← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 117

Sashe 85

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka tayo gaba daya,sosai taji dadin jikinta,tana shiryawa tana tuna yadda ya dinga treating nata jiya with care,saidai kuma ya haifar mata da feelings da wasu abubuwa masu wuyar mantawa cikin zuciya,saboda wannan shine karon farko da suka taba zama kusa da juna very close irin haka,wannamn shine karo na farko data taba kallon fuskarsa sosai,fuskar da take cike da kwantaccen saje mai duhu sosai,wanda ya qawata ta ya kuma qawara labbansa masu tudu da suka yiwa fuskarsa kyau.

Tsaf ta gama shirinta kamar ba ita tayii fama da ciwo jiya ba,tayi cas cikin uniform din da akullum suke mata kyau kamar kayan gida,tsai tayi gaban madubi tana kallon fuskarta,sai ta sanya hannu tana shafar gefan fuskarta tana jiya yadda yayi.mata jiya,idanunta ta lumshe murmushi yana qwace mata,sai kuma ta bude idanun da hanzari sanda taji alarm na agogon ya buga qarfe bakwai.

A kitchen ta samu su baba,suka gaisa a gurguje,ta karbi wani daga cikin breakfast din daya zama ready ta soma karyawa dashi,baban na tambayarta ya jiki tace mata aita samu sauqi,don babu wanda yasan ma ciwon da tayin a jiyam cikin gidan daga ita saishi.

Tea din data kurba ya tsaya mata a wuya sanda taji tattausan muryarsa na magana cikin kitchen din,cikin girmamawa baba ke bashi haqurin rashin kammaluwar abincin da wuri

"No,no need to worry.....zanyi break a waje" ya furta maganar yana sauke idanuwansa akanta,duk da baya ganin fuskarta yasan cewa itace.

Ajjiye cup din tayi,ta juyo a hankali,kallo daya tayi masa tayi qas da idanunta,yau shigar ta fari ce,suit ce wadda ta amsa sunanta three in one,saidai komai nata fari ne kamar yadda shima duk abinda ya saka a jikinsa yake fari,wataqa hakan yana da nasaba da kasancewar ranar juma'a ce,ba qaramin zama shigar tayi a jikinsa ba,itakam ba zata iya cewa ga wasu kaya da ya saka basuyi masa kyau ba,ba tare data bari sun hada ido ba tace

"Ina kwana"cikin rusunawa

"Lafiya lau" ya amsa mata yana juyawa tare da fadin

"Muje na saukeki,ya kirani ya gayamin bazai samu zuwa yau ba" da sauri ta bi bayansa bayan ya fice tana yiwa baba sallama.

Cikin motar saukar numfashinsu gami da qamshin turarukan jikinsu,jinta take gaba daya a takure,wani kwarjini yake mata matuqa

"Ya jikin naki?" Sai data dan qwato numfashinta sannan ta amsa

"Na samu sauqi" shuru na second biyu ya sake cewa

"Ma sha Allah,but idan kikaji ko kikaga wani abun daban kiyi magana,yace a gaya masa zai duba"

"In sha Allah,na gode" ta furta qasa qasa,kansa kawai ya gyada yana ci gaba da tuqin,amma kuma wani abu yana dawo masa a kansa shima,wanda daga jiya zuwa yau mutuwar jikin da yakeji bata sakeshi ba,har i yanzu babu wani qwaqwwaran kuxari tattare da shi,har ya sauketa makarantar,ta jawo jakarta ta rataya,sai kuma tace dashi

"Don Allah inason inje gidan mummy....." Dubanta yayi

"Kiyi me?,suma daxu sun tafi azare,su biba kawai suka rage"

"Abubuwana na manta nakeso na dauko" kamar ya tambayeta wanne abu sai kuma ya fasa,ya gyada kai yana cewa

"Is okay" hannu ya zura aljihun gaban motar ya ciro kudi ya miqa mata,kudin ta kalla ta kalleshi,ta girgiza kai alamun a'ah,yadan matse fuska kadan yana dubanta

"Jawahir ta gaya min bakya karbar wani abu cikin kudinki na wajenta....me yasa?" Kai ta kada,tana jin zuciyata na karyewa,duk sanda tatuna da cewa ummanta nacan cikin tsananin buqatarsu,sai taji tamkar taci amanarta idan ta karba tayi amfani dasu taji dadi alhali umman nata nacan a wani hali da batasan wanne iri bane

"Ohhhh....na manta fa,bakyason sababbin kudi kudi ko?,to amma fa.....wannan mijinki ne ya baki su ko?" Furucin nasa ya sanyata daga kai da hanzari zuwa gareshi,cikin sa'a suka hada idanu,kunya ta sanyata sadda kai tare da kubucewar murmushin da bata shirya masa ba,sai yaji dadi a ransa,yayi hakanne don yaga murmushinta kuma haqansa ya cimma ruwa,a taqaice yace

"Take it" hannu biyu ta saka ta karba

"Na gode,Allah ya biya" tayi maganar sanda ya sake kunna motar yana gyada mata kai,ta juya ta nufi ajujuwansu.

"Mijinki" kalmar data dinga yi mata amsa kuwwa kenan cikin kunnuwanta,da qyar ta samu ta kori sautin muryar sanda aka gama raba musu question paper ta fara amsa tata.

Tana daga dalibai na farko da suka gama amsa tambayoyinsu suka kuma yi submitting,saita zauna daga bishiyar dake gefan ajinsu tana jiran fitowar saliha.

"Anya ba umara ko hajji aka biya miki ba?" Ta tsinci muryar saliha daga saman kanta,saita daga kai

"Me kika gani?" Kaltum ta tambayeta tana matsa mata wajen xama

"Tunda kika shigo aji kike murmushi,yanzun kuma tunda na fito nake daga miki hannu amma baki ganni ba" husna dake tsaye tana maida question paper Jakarta tace

"Indai ko hakane wannan sign ne na falling in love wallahi,irin farin shigar nan,kin manta alamunsu ne?,yawan tunanin da yawan murmushi kai kadai?" Dubanta sosa kaltum tayi,maganar husna kusan tafi jan hankalinta,me husna takeso tace?,indai ko ta fahimta wani abu,lallai husna dince tafi cancanta tayi mata tambayar da take damun ranta.

50
DZ

Wani littafin ta sake karba wajen salaha,tanaji suna mata tsiya amma batabi ta kansu ba,ita kadai tasan yadda take qaruwa da karatun da takeyi din,wanda ya haska mata abubuwa da dama

"Husna muje tare mu taru napep,nima yau mai daukan nawa baya kusa" kaltum tace da husna,saida husnan ta tsaya ta siya agwaluma daga bakin makarantar sannan suka soma takawa zuwa bakin titin

"Nikam husna.....wata tambaya nakeson yi miki"

"Duk yadda kike ja kaltum?,kece fa kike daukan 1st position a ajinmu duk term" kafadarta kaltum ta daka tana murmushi me kama da dariya

"Ke dalla,ba akan karatu bane,wannan karatun kun fini ilimi ta fanninