← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 117

Sashe 105

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sanda raihana ta sake samun ciki abun yayi matuqar daga hankalin jidda,kuma ya tabbatar mata da cewa lallai ka samu sauqi,tana tsoron kada raihana ta sake haihuwa ta samu da namiji ita tana zaune,abinda yasa ta yanke shawarar kau da ita,ta kuma yita qoqarin ta samu haihuwa da kai koda sau daya ne.....saidai inaa,bata samu wannan rabon ba har yau........

"Wadan nan takardun na qasa sune zasu baka tabbacin maganganuna na yanzu......raihana kuwa......" Gabansa yaji yayi wani mummunar faduwa data kira sunansa

"Ya Allahu" ya furta a sarari,hakan baisa haj shuwa ta tsaya ba,don burinta kawai ta gama kwancewa mummyn zani a kasuwa

"Bayan ta gaza kau da ita daga duniya.....Gidan mahaukata jidda ta kaita.....har yau kuma tana raye......saidai ni kaina bansan wanne gida bane,kuma a ina yake......ga wadan nan,duka takardun kadarorin raihana ne data sace ta rabawa yaranta,wadan nan kuma kudaden kamfanin saraki da 'yarka tasa dana ya debo mata,ta hanyar amfani da siddabarun na'ura........

Tunda ta fita daga gidan takejin gabanta yana faduwa,abinda ya hanata dogon tsaiwa kenan cikin asibitin,ta kasa tsaiwa ma taga likitan ta juyo gida.

"Sannu da zuwa hajiya" saude mai aiki ta fada ga jidda,saidai bata amsa mata ba ta jefa mata tambayar dake cin ranta tunda ta shigo,saboda taga motar hajiya shuwa a farfajiyar gidan,batayi mamakin zuwanta ba,saboda a jiya sunyi waya,tayi mata cin mutuncin da dukka yazo bakinta,gami da kakkausan gargadin ta jawa fawwaz kunne ya maido komai dake.hannunsu,ta daukoshi zuwa daular gidanta ne saboda ya amfana shi da uwarsa darajar amintar dake tsakaninsu,hajiya shuwan batace mata ta tafas ba,wanda mummy ta dauka shakka ce tasa haka,har sai data gama sannan tace

"Ki kwantar da hankalinki,gobe zan dawo miki da komai da kaina ba saqo ba" tayi zaton zata sameta a falo a zaune,sai kuma taga falon wayam

"Su waye sukazo?"
"Hajiya shuwa ce da fawwaz,amma suna wajen alhaji" saude ta amsa mata,gabanta yayi mummunar faduwa,me ya kaita wajen daddy kuma?,me taje yi?,a iya tsahon zamansu bata taba haka ba,amma sai zuciyarta ke qoqarin gamsar da ita cewa dubashi suka shiga yi,don haka ta sauya akalarta zuwa parlor din daddyn a sukwane tun kafin hajiya shuwan ta mata wata barnar,tasan halinta sarai,bata barin kota kwana,hakanan koda zatayi asarar wani abu nata muddin zata dauki fansa zata iya aikata komai.

Najwa dauke da babban faranti data cika da fruit tabi bayan mummy,wadda batasan tana biye da ita ba,itama bata kirata ba saboda mugun haushinta takeji,saboda tana son kawowa soyayyarta dama plans dinta tarnaqi,don haka taci gaba da bin bayanta har suka shiga falon.

Kallo daya ta yiwa daddy kamar yadda shima yayi mata ta fuskanci lallai akwai gagarumar matsala,hakanan kuma komai ya qare

Dukka wanda yake cikin motar kuka yake riris,amiru ke driving kaltum na zaune daga gefansa gidan gaba,daga baya kuwa bibi ce riqe da hannun momma,sai samir daga daya side din ruqunqume da ita,zaka zaci cewa zata sake bace masa,kanta na boye cikin qirjinsa saboda haske da ya yiwa idanunta yawa,sakamakon dadewa da tayi bataga hasken rana ba.

Hadiyar wani abu kawai yake daga maqoshinsa zuwa cikinsa,idaunsa tamkar garwashin wuta,zuciyarsa na ayyana masa wanne irin hukunci ya kamata ya dauka akan duk wanda keda hannu wajen qarara da rayuwar mahajfiyarsa cikin wannan wajen?,wajen da duk wanda ka ganshi a ciki to dole ce ta kaishi bawai son rai ba?,ya dauko mahaifiyarsa ne cak ya fito da ita daga wajen,ba tare daya tsaya yabi ta ba'asin komai ba,don a yanzu ta tata yake tukunna kafin zuwan komai.

