← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 117

Sashe 23

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da maka makan takardu guda uku masu tsaho da fadi,ruler da abun rubutu,sai marker da colour da drowing ya zube a gabanta.

Ido ta fitar tana duban kayan sannan ta dubeshi kusan lokaci daya ita da umma
"Bilalu,ina ka samo wadan nan?"sai daya zauna sannan ya amsa mata
"Wadan nan takardun na jikin bangon ajujuwan da aka rushe ne,aka ce mu dauka idan muna so,su kuma saura kudin abincin aikina ne,na raka bashir kasuwar lahadi na gansu acan na siya miki".

Fuskarta ta cika da murmushi da wani irin qaunar dan uwanta,farinciki sosai ya kamata na abinda yayi matan
"Kai....kai bilalun umma,da gaske kake kuwa?"
"Gasu gabanki yaya?"
"Ashe dama kana sona haka?"ta fada tana dariya idanunta a kanshi,sai yayi murmushi kawai ba tare daya amsa mata ba
"Umma.....kinga abinda Bilal ya siyomin dan Allah"
"An gode maka Allah ya qara zumunci ya hadamin kanku"
"Amin umma wallahi" ta amsa tana jujjuya takardun tare da sake qare musu kallo,tana tunanin abinda zata zana a cikinsu.

Sai data gama murnar sannan kuma ta dubi bilal din
"To a ina kake cin abinci?,kai daba gida kake dawowa kaci ba?,kuma gashi ka tattara kudin haka kawai ka siyomin kayan zane?"
"Ana kawo mana abinci lokaci lokaci,ko a kira masu talla a siya mana,ko mantawa suke sun bamu kudin?" Kai ta jinjina,taga qoqarinsa,shi da bai iya tara kudi,daya samu aci cikin ciki kawai,idanunta ta dauke daga saman kayan ta mayar kan fuskarsa
"Amma dai zanfi so ace ka tara kudadenka bilal,idan aka gama ginin nan,koda ni ban samu shiga ba....kai ka shiga bilal,kayi karatu don Allah"
"Tare dake fa muke zuwa makaranta duk bayan sallar asuba yaya kin manta?"kaita kada tana ci gaba da kallonsa
"Na sani,karatun zamani bilalu,karatun boko.kamar kowa,ni ina sha'awarsa sosai,amma tunda bani da wani isashen lokaci babu kuma dama zanso ace kai kayi,ko don ka taimaki kanka,ka kuma taimaki ummanmu" shuru yayi na wasu sakanni,sannan daga bisani ya amsa
"Me zai hana yaya ke na tara miki kudin ki shiga?"kanta dai ta kuma kadawa
"Kai yafi cancanta kayi bilal,kainw namiji,ni dana fara za'a fara batun aurena,azo a cireni kaga anyi asarar kudin da aka kashe"
"Zanyi yaya"ya bata amsa yadda ya saba bata,da alamun baison zancen ma gaba daya.

Murmushi ummansu tayi,ta jima da fahimtar bilalun baya son makaranta sam,musamman karatun boko,shi yasa duk yadda kaltumen tayi dashi yake zillewa,itama kaltum din dole tayi shuru ganin ya miqe,saiya qarasa ya dauki wata tsohuwar hularsa daya wanke ya sanya a kansa yana cewa
"Umma zani dandali......yaya gaba daya kin rabu da zuwa"
"Hmmmm"kawai tace,don ita kanta tana son zuwan,amma hakanan zuwan ya fita a kanta,tun wancan ranar da babansu ya fadi mummunar kalma a kanta
"Zanje,sai wani lokacin saimu tafi tare" kansa ya gyada ya fice abinsa ta bishi da.kallo.

Bilal kenan,shi sam a rayuwarsa bashi da tension,duk da tarin qalubale iri iri dake bibiyar rayuwarsa,amma kamar baisan dasu ba,duk da cewa akwai quruciya a sha'aninsa,tunda har yanxu shekara sha hudu yake,sai tsahon qafa da zai sanya mutum yayi tunanin yakai shekara sha bakwai.

12
D/Z
*Zafafa biyar na kudi ne,ki biya ki karanta ciki aminci,yadashi wato sharing tamkar xalunci ne,Allah kuma baya barin zalunci*

Ku tuntubemu ta nan
08184017082
Ko
09134848107

Sanye yake da jallabiyya fara qal mai sulbi,wadda ta saukar masa har daidai idanun sahunsa,bata qarasa masa har qasa ba saboda yanayin tsahonsa,tattausan farin slippers ne a qafarsa,idanunsa saye da farin glasses,sai jarida dake riqe a hannunsa wadda suke buga bayanan kasuwanci da kamfanunuwa,tattausan qamshin turaren tuscany ne ke fita a jikinsa,kamar yadda sumarsa ke sheqi,duk kuwa da cewa dare ne.

Yana tsaka da dubawa ne kiran prof ya shigo wayarsa,don haka ya miqe ya tattara dukkan abinda yake ya fito don amsa kiran nasa.

Qasa qasa yayi sallama cikin falon nasu,wanda yake shuru sai qarar na'urar sanyaya daki hade da qamshin turaren daki.

Mutum uku ne xaune a falon,wanda kusan koda yaushe haka zaka samesu,kowa yana abinda yafi qwarewa akai.

Jawahir wadda ke kwance rub da ciki tana game a tab,sai najwa sata tasa litattafai a gaba masu tulin yawa tana dubawa,yayin da humaida ke gyaran faratanta,a yadda suke zaunen saika dauka kowa a cikinsu baisan da zaman dan uwansa ba.

Sallama yayi muryarsa can qasa,idanunsa saman tvn wadda babu wanda yake ta kanta a cikinsu,hasalima volume dinta can qasa yake,kuma suna wani program ne mai muhimmacin daba lallai su ya burgesu ba,saboda basu san muhimmancinsa ba.

