← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 117

Sashe 2

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta kaltum tayi,iya saman fuskarta kawai tasan itama ranta ya baci,ci gaba da maganar tata kuwa tasan bashi da wani alfanu,hakanan bazai haifar da da mai ido ba,don haka ta sauya akalar zancanta zuwa neman mafita
"Yanzu umma ya za'ayi kenan?" Shuru nadan sakanni tayi kafin ta amsa mata
"Babu komai,zanci gaba da nema kawai har Allah yasa a samu,idan ban samu din ba....zanci gaba da amfani da wannan maganin muga abinda Allah zaiyi" shuru kaltumen tayi tana hadiye wani yawu mai tauri,saita kalli sashen da suke girki wanda yake a bushe ba girki babu alamarsa,ta maida dubanta ga umman
"Baba bai dawo bane har yanzu?,naga baku dora komai ba" kamar ba wata tambaya tayi mai muhimmanci ba haka umman tata ta bata amsa
"Bai dawo ba,amma nasan yana kan hanya in sha Allahu" miqewa kaltum tayi,saboda ba abinda ranta ke sakeyi sai baci,tasan umman ta fada ne kawai,umman ta fada ne saboda ta bashi kariya a idanunsu,bayan babu wata kariya data rage masa da zai samu a idanuwansu,ya gama wargaza komai,ya kuma gama kwancewa kansa zani a kasuwa,don ba zata iya tuna sau nawa ta fita tayi kitso ta dawo ta kawo kudin sukaci abinci dashi ba,to kuma me yayi saura?.

Buta kawai ta dauka,har zata wuce bayan gida ta juyo ta dubi umman tasu
"Umma ina bilal ya shiga ne?"
"Bai jima da fita ba kika shigo,yacemin zaije wajen dan bala,yace kamar akwai aikin da zasuje yau" kai kawai ta gyada,bacin ranta yana sake ninkuwa,bilal da gaba daya bai cika shekara sha biyar ba amma yasan dukkan wata wahala ta duniya,yaro ne da gaba daya kamar baisan ciwo ko dadin jikinsa ba,Allah ya zuba masa tausayin mahaifiyarsa da son 'yan uwansa,dukkan wani aiki da za'a kirashi na wahala bilal ya iyashi,kama daga kwabin bulon qasa,aikin gini,kwasar qasa,haqar masai ko rijiya,kai hatta da kiwon dabbobi idan mutum nada buqata zaije ya karba yayi masa,burinsa kawai a biyashi kudin,burinsa kawai su samu abinci suci,tun yana aikin wahala ya dawo gida yayi jiyya har ya saba.

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

Duk wannan aikin da yake baisan tari ko adani ba,burinsa daya samu kudin ya siya abu mai dadi yaci,ya kuma kawowa mahaifiyarsa a boye,baya taba bari mahaifinsa ya gani,don yana da tabbacin indai ya gani ba rabonsa bane kudi ko abinci,koda na nawa ne kuwa,zai karba ya kalmashe a aljihunsa,rashin kawo musu baisa yaji kunya yaqi amsar nasu idan sun samu.

Sosai abun ke cima kaltum tuwo a qwarya,tana qaunar bilal sosai,yana da sauqin kai,bashi da rashin ji ko hayaniya irin ta yara,wahalar da yakeyi tana ganin tayi yawa,saidai kusan ta zame masa jiki ma,ya zama tamkar bawa,don baya iya zama wuni guda a gida ba tare da yayi aikin komai ba,saidai idan bashi da lafiya.

Shi dinma da kaltum taso yayi karatu koda su din basuyi ba,tunda shine da namiji guda daya tilo da mahaifiyarsu keda shi,amma sam yaqi,ya nuna aikin neman kudinsa ya fiye masa,koda ta zauna tayi tunani,sai taga idan ta takura dinma sai yayi karatun dame zaiyi?,su din da kullum sai sunyi fafutukar abinda zasu ci?,saidai taci alwashin dagewa tuquru ta tara kudin da bilal din zai koma makaranta,koda baya so,saboda tana kallon shi ne tamkar shine madubin rayuwarsu,kuma wani tsani da zai kai rayuwarsu izuwa tudun mun tsira anan gaba.

Har azahar suna zaune zaman jiran gawon shanu,babu baban nasu ba alamarsa,dukka sun ukun idan ka kalli fuskokinsu babu tantama yunwa suke ji,daga nan sashensu suna iya jiyo qamshin man ja,wanda da alama ana soyashi ne daga sashen baba iliya,wato sashen dake fuskantosu,amma ba qamshin manja ba,ko qamshin me zasuji babu lallai a miqo musu koda babu yawa saboda haqqin maqotaka dana zumunci,saidai idan Allah ya tsaga da rabonsu.

Tana idar da sallar azahar ta miqe tana karkade baqin hijabinta daya kwashi qasa,ta dubi ummansu
"Ummanmu.....na tuna ina bin ladingo kudin kitson da nayi mata tun rannan ita da 'yarta,bari naje ko zan samo,saina siyo mana ko gari ne" cike da tausayi ta dubi diyar tata,wannan rayuwar da suke sam bata qaunarta,to amma ya zatayi da ranta,ita ba sana'a gareta ba,hasalima bata da jarin kuma bata dame bata,bata da wata kadara da zata saida ta zame mata jari,kai koda ta fara sana'arma mai gidan shike amshewa da wayo har sai ya durqusar da ita,dolen dole ta zuba idanu komai ma ke faruwa.