Wayarsa daya manta da ita gaba daya cikin motar ta dauki tsuwwa,tafi kusa da amiru saboda tana kusa gear

"Sabi'u yana kiranka" baiyi niyyar amsawa ba,amma jin sunan me kiran nasa yasa ya karba wayar ya kara a kunnensa.

"Najwa?,najwa kuma?" Shine abinda ya maimaita,bayan sabi'un ya bashi bayanan cewa itace waya ta qarshe da bala yayi da ita bayan ta sanya an tsinke birkinsa dana mahaifinsa,bisa taimakawar fawwaz.

"Wuce gida damu" samir ya gayawa amiru a tsawace,kamar wanda ya fara fita a hayyacinsa,yana jin cewa tabbas akwai babban tashin hankali kenan,abinda da farko ba haka ya tsara ba,ya tsara ya wuce da momma din daya daga cikin gidajensa.

Dadi ya saukarwa bibi,don dama haka takeso,tanaso taga yadda qaryar jidda zata qare,tana son taga tadda zata kalli momma raihana......

A rikice ta maida dubata ga hajiya shuwa,wadda take binta da kallo tare da murmushin mugunta a fakaice,ganin mummyn ta gaza cewa komai sai kallo da take rarrabawa a tsakaninsu tace

"Yauwa.....gwara da Allah yasa ma muka hadu,ga saqonki nan dukka na damqa hannun mijinki" take qafafun mummy jidda suka dauki rawa,wato an samu sabani kenan?.

Ta aika yara bayan fitarta su qaddamarwa hajiya shuwa su dauko mata dukkan wasu takardu nata da suka shafeta na sirrinta da take bata ta adana mata,sannan su karbo dukkan wasu kudi da takaddar kadara ta najwa dake hannun fawwaz,ashe ita nan ta nufo kenan?,ko kuma sun sameta tsallakewa tayi?,kamar tasan abinda take tunani sai tace

"Ai yaran da kika tura ya karbo miki saqon munyi sabani dasu ne,muna fita daga layin suna shiga......"

"DAGE da gaske shine mahaifin najwa?,lecturer mahaifin jawahir?" Daddy ya jefi mummy jidda da tambayar don tabbatarwa da kansa abinda hajiya shuwa ta fada.

Yadda tayi wani mugun shock daya sanyata yin taga taga zata fadi saboda girma da nauyin tambayar ya sanya duk wanda ke wajen fahimtar gaskiyar maganar,ciki kuwa harda jawahir da maganar ta sanyata kurumta na wucin gadi,basu kuma fahimci tana wajen ba sai da plate din hannunta ya fadi ya tarwatse da dukkan abinda yake ciki

"Qar.....qarya take min,so take taga bayana......qarya take" mummyn ta fada jikinta yana rawa

"Da dukka wadan nan shaidun dake hannuna?.....duk da hakan qarya take?!" Daddyn ya qarashe tambayar cikin daka tsawa mai kada hantar mutum,ya wani jirkice zuwa mayunwacin zaki dake farautar dukkan dabbar data gifta ta gabansa.

Ja da baya mummyn ta fara yi a tsorace sanda daddyn ya miqe yana tsuma yana nufota,idanunsa a birkice,tunda take bata taba ganinsa cikin siffa irin wannan mai ban tsoro ba,gaba daya ya sauya daga rashid din zuwa wani mutum da zuciyarsa da kuma fuskarsa ke cike taf da bala'i.

Cak taga ya tsaya ya tsurawa bayanta idanu ,abinda ya sakata waiwaya itama da hanzari.

Tashin hankalin da tayi arangama dashi sai taji yafi wanda ta shigo ta taras cikin dakin,tayi wata muguwar girgixa da razana kamar zuciyarta zata yanko daga qirjinta ta fado qasa.

,sai data gwammace dama bata waiwaya ba,ina ma suman qarya tayi kafin idanunta suga wannan babban bala'in da tashin hanakalin,yau din wacce irin baqar rana ce a gareta?,wanne abu ne yake shirin samunta haka?.

Tuni daddy ya miqe tsaye,labbansa suna haduwa suna rabuwa,jikinsa ko ina rawa yake,idanunsa qyam saman fuskar momma,yana son magana amma kowanne furuci ya kasa fita daga labbansa.

