← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 117

Sashe 70

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da fara'ar shima ta amsa gaisuwarshi tana masa tayin zama yaci abincin,saidai shi ya kada kansa

"Sauri muke mummy,man,mu suke jira fa"

"Sai ina haka 'yan samari?hala surukan nawa zaku ganomin" Ta tambayesu tana murmushi

"Zamu daukarwa abokinmu amarya ne" samir daya miqe daga kan abincin ya bata amsa yana goge hannunsa da tissue

"Allah ya bada sa'a,saikun dawo" ta rakasu da addu'a sanda suke ficewa,idanunta na kan amiru,saita koma ta zauna,taja wayarta tana neman wata number,tana jin a yau ya kamata ta tada zancan,bai kamata tayi sake akansa har haka ba,kamar yadda hajiya kulu ta shawarceta.

"Pls kayi tuqi da kyau mu isa on time,wai me yasa kake hakanne,baka kyautawa IB bafa,tunda aka fara bikin nan babu abinda kaje masa,yau dinma kuma kana wani yanga akan titi kamar ba zamuje ba"

"Nayi maka kama da mara aikinyi da zan yita zaryan bikin abokai?" Ya fada tana dan jefawa amir harara,duka amiru yakai masa a kafadarsa yana dariya

"Allah ya sakamin,nine mai kama da marasa aikinyin kenan ko?,na gode"

"Wa yasani,abu a duhu" ya fada yana qaramar dariya,sannan ya qarawa motar wuta kamar yadda aboki kuma dan uwan nasa ke so.

Kamar kowanne qofar gidan amare sanda ake shirin daukar amarya,shima wannan a cike yake da motocin dake jere bisa tsari,yammata kowacce na nufar motar datafi kusa da ita.

Amiru ya sanya hannu zai bude motar saraki ya tsaidashi

"Me zaka fita kuma kayi,just ka bari ma hadu dasu a can"

"No,kasan yanzu an canza tsari saboda rashin tsoro,sai anyi marking motarmu a cikin masu kai amarya"

"Ok.....but pls" yayi maganar idanunsa nakan gungun wasu 'yammata dake tsaye,da alama suna laluben motocin dq zasu hau ne

"Kada ka kwasomin yaran can masu rawar kan tsiya,a bani dattawan mutane" harara amiru ya jefa masa

"To baba na" saiya saka qafa zai fice

"Am telling you ne....duk wadda tayimin rawar kai saita fice" daga haka amiru ya rufe masa qofar yayi gaba.

Mintuna kusan goma yaji ana knocking Glass din motar,ya daga kansa a hankali ya sauke glass din

"Saraki...... best friend din amarya zata dauka pls,bata jin dadi ne sosai" qaramin tsaki yaja yana mita qasan ransa,me yafi lafiya dadi ne wai?,amma su mata akan kai amarya basa ji basa gani sai sunje,kafin ya gama mitarsa ma amiru ya buda gaban motar,ta shigo a hankali,dai dai sannan ya buda murfin motar shi kuma ya fice ta side dinsa.

Sai data zauna sosai qamshin daya cika motar ya soma shiga hancinta,da alama na turaren mamallakin motar ne,wani qamshi mai taushi da dadi,sai ta waiwaya ta dubi drivern,take ta lumshe idanu,ta dora kanta saman qafafunta tana jiyo hayaniyar yammatan daga waje.

Minti kusan goma taji wasu mata an bude musu murfin baya sun shigo,daga muryoyinsu tasan cewa dattijaine,ci gaba tayi da kwanciya har sanda taji an sake bude mazaunun driver an shigo

"Bismillah" ya furta,muryar data ja hankalinta,har ta dago da kanta tana dubansa,suka hada ido,ya janye nashi idanun yana tayar da motar,yayin data lumshe ido tana jin kanta ya sake wani sarawa.

