← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 117

Sashe 109

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da zafi zafi yaji ana knocking glass din motar,ya zare jikinsa a galabaice yana duban wanda ke bugun glass din,amiru ne,bai sauke ba sai daya tabbatar ta gyara daurin da kwalinta,ya gyara xaman rigar jikinsa,sannan ya dauki ruwan dake ajjiye kusa dasu ya bude ya kafa kai ya fara kwankwada,zuwa sannan amirun harya qagauta,ya zagayo ta gaban glass din motar yana duban samir,wanda baiyo ko darr ba sai daya gama shan iya yadda zai iya ya miqawa kaltum sauran sannan ya sauke glass din

"Kaima fa dan iska ne da alama inda ka samu waje....ka fito mummy nason ganinka urgently, she's in serious condition,da gaske nake,jawahir ta kasa riqe kukanta,ni kaina na kasa controlling nata please......" Da sauri ya buda murfin motar ya fito,sannan ya zagaya ya budewa kaltum,ya riqeta sosai cikin hannunsa suka fara takawa zuwa cikin asibitin,kome zaiyi zaiyi ne saboda jawahir badon mummy ba,don ko sau daya a rayuwarsa baya buqatar sake ganin fuskarta indan ta shine.

Duk wanda yaga mummyn yasa a gargara take,banda gursheqen kuka babu abinda jawahir keyi,shigowar samir gaba daya hankalin mommy ya karkata a kansa,saidai duk yadda taso bude baki tayi masa magana abun ya gagara,'yan maganar sun tafi,kalamanta na duniya sun gama qarewa,sai jawahir ta hau girgizata

"Mommy na yafe miki,ga ya sarakin,kice su yafe mikin.....ki fada musu" gaba daya jikinta ne ya saki cikin yan qananun daqiqu,taja wata qatuwar shaquwa me qarfi,abinda ke alamtawa duk wanda ke dakin cikawarta,bayan likitoci sun duddubata suka tabbatar masu da hakan.

Kuka sosai kaltum itama ta saki,mutuwar bilalunta ta zamar mata sabuwa,mikin dake zuciyarta ya dawo sabo,kama hannun samir yayi ya maidata mota ya zaunar ita da jawahir,ya bar amiru ya kula dasu,ya koma cikin asibitin,ya biya dukka wani bill nata dana sauran jama'ar dake dakin,wanda dama ya saba hakan,kusan dabi'arsa ce,bawai yayi ne kawai don ita kadai ba,yayi ne saboda Allah,yayi ne kuma saboda ranar gobe.

********Cike da farinciki take hada kayanta cikin wani qawataccen akwati,duk da cewa tana qoqarin danne farincikin nata saboda ta yiwa jawahir dake zaune a gefanta kara,wadda a jiya akayi addu'ar bakwai na rasuwar mummy.

Bayan shafe watanni masu tsaho da yawa,sai gashi a safiyar gobe zata sauka garinsu na dinya,zata yi tozali da ummanta,zataga habiban ta,yakumbo indo kawu ado umma suwaiba sai kuma lantana,wadan nan kusa sune mutanen da take muradin gani kaf fadin qauyen dinya,masoyan da bata da tamkarsu,ji take a goben kamar zata tafi saudiyya ne aikin hajji.

"Nayi mamakin yadda kika iya jarumta da qarfin hali.....wadda keda miji kamar ya saraki.....amma kika zauna a wancan lokacin 'yammata na miki farautarsa?,bansan baki da wayo bafa sai da nasan cewa yaya saraki mijinki ne" ta tsinci dakusashshiyar muryar jawahir na fada sanda take zuge jakarta.

sakin aikin tayi,ta juyi fuskarta dauke da fara'a tana kallon jawahir dake zaune saman abun sallah,sanye da hijabi,gefanta alqur'ani ne data gama karantawa,tayi matuqar jinjinawa gami da sarawa dauriyar da jawahir ta nuna,idan ka ganta a yanzu,zaka tsammaci ba itace wadda abubuwan nan suka faru da ita ba,saidai tayi imani da cewa QUR'ANI WARAKA NE kuma ambaton Allah shike sanyawa zukata nutsuwa,tun daga ranar kullum sai kaltum ta yiwa jawahir tofi a ruwa ta bata tasha,daga qarshe sai ya zama ma tofin ne ruwan shanta,bugu da qari da qur'ani take wuni a hannunta,tunda ta samu izifi me yawa a wajen kaltum din,sanda suke musayar karatu da ita,sannan idan xasu kwanta dashi suke kwana cikin wayar jawahir din.

