Sashe 28
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta qofar gidan me gari ta ratsa saboda sai tafi mata sauri,tun daga nesa take hangen wasu maka makam motoci da suke zamewa 'yan karkara irinsu da basu taba leqa birni ba abun tsoro,saboda haske da walqiyar da suke cikin hasken rana,yara da manya ne tsaitsaye gaban motocin guda uku,da alama suna morewa idanuwansu kallon abunda basu taba gani bane,ta haka ta ratsa ta tsakiyarsu ta wuce,tana tafen itama tana waigen motocin,tare da mamakin wai wadan nan abun hawa ne,kuma sunansu mota kamar sauran motocin da suke gani suke safararsu zuwa qauyensu,bata taba zaton ma akwai samfurin wata aba wai mota irin wannan qirar ba,kwata kwata babu hadi da iein nasu motocin,don idan aka kwatanta wadan nan da nasu,toba shakka sunayen nasu motocin gwangwani ko kuma kace fanko kai tsaye,Allah daya gari banbam,da irin wannan tunanin ta qarasa gidan habiba.
Bata sameta a sassanta ba,a sashen surukarta ta sameta,suna zaune qasan rumfarta mai sanyi suna barar gyada abinsu suna hira,fuskarta wasai take fadin
"Maraba da kaltume,kaltume kinyi tsada kamar kudi?,idan za'a leqomu dinma sai munyita roqo?" Tafadi tana miqa hannunta tana warewa kaltum gefan tabarmar da suke kai,tana murmushi ta zauna,cikin kamewa da kunya ta gaida babar yusufa din,ta amsa mata cikin kulawa da dattako,tana tambayarta ummansu da kuma jikinta,ta amsa mata da sauqi,saita miqa hannu ta debo gyadar da zummar tayasu ɓarar.
Dakatar da ita baban tayi tana fadin
"A'ah,ajjiye kada ki bata jikinki,ke habi dauketa maza ku wuce bangarenki,idan na gama dambun zan aiko muku dashi,ba sai kin fito ba" cikin ladabi habiba ta miqe tana cewa
"To baba" dole kaltum ta miqe itama tabi bayan habiban suka wuce sashenta.
Daga tsaye kaltum ta qarewa rumfa zuwa dan tsakar gidan habiban kallo,ko ina fes qal kamae yadda suka gada daga mahaifiyarsu,hakan ya yiwa kaltum dadi qwarai
"Gani,lafiya kike nemana?"ta fadi tana duban habiba wadda tayi qiba abinta,koda ba'a gaya maka ba kasan tana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa,duk kuma sanda suka daga idanu suka kalleta ita da ummansu,suna samun wani sukuni da farinciki na dacen gidan aure da habiban tayi.
Kama baki tayi tana kallon kaltum
"Kai yaya?,kamar akan qaya kike?,Allah da yau yaya yusufa cewa yayi indai bakizo ba da kansa zaije ya tahomin dake,shikenan saiki yanke zumunci dani?,watanni nawa da aurena amma har yanzu bakizo min sau uku ba?,bilal kawai fa ke leqoni lokaci zuwa lokaci,ko ummanmu taqi zuwa har yanzu,dama ni bana zancan baba,anya kuwa baku daina sona bq?" Tayi maganar kamar zata saki kuka,hakan ya sanya kaltum nema waje ta zauna tana cewa
"Idan ma mun daina sonki aikin samu wasu sabbin masoyan da suka fimu iya kula da habi ta" maganar ta sanya habiba dariya,da alama kaltum din ta sauko kenan daga niyyar komawa cikin gaggawa datayi aniya,habiba bata zauna ba,saita dinga rakitowa kaltum din duk wata cima da take da ita ciki da wajen dakin,gyada ce,rake ne,ragowar tsirenta na jiya,harda kiifi ma da kantu.
Dukkansu kaltum tana sha'awar ci,saboda an jima ba'a hadu ba,saidai ta kasq cin komai a ciki idan ta tuna ummanta,ba zata iya ci ita kadai ba,duk da cewa habiban na yawan yi musu aike irin wannan na kayan taba ka lashe.