Ta nemeshi har ta gaji,layin data taba ganinsa tayi bulayin nemansa a fakaice amma bata sake ganinsa ba,number daya bata idan ta shiga ba'a dagawa,abinda bata sani ba shine ba kasafai jawahir ke daga baquwar number ba,yau sai gashi dab da ita,amma yadda taji ciwon kanta yana qaruwa ya hanata yin komai ko cewa komai,sai komawa da tayi luf ta sake kwantar da kanta saman cinyarta tana shaqar daddan qamshi,wanda zata iya cewa hancinta bai taba shaqar mata turare mai dadin wannan ba.

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

41

Tunda suka tafi hankalinsa naga titi,tuqinsa kawai a hankali cike da nutsuwa har suka kawo gidan amaren,jama'ar daya debo suka fita,saidai mubina ta kasa koda motsawa,saboda yadda kan mata ciwo ainun,ya kuma qaru ke ciwon saboda saraki,wanda baisan meke faruwa ba,don suna zuwa bayan ya kashe motar ya fice daga ciki shima.

Baisan tana ciki ba sai sanda zasu koma,da yake wadanda ya debo din ba komawa zasuyi ba,amiru ya bude gaban da niyyar shiga ya ganta,ya shaidata don haka ya tambaya,da qyar ta iya amsa mishi

"Please saraki ka daure mu ajeta koda pharmacy ne ta amshi magani,daga nan ta kira wani ko daga gida ne ya maidata gida" yace da samir sanda yake tada motar,shuru ya masa bai amsa masa ba,ya fara tuqinsa abinsa.

A bakin wani madaidaicin private hospital ya tsaida motar,yayi horn sau biyu mai gadi ya taso ya bude masa ya saka motar ciki

"Ho samir" amiru ya fada a ranshi,bai tsammaci ma yana da niyyar yin abinda ya sakashi ba,duk da yasanshi sarai,yana da matuqar tausayi da kulawa,mutum ne kuma shi mai tausayin mace qwarai.

Nurse ce ta fito ta kamata zuwa ciki saboda yadda take tafiya da qyar saboda ciwon da kan nata yake mata.

Mintina qalilan ta gama ganin likita,amiru na zaune yana waya yaga shigowarta,ba jimawa samir din ya shigo shima ya tada motar suka wuce.

Bakin wani pharmacy ya tsaya,ya wurgawa amiru dake zaune a baya takardar hannunsa ba tare da yace masa komai ba,ya dauka ya duba saiya saki qaramar dariya,ya fuskanci kamar bisa dole yake duk wannan hidimar,kuma yasan dama baiso zuwa kai amaryar ba,shi ya tattagoshi,don haka baice komai ba shima ya fita,ba jimawa ya shigo da ledar magungunan,samir din ya kuma tada motar suka wuce.

"A wacce unguwa zamu saukeki,zamu wuce gia dare na dada yi" lallausar muryarsa ta sauka a kunnenta ta sake haifar mata da kasala,saita lumshe idanu,murya can qasa ta gaya mishi sunan unguwar,tana kallonshi ta gefan ido.

Nutsuwarsa da jan ajinsa sunyi yawa,komai nashi bisa salo me qayatarwa,abinda ya fara fusgarta akanshi kenan tun karon farko.

Dai dai sanda zasu wuce ta wani waje taji amiru ya sako masa hira kan wajen,wanda dukka maganar tasu kan kasuwanci ne,sai tayi fakare tana sauraren yadda muryarsa ke fita da haruffa a jere masu cike da nutsuwa da kamun kai,hakan ya sake dulmiyata cikin wata duniya,har batasan sun shigo unguwar tasu ba,tadai ji amiru na tambayar number gidansunta gaya masa.

"Na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi,na gode" ta fada cikin raunanniyar murya,tana wassafa yadda zata samu number dinsa cikin sauqi.

Sai a sannan ya kalleta,ya gyada kai kawai yana kauda fuskarsa,tadan leqa baya kadan tana yiwa Aamiru godiya sannan tayi hanyar gida.

