← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 117

Sashe 76

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo suka bita har ta iso gabansu,ta ajjiyewa kowa plate din sannan ta bude masa ta sanya masa spoon

"Kuci kuji don Allah" ta fada tana dubansu,duban plate din sukayi hajiya tace

"Meye wannan ne kamar dambu"

"Kici don Allah hajiya.... please yaya kada kace ka qoshi" ta fada tana marairaice masa,basu sake cewa komai ba kowa ya dauki nasa cokalin.

"La'ilaha illallahu....wai dambu kukayi haka a dan wannan lokacin me shegen dadi?" Dariya ta qwacewa jawahir,kafin ta dakata

"Hajiya dambun couse couse ne fa?" Idanu hajiyan ta fitar

"Couse couse dai da nake kallonshi a abun banza shine haka?" Dariya ta basu harda samir daya dan murmusa,dadin abincin shima yana ratsashi,duk da dama shi cimarsa ce couse couse,musamman da vegetable soup liver or kidney soups

"Wallahi hajiya aikin kaltum ne,ni kaina abun ya bani mamaki"

"Ikon Allah,wannan yarinyar dai da kuka shigo tare?" Hajiyan ta fada tana fara kai lomomi bakinta,gardin gyada dana zogale gami da wadatacciyar albasa da kayan dandano na hadewa a bakinta

"Ita"

"Ina kuka samota ne?"

"Na daukota ne daga garinsu" samir ya bawa hajiyan amsa sanda jawahir ke niyyar bude baki tace 'yar aiki ce,kai hajiyan ta kada tana ci gaba da kaiwa cikinta abincin.

Ganin hajiyan ta nutsu da abincin,saita juya ta koma kitchen wajen kaltum don bata labarin yadda ta kaya tana dariyar yadda taga hajiyan na cafkar dambun babu qaqqautawa.

Tana mamakin ta yadda aka sarrafa couse couse haka aka baddan masa da kama.

Tana dab da cinyewa suka fito daga kitchen din,hajiyan ta daga kai tana kallon

"Sannu 'yar nan,sannu da aiki kinji?" Murmushi kawai ta saka,ta qarasa tana daukowa hajiyan ruwan da take yunqurin daukowa hannunta baikai ba,ta bude mata ta miqa mata

"Aini mamaki ne ya kamani,kin samu ladana ba kadan ba" murmushi ta sakeyi tana samun gefe kusa da jawahir ta zauna

"Allah yayi albarka"

"Amin" ta amsa da muryarta qasa qasa,yayin data maida hankalinta ga jawahir dake nuna mata wata drama da ake nunawa.

"Yauwa....yanzu sai nafi fuskantarka,me kake cewa?" Tafin hannunsa yasa ya shafi sumar kansa

"Ba wani magana bane dama,yarinyar da xan aura ne muka daidaita kanmu,so inason shaidawa daddy,nayi magana da mummy sai tace na gaya miki,saiki gaya masa" bakinta ta tabe,kana ta dubi inda su jawahir take,sam hankalinsu baya wajen

"Waini za'a yiwa bariki,da ta zartar kawai ai yadda ta saba....wacece ita ya sunanta?"

"Jauhar ce"ya amsata a nutse bayan yin shuru na 'ya sakanni,tsareshi tayi sosai da idanu

"Jauhar dai,yar wajen murjana?" Ta tambayeshi tana tattara hankalinta a kansa

Kansa ya jinjina mata yana kallonta,saita hade ranta tsaf

"Eh lallai....jidda taci alwashin daga qarshen rauwarka ma kenan itace zata zaba maka mata,to ba zata sabu ba,tunda shi yayan ya zama sai yadda aka juyashi,wannan wacce irin masifa ce ke bibiyar rayuwar raihana har yanzu bata huta ba?"

Idanunsa ya lumshe yana jin sunan har tsakiyar zuciyarsa,yana kuma jin wani abu me daci yana motsa masa,cikin muryarsan nan me cike da nutsuwa yace

"A'ah hajiya...,.ki fahimta mana,babu ruwan mummy a wannan maganar,amma idan baki gamsu ba kina iya tuntubar daddy da kanki" shuru hajiya qaramar tayi tana kuma karantar fuskar samir dake kallonta shima,tsahon wasu sakanni kafin ta gyada kai

"Shikenan tunda har kace haka....idan akwai alkhairi cikin lamarin Allah ya tabbatar,idan kuma babu alkhairi....ina roqon Allah ya watsa abun,ammafa ka sani,wannan ba yana nufin na gamsu duka bane na miqa wuya,daga yanzu zuwa ko yaushe ma,idan na gani ko.naji abinda baiyimin ba,to tabbas babu abinda zai hana a fasa ko a dakatar da komai" kansa kawai ya gyadawa hajiyan,har yanzu baisan me yasa ta kasa so ko jituwa da mummy jidda ba.

