← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 117

Sashe 84

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata jima ba ta fito ta hijabin sallarta har qasa,ta sameshi ya bawa tv attention,da alamu yana jin dadin kallon,saita saci kallon tvn don ganin me yake kallo haka,a iya dan zamanta dasu ta karanci yana son doki da wasan dokin ma gaba daya,duk da haka haka ya ajjiye remote din ya miqe ta bishi a baya.

Kamar kowanne lokaci shuru ne ya musu rakiya har zuwa makeken kantin zamani,wanda yake maqare da dukka nau'in kayan amfani.

Yadda suke haba haba dashi ya tabbatar mata ba qaramin customer bane,kuma ba qaramin jin dadin zuwansa suke ba da alama,kujera ya samu nan ya zauna,yace ta shiga ta zabi dukkan abinda taga tana so,sai tayi saroro,saboda sam bata taba zuwa ita daya ba,yawanci da jawahir suke zuwa,daga bisani ta fara takawa a hankali a tana duddubawa har tayi nesa da wajen da yake zaunen.

Tayi nisa sosai cikin babban kantin amma haka taketa shawagi,ta kasa zaben wani abun azo a gani,saboda kome tayi niyyar dauka sai tayi tunanin me tsada ne,ta qyale kada taje a lafta masa kudi,saboda nan din ta fuskanci komai nasu kudi ne tsububu a cikinsa.

"Hey baby" taji an fada daga bayanta,saita waiwaya da hanzari,suka hada idanu dashi yana jifanta da murmushi,matashin saurayine wanda a qiyasce bazai wuce shekara ashirin da biyar ba,sanye da qananun kaya,hannunsa riqe da wayarsa,yana da kyau dai dai misali,hakanan kana kallonsa kasan dan gayu ne

"Bari na tayaki zaben,na fuskanci tun dazu kike yawo kin kasa daukan komai" kafin tace wani abu ya karbi dan kwandon hannunta,ya fara duba kayan mata na amfani yana jefawa a kwandon,yana kuma dan janta da hira ta yadda zata saki jikinta dashi.

Sannu a hankali ya fara cika kwandon da kayyakin amfanin mata,saita ci gaba da binsa a baya,duk da cewa amsar kowacce tambaya tasa daga eh sai a'ah.

Sun kusa qarshen layin da suke ciki,kamar ance ta daga idanu ta hangi samir a tsaye daga qarshen line din kayan turaruka,dukka hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya kum tsaya qyam ya raba qafafunsa kamar wani soja,babu digon annuri a saman fuskar tasa,sai idanuwa daya kafesu dashi ita da saurayin........

D/Z
49

Wani mummunar faduwa gabanta yayi,saita dakata da bin saurayin,wanda sam shi baima kula da abinda akeyi ba,saboda ci gaba yayi da tafiya yana zuba kayan,har yakai gab da samir daya soma takowa shi kuma inda take yana ci gaba da kallonta.

Gab da ita ya tsaya,taku kadan zai qara su hade da juna,numfashinta kamar zai dauke tayi qas da idanunta,ta kuma qame waje daya tana runtse idanuwanta sanda taga ya daga hannunsa zuwa gareta,daga bisani ta budesu a hankali lokacin dataji motsin daukar cart din dake ajjiye gefanta.

Kusan lokaci guda kowannensu ya sauke boyayar ajiyar zuciya sanda ya kama tsintsiyar hannunta ya riqe,ya fara takawa a hankali riqe da ita suka fara daga farkon layin.

Mamaki ne ya cikata sanda taga irin kayan da yake zaba,kusan duk abinda ya taba ya daukoshi yayi mata choice dinta ne,kaya yake zubawa kamar baisan mutuncin kudinsa ba,tsoro ya kamata,amma daga bisani saita dan sake data tuna maganar da suka tabayi da jawahir sanda ya taba siya mata wani set na man shafawa

"Allah dai ya biya ya saraki,Allah yaci sunansa,ba don yayana bane da tuni nayi wufff da abina,harso nake mu fita shopping dashi,bayajin komai ko meye zaki zaba,ba kamar mummy ba da zata yita mitan zamu qarar mata da lalitarta,yana da kyauta kaman ba gobe,babu ruwanshi"

Nauyinsa ya cikata sanda ya sakar mata hannu,ya bata damar ci gaba da zabar ra'ayinta,shi kuma yana tura cart din kamar wani me aikinta,ya ilahi,ta kasa gano ainihin halinsa,wani lokaci kamar zazzafan mutum,wani lokaci kuma sai taga sauqinsa da sanyinsa yayi yawa,har yayi kamarma ba kowa bane shi.