Ganin taqi ci habiban tasan halin yar uwar tata sarai,don haka saita samu leda ta juye mata komai,sannu sannu kaltum ta saki jikinta,suka dinga hira sosai da habi,har babar yusufa ta kammala dambun,ta aikowa da habiba nata cikin qatuwar kula da kaltume ta tabbatar tafi qarfinta,sannan kuma ta ciko wata babbar samira tace ta kaltume ce,miqewa kuwa tayi tace gida zata tafi,ita baci zatayi ba,habiba ta kada ta raya taqiya,har sai data hadota da babar yusufa
"Ke kaltume,karbi maza,keda gidan 'yar uwarki?,banda ma shirme irin naki a mu yanzu 'yan uwa ne,babu abinda zance da habiba ni sai godiya,don tq zamarmin diyar cikina ba suruka ba,Allah ua bani 'ya daga sama,babu abinda zan masa sai godiya,na kuma godewa mahaifanku da suka tarbiyyanceta da kyawawan dabi'u" wannan kalaman suka qarawa kaltum qaunar matar,suka kuma sanyaya mata zuciya saboda yabo da ummanta ta samu.
Ko da tazo dawowa a yanzun babu motocin data gani dazu,hakanan babu taron mutanen nan,sai dai daiku da suke zuwa gidan,wasu matsala ce ta kawosu wasu gaisuwa,haka ta wuce zuwa nasu gidan.
Tun kafin ta isa sassan nasu ta jiyo muryar inna,gabanta ya fadi,me kuma ya kawo inna yau gidan nasu?,ta sani da wuya alkhairi ya kawota,ku kumq tazo a qarke qalau da ita,saita fara jan
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kamar yadda aka koyar dasu a makarantar asuba ga wanda bala'i y asameshi,don ita a wajenta inna bala'i ce cikin rayuwarsu,domin bata kawo musu kowanne alkhairi face sharri,da tana da iko,da tana kuma da hali data shafeta cikin babin zuri'arsu,ta kuma canzawa ummansu mahaifiya da wata ba innar ba.
Sosai ta tamkae fuskarta,ya aro duk wani bacin ran duniya ta azawa fuskar tata sanda take sallama a tsakar gidan nasu,innar ce kuwa,tana zauna akan kujera 'yar tsuguno,yayin da ummansu ke saman tabarma,da alama ma zuwan innar ne ya tasheta daga baccin data tafi ta barta tana yi.
"Har kin dawo kenan?"umman ta tambaya tana duban fuskarta,kai kawai ta gyada mata,ta isa gefan umman ta ajjiye kwano da ledar hannunta,sannan cikin cushewa ta soma gaida inna
"Lafiya lau"ta amsa mata,amma idanunta kacokam na kan kayan da kaltume din ta ajjiye
"Nazo akace kina gidan habiba,itama shegiyar da bata neman kowa sai uwarta da yan uwanta.....wannan din meye kikq shigo dashi?,me aka same acan din?,Allah yasa ana qulla abun arziqi itama bata fada irin gidan da uwarta ke ciki ba"innar ta fada wuyanta kamar zai tsinke ya isa ga kwanon,tuni kaltum tasa hannunta ya dafe kayan,don bata jin innar ko mayyace zata bata kayan nan,saidai kallo daya umman tayi mata ta janye hannunta daga kai,don babu yadda zatayi
"Dauka kikai mata"unma ta umarceta,kamar zata sanya hannu aka ta zunduma ihu haka taji,ta jefi innar da harara,saidai ina batasan tanayi ba,zuba surutu take idanuwanta kan kwanon dai,haka ta miqe ta dangware mata komai tayi wucewarta daki abinta,inda tasan zata zo ta taras da ita wallahi ta gwammace tabar abincin bata karbo ba.
Rub da ciki tayi saman shimfidarta,tana jiyo yadda innar keta zuba surutu taga dambu,ga nama harda kifi,tana jin sanda ta saki guda
"Kai lallai ba shakka,habiba Allah ya tseratar dake,ai nima na leqa mu gaisa" maganar tata tadan cunkushe daga qarshe,wala'alla dambun ta cika bakinta dashi.
Tsaki kaltum taja kamar zata tsinke harshenta,ta juyar da fuskarta ta daina kallon qofar dakin wai ko zata rage jin kalaman zalama da tsantsar kwadayi daga bakin innar
"Kema kiyi kiyi ki tattara ki qara gaba,har yanzu shuru,shi yaron da yace adaga masa qafa gashi wata nawa basu sake magana ba,sai kace wadda ta ɓincino baqin jinin ubanta,don dai wannan baqin jinin bana uwa bane,saboda ni kaf yarana babu wanda ke wuce shekara goma babu baiko,itama donta biyewa son raine tazo tq haifeku a wanna qangin" kalaman da suka sanya kaltum miqewa sa sauri ta tura qofar dakin nata ta rufe abinta,sannan ta dawo ta kwanta.