Sun dan jima a gidan,don har bayan sallar isha'i,sai da suka jira hajiyan ta kira wadda zata tayata zama,saidai har suka zo tafiya bata qaraso ba.

A sace kaltum take kallon hajiyan,itadai duk yadda jawahir ke cewa mafadaciya ce bata gani ba,hasalima saboda ciwon qafarta sai take jin kamar ummanta,duk wadda ta gani da ciwon qafa saita dinga ganin kamar ummanta

"Don Allah kice ya barni na zauna tunda me zaman bata zo ba" ta radawa jawahir,ta dubi samir ta gaya masa,saiya waiwayo yana dubanta

"Makaranta fa?" Ya tambayeta kanshi tsaye,sai sannan ta tuna

"Kwa dawo gobe" hajiya qarama na murmushi,cikin jin dadin yadda take ta nuna kulawarta a kanta tunda tazo tace

"Allah sarki yarinyar kirki,kada ki damu kinji,mubina na hanya,ba jimawa zaki ganta" da wannan sukayi sallama,bayan ta baiwa jawahir wani abu a leda tace su raba ita ba amfani dashi zatayi ba.

Saida suka shiga motar,samir yana qoqarin tada motar jawahir ta bude ledar

"unbelievable...." Saita saki dariya

"Wlh hajiya nada abun dariya,ta rasa yau kuma me zata bamu sai pad?,to ai wanna ni ta yiwa wannan kyautar,don kaltum ma yaa har yanzu bata fara period ba bare mu raba tare" tayi maganar tana ajjiye ledar gefanta

Kamar motar ta tsage ta fita ta qasanta haka kaltum taji,wai yau me ya samu bakin jawahir ne take ta bare magana haka?

"What?" Samir dake qoqarin tada motar ya fada bayan ya tsaida abinda yake qoqarin yi din

"Me kace yaya?" Jawahir ta tambaya,bai amsa ba,saiya waiwaya gefansa a nutse,ya dora idanunsa kan kaltum

"Shekararki nawa?" Ya tambayeta kai tsaye,tambayar data bata kunya

"Sha biyar" ta amsa masa a hankali,saiya janye idanun nasa daga kanta

"Akwai matsala" ya fada yana tada motar tashi,sannan ya fiddata daga jerin motocin gidan inda ya ajjiyeta,yana qissima lallai akwai wani matsalan,amma bata tadda za'ayi tana da 15yrs ta kasa period.

A komawan ma shuru tayi,saboda kunyar da jawahir ta gama bata,don damuwar maganar biba ma ta fita a ranta ba kamar dazu ba,bayan ta yankewa ranta yin shurun kamar yadda biban tace da ita.

Washegari ita da jawahir suka sake shiryawa zuwa duba hajiyan,bayan sunyi waya da saraki yace shima zaya biyo daga gurin aiki saisu wuce tare.

A falo suka tadda hajiyan,taji dadin ganinsu sosai,ta amsa gaisuwarsu cikin kulawa da tambayar yadda sukaje gida.

Suna tsaka da gaisawa yar matashiyar budurwar da kadanne bata qarasa sa'ar jawahir ba ta fito daga kitchen,hannunta jiqe da ruwa da alama aiki takeyi.

Qarasowa tayi tana dubansu,da alama sunsan juna ita da jawahir,saidai ba wani sanin can can ba,ta zauna kan daya daga cikin kujerun suna gaisawa da jawahir sannan ta dubi hajiyan

"Me za'a dafa?"

"Idan na gaya miki ma me nakeso quiya irin ta 'ya'yan yau ba lallai ta barki ki iya dafamin ba" duban hajiyan tayi,tadan maida bayanta ga kujera ta jingina bayan tayi luu da idanunta

"Kamar kuwa kinsan na gaji,ga baqi mun sake qaruwa,kawai ayi spaghetti jallope" idanu ta fidda

"Wa?,Allah ya sawwaqe,bama ta shinkafa ba saita taliya,nikam ba dani ba,ni ason raina ma na sami lafiyayyen tuwon dawa da miyar kuka" daga jawahir har mubina dariya suka fashe da ita

"Allah ya sawwaqe,haba hajiya me kika rasa da zakici wani dawa?" Cewar jawahir,mubina ta dora da

