da suka fita dama dama da yawa tsakiyar dandalin.

Mutum ne shi maison barkwanci wani lokacin,don haka sai yadan matsa gefan samarin,ko banza daren yau zai samu abunda zai sanyashi nishadi yadda ya kamata,gyaran muryar da yaja hankalin samarin guda biyu yaja,haqarsa ta cimma ruwa kuwa,don waiwayowa sukayi suna dubansa
"Ammm,abokina salamu alaikum"ya fada yana miqa musu tattausan hannunsa,duk da ya hangi nasu hannun daqal daqal da raken da suka gama danqa,cikin yanayi na rashin sani da baqunta suke kallonsa,kafin suyi qarfin hali bashi nasu hannun sukayi musabaha sannan ya dora da cewa
"Kuna bayana naji duk abinda kuke tattaunawa,yawa ne abokina ka dinga tsoron tunkarar mace,haba kamar ba namiji ba?,be a man mana" tsaiwa sosai haladu yayi saman qafafunsa jin an samu mai bashi qwarin gwiwar daya dade yana nema,duk da bai gane jimlar samir ta qarshe ba,ya washe haqoransa talatin da biyu yana duban samir,duk da baisan wayeshi ba
"Alqur'an abinda naketa gayawa kaina kenan,amma yarinyar ce abokina ba sauqi fa...."maganar data sake sanyawa samir ya kuma maida idanunsa kan kaltume,wanda zuwa yanzu ya tsayar da tafin,ta goye hannuwanta a qirji kamar maijin sanyi,still amma tana tsaye tana ci gaba da kallon masu gadar,haladu yaci gaba
".......bata kula kowa,bata sakarwa kowa fuska,qawance ma bada kowa takeyi ba,bata taba saurayi ba sai yanxu,na dade ina sonta na kasa furta mata"
"Wannan din?" Samir ya samu kansa da furtawa cikin subutar baki idanunsa har yanzu saman fuskar kaltum
"Ita din fa"haladu ya fada yana qura masa ido,sai sannan ya fahimci yayi subutar baki,don haka ya waske da sakin murmushi
"Aita hadu" hakan yasa haladu sake washe bakinsa sosai
"Allah ko abokina,shi yasa na dage fa,amma kayi a hankali karka fada tarkon sonta,don ina kishinta sosai" kamar samir ya bushe da dariya amma saiya dake yana fadin
"Ai taka ce,kada ka damu,idan kana so zan tsara maka ita yau din nan" dubansa haladu yake sama da qasa cikin kokwanto

18
D/z
*_manzan Allah S A W yana cewa:musulmi dan uwan musulmi ne,kada ya ha'inceshi,kada yayi masa qarya,kada ya tabar dashi ko wulaqantashi,kowanne musulmi akan dan uwansa musulmi an haramta masa yaci MUTUNCINSA DA DUKIYARSA(ba tare da yardarsa ba) KO JININSA,YA ISHI MUTUM SHARRI YA TOZARTAR DA DAN UWANSA MUSULMI_*
_sadaqa rasulul kareem_
________________________________
*_Littafin kudi ne,sharing mana ko karantawa ba tare da kin biya ba tamkar zalinci ne,ki tuntubi wadan nan numbers ki biya naki ki karanta cikin aminci_*

08184017082
Ko kuma
09134848107
_____________________________

Ya lura da kyau ya fishi kyan fata da kuma kyan fuska,duk da cewa sutura jikinsan ba wata ta az a gani bane,amma sai yaji shakka da kokwanto,kada fa yabar wannan baqon yaje labari yasha bamban,saboda yana da labarai da dama kan irin hakan data faru akan wasu samarin,wasu ma rakiya suke zuwa,amma daga qarshe suke yin wufff da 'yan matan.

Jin cewa har zuciyarsa bata gamsu ba saiya girgiza kai
"Kai anya kuwa?,aradun Alla tsoro nake,bansan irin zaqin baqinka ba,kada ka janyomin asara" Dariyar dake cin samir ji yake kamar ya saketa,musamman idan ya hango kaltume a tsaye a yadda take,ana zancan wai kada ya qwacewa wani ita,yarinyar da ko 'yan aikin gidansu sunfita kyan gani.

Abokinsa dan ladi ne ya daki kafadarsa
"Dalla malam wannan baiyi kama da masu cin amana ba,tunda yace zai maka naji na amince dashi,kuma ma ai kai kankarowa kanka girma zakayi ma,ka bashi dama,mu tsaya muga ikon Allah" Dan jimmm haladu ya sakeyi,alamun har yanxu yana kokwanto,daga bisani saiya gyada kai
"Naji na amince,Allah ya bamu sa'a"
"Amin" samir ya fada,a halin yanzu babu abinda yakeso irin ya samu sarari ya kwashi dariya,yadda haladun duka ya rude ya tsure kai kace mai tallan yalone zai shiga fadar shugaban qasa neman aurenta,amma dai yana son ganin qwaqwaf ne,saboda haka yace su biyoshi sanda yaga tana neman hanya tana barin filin,da alamu gida tayi.

Saida suka gota wajen hayaniyar yace su tsaya daga wani waje daura da inda kaltumen take tafe a hankali,suka tsaya suna binsa da kallo,tare da dakon abinda zai biyo baya.

Sai daya dan tsaya yana qoqarin controlling kansa saboda dariyar dake cinsa,wai yau shine lokaci na farko a rayuwarsa zai tsaida budurwa,budurwar ma ta qauye,inama ace Aamirunshi yana kusa suci wannan dariyar tare?,kai yama zama dole ya tattagoshi daga inda yaken ya dawo gida,zaman ya isa haka.

Kamar gaske ya matsa daura da ita ya rangada sallama,da fari ta tsorata,don a firgice ta waigo,sai taja burki ta tsaya gami da matsawa gefe kana ta tsura masa idanu,tana kallon baquwar fuskar da bata taba ganinta ba tsahon rayuwarta
"Yammata....an yini lpy?" Muryarta can qasan maqoshinta ta amsa masa tana sake matsawa nesa dashi,wai koda abun gudu zai taso.

Tsaf ya soma tsaratan cikin mintunan da basu gaza biyar ba sannan ya dora da cewa
"Ni aikoni akayi,dubi can" waiwayawa tayi a mamakance tana duban inda yake nuna matan,inda su haladu ke tsaye,ta gansu sarai,ta kuma dama fahimta take takensa,saita janye idanunta,ta maido kan mutumin da batasan waye ba.

Tsaki takeso taja,amma hakanan sai harshenta yayi mata nauyi ta kasa,haka kawai taji mutumin ya cika mizani da ma'auninta na ganin girman mutane,cikin jerarrun kalamanta wanda bai zaci jinsu a haka ba,duba da yanayinta tace
"Ka shaida masa ni an riga an aiko gidanmu,an kuma bada ni,kada ya sake tsayar dani ko ya aiko wani" abinda bai taba kawowa ba sai yaga ta juya tayi tafiyarta abunta.
Chapter 33 · 0% Book details