← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 117

Sashe 80

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah ya bamu alkhairi,Allah ya qara lafiya" ta fada tana binta da kallo,tsakanin ita da jawahir batasan waye yafi wani sonta ba,saita girgiza kai,tana sake daukan littafi,duk da karatun jarrabawa takeso tayi,amma labarin ya soma daukan hankalinta,tanason sake qarawa kadan kafin ta ajjiye.

Tsahon wasu mintunan suka shude,wasa wasa sai gashi ta kwashi lokaci mai tsaho tana karatun bata sani ba,sai data duba agogo taga lokaci yaja,sannan ta rufe,ta nufi bandaki da zummar yin fitsari tazo ta kwanta.

Kanta ta kalla sosai a mudubi bayan shigarta bandakin,tuna jarumar littafin kawai take tana fidda murmushi,saita samu kanta da tube kayanta tana tara ruwan zafi,rayawa take a ranta bari ta gwada wanka yadda ta karanta jarumar nayi.

Wanka tayi sosai tayi brush,saita dinga jinta wasai,bacci na sake kama idanunta,ta daura alwala ta fito daga bandakin.

A dakin nata ta janyo kayan shafarta,dan murmushi ta saki,jawahir kenan,ta sako mata kayan sawa kala biyu don kada ta jima,amma kuma ta hado mata dukka kaya shafarta data siya mata,wanda har yanzu da yawansu,sabida bata basu muhimmanci sosai ba,saidai duk da haka ita a karan kanta take ganun canji gyaruwa da kwanciyar fatarta,sai ta samu kanta da duba sunan man shafawar nata,abunda bata taba yi ba,iyakarta da man ta lakata ta shafa.

Ido ta fiddo da taga yayi daidai da sunan man data gani cikin littafin,sai kuma ta maida idon tana sakin murmushi,mamaki na kamata,ta matshi a hannu ya fara shafe ilahirin jikinta dashi.

Tana gamawa ta feshe jikinta da turarenta,karon farko data fara amfani dashi,da iya body spray din kawai da roll-on take sakawa.

Ita kadai take sakin murmushi sanda tayi rub da ciki saman gadon tana qanqame pillow,ashe dai da gaske ne,wani sirri ne a cikin wankan dare a duk sanda zaka kwanta,taso ta sake duba ci gaban labarin,amma hakanan fa haqura,ta dauki daya daga cikin litattafan karatunta ta fara dubawa,saidai duk da haka lokaci lokaci labarin yana fado mata tare da jin shauqin ci gaba da karatun,a haka bacci ya dauketa da litattafai tule a gabanta.

Washegarima sai data gama komai sannan ta tafi makarantar,saidai a yau din sunyi sallama da hajiya qarama,harda bata kudin makaranta wanda batasan me zatayi dasu ba,ko nata da samir ya ware mata ma yana wajen jawahir bata karba,ganin hakan sai jawahir din ta qyaleta,tare da cewa zata yita ajjiyemata har ranar da zata buqacesu.

Sannu sannu sai gata ta kwashe kwana hudu gidan hajiya qarama zata shiga na biyar,a kwanakin ta saki jiki da hajiyan kamar yadda ta shiga ran hajiya qarama sosai,sai takejin kamar daya daga cikin yaranta data aurar aka dawo mata da,don duk wani abu da 'ya zata yiwa uwa shi kaltum ke mata.

Ita kanta kaltum din tana jin sakewa a gidan fiye da can gidan professor,har mamakin yadda ta sake din takeyi,amma takance qila a nan din saboda babu idanun mummy,qila saboda babu kowa daga ita sai hajiya qaraman,sai kuma baqon da Allah ya kawowa hajiyan,ta sakar mata ragamar komai,ta bata yarda sosai kamar diyarta.

Cikin kwanaki biyar din kacal ta gama littafi uku,wanda ta dauki abubuwa masu yawa na darasi a ciki,ta kuma tsinta wasu ta fara aiki dasu,banda jarabawa dake gabanta ma batason labarin ya dauke mata hankali ya hanata karatun da batasan guda nawa zata dinga gamawa a rana ba,don tana kaiwa dare can batayi bacci ba.

Koda jawahir ma tazo gidan sai data tambayi kaltum me ya canzata haka?,wanda ita babu irin qoqarin da batayi ba ma ta wofantar,sai dan abinda ba'a rasa ba?.