"Tayani gani dai,wai makaho yaso gulma" baki hajiyan ta sake,kamar yadda kaltum ke binsu da kallo kawai,tana dan qaramin murmushin da bai bayyana a saman fuskarta ba,tausayinsu take da suka jahilci amfanin dawa da har suke ganin baikenta,gayu da gata suka sanya su hasarar alfanu me yawa,tabbas da sunsan amfani da Allah ya zuba a cikinta wawasonta za'a dinga yi,amma abunda ta fuskanta a rayuwar maraya shine,kawai duk gidan da akaga suna cin tuwon masara ko na dawa,to talauci ne yake damunsu,idan kuma masu wadata ne,tofa la shakka za'a lasafta mai gidan cikin sahun mutane masu rowa qanqamo da dan hannu.

Bayanin amfaninta hajiya qarama ta fara musu,amma saita fuskanci basa ganewa,jawahir na dariya tace

"Hajiya,abincin dokuna ce fa?,ita naga ana yamutsawa da wani abu ana bawa dokunan ya samir"

"Me yasa dokunan suka fimu qarfi da lafiya?" Kaltum ta jefa musu tambayar ba tare da tasan ta fito a bakinta ba,dukka sai hankulansu sukayo kanta,saboda funda aka fara maganar batace komai ba kallo ne nata,sai taji wani nauyi,amma kuma haka ta daure taci gaba da magana

"Dabbobinmu wani lokacin sun fimu lafiya qoshi da kuma kitse ajikinsu,saboda muna daukan dusar kayan amfaninmu dama tsabar muna basu,da sunan shine abincin daya dace dasu,mu kuma muqi ci saboda muna neman dadi,bamu damu da kyau ko ingancin abinda zamu ci ba,dadi kawai muke yiwa" sai sukayi shuru suna nazari,zuwa can jawahir tace

"Kuma fa hakaneeee kulsum na yadda dake wallahi" yayin da hajiya qarama ta zuba mata ido,tana mamakin fasaharta da kaifin hankalinta a shekraun da take dasu,duk kuwa da cewa.ba wami abun mamaki bane ga duk mutumin daya rayu cikin karkara,wata baiwar basira hikima da fasaha Allah ke musu,wala'alla kyan nature irin nasu da bata baci da hayaqin kamfanoni da ababen hawa bane,da kuma cimar ganyayyaki da zallar abinci masu gina jiki damu muke musu kallon banza da suke ta'ammali dasu

"To kundai ji" hajiyan ta dora da fada musu,ita dai mubina sam bata gama yarda ba,daga qarshe dai kaltum tace suje ta tayata ta dora girkin,sai gashi sun buge da barwa kaltum din girkin,wanda ita kuma ta sauya akalar abinda sukayi niyyar dafawa ta maida tuwan dawar da hajiya qarama keso,dawarta me kyau kuwa,jar dawa wadda tafi kowacce amfani,niqanta kuma yayi laushi yadda ya kamata.

Sanda ta jerewa hajiyan komai bayan sun gama sallar magariba,hajiyan don dadi kamar tayi me,albarka kawai take sawa kaltum din

"Hajiya mu ba zaki gode mana ba" jawahir daketa kai lomomi bakinta ta fada,don ita ba zata iya tuna when last data ci tuwon dawa ba,don haka ta manta dadinsa ma kwata kwata,saidai babban abun mamakin shine,ashe haka kaltum din ta iya girki?,eh tabbas don girki ummansu ta horesu dashi,tun tana da shekara goma take dora sanwa,shekararta biyar tana girki,girki kuma kowanne irin irin dai wanda suke tu'ammali dashi zata yishi fes aci ayita santi,abu daya ne zuw biyu dama bata iya shi ba,girke girken da tazo ta tarar suna yi na zamani,sai kuma kayan dandano dana qamshi kala kala dasu basa amfani dashi,amma zama da take yawan yi a kitchen yasa ta gane amfanin da yawa daga cikinsu,ta kuma iya sarrafasu,amma yanzun data tashi yiwa hajiya qarama girkin ma,dukka ajjiyesu tayi,tayi amfani ne kawai da komai a gargajiyace,nan ta barsu suna santi,tayi dakin da mubina ta sauka don daura alwalar magariba.

*SAƘONE MAI NAUYI,BUDE IDANUNKI DA KYAU KI KARANTA!!*

*_RAMUWAR SALLAH GAME JININ AL'ADA!!_*
Chapter 76 · 0% Book details