Sashe 64
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sanda ya tsaida motar a harabar wajen bayan ya gama dai daitata,ya dinga bin wajen dake cike da 'yan jagaliya da kallo,dukkaninsu matasa ne masu jini a jika,wanda ya kamata a ce a dai dai wannan lokacin tunaninsu fresh yake,yana kuma gudana ne kan yadda zasu gina rayuwarsu data al'ummarsu dama qasarsu gaba days,sai gasu sun qare a wani waje zaune zube a wulaqance,mutum sama da ashirin na jiran mutum guda da sunan yi masa hidima ko bashi kariya,wanda basu da wani alfanu da zasu samu wanda ya wuce rugujewar rayuwarsu,da dan kudin dako cikakken abincin wuni guda babu lallai ya samar musu.
Idonsa ya lumshe yana jin ciwon hakan cikin ransa,yana daya daga cikin abinda yasa har kwanan gobe,ko sau daya siyasa bata taba burgeshi ba,yana ganin duk yadda kakai ga son tsaftace kanka ko zamewa hakan ba zai yiwu ba,wata qurar saita taddaka,inama ace mahaifinsa zai fuskanceshi yadda shi yakeso?.
A yadda ahalan ya gaya masa,mintuna biyar kenan suka rage su fito daga hall din,saboda haka saiya fito daga motar baya ya kasheta,ya tsaya a jikinta ya jingina yana ci gaba da nazarin wajen,har zuwa sanda aka fara fitowar,hakan yasa ya janyo hular kansa ya rufe fiye da rabin fuskarsa,don baisan yin magana da kowa,mahaifin nasa kawai yazo dauka.
Sannu a hankali ya tunkareshi sanda yake fitowa shida jama'arsa
"Barka da fitowa daddy" ya fada cikin girmamawa,saiya maida hankalinsa gareshi,yana masa wani duba na sama da qasa,gaisawar da suka fara yi da jama'ar dake tare dashi ta hana maganar da yaso yi din,saidai duk motsin da samir din zaiyi sai yaga idanunsa a kanshi,har zuwa sanda ya take masa baya zuwa bakin motarsa ya bude masa ya shiga,shima ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar suka fara tafiya.
"Idan har kazo wajen nan ne don ka burgeni,babu abinda kayi illa ma bata min rai da kayi,ka duba tarin jama'a masu girma da mutunci a wajen nan,ka rasa dame zakazo min sai da qananun kaya?"professor ya fada cikin nuna zallar bacin rai,kafin samir yace wani abu ya sake magana
"Sai yau kaga damar dawowa kenan?,me yasa a kullum kai maqiyin burina ne da muradina?" Sosai furucin ya daki samir har zuciyarsa,ko yaushe yana aiki don ganin ya dai doita komai,amma idan komai yayi kamar zai gyaru saiya sake tabarbarewa da zarar ya danyi nesa da mahaifin nasa na wani lokaci
"Nakanji a raina wani lokaci inama ace kaine najwa....najwa ce kai,da nasan hakan ba zata faru ba" hannunsa ya dora kawai saman kansa yana shafan kan nashi tare da son hadiye abinda ya riqe masa wuya,ire iren wadan nan lokutan yafi qyamata cikin rayuwarsa,shi yasa koda zuciyarsa ta bashi shawarar kusantar mahaifin nasa,sai wata zuciyar ta haneshi,ya gwammace nesanta dashi saboda kubuta daga kalamansa masu ciwo irin wannan.
"Kayi haquri daddy" itace kalma guda daya daya iya furta masa,ya kuma maimaita masa ita kusan sau biyar kafin isarsu gida,wanda yana saukeshi ya wuce sashensa kai tsaye.
Kasa zama yayi ya dinga kai kawo a tsakiyar dakin yanason lissafa abubuwan da yawa da suke zuwa kanshi,kaushin daddyn agareshi kullum abune da bashi da sauqi ko rangwame,bayaga sabanin ra'ayoyi da zabe zabe na rayuwa babu wani mai muni tsakaninsu,amma a yadda yake mu'amalantarsa saika fassara abun da wani lamari mai girma wanda bashi da kyau.
