← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 117

Sashe 111

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanu ta zuba mata daga inda take tsaye,mamakin abinda ya samu wasilan takeyi data sauya haka gaba daya,saika dauka kakar kaltum ce bawai sa'anni suke ba,banda ma tayi mata farin sani ba zata shaidata ba,tana tsaye taga samir din ya sanya an loda mata abincin me yawa ya bada umarnin a daukar mata,sannan ya fidda envelope din guda uku ya miqa mata,tana hangen sanda ta durqusa har qasa tana godiya,yayi mata alama da hannu ta tashi,yayi taku uku ya koma cikin mutanen yana ci gaba da kula da yadda ake gabatar da rabon.

Kamar wanda aka gayawa ko kuma wanda jikinsa ya bashi,saiya waiwaya saitin window din sanda yake qoqarin jingina da itaciyar dake wajen,karaf idanunsu suka hadu,sai taja baya da wani mugun sauri cikin faduwar gaba.

Sarai ya ganta,sai ya saki wani miskilin murmushi,ya kirayi umar daga inda yake,ya danyi magana dashi na wasu mintuna sannan ya juya ya fara takawa zuwa cikin gidan.

Da sauri sauri tayi hanyar fita,saidai yana sako kai itama tana sanyo nata,abinda ya basu damar yin karo kenan da juna,sai yaci gaba da tafiya zuwa ciki,yana korata da baya a baya zuwa cikin dakin,kana ya sanya qafarsa daya ya maida qofar ta bame,bai barta ba har sai da suka dagana da bangon dakin,takai qarshe,sai ya sanya hannunsa daya ya dafe bangon dakin,idanunsa akan kyakkyawar fuskarta,bugun zuciyarta ya qaru saboda yadda take iya jin saukar numfashinsa saman fuskarta

"Meye hukuncin mutumin daka kama yana satar kallonka?" Kunya da nauyinsa suka rugo suka dabaibayeta,ta kasa magana,ganin bata tanka ba sai ya qara matsarta sosai,tayi gefe zata goce,ya tarota ta hanyar sanya daya hannun nasa ya sake dafe bangon,ya sakata a tsakiya kenan

"Babu inda zaki motsa daga nan,saikin bani amsa" a dan tsorace ta kalleshi,tana iya jiyo hayaniyar mutane har yanzu daga waje,kada wani ya shigo dakin ya samesu a haka

"Ni ba kai nake kallo ba" ya saki da qaramin murmushin gefen baki,yana tuna wasu abubuwa da suka shude,kaltum me tsiwa,kaltum mara tsoro,gata yau gaba daya ta sukurkuce tsakanin hannayensa,tun baikai ga tabata bama

"To wa kike kalla idan bani ba?"

"Yan garinmu" tayi hanzarin bashi amsa,waiko hakan zaisa ya kubuta,fuska ya bata sosai

"Wasu mazan kike kallo ma ba mijinki ba?.....lallai sai na hukuntaki" yana kaiwa nan ya tallafo kanta,ya kuma hade bakinsu waje guda.

Wani salon tsotsa yakewa lips dinta,har sai da sukaso sakwarkwacewa gaba dayansu,dama ga sauran dafin jiya da bai gama barin jikinsu ba.

Baya ya koma a hankali ya zauna dabas a qasa,banda cikin tahowar kaltum din akwai umarnin momma da baisan hikimarta na yin hakan ba,da babu shakka bazai iya tafiya ya barta ba,bazai iya nesa da itaba na wasu kwanaki.

Sai da nutsuwarsu ta daidaita sannan ya karbi zuba abincin da kansa,yace ta zauna gabansa kawai yayita kallonta ya wadatar,ya fuskanci zallar soyayyarsa ke ci mata zuciya,amma batasan ya zata sake dashi ba,don haka bai barta ba a sannan sai daya samo kanta da kaso sittin cikin dari,yana cin abincin da bata tsammaci xaici ba yana janta da hira,har tazo ta iya maida masa.

Sake kallon agogon hannunsa yayi,qarfe uku na rana,a qalla sun shafe kusan minti ashirin xaune cikin motar kawai yana kallonta,bayan ta fito ne kawai da sunan yi masa rakiya.

