← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 117

Sashe 114

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan tafiyarki abubuwa da yawa sun faru,ciki kuwa harda yankewa najwa hukuncin daurin rai da rai da kotu tayi" tayi maganar idanunta na tara qwalla,jikin kaltum yayi sanyi itama,ta fara lallashin jawahir tare da bata baki,har ta samu tadan nutsu sannan ta dora

"Lefen aurena yana gida irin naki kuma kamar naki,Amiru ya karbi soyayyata,ya kuma nemi yardata kan zai aureni....bisa goyon bayan hajiya qarama da momma harma da daddy,bayan sun lalubi dangin mahaifina.....da farko sun doje,amma da suka bincike sosai,sai suka samu dama akwai abinda ke damunsa kafin ya rasu,cikin rubuce rubucen wasiyyar da ya bari suka samu nice,sun karbe ni sun kuma mutuntani,musamman mahaifiyar abbana,qannensa dukka maza ne,don haka babu wani cece kuce me yawa suka girmamani ba wulaqanci,saidai ya samir ya roqesu kan su boye al'amarin,saboda sunaso duniya taci gaba da kallona a matsayin diyar professor rashid azare kamar yadda take kallo na a baya......saidai nidin kunyar kallonsu nakeyi....saboda hanyar da mummy tabi ta samar dani.....abun yana min ciwo kulsum,naga matuqar qoqarin ya amiru daya bugu qirji zai aureni....." Ta qarasa maganar qwalla na sauko mata.

Cikin sigar lallashi da kwantar da hankali kulsum ke mata magana

"Duk abinda ya faru ya riga ya wuce jawahir,kada jiyanki tasa ki rushe gobenki,yanzu babu abinda yafi kamata dake illa ki fuskanci gobenki,sannan shi a aure.....nagartar mace na iya shafe duk wani aibu dake tattare dashi...kedin nagartacciya ce jawahir,kina da dukkan DABI'A ta qwarai,baki bari ƊABI'AR ZUCIYA na son rai da son kanta ya rinjayeki ya gurbata miki halayya da ƊABI'A ba,kina da matuqar kirki da tausayi,na tabbatar wannan yaa amiru ya kalla,Allah kadai yasan manufarsa na fiddoki a haka da yayi,wala'alla ke wannan ce taki jarrabawar nan gidan duniya,kuma nayi imanin idan kika cinyeta....zata iya zame miki silar shigarki aljanna" kalamai masu taushi tayi amfani dasu wajen kwantarwa da jawahir hankali,ta kuma samu nasarar hakan,don ta sake sosai,suka dinga hira,jawahir na bata labarin abubuwan da suke faruwa da bata nan,gidan yayi dadi sosai,ya koma kamar da,yadda momma ke bata kulawa har yafi yanda mummy ke batan,saboda lokacin mummy tana fuskantar tsangwama saboda ra'ayinsu baizo daya da mummy da jawahir ba,amma a yanzu duka babu wannan.

Ya samir kuwa tace yafara zama mara kunya ta fadi tana dariya,wallahi baya iya boye soyayyar da yake miki,kinsa momma ce taja masa kunne kan ahir dinsa yazo ya dameki?,ai inajin da ko kwana hudu vakiyi cikin qauyen nan,gaban kowa kuwa banda momma da daddy amsa waya yakeyi,shi da ya amiru kuwa yanzu baram baram jawahir ta fada tana tilliqa dariya

"Me yasa?"kulsum ta tambayeta itama tana tata dariyar tare da jin wata kewa ta mijin nata na kwarara sassan jikinta

"Yace wallahi ya samir din ya fara zaucewa,baya barinsu suyi barci,bashi da aiki sai waya" sai suka sanya dariya gaba daya.

To sai yamma lis su momma suka tashi tafiya,ciki har da 'yan uwanta daga sudan mutum biyu,sai wasu daga azare 'yan uwan daddy mutum uku suma,saidai kulsum ta kasa zuwa bare ta hada idanu dasu, momma ta dinga mita

"Shikenan samir ya shiga tsakaninmu kenan yayi mana farraqu?,to ban yarda ba,da sake" da kanta tayi tattaki har gidan habi ta ganta sannan sukayi sallama,saidai jawahir ta roqi momma ta barta,sa dawo tare da kulsum din.