Ya tafi da baya saboda samawa kansa mazaynu gefan gadonsa ki zuciyarsa zata samu nutsuwa,qafarsa ta daki locker gefan gadonsa,yakai kallonsa ga wajen,saiya fasa zama gefan gadon ya zamo ya zauna gabanta,ya zura hannunsa wani saqo dake jikinta ya fiddo muqulli ya zura ya budeta,ya sanya hannu ya fara fitar da abubuwan dake ciki yana binsu da kallo daya bayan daya.
Tarin hotuna ne mabanbanta,duk da cewa kowanne hoto mutanen jiki daya ne,amma yanayin sutura da kuma wajen da aka daukesu ya banbanta,a hankali wani abu ya fara taso masa mai kama da bege kewa da kuma qauna,saidai tashi daya wani abu mai qarfi ya taso ya dannesu,wanda hakan har yasashi miqewa daga tsugunnon da yayi,har zai bar wajen a haka ya tuna akwai Aamir a dakin,dalilin daya sanyashi dawowa ya tattara komai ya mayar muhallinsa kenan,saidai wannan feelings din daya taso masa yana jinsa yana motsawa a qasan zuciyarsa yana ci gaba da kaiwa sassan zuciyar nasa.
*********Zaune yake a gabansa da sanyin safiyar,zaman daya kusa kaiwa na mintuna talatin bayannya gama masa dukkan bayanin daya jima yana tsarawa zai gaya masan dangane da zaman kaltume a gidan,zai iya cewa tunda yayi hankali,kusan wannan shine kari na farko daya taba gaya ma daddyn abinda ba haka yake ba ma'ana qarya,komai tsanani ko kuma rintsi baya boye masa gaskiyar abu,kome gaskiyar kuwa zata haifar masa,har sai daya gama jiransa ya qarashe kallon labaransa,sannan ya maida kansa gareshi da wani irin duba,sanda mommy ke ajjiye masa zazzafan ruwan baqin shayi don ya dumama jikinsa da hanjinsa kafin lokacin cin abincin safensa yayi
"Kafin ka sanarmin komai.....mommynka ta riga data shaidamin" ya fada muryarsa a nutse,a hankali samir din ya daga kai suka hada idanu da mommyn,don basuyi haka ba,ya shaida mata da kansa zai gaya masa,to amma kamar yadda zuciyarsa ta gaya masa tayi hakanne don bashi kariya kamar yadda ta saba,hakan ce ta faru,don alamun kada ya damu tayi masa da idanu,dai dai sannan kunnuwansa sukaci gaba da dauko masa maganganun daddyn
"Abun mamaki,koda yaushe jidda qoqarin baiwa samir kariya kikeyi akan duk abinda yakeso,kina sanya qafa kina fatali da nawa muradin,basan me yasa kike daure masa qarqashin yin duk abinda ya tsarama kansa ba" cikin salo da kwantar da murya tace
"Banda abinka daddy,meye ne da son yakeyi wanda ba dai dai bane ba?,shi daya fa Allah ya bamu,yanzu idan ban bashi qwarin gwiwa da kariya ba?,waye zan bawa?"
"Ok,hakan shi ya baki qarfin gwiwar tayashi ya dinga karya min tsaruka da dokokina ko?" Da sauri ta girgiza kai
"Ba haka bane.....daddy yaran yanzu bada qarfi ake binsu ba,ba'a son a dinga tilastasu saboda gudun abinda zaije yazo" shuru ya ratsa falon,wani abu ya sauka zuciyar samir,hakanan yaji kamar wannan amsar batayi masa ba,shi ba yana yin komai sabida bijirewa ba,ba yanayin komai saboda yana tunanin shine dai dai ba,a'ah,yana yin komai ne saboda yana da tabbacin haka komai din ya kamata ya kasance,maganar momy ta gaba ta tsaida tunaninsa
"koda raheena bata a nan,ina kallonshi a matsayin amanar....."
"Dakata....kada ki sake min magana makamanciyar wannan" daddy prof ya katseta yana dubanta,saita kafeshi itama da nata idanun tana karantarsa,akwai wani abu data jima tana qoqarin karantarsa tattare dashi,wanda har yanzu hangen ta da tsinkayenta ya kasi canko mata ainihin meye shi,saidai ta karanci akwai fushi daya cakuda da wani abu,abunda shi dinne takeson ganowa.