"Raihana.....ya akayi kika fito?" Kalaman da suka subuce kenan daga bakinta sanda momma raihana ta kafeta da idanu,a zatonta tana zanta hakanne a zuciyarta,batasan cewa maganar ya fito fili ba sai sanda taji bibi na maida mata amsa

"Ubangijin da baya barci bare gyangyadi shi yayi ikonsa ya fiddata daga kurkukun da kika jefata ba tare data aikata laifin komai ba"......

Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sai jin qarar mummy sukayi,dafe da gefan cikinta jini yana bin qafafunta,kafin hankali yakai ga abinda ga sameta cikin qiftawa da bismillah muryar najwa cikin wani mahaukacin sauti ta mamaye wajen

"Gwara na kasheki na kuma kashe kaina,gwara na dawwama a gidan prison,da ace wani riqaqqen dan daba talaka shine mahaifina,Allah ya isa tsakanina dake......Allah ya isa,bazan taba yafe miki ba,kin cuceni daya zama ba daddy ne ubana,gwara na kasheki....." Ta fada tana daga wuqar hannunta,wadda ta daukota ne cikin fruits din data kawowa su hajiya shuwa.

Babu wanda ya motsa saboda cetar mummy,sai zagaye da suka fara yi a parlor din,duk da jinin dake diban mummyn amma najwa yunqurin binta ta qara mata takeyi.

Hajiya qarama ce wadda basusan sanda ta iso ba ta hankade najwan ta fadi gefe

"Meye hakan?,kinyi hauka ne?ku dukanku kuna kallonta tana yunqurin kash......"maqalewa maganar tayi a maqoshinta sanda idanunta suka sauka fuskar momma,fuskar data jiqe da hawaye tana bin hafsanta da kallo.

"W.....waw.....wa nake gani kamar raihana ta?" Kusan tafi momma kuxari,saboda haka kafin ta qaraso ita ta rigata,suka rungume juna kana suka fashe da wani nannauyan kuka mai ratsa zuciya.

Hayaniyar da ta barke cikin falon yasa suka saki juna,najwa ce ta isa ga hajiya shuwa taci kwalarta da kyau,fawwaz na tsaye daga bayanta yana qoqarin rabata da wuyan mahaifiyarsa qarfi da yaji

"Munafuka algunguma,ki gaya musu gaskiya,ki gaya musu gaskiya,dama ba qaunata kuke ba?,zuwa kikayi ki rabani da ubana ki manna min wani uban?" Murmushi hajiya shuwa ta saki

"Sakeni 'yar nan,yanzu kuwa zan maimaita a gaban kowa saboda su xama shaida"

Hankali kwance hajiya shuwa ta maimaita dukkan maganar data gayawa daddy,sulalewa hajiya qarama tayi qas kamar yadda momma ta sulale itama,yayin da samir ya dafe bango jiri na shirin kada shi,kaf cikin zancan ba wanda yake hangowa.....tausayinta keson wasa da numfashinsa irin jawahir, innocent girl......son zuciya yasa mahaifiyarta ta bata mata rayuwa.....ta jirkita mata asali,ya Allah.....yanzu jawahir ba jininsa bace?,ba daddy bane ya haifeta?.

Amiru da idanunsa suka kada jazur ya dubi sashen da hajiya jidda take,jini take zubdawa sosai,kuma ci gaba da zamanta a haka dai dai yake da rasa ranta,sai ya hango fuskar jawahir.....mutuwar mummy da mummunan labarin professor rashid ba shine ainihin mahaifinta ba abun zaiyi mata yawa,abinda yasa yayi tattaki kenan ya fita ya kira driver ya taimaka suka kamata zuwa mota

"Ko kwana daya baxan iya qarawa da igiyar aurena a kanki ba.....na sakeki saki daya,na sakeki saki biyu,na sakeki saki uku jidda.....daga can idan kin rayu kada ki dawomin gidana,ki jirayi kuma sammaci daga kotu" wadan nan kalaman sune suka yiwa mummy jidda rakiya sanda su amiru suke fita da ita,abinda yasa numfashinta ya qarasa tsaiwa cak daga qirjinta......

Kansa samir ya girgiza,ya zaro wayarsa ya kira jawahir,bayan yayi qoqarin dai daita muryarsa

"Kina ina?"
"Ya saraki....ina makaranta"
"Idan kin fito ki wuce gidan hajiya qarama,gobe da safe da wuri xan turo driver ya kaiki azare wajen yadikko"

"Azare kuma yaayaa?" Ta fada a shagwabe cikin mamaki

"Eh azare, just say yes"
Chapter 105 · 0% Book details