Sun gama da inda suke suka shiga bangaren undies,kamar ta nutse a waje taji sanda suke ratsawa ta sakanin panties da braziers,sai ta dinga tafiya da sauri da sauri don sunyi su fice a gun.

Danqo hannunta taji anyi daga baya,ta tsaya cak kana ta waiwayo,idanunsa akanta,ya mata nuni da wani abu,saita maida ganinta zuwa abinda yayi mata nunin dashi.

Brazier ce a hannunsa,daburcewa tayi tana dauke idonta,bakinta na dan rawa tace

"Ni...bana sawa" baisan sanda qaramin murmushi ya qwace masa ba,ya yadda da abunda jawahir ta fada,da gaske pretending takeyi,shi yasa zakayi tunanin bata da komai din.

"Wanne size kike sawa?" Dagowa tayi a dan diririce,saiya lumshe idonsa cikin second daya ya bude,saboda wani kyau da yaga sunyi masa a karon farko,sunyi haske sosai,dama can kuma suna da hasken yasan da wannan,amma a wannan karon sun sake kyau saboda girma da suka dan qara yi.

Kai ta sake girgiza masa

"Bana sa......"
Bata ankara ba taji ya fusgota a tausashe,sai gata dan dashi,wanda motsi kadan zatayi ta hade da jikinsa

"Idan na auna da hannuna zan gane ai" ya fada yana daga hannayensa,hijabinta taga ya fara tattarawa tare da qoqarin zura hannayensa ciki,batasan sanda ta cafki hannun nasa ba ta riqe,a rude kuma ta gaya masa number din tana jin yadda mararta tayi wani mugun murdawa,da alamu kuma tsoratar da tayi ya kawo hakan.

Murmushi ya saki ganin yadda gaba daya ta wani rude,sai ya janye hannayen nasa ,amma duk da haka baija baya ba,saiya qara ma matsowa,hakan yasa ya hade gap din dake tsakaninsu,jikinsa na gogar nata,baisan sanda ajiyar zuciya ta kubce masa ba

"Na zaci kinmin qaryar size ne......but ki daina takurewa haka,suna iya lalacewa ko su zube tunda wuri.... brazier is necessary for you tunda kinkai shekarun"

Ji tayi inama qasa zata tsage ta shige ciki ta huta,jikinta ya dauka rawa ta rigashi ja da baya tana dafe mararta data sake murdawa kamar ta tsage,har sai data dan sunkuya

"Are you okay?" Ya tambayeta muryarsa na shaking kadan,dagowa tayi yana gyada masa kai,saiya juya yana duba size din data gaya masan,ya saka iya yanda ya kamata,tana kallonsa ya hada harda pad.

Da qyar take takawa zuwa motar,ta bude seat dinta ta zauna,tana jin sanda ya qaraso shima ya bude ya shiga,baya an saka musu kayan a booth ya tada motar suka fara tafiya,saita cure waje daya,tare da dora fuskarta saman cinyoyinta,tana jin yadda pain ke tasowa daga mararta har zuwa qafafuwanta,wanda dauriyarta ta fara qarewa,harta fara motsi kadan kadan wai ko zataji sauqin radadin.

"Are you okay?"ya sake tambaya karo na biyu,bayan ya fuskanci yadda taketa motsawa,saita gyada masa kai,saidai suna gab da isa gida juriyarta ta qare ta soma fidda qaramin sautin kuka.