Sauke idanunsa samir yayi daga yake rarrabawa a tsakaninsu,ambatar sunan kadai ya daki zuciyarsa,baikai ga rarrabe tunaninsa ba muryar daddy ta sake ratsa kunnensa
"Bana daukan masu aiki underage,ka sani dokata ce,don hakan kamar kashe musu rayuwa ne,kuma koda zan dauka mutual person sai nasan daga ina mutum yake.....saboda haka ka dauka yarinyar mutane ka maidata inda ka daukota tun muna shaidar juna dani da kai" sosai gaban samir din ya fadi,in har daddyn ya kafe akan haka ba shakka akwai matsala,saboda ba yanxu ya shirya fuskantar wannan damuwar ba,ya bada lokacine zuwa sanda qura zata lafa
"Daddy.....amma da zaka saurareni da ka fahi......"
"Samir......na gama magana,gobe idan Allah ya kaimu akwai tafiyar dake gaba na,kada na dawo na sameta a gidan nan,bijirewa hakan xai iya zama ggarumar matsala tsakanina da kai" daga hakan ya dauki cup din dake gabansa ya fara shan tea dinsa,sai kawai samir din ya miqe,yana jin sanda mummy ke qoqarin sanya baki a cikin matsalar amma daddyn ya dakatar da ita.
Tunda tayi alwala da taimakon biba ta bada faralin salla take xaune a inda ta idar da sallar,har zuwa lokacin da biba zuwaira ta turo qofar a karo na biyu tun bayan fitarta
"Har yanzu kina zaune?,inaga ya kamata kiyi wanka ko?,tunda na nuna miki yadda zaki kunna shayar" dan gyara zamanta kadan kaltume tayi,tana qoqarin sake fuskarta,ganin yadda duk abinda biban zatayi,tana yi mata shine fuskarta cikin fara'a
"Da cewa nayi sai zuwa anjima"ta bata amsa tana wasa da qasan hijabinta daya dan bule.
Kai biba ta girgiza
"A'ah fa,gidan nan dabam yake,kamar yadda mutanen ciki suke na daban,kiyi wanka,saiki fita ku gaisa,sannan ki samu abu kici karki zauna da yunwa irin ta jiya" kai ta daga mata a sanyaye tana duban agogon dake maqale a bango,duk da bata gane qarfe nawa yake bayarwa,amma a jikinta tasan safiya ce sosai yanzu,wanda bazai wuce tara na safe ba,duk da ko a gida bata kaiwa rana sosai ba tare tayi wanka ba,irin na 'yammatan garinsu da suke kaiwa yamma lis,sai an dawo daga tallah,la'asar sakaliya,sannan ayi wanka,a hade harda kwalliyar zuwa dandali.
Kalle kallen data tsaya yi a bandakin ya sanya ta bata lokaci sosai,ta tsaya gaban babban madubin dake bandakin tana kallon fuskarta,kallo na sosai a karon farko.
Koda ake cewa tafi habi duhu bata taba zata duhun nata yakai haka ba,a gurguje ta cuccuda abinda ya samu sanda taji muryar biba ta sake dawowa,ta maida kayan jikinta ta fito.
Dubanta biban take cikin mamaki
"Bakizo da wasu kayan bane?" Sai data kalleta kafin ta bata amsa,tun sanda wancan da batasan sunansa ba ya kirata take kula da damuwa da al'amarinta,tana ganin hakan muraran cikin idanunta
"Nazo dasu"
"Yauwa,dauko ki canza wasu,ki ajjiye wadan nan" qarasawa tayi inda ta sakaya qullin kayan nata,ta bude ta soma dubawa,biba na tsaye tana bin kayan da kallo
"Sune kayan naki wai?"ta sake tambayarta,dauke idanu kaltum tayi daga kan kayan ta mayar ga biban,tana mamakin yadda ta tambayeta
"Eh" ta amsa mata a gajarce
"Shikenan ba laifi,dauki daya a ciki ki saka" ta qarashe maganar tana ajjiye mopper da abin shara don kintsa dakin.
Da hanzari kaltume din ta karba
"Ki barshi zan share" da tace ta barshi,don batasan matsayinta cikin gidan ba,kada ta aikata ba dai dai ba ta jawa kanta wani abun na daban,ganin ta dage sai ta sake mata,ta koma bandaki ita ta fara gyarashi.
Tana tsaka da sharar tana cike da mamakin yadda wajen yake sharuwa subul subul,babu qasa,babu qura,ga sauqin shara.