Saidai ko kadan bata bari ba,bata sanya idanu ba,hakanan batayi sanyi ba kan tarbiyya 'ya'yanta,bata da sauqi ko sanya wajen kula da tarbiyyarsu,kuma kowa yasan da hakan
"Karki dade,idan baki samu ba ki maza ki dawo gida"
"In sha Allahu....habiba zo muje" tace da qanwar tata,itama bata dade da idar da sallar ba,don haka ta miqe suka fice a tare.

Suna tafe a hanya saidai babu wanda ke magana a cikinsu,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,basuyi nisa ba suka hangi asiya tana tahowa,dauke da jakar makaranta kamar gaske,wato yanzun yayi dai dai da lokacin tasowarsu kenan,shine ta dawo gida.

Suna hada ido da kaltum tayi kicin kicin da rai,ta kuma dauke kanta bayan ta gasa mata harara,wanda kaltumen batasan daga inda ta faro kota samo asali ba,saidai hausawa sunce....tabarmar kunya da hauka ake nadeta,wala'alla abinda tayi shirin yi kenan.

Sai da suka giftata sannan habiba tace
"Wai yaya bakiga kallon da asiya tayi miki ba?" Kai ta jinjina
"Na gani habiba,tana son nannade tabarmar kunya ne da hauka" cikin alamun son qarin bayani habiban tace
"Me ya faru?" Kamar ba zata gaya mata ba,sai kuma taga cewa barin kashi a ciki baya maganin yunwa,hasalima duk duniya bata da kamae habiban,hakanan tafi kowa sanin halin habiba,bata da yawan surutu ko yarin qawaye,hakanan nutstsiya ce bare tace zata yi zancan da wani,abinda yayi habiba shi yayita.

Ta yadda zata fahimta ta gaya mata komai,ga mamakinta sai habiban ta tabe baki
"Na saba ganin asiya a wannan yanayin yaaya,saidai fatan Allah ya shirya" cike da mamaki da kuma baqinciki ta ware idanu tana dubanta
"Amma habiba kin sani baki taba yin wani abu da zai daqile 'yar uwarki daga fadawa halaka ba?,kinsan cewa kema kina da kamasho duk abinda ya faru tunda baki taimaka mata kin tunkudeta daga cutarwar da takeson jefa rayuwarta ba?" A sanyaye tace
"To ya zanyi yaaya?,na gayawa umma,tace mu tayata da addu'a kawai,kada nayi magana,saboda ita batason tashin hankali,don babu lallai baaba lami ta fahimci abinda zan gaya matan,kinfi kuma kowa sanin halin jarabarta,da yadda ta tsangwamemu hakanan babu gaira babu dalili" shuru kaltum tayi,ta kasa furta komai,hankalinta na wani irin tashi,jininta ce keson fadawa wannan hanyar?,me yafi wannan tashin hankali?,sam bata jin zata iya shuru koda baba lami zata tsireta,duk da ma basu da tabbacin zataqi amsar maganar,don babu wata uwa ta gari da zataso ganin lalacewar diyarta,itace mutum na farko da zataso ta gyaru,don haka taci alwashi cikin ranta ba tare data furtawa habiba ba.

Basu sake magana ba har suka iso gidansu ladingo,shima dai babban gidane irin na karkara,mai dauke da sassa sassa,ta gaida mutanen data taras a harabar gidan ta wuce sashen ladingo.

Zaune ta sameta daure da zani da riga mabanbanta,yaronta na saman cinyarta yana shan nono,ita kuma tana irgen kudi,fanteka ce a gabanta wadda take duqun duqun,ba'a jima da dawo mata da ita daga tallar awarar da take bayarwa tana biya ana yi mata ba,kitson da kaltum tayi mata har ya fara soshewa,amma har yau ta kasa biyan kudinsa,kamar yadda wasu daga cikin matan qauyen keyi mata,takanyi kitson ne kawai saboda ko banza yana toshe mata wata kafar,duk da cewa su din talakawa ne tilis....basu mallaki komai ba,amma mutane ne masu tsananin tsafta,kamar yadda suka gada daga mahaifiyarsu,ita dinma haka take,ta washi qazanta gaba daya,tana da tsafta qwarai,ta yadda duk kodewar kayanta da rashin kyansu ba zata ga datti kowani abu mai kama da qazanta ba,dalilin da yasa da qyar take iya kama kan wasu ta kitse saboda tsabar rashin gyara da tsafta,da yawansu suna ganin cewa zallar wulaqancine kawai da girman kai,saidai ba haka take ba,qazantarsu ce kawai ke damunta,tana mamakin yadda basu damu da jikinsu da kawunansu ba,mace saita wuni a tsaye tana aikin neman kudi,amma gyaran jikinta saiya gagareta,ba zata iya siyan man shafawa dangwali yaba ko turaren abulbula ta siya ba saboda kauda wari da qarni,duk da talaucinsu wanda da yawansu wasu sun fisu,bata taba ganin qazanta jikin mahaifiyarsu ba.

Tana jin sallamarsu ta soma qoqarin boye kudin ta hanyar cusasu cikin zaninta,sarai kaltum ta gani,amma saita dauke kai kamar bata gani ba,ta soma washe musu bakin qarfi da yaji.

Da qyar habiba ta samu wajen da yayi mata ta zauna,kaltum kuwa kasa zaman tayi,saita jingina da bango kawai tana gaida ladingo,yarinyar macace mai haihuwa daya tak,amma qazanta da zafin nema sun qara mata yawan shekaru a fuska da jiki gaba daya.
Chapter 2 · 0% Book details