Hakan kuwa akayi,a nan qauyen suka barta,tare da ita suka dinga zagaya dangi,har gidan inna,wadda ta fashe da kuka sanda taga uban kabakin da su momma suka ajjiye mata a matsayinta na kakar kulsum,saboda momman tace duk wani daya danganci kulsum sai yaci arziqinta ya kuma ya qara,kulsum mutum ce,kulsum nagartacciyar mace ce mai kyakkyawar zuciya,wadda kudi ko dukiya ko wani qyale qyale na rayuwa bai dameta ba,sanda zata tafi saiga innar ta zube tana roqarta gafara

"Basai kin nema gafarata ba inna,badai abun duniya kikeso ba,kuma gashi an baki,zaki iya ci gaba da tsinema muda ummanmu" sarai innar ra gane magana ta gaya mata a fakaice,to amma tasan yaran sunyi haquri,sun kuma yi kawaici,kome zata fada kuwa,ita a yanzu nadamarta hade da kunya take,ashe wanda ka raina watarana shine zaiji qanka ya rufa maka asiri?,ashe RABON BAWA DA ARZIQI MUTUWA ce?.

"Allah ya yafemu gaba daya" itace kalmar qarshe da kulsum tayi mata suka baro gidan.

"To haka kawu ado yakumbo indo da umma suwaiba,kaf dangi 'yan uwa abokan arxiqi babu wanda baice HAIHUWA TAYI RANA ba akan su kulsum din,abun sai son barka da godiya ga Allah S W T wanda yake azurta bawa a sanda yaso.

Yakumbo indo ita ta dauke kulsum da jawahir ta ajjiye gidanta ta fara tsumasu,gyara na gaske take musu musamman kulsum da take ganin 'yar hannu ce,batasan komai bai gudana ba,har sai wani dare an hadu ana hira,kwanaki bakwai da suka rage su koma gida ayi walimar da za'a raka amare gidajensu,da ita da fatsima da karima wadda a yanzu itama ta sauko take kuma jin kunyar abinda suka yiwa kulsum din a baya,ashe arziqinta yaci uban nasu,gefe ga jawahir da habi dake baiwa danga nono,karime ke tsokanarta kada fa ta koma asake sabon gashi yawa sabuwar amaryar da aka kawo yau yau.

Yatsina fuska tayi tana dubanta
"To da mecece?,kar nake a leda,babu wani abu daya gudana" dariya suka sanya gaba daya,habi ta kama baki ta kasa magana,jawahir tace

"Allah ya samir ya gama hure miki kunne,ya koya miki rashin kunya"

"To meye laifinsa?,yama yi qoqari ai" shewar suka sake saki

"Zaki bayani da babban baqi wallahi,don indai wannan mijin naki ne a yadda dai na ganshi ko.....hmmmm" dukkansu suka sake saka dariya,sai kuma tsoro ya dan tsarga mata,ta basar da zancan aka shiga wata hirar.

Da magariba bayan sun bar gidan habi tayo wajen ummanta,sai umman ta kama hannunta zuwa qofar wani daki,ta tura ya bude,cike fal dakin yake da kayan jeren cikin gida da kayan qyale qyale,masu kyau masu tsada kuma na zamani

"Ki duba da kanki kaltum,kar kiji kunya,idan akwai abinda babu kiyi magana za'a siyoshi kafin ku tafi" idanunta cike fal da qwallar qaunar da umman nata ke mata

"Ummanmu....duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata

"Nakine kaltum,duka abunda na mallaka a duniya naku ne keda habi,saboda bani da kwafinku" rungume umman nata tayi a jikinta sosai,tayi kuka tayi kuka,tayiwa bilalu addu'a,sannan tana tsaye aka dinga fito da kayan tana gani.

Komai yaji yayi daidai,babu wani abu da babu shi koda kuwa ina za'a kaita a aure,sun jima suna hira da ummansu har zuwa sanda babansu ya shigo,bakinsa dauke da sallama,kai bakace shi bane.