Shigowar kira wayarsa ya sanyashi waiwayawa ya dubi Aamiru

"Pls karbi driving din nan" sai ya fito suna qoqarin musayar sit,yana shiga wani yaro ya fito da hanzari daga cikin gidan,dai dai sanda amiru ke fitowa shima don shiga gidan driver,yana amsa wayar,baiji abinda yaron ke cewa ba,har sai daya gama wayar,dai dai sanda suka dauki hanyar barin unguwar

"Ta aiko a bata phone number din ka zata maka godiya idan ta samu sauqi"

"Kai kuma saika dauka ka bata kenan?" Samir ya tambayi amiru ba tare daya waiwayo ya dubeshi ba,yana qunshe dariya ya amsa masa

"Tunin ma,mukasan inda rana zata fadi,tunda kaine a kasuwa ai gwara a bata,mu mun riga da mun sayar" harara ya balla masa

"Idan ban girgide maka auren ba kace bani bane"

"Tuba nake the giant saraki" ya fada yana daga hannayensa sama alamar surrender,saiyayi qwafa kawai,bai sake ce masa komai ba.

***********Gefanta ta ajiye wayar kana ta miqe tsaye,goye da hannayenta a baya ta soma kai kawo da alamun zuzzurfan tunani.

Wayar landline dake dakinta ta daga kai ta kalla,kana ta isa wajen da hanzari ta zauna daga gefan gadon,ta fara kiran sashen masu aiki.

Bugu biyu aka daga

"Turomin saratu" ta bada umarni sannan ta kife wayar,taci gaba da xama a bakin wayar,har zuwa sanda taji ana knocking qofar bedroom din nata.

Zamanta ta gyara sannan ta bada izinin shigowar,cikin daqiqu kadan matar ta bayyana,kakkaura ce baqa,bata da tsaho sosai,saidai da alamu shekaru sun fara zuwar mata,duk da ba wani masu yawa bane amma tayi qaura daga gurbin quruciya zuwa na manyance.

"Zauna saratu" mummy ta bata umarni tana bin saratun da kallo,saidai abinda ta kirata dominshi har a sannan bataji nutsuwar hakan cikin zuciyarta ba.

Bata saba saka kowa cikin sabgar ba tsahon shekarun data dauka tana gudanar da al'amuranta a sirrance,to a yanzun ma batason ta soma sanya kowa gudun cabewar lamura,duk da cewa saratu amintacciyarta ce,saidai bata sakar mata ragamar komai ba,ta barta ne tasan iyakar abunda taso ita saratun ta sani

Dan tsakin da batasan ya fito ba ta saki,saita dubi saratun

"Jeki abinki" har ta isa qofa tunaninta yakai mata ga yarinyar

"Ki kiramin wannan baquwar me aikin"

"Kaltume?"kai ta gyada

"Eh ita"

"To hajiya" ta amsa mata tana ficewa daga dakin.

Karamar ajiyar zuciya ta saki,bata kaisu shekaru ko wayewa ba,bare aje ga batun wayo ko gogewa da sanin rayuwa ba,hakanan tafiya da itan zai sake zama mata tamkar wani tsani izuwa wani bigire. Kanta ta sake gyadawa tana sake tabbatarwa da kanta hakan yayi.

Daga karatu kaltum din ta shiga bawa jawahir labarin qauyensu,bada labarin a wajen kaltume dai dai yake shawagin ruhinta cikin qauyen,tana jin nishadi har tsakiyar zuciyarta duk sanda zata bawa jawahir labarin,kamar yadda jawahir din labarin ke burgeta,tana jin kalar wata rayuwa ta daban da batasan da wanxuwarta ba.

Dai dai nan saratu ta shiga dakin,ta kuma shaidawa kaltum kiran mummy,gabanta ya fadi,suka hada ido da jawahir,sai jawahir din ta miqe

"Muje na rakaki" kanta ta girgiza
Chapter 70 · 0% Book details