Gefan jawahir ta dawo ta zauna tana murmushi

"Ban taba kawowa cewa akwai randa zatazo da zaya soni ba,ban taba hada kaina dashi ba,saboda nasan akwai tazara me tarin yawa a tsakaninmu,nafi kowa sanin cewa ceto ne yasa ya aureni bawai soyayya ba,amma a yanzu.....banajin akwai wadda zan iya barwa shi" murmushi jawahir ta saki

"Koni bazan bari ki barwa kowacce mace shi ba,saboda ke kikafi cancanta....." Tsagaitawa kadan jawahir din tayi

"Inaji a raina inama ace nice ke?,inama ace cikin tsanani irin naki na taso?,a yanzu rayuwa tayimin kyau kamar haka?" Qwalla ta cika idanunta sanda takai qarshen maganar.

A tausashe kaltum ta dafa kafadarta
"Ki godewa Allah da yayoki musulma,cikin al'ummar annabi muhammad.....ya kuma barki da imaninki.....sannan ya hadaki da mutane irinsu daddyn,da Allah yaso sai ya halicceki akuya ko tunkiya ko kuma zaki,ko ya halicceki kafura,kinga ko iya wannan ni'imace,duk wani yanayi da dan adam yake ciki mai gushewa ne watarana,a shekarun baya sanda nake cikin tsanani nida mahaifiyata da dan uwana,ban taba kawo cewa watarana komai zai wuce ba,to kamar hakane....kema wataran zakiga kamar komai bai faru ba"

"In sha Allah" ta amsa tana dauke qwallarta,sannan ta miqe ta ciro wata jakarta,ta dawo ta zazzageta,kudadene suka fado masu yawa,kusan dukka sababbi ne,saita tura gaban kaltum

"Kudaden break dinki ne da yaya saraki yake bani na baki,tun sanda kika fara zuwa makaranta wadanda baki taba amsa ba,dama ya gayamin gasunan na baki,amma bai sani ba.....ba lallai bane ki amsa,saboda bakison sababbin kudi bakya amsarsu....." Ta qarashe maganar qaramar dariya na kubce mata,tayata kaltum din tayi sannan tace

"Bari na baki labarin abinda ya sanya yake tsokanata har yau" tiryan tiryan ta gaya mata,abun da ya sanya jawahir din dariya sosai,ganin labarin ya sanyata nishadi,sai taci gaba da bata wasu labarai na wautarta sanda take a matsayin kattume,har zuwa sanda wayar jawahir tayi qara ta daga tayi magana ta sakanni sannan ta sauke

"Kije ya samir yana kiranki" miqewa tayi tana laluben hijabinta

"Bari naje na dawo na qarasa baki labaran" harara jawahir ta jefa mata

"A haka ake zuwa turakar mijin?" Saita miqe tana qwace mayafin,ta kama hannunta zuwa gaban madubi,duk da jikinta tashin qamshi yake,don bata jima da fitowa a wanka ba,amma sai da jawahir ta sakeyi mata wankan turare tun daga gashinta har qafafunta

"Duk inda zai shanshana yaji qamshi.....kuma karki dawo min,kawai kice min sai da safe" ta fada tana jefa mata wani farin mayafi mara kauri instead of hijabin data saka dazu.

Sakato tayi tana duban jawahir sanda take komawa saman abun sallarta tana zama

"Amma qamshin nan yayi yawa,zan keta ta falo ne fa,yanzu idan na hadu da daddy ko momma fa nace meye?"