Sannu da zuwa tayi masa ta miqe zata shige daka kamar yadda suka saba a baya

"Kulsumu" taji yayi kiranta,saita tsaya cak

"Zo nan" ya kirayeta,ta dawo da baya,tazo gabansa ta tsugunna

"Fushi kike dani har yanzu ko?" Yayi maganar muryarsa na rawa,saiga hawaye na sauka,abinda ya daga hankalin kaltum kenan,ta girgiza kai da hanzari

"A'ah baba"
"Idan ma kinyi ai bakiyi laifi ba,amma ina roqonki don girman Allah ki yafeni,bana buqatar komai daga wajenki banda yafiyar,koda bazan tsira da komai ba a rayuwata ba damuwata bace indai na tsira da yafiyarku"

"Ban riqeka ba baba,kai kayi silar kawoni duniya,na yafe maka,kuma kaima ka yafemin idan na taba bata maka" adaren su ukun suka zauna sukayi hirar da suka kafa tarihi,irin hirar da tun haihuwarta basu taba ba.

Ana ya gobe zasu tafi saiga lantana Allah ya kawota ita da nasuru,da fari kunyar kulsum ta dunga ji tana buya,wai kada taga kamar taci amanarta,saida zasu fita da yammaci xasu karbo wasu kaya wajen yakumbo indo,tayi wa lantana ba zata ta fada gidanta,sun sameta tana ta ware tsarabar doya da manja da dankalin turawa da takanyo,ta saukesu da ruwan da lemon roba cikin mutantawa da kuma jin kunya,xata fice kulsum tayi caraf ta damqota

"Na kamaki,waini lanatana kikejin kunya?,me kika yimin banda alheri?" Kanta ta sadda qasa,saidai yadda kulsum din keta dibanta da tuna mata da rayuwarsu ta baya ya tabbatar mata babu komai a ranta kulsum din,daga qarshe ta shaida mata ita dadi ma taji data auri nasurun,saboda sun dace matuqa,sukayi sallama ta hada mata doya da yawa tace ta kaiwa ummanmu,dama kuma ta saba kai mata duk sanda ta dawo,ba zata samu zuwa walimae tarewar kulsum din ba saboda tayi nauyi,amma ta karbi address dinta,ta tabbatar mata da cewa tana nan zuwa in sha Allah duk sanda suka shiga garin.

Kudin da tazo dasu taga sam babu wata buqata da ummanta ko babanta ke dashi,saita rabasu gida hudu,kaso biyu ta bawa habi wadda keta tunanin irin san'ar daya kamata tayi,ta bata shawarar sarar atamfofi da hijabai,kaso daya ta aikawa da wasila,daya kashin kuma ta aikawa da asiya,duk da tana tunanin ba zata karba ba,saiga asiyan da kanta tazo godiya,inna laure ta rakota,saida suka gama godiyar asiya ta fashe da kuka,suna neman gafarar ta,bata wani tsaya batama kanta lokaci ba tace ta yafe mata,sabida ta riga ta wucen wajen ita.

Bata jima da fita ba wasila tazo da nata kukan da neman gafara,itama cewa tayi ta yafe matan,saboda ubangiji ya ruga daya hukunta kowa dai dai da laifinsa,to me yayi saura?.

******** Cike da wata irin nutsuwa me ratsa zuciya gangar jiki da ruhi yake rufe kowanne sashe na gidan,har zuwa sanda yakai ga qofar qarshe wadda zata sadashi da ainihin falon gidan,saiya daga kansa a hankali yana kallon sama,wadda ta hada hadari me kyau daya fara feso yayyafi yas yas a jejjere me dan yawa.

"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat" shine abinda ya furta,bayan samun kansa da yayi tsakiyar falon gidansa da yake mallakinsa,wanda tako ina qamshi yake fitarwa mai taushi da dadi,komai kuma na falon kalar fari ne da light ash.

Tafiya yaci gaba dayi yana sanya hannunsa yana fidda babbar rigar jikinsa ya riqeta a hannunsa,komai na jikinsa farine qal kamar hannu bai taba tabashi ba,tun daga samansa har qasa.

A hankali ya tura qofar dakin da yake da tabbacin a ciki take a zaune,dakine wanda babanta yayi mata komai na ciki,bayan dakin da umman ta ta shirya mata,da kuma wanda shi karan kansa samir din yayi mata,amma sai ta zabi zama ana babanta,saboda tasan cewa da uba ake ado.
Chapter 114 · 0% Book details