Numfashi ya sake ja yana dubanta,sai ya kamo hannuwanta zuwa cikin nashi yana murxa tafin hannun nata,abinda yasa ta dunqule jikinta waje guda,kwanakin nan gaba daya wani dafi yake saukarwa jikinta,wanda mutum bai isa ya kauce masa ba.

"Suna jiranka fa,kamar sun gaji" tayi jarumtar fada sanda take hango tsaiwarsu murtala ta baqin gilashin motar da suke ciki ita da sarakin

"Zan tafi.....amma,sai kinyimun abu daya" wannan karon samun kanta tayi da sanya qwayar idanunta cikin nasa,har cikin jiki da jininta itama cikin wadan nan daqiqun takejin cewa zatayi kewarsa,kamar kada ta barshi ya tafi

"Ya salam..... what a beautiful eyes..... kada ki zubamin dafin da zan kasa tafiya na barki mana" tattausan murmushi ma cakude da kunya ya sauka saman fuska da lebanta,sai ta sadda kanta,amma kafin ta gama saukarwar ya kama fuskarta ya dago zuwa gareshi

"Nooo......ki barni na kalla na mitunan da suka ragemin na tafi" fararen idanun nata ta zaro

"Mintuna kuma?"
"Yes....so kike na tafi ko?" Kasa amsa masa tayi,saita maye gurbin amsar da murmushi

"Is okay,nasan kinyi missing ummanmu.....but before na tafin, give me a kiss" ya fada yana miqa mata tausasan labbunansa sirara masu taushi da sanyi" sake fito da idanun nata tayi waje tana girgiza kai alamun a'ah,sai shima ya fitar mata da nasa idanun

"Just do it....idan ba haka ba kuwa,zamuyita zama anan"kafin ya rufe bakinsa tayi saurin dora nata bakin ta manna masa kiss din mai tsaho kuwa,wani numfashi mai nauyi yaja,ya koma da baya ya zube cikin kujerar yana shafa qirjinsa,bata ankara ba yasa hannunsa daya ya fuzgota cikin jikin nasa,tsahon wasu mintuna har sai da nutsuwarsa ta daidaita.

Hannunta ya kamo ya saka mata sabbin kudi masu kauri yana cewa

"Wannan dai kyautace daga mijinki,don naga alama fada kike da sabbin kudi...... don't say no" dariya da kunya suka cikata,cike da girmamawa tayi masa godiya,ya fito da kansa ya bude mata qofar motar,yana tsaye yana binta da kallo har sai data shige gidan,sannan a sanyaye ya kada kai ya koma cikin motar,su umar dake tsaye gefe suna gulmar kallon da yake binta dashi,suna masa tsiya da dariyar ba sabon ba,suka shige motar

"Ku kuka da kanku akan gulmata,ku kuma dauke idanunka daga kan matata,if not, I'll definitely deal with you" saraki ya fada fuskarsa a washe,saidai kuma akwai alamun da zai nuna maka shi dinne boss.

"Sorry sir" suka fada cike da mamakin yadda akayi ya fahimci gulmarsa suke,sai kowa ya shiga taitayinsa,suka tada motocin.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_DA ZAFINSU_*

*_A TSARE SUKE_*

*_SUN TANADESU_*

*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*

*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*

*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*

*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*

_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_

08184017082

_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107

*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*

64

Farincikin data tsinci kanta a ranar bazai misaltu ba,gata ga ummanta,ga kuma habi dinta,bata manta da bilalu ba,sai data kokawa rashinsa a dai dai wannan lokacin.

Hira iya hira,labarai rankatakaf na abubuwan da suka faru cikin gidan dana qauyen sanda bata nan sai da habiba ta sauke matashi,ko abinci saida ummansu tayi da gaske sannan ta tsaya taci.