"Haram ne?,wurin mijinki zaki fa,lada zaki samo...."kafin takai qarshe wayarta ta sake tsuwwa

"Ki rufan asiri ki tafi,Allah shine yake sake kira" dariya ma jawahir din ta bata,yadda ta hade hannayenta waje daya tana roqarta,saita yi gaba a hankali ta fice,tausayin jawahir din na sake cikata,ta samu zuciyarta da yi.mata addu'ar samun miji nan kusa da zai zame mata sanyin idaniya itama.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*_DA ZAFINSU_*

*_A TSARE SUKE_*

*_SUN TANADESU_*

*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*

*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*

*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*

*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*

_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_

08184017082

_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107

*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*

63

A bakin qofa ta taras dashi a tsaye kamar wanda aka bawa gadin qofar,cikin wasu Cotton kayan bacci na maza ash colour,qamshinsa ya budade ko ina,iskar damina na baza qamshin daga hagu zuwa dama,fuskarsa tayi wani fresh,duk da qarancin hasken dake sararin samaniya,sakamakon kwantaccen hadarin dake linqaya a saman,wanda yake bada iska me sanyi,me kuma cakude da qamshin qasa.

Birki taja ta tsaya saboda yadda ya cinye qofar gaba daya babu hanyar da zata raba ta wuce,idan ta matsa kuma sai ta raba din to tabbas sai ta fara masauki a jikinsa kafin ta samu wucewar.

Idanu ya zuba mata, Adams apple dinsa na sama da qasa kamar me hadiyar wani abu,daga nan inda yake tsayen yana iya shaqar daddadan qamshinta dake sake ta'azzara yanayin da yakeji dangane da ita a jikinsa.

A tausashe ya cafkota ya kuma yi mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,ya zagaye hannyensa gaba daya ta bayanta,da wata iriyar murya dake shaking yace

"na gode da jan aji.....amma ki sani.....bazan iya jura ba,bazan iya jurar jan ajinki ba,rauni na a kanki yawa ne dashi" ya qarashe maganar yana cusa kansa tsakanin wuyanta zuwa qirjinta,da wani irin zafin nama,wanda cikin sakanni 'yan kadan ya birkice ya kuma birkitata itama,tsaiwa ta gagaresu gaba dayansu,saiya tallafeta ya wuce da ita kai tsaye zuwa bedroom dinsa.

Kyakkyawa masauki yayi mata kan tattausar katifarsa,cike da wani irin shauqin so da qauna,wadda ta bayyana kanta muraran har cikin idanuwansu.

Da zafi zafi ya shiga aika mata da saqonni,kamar zai cinyeta danya,zafafan kisses masu badda hankalin masoyi,daga dama ya maidata hagu,daga hagu ya maidata dama,tun yana yi da ragowar hankalinsa cikin jikinsa.....har ragamar hankalin ta qwace daga hannunsa gaba daya,yaji a ranar a wannan daren yanaso qetare shingen da yake tsayawa a baya.

Ta bangaren kaltum tun tana iya karbar saqonnin da yake aikata mata har suka qetare saninta da hankalinta,jiki da zuciyarta suka fara gaya mata lallai muhimmin al'amari ne zai faru,kafatanin jikinta ya fara rawa sanda hannunsa ya tsallake boarder,tayi caraf ta riqeshi,hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta.

Cak ya tsaya,ya sanya hannayensa duka ya tallafo kanta,yana kallon fuskarta data cakude da hawaye,gashin kanta kuma ya barbazu saman fuskar,sai ya saka hannunsa guda daya ya yaye mata gashin gefe,abinda ya bashi damar ganin sukarta da kyau.

Da wata iriyar kwantacciyar murya me cike da nauyi da kuma taushi,cikin kuma rawar muryar kamar wanda xai saki kuka yace mata

"Dukka jiki da xuciyata sunyi amanna dake........cikin qanqanin lokaci kuma sun cika sun tumbatsa da soyayyarki,ban taba kawowa soyayya me zafi irin wannan tana yiwa mutum kamu kamar haka ba sai a kaina........" Sai yadan rage nauyin da ya aza mata,ya miqe a mugun kasalance ya zauna sosai bayan ya juya mata baya

"Duk yadda nakai ga dokanta na kasance tare dake.....na maishemu abu daya,bazan iya aikata komai ba saida gamsuwarki......,zan baki lokaci ki nutsu har cikin zuciyarki dani" saiya fara jan jikinsa yana saukowa daga saman gadon yana layi ya nufi bandaki,ta bishi da kallo a sace,tana jin wata soyayyarsa na tsarga mata,dama haka yake?,saita cusa kanta cikin pillow cike da kunya.
Chapter 109 · 0% Book details