Dukkaninsu kowacce cikinsu tadan gyara yanayin yadda take saboda nuna sunsan da shigowarsa,jawahir ta miqe zaune daga rub da cikin data yi,najwa ta gyara glass din fuskarta bayan ta kalleshi,humaida ta lanqwashe qafafunta,duk da bata gama yankan farcen ba.

Kusan kamar a tare humaida da jawahir suka gaidashi,ya amsa cikim yanayin kulawa yana dubansu,sannan idanunsa suia sauka kan najwa,saita sake sanya hannunta ta gyara glass din fuskarta sannan cikin wani yanayi kai kama da jin isa isa tace dashi
"Barka da dare"
"Barka"ya amsa a taqaice yana duban hanya,inda hajiya jidda ke fitowa,kamar kullum kamar kuma kowanne lokaci daya kasance prof yana gida ta fito cikin shiga ta alfarma,wani dandatsetsen lace ne da duwatsun jikinsa keta bada qyalli da walqiya,isan ka ganta a sannan zakayi tsammanin zata wata dinner ce,bawai kwalliyar me gida a cikin gida ba.

Fuskarta dauke da madaukakin murmushi take dubansa,cike da kulawa da tsantsar qauna data bayyana cikin qwayar idanunta
"Son....kada dai ace ka gaji da jiran abincinka ka biyo sahu?,yau ba favourite dinka akayi ba,sai nasa hasana ta sake girka maka wani abun,don banson ka fita waje neman wani abun,ko ka kwana da yunwa" dan murmushi ya saki,wanda yafi kama da washewar fuska,koda yaushe kulawa take bashi ta musamman,a kullum soyayyar da take nuna masa tafi ta kowanne mutum dake cikin gidan,idan ua debe mahaifinsa kawai,koda yaushe kuma kowanne lokaci komai nasa yakan kasance na daban kuma na musamman a wajenta,saidai kuma.....baisan dalilin da yasa zuciyarsa ta zama wata irin zuciya mai tarin butulci da saka alkhairi da sharri ba,ko sau daya ta kasa jin farinciki da wadan nan shekaru data kwashe tana bashi dukkan kulawa goyon baya da qauna,ta kasa jin nutsuwa akan kanta na dinga alkhairi da hidima da takeyi dashi,idanunsa sun kasa manta ta,itace dai a wannan matsayin daya santa,itace dai wannan din daya sani,ta kasa gogewa daga yanayinta na baya,duk da tarun shekaru da kuma sauyawar rayuwa da kuma yanayi,wanda dukkan dan adam yake samun kansa a ciki.

"Yau din ban shigo da yunwa ba mommy,da kin qyaleta,abba nazo gani,yace min yana son ganina,ina tsoro kada naje bacci ya debeni ban samu zama dashi ba,kada ya tsammaci ina gudu ne kamar ko yaushe"murmushi tayi
"My son....dan abbansa,nikam naga sanda wannan dramer taku kaida abbanka zata qare,shi har yau ya gaza fuskantarka,ya sallama...,kai kuma kana kam bakanka.....ka gaza sakar masa...."
"Wacce gulmar tawa akeyi?"suka tsintsi muryar prof daga bayansu,yana fitowa daga qofar data sada wannan sashen da nasa sashen,cikin doguwar rigar jallabiyya,shi dinma kamar dai samir din,sai jini yayi aikinsa,daka kalli samir ta yanayin qirar jiki....sak prof din,saidai kuma kamanni a fuska bashi bane,kana iya daukan wanna ka baiwa jawahir dake zaune,itace Prof din zammm,don najwa ma mommynta ta biyo.

Dukkansu suka waiwaya suna dubansa sanda yake fitowar,jawahir da mommy murmushi sukeyi,yayin da najwa ta dake kamar bata a wajen,duk sanda irin haka zata faru takan yi dif kamar bata wajen,tana matuqar kishin samir,sau da dama tana jin inama ace itace shi,inama ace itace babbar diya namiji kuma ga professor din ba samir ba.

Inda suke tsayen ya qaraso,fuskarsa kadaram kadaham,cikin girmamawa kowa ke gaidashi,sannan daga bisani ya waiwayo yana duban samir din
"Ba don nayi kiranka ba da ba zaka nemi ni ba kenan?"ya fada da wata murya mai nauyi,idanuwansa saman fuskar samir din,wadda take fayau,bata dauke da kowanne irin emotion,a ladabce yace
"Afwan daddy....."yayi maganar ne yana dan ranqwafawa alamun girmamawa,shuru yayi bai sake cewa komai ba,saiya juya yana neman wajan zama nan cikin falon,duk da cewa ba dabi'arsa bace yin hakan,da wuya ka sameshi zaune a nan,indai ba abinci zasu ci su dukka gaba dayansu ba,ganin haka ya sanya humaida miqewa,don ba kasafai take zama cikinsu ba idan tagansu dukka tare waje daya kamar haka,kuma tasan ba wani kira ko zama daddyn ya umarxi kowa da kowa ba.

Qasan carfet din samir ya samu ya zauna sosai daura da daddyn,don taqin dake tsakaninsu kadanne,a sannan jawahir tuni harta miqe,ta shiga kitchen ta hado musu abunsha mai sanyi,irin sanyin nan baina baina mai saukar da nutsuwa,wanda bazai cutar da haqora ko bakinka ba,ta hadashi ne da kanta,saboda sanin da tayi,daga daddyn har samir din suna son natural juice.

Sai data zubawa kowa cikin cup sannan ta turashi gabansu,ta miqe tabar falon,saiya zamana daga mommy najwa sai samir din da daddyn.
Chapter 23 · 0% Book details