Habiba da umman sun fara mata ne da labarin abinda ya faru cikin gidan,bayan tafiyarta ummanta ta shiga damuwa qwarai,saboda rashin sanin taqamaimen inda aka kaita,sanda kawu as ya shaida mata ya karbi address na samir ta dan samu sauqi cikin ranta na wasu lokuta,daga bisani kuma kwanciyar hankalin ta wargaje,saboda jin an debi watanni shuru babu kaltum din babu labarinta,gefe guda kuma inna laure tana murza tsiyarta,tare da baza habaici akan auren kaltum,saidai cikin hikimar Allah,data durfafi tashin dare tana kaiwa Allah kukanta,sai ya sanya mata dangana,ya fidda mata damuwa,har ma tayi mafarkin kaltum din sau biyu cikin kyakkyawan yanayi a wasu darare guda biyu bayan ta gama sallar bacci ya dauketa,abinda ya sake sanya mata kwanciyar hankali kenan.

Babu dadewa sai ga wata qungiya me suna professor rashid women aid forum,wadda tazo rabon jari ga matan karkarar,ummanmu bataje ba,amma sai gashi anzo har gida an kawo mata nata tallafin jarin me tsoka,wanda kusan yafi na kowacce mace yawa,suka dinga qara mata kudin da kadan da kadan,ta cika da mamaki da kuma tsoro,daga bisani zuwan qarshe da suka kawo.mata tace ba zata karba ba,saiga samir yazo da kanshi,ya bayyana mata kansa,bai boye mata komai ba,saboda yace yasan ita din uwace,tsayayya jajirtatta,kuma a soyayyar uwa da yarta tabbas hankalinta bazai taba kwanciya ba idan batasan inda diyarta take ba,saidai bai bayyana mata yadda zaman aurensu yake da kaltum ba.

Sosai hankalin umman ya kwanta,ta kuma samu salama mai tarin yawa,taja bakinta ta rufe kuma,bata gayawa kowa waye samir din ba,saidai kuma tun daga wannan lokacin ya dauke musu nauyin ci da sha,gefe daya ga sana'ar ummanmu nata habaka,kasancewarta dama mace mai tarin kirki tun da can,tun mijinta malam amadu nada dukiya,kasancewarsa mutum me arziqi ada,bayan aurensu ya soma tsiyacewa,mutane suka fara cewa ya auri mai farar qafa.

Tun baya dauka har ya soma yarda,abinda yasa ya tsaneta ya tsan gwameta kenan ita da yaran.

Abun mamakin da ya faru a lokacin shine,yadda hankalin malam.amadu ya fara tashi,saboda jita jita da laure ke yadawa cewar anya ba kudin diyarsu sukeci ba kuwa?,sai a sannan ya fara tada hankalinsa nason sanin inda ya miqa kaltum din,ummansu tana kallonsa bata ce masa ta tafas ba,haka zai qaraci zirgillonsa kullum rana yana zuba idanun ganin samir ya kaishi inda diyarsa take,ko sau daya ummansu bata taba tanka masa ba.

Ba jimawa kuma sai ya fara wani zabura,yana tsaka da barci sai aga ya farka a firgice ya fito da gudu yana kiran sunan bilalu,yana hirji kan bilalun ya yafe masa,gaba daya sai ya koma wani firgitacce,ko baccin rana baya samun yi bare na dare,daya fara gyangyadawa zai farka a firgice.

Da farko ance masa wai fatalwa ce,umma ta kafe kai da fata kan cewa ba ita bace ba,danta bazai taba fatalwa ba,tunda ma ai saiya kwanta bacci yake ganinsa,daga bisani da suka samu wani malami masanin addini sosai,yayi masa bayanin komai,sai ya tabbatar masa haqqin bilalun ke bibiyarsa,ya bashi shawarar ya tuba ga Allah,ya kuma yawaita sadaqa wa bilalun,da ziyartarsa duk ranar juma'a idan hakan zata yiwu.

Da taimakon wadan nan addu'o'in ya fara samun salama,sai ya jima baiyi mafarkin ba,saidai gaba daya yayi laushi ya kuma canza,bashi da buri da addu'a koda yaushe illa addu'ar Allah ya bayyana kaltum din.

Ana tsaka da wannan samir din ya dawo da plan na canza musu ginin gidan gaba daya,saidai hassada da qyashi suka sanya laure d kawo iliya cewa basuso,yarsu asiya wadda tayi aure tace zaa canza musu suma.
Chapter 111 · 0% Book details