Bata qara miqewa ba sai da taji ummansu na kiranta,ta miqe a hankali taja dankwalinta ta daura,sannan ta fito,ta samu innar ta gama kasafta komai ta dauki nata,dubanta umman tayi
"Ki dauka abincin kici" fuskarta a hade tsaf tace
"Na qoshi,ki qara mata kawai" sarai umman ta fahimci magana ta fada a fakaice,amma batason cewa komai kada innar ta samu wata mafakar,tana son su rabu lafiya,ko banza yau dai ga innar tata a gidanta.
Washe baki innar tayi
"Aina qoshi 'yar nan,kedai Allah yasa kema ki dace kamar habi" batace mata ci kanki ba bare ta amsa mata,saita gyara zama,sanda ummansu ta miqe ta dauki buta don zuwa bandaki
"Nace ba......zuwa nayi ki bani aron dubu da dari biyar,wallahi jiya jiya ado da indo suka aikomin da kudi,zan siya kiwo,to saura cikon dubu da dari biyar,babarki tace min kina tara kudin magani,ko su zaki aramin,koma dai ki bani kyauta,tunda kukan jima baku yiwa kowa alkhairi ba,na tambaya babarki ko akwai sauran na gudunmawar bikin habiba ta bani,to ashe babu duk kun qurmushe" mamaki ya cika zuciyar kaltum,ta soma bin innar da wani kallo.na mamaki,tana ji har cikin zuciyarta,data dauki abunta ta baiwa innar ta mora,gwara su fadi
"Ina zuwa" kaltum din tace da ita tana miqewa,saita sake washe baki,murna sosai ta cikata
"Allah dai yayi miki albarka,kare ma yana da ranarsa gaskiyar bahaushe" ta fada innae tana gyara zama.
Inda take ajjiye kudin ta soma bankadawa ta debe kudin,ta dauresu sosai bakin habar zaninta,sannan taja hijabinta daya cire dazu ta mayar jikinta,ta saka slipper dinta ta fito.
"Yauwa miqosu nan,sauri nake nayi na koma,na baro gidan babu kowa" tsaiwa tayi saman kanta ya dubeta,saita kwance kudin ta dagasu sama
"Kin gansu nan?,to wallahi sisi a ciki ba zakici ba,saboda gumina ne bana wani ba,aimu marasa amfanine a wajenki,to a tafi a hakan har duniya ta nade,kuma gidan habiba indai kika sake kika je,yasin saina sakar miki karnukan gidan mati dake hanyar" saita sura da mugun sauri tayi waje,saboda taji ummansu daketa doka mata gyaran murya tana gaggawar fitowa,da alamu taji komai a kunnenta.
Hanya kawai ta miqa ta dinga shawagi abinta,ta dade bakin rafinsu zaune,abinda bata taba yi ba,saidai wajen yayi mata sosai,batasan haka wajen yake da dadi ba sai ranar,saitaga zai dace da wajen zamanta idan zatayi zane,taga abubuwa da yawa da zata iya zanawa tana zaune daga wajen.
Anan ta shimfida dankwalinta tayi sallar azahar,batason komawa gida a yanzun,saboda wata nutsuwa da wajen ya saukar mata,sai data qara awa guda sannan ta miqe,ta yanke tabi ta wata hanya,duk da batasan ainihin inda zata maidata ba,amma tana da tabbacin xata kaita gida.
Ga mamakinta saita bulla da ita layin gidan yaya muzammilu,gidan da aqalla ta kusa shekara uku rabonta da zuwansa,ta laluba kudinta taji suna jikinta,zuciyarta ta bata shawarar ta kaiwa matarsa lariya ajiya,don haka ta kutsa kai gidan da sallama.
Kadaran kadaham ta karbeta,suka gaisa,bata zauna ba ta kwance kudin tace
"Babar haruna,ajiyemin zakiyi,zan dawo na karba nan da kwana uku" jikinta na rawa ta karba,kudin sunzo mata akan gaba,dama su take nema
"To kaltume,Allah ya kaimu" daga haka sukayi sallama ta juya gida.