Dariya tabi jawahir dashi,saita dafe baki

"Ni sai nakega dariyarma kamar ta canza taki,amma gaskiya kinso jamin asara da baki amfani da mayuka da sabulan nan ba,kaltum,kinga yadda kika soma zama fresh?,ashe da gaske keba baqa bace,hasahena ya tabbata cewa kalar fatarki chocolate ne?. Maganar data sanya kaltum kallon fuskarta a mudubi,tabbas itama fa hangi abinda jawahir ke fada,bata taba zaton fatarta me kyau bace sai yanzu,bata taba sha'awar kalar fatarta ba kamar wannan lokacin.

Sanda ta raka jawahir bakin motar da taxo maidata gida ta kalleta

"Na debo miki wasu kayan suna nan saman gadon dakin,amma sababbi ne, mummy ce ta siyamin na daukar miki guda uku,karfa kiga na kawo miki kaya ki shantake,Allah hajiya qarama najin qwarin jikinta zamu koma gida,bakiji ba gaba daya gidan babu wani dadi" yar dariya kaltum tayi

"Amma baga yaya najwa ba?" Baki jawahir ta tabe tana shigar da qafafunta cikin motar

"Wannan an gaya miki ana abun arziqi da ita?,ya jauhar cema naketa lissafin sanda tace min zata zo,to itace ma idan tazo mukan taba hira....itama tata matsalar ta bawa waya lokacin da muhimmanci mai yawa,ba kasafai take iya daurewa zama babu waya ba" rufe mata qofar kaltum tayi tana dan murmushi gami da cewa

"Allah ya kyauta to" don ita batasan ma wacw jauhar ba,ko matsayinta a gidan.

Sai da taga fitarsu sannan ta dawo cikin gidan da dan sassarfarta,saboda tana son jiqa shinkafar tuwo,don gobe tashin asuba takeson yi ta yiwa hajiya qarama wainar shinkafa,don yau din da sha'awar cinta taga ta tashi,kuma tayita aikawa duk inda tasan za'a samu ba'a samo ba,shi yasa ta qudirta yi mata kafin ta wuce makaranta.

*******washegari********

Karfe bakwai da rabi na safiyar washegari ta kammala komai,tana tsaye a falon gidan sanye da uniform dinta da sukasha guga,fes gwanin kyau,riga ce wadda ta fitar da qugunta sosai,saboda daga sama cas jikinta take,yayin data bude daga qasa,tsahonta gaba daya iya qaurinta ne,sai farar safa data kai mata har gwiwa,wanda ita ta taimaka wajen rufe qaurin nata.

Hijabin makarantar tasu qarami ne sosai,don iyakarsa saman qirjinta,wannan dalili yasa take amfani da abaya,wadda bata cireta sai zata shiga aji,hakanan koda waje zata fita siyan abu sai ta sanyata take fita din.

Ta gama komai,doguwar rigarta ce kawai bata dauko ba,jakar makarantarta na gefe a ajjiye,hannunta daya riqe da littafin makaranta tana dubawa,lokaci lokaci tana daga kai ta kalla agogo,saboda ganin yadda lokaci keta quracewa amma har yanzun me kaita baizo ba.

Qarar bude gate din gidan da taji ya sanyata sakin ajiyar zuciya,ta miqe da hanzari ta nufi window din da tasan zata iya hangen wanda ya shigo,ta yaye window din tana leqawa,saidai bata iya hangen wanda ya shigo din,hakan ya qara mata qaimi,ta dinga dage tana leqawa,a tunaninta driver dinne.

Sannu a hankali yake takowa zuwa qofar falon,cikin wani sanyi nasa daya wayi garin safiyar yau dashi,safiyar data yakejin kansa fresh,babu komai a cikinsa sai abubuwan da zai iya fuskanta a yau din.

Sanye yake cikin wasu sexy slim fit one button blazzer Baqaqe,da ratsin ash,kamar yadda takalmin qafarsa yake baqi,wanda ba abinda yake sai daukar idanu saboda yanda yake fes dashi,ya saka ash socks,agogon kamfanin D&G me asalin tsada ne daure a tsintsiyar hannunsa,yau din idanunsa sanye suke da wani sun glasses mai kyau,wanda ya dace da zagayayyar fuskarsa mai dan tsaho kadan.