"Marata" ta amsa masa

"Ya salam" ya fada yana tsaida motar

"Kin gama shan magungunanki?" Kai ta gyada masa

"Ok...." Ya amsa yana dauko wayarsa,number din dr labaran ya laluba ya kirashi,cikin sa'a kuma ya sameshi,ya masa bayani

"Babu komai,dama hakan na iya faruwa saboda motsawar mahaifa,zata fitar da jinin dake cikinta ne,zan tura maka pain reliever tasha,zata samu sassauci,sai kuma hot or cold water therapy,amma fa,zata iya samun kamar bleeding haka,so she needs somebody else close to her"

"Okay dr, thank you for your help"

"Ba komai" suka kashe wayar,ya maida dubansa ga kaltum wadda batasan ma bayanin da akeyi ba,saiya tada motar yasa kafin su isa bakin pharmacy din ya turo da maganin.

A gaggauce ya karbo magungunan ya dawo ya sake tada motar suka wuce gida,kokaci lokaci yana juyawa yayi mata sannu.

Da kansa ya zagaya ya bude mata murfin motar,yadan matsa gefe don ya bata damar fitowa.

Kasa motsawa tayi,sabida a jikinta take jin danshi,wanda batasan na meye ba,data duba kadan sai taga kamar jini,don haka ta sauke idanunta qasa,ta kuma kasa motsawa.

"Taso" taji ya fada,sai taga hannunshi yake bata,rau rau tayi kamar zata saki kuka,sai kuma ta hadiye ta miqa masa hannun nata a hankali ya dagota,qin motsawa tayi,don tana ji a jikinta ta bata masa seat,tana kuma kunyar ya gani,amma ba yadda zatayi haka ta motsa.

Karon farko ya hangi inda ta bacin,saiya sake mata hannu,ya zagaya ya bude booth din ya zaro ledar siyayyar ya sake dawowa inda take tsaye.

Tafin hannunta ya sanya cikin nashi ya hade yatsunsu waje guda,abinda yasa wani shock a jikin kowannensu kamar haduwar wutan nefa da ruwa,sai yaci gaba da takawa zuwa cikin gidan sannu a hankali tana biye dashi.

*BAYAN AWANNI*

A hankali ta bude idanunta daga nannauyan baccin da yayi awon gaba da ita,wanda batasan yaushe ya dauketa ba.

Ci gaba tayi da bude idanuwan,har sukayi tarwai,saita dan dakata tana duban dakin,take abinda ya faru awanni uku da suka shude suka dawo mata,ashe komai a gaske ne ya faru ba mafarki ba yadda ta tsammata

A hankali ta juyar da fuskarta muhallin daya zauna a dazun kafin bacci yayi awon gaba da ita,wayam yake wajen babu kowa,da alama ya fice ne daga dakin,saita dora hannunta saman shafaffen cikinta zuwa mararta,tana iya jin yadda hannunsa ke yawo har yanzu a wajen,tsigar jikinta ta zuba,saita runtse ido tana girgiza kai,abinda bata taba kawowar faruwarsa ba,wai wani namijin da taba jikinta ba tare data iya hasala komai ba.

A hankali idanunta suka doru kan agogon dake dakin,qarfe shida na safe saura minti daya,da sauri ta miqe,saboda yau din suna da jarabawa,kuma qarfe takwas invigilator din zaizo,sai kuma ta tsaya cak tana wara idanu,saboda canjin da taji a jikinta,sai a sannan ta tuna cewa itama yanzu ta fara period kenan kamar yadda sauran mata keyi,hakan yasa ta fara takawa a hankali ta nufi bandaki.

Tana gab da qarasawa taji an tura qofar dakin,batakai ga waiwayawa ba,hakanan baikai ga magana ba ta gane cewa shine ta hanyar sassanyan qamshinsa,baice komai ba ya koma da baya,a hankali ya mayar mata da qofar ya rufe mata.

Ajiyar zuciya ta saki da taji ya koma din,don nauyinsa ma bazai bari ta iya hada ido dashi ba

"Yanzu bakan kalar pant dina da brazier din da nake boye masa duka ya gani,innalillahi" ta fada tana dafe qirji,bayan tayi tsaye a gaban mudubi,saita kauda tunanin,ta fara cire kayan jikinta.
Chapter 84 · 0% Book details