Tun kana daga nesa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa mai saukar da nutsuwa.

A hankali ya dora hannunsa ga handle din qofar ya budeta kana ya tura yana sako kanshi falon a hankali,saboda ya qudurce idan bai samu hajiya qaraman ta tashi ba zai wuce ne kawai office,idan ya tashi ya samu dama ya dawo ya dubatan.

Ko kusa ko alama bata ji alamun shigowar mutum ba,saboda yadda ta bada himmar leqen isowar habibu driver,uwa uba ma qofar falon sam bata da qara ko qanqani bare kayi noticing shigowar wani.

Yana sako kai falon a kanta idanuwansa suka fara sauka,tana ta dage don ta hango waje sosai,saiya sakaya qofar,yatsaya daga bakin qofar yana harde hannuwansa a qirji,tare da binta da idanu tare da mamakin meya hanata wucewa makaranta a irin wannan lokacin.

From head to toe ya bita da kallo,bai tana sanin haka uniform din makarantar tasu yake ba, infact ma ko color dinsa bai sani ba sai yau,ya tsaya cak da idanunsa daidai qugunta,wanda shape din da aka fitarwa rigar makarantar ya taimaka wajen fitar da qugun nata.

Dai dai lokacin data saki labulen tana juyowa a sanyaye,saboda ta fuskanci lallai yau din da qyar idan bata makara ba.

Bata taba kawowa ranta ganinsa ba,sai gashi tana juyawa itama shi ta fara gani unexpected,a tsaye cak yana binta da kallo.

Zuciyarta tayi wani irin bugawa,tayi qas da kanta da sauri bayan ta qare masa kallo cikin sakannin da basu wuce biyar ba,ba abinda ya fado a ranta irin jarumin littafinta na jiya,a yanzun da take ganin samir din sai taga kamar jarumin ne ya fito a zahiri

"Ina kwana" ta fada tana jin kamar wadda akayiwa dabaibayi,saboda tunda take ba wanda yataba ganinta da uniform din nan a haka a tsaye,daga jawahir sai biba

A hankali yanjanye idanunsa da yakejin kamar zasu lumshe,ya mayar dasu kan agogon dake hannunsa yana duba time,kana ya sauke hannun yana hadawa da amsa mata gaisuwar,ya jefa mata tambaya kuma a jere

"Meya hanaki tafiya makaranta har iwar haka?" Yayi mata tambayar sanda yake bin fuskarta da kallo,fuskar da tayi wani smooth,ainihin kalarta tana fita,wanda hutu zama waje daya,sauyin muhalli da kuma ingantattun sabulai da mayuka suka taimaka wajen fitarta,to me ya haddasa wannan baqin?.

"Bai qaraso ba wanda yake kainin,nima shi nake jira" maganarta ta katse masa tunanin da baisan daga inda ya ratso ba,kai yadan kada yana dan cije lebansa na qasa

"Hajiya fa?"

"Ta tashi,tana daki"

"Ok, call her" ya bata umarni yana saukowa daga steps din dake bakin qofar falon zuwa ainihin cikin falon yana dan bin bayanta da kallo,haka kawai yaji wani abu ya tsaye masa.

Duk taku daya da zatayi zuwa wajen hajiya qaraman sai taji wani mugun nauyi ya saukar mata,saita waiwaya kadan inda jakarta take da niyyar dauka ta goya ko zata rufe mata wani abu.

Hada idanu sukayi,ya zare idanunsa daga kanta yana zama hannun kujera

"I hope ba haka kike fita makarantar ba?" Kai ta gyada masa tana saurin rataya jakarta,sannan ta amsa masa da
"Eh" tana qara sauri zuwa ciki.

Ajjiye carbin hannunta hajiya tana murmushi

"Kada dai kicemin duka aikin nan kin gamashi?,indai kuwa hakane dole ki makara kultum"

Murmushi ta sake
"Tun dazu,donma bai iso ba da tuni na tafi...."

"Subhanalla,garin yaya?,kuma maimakon ki shigo ki gayamin.....miqomin wayarcan na kirayeshi" tana nuna mata saman bedside drawer,ta qarasa tana dauko wayar gami da miqa mata sannan ta shaida mata zuwan samir din
Chapter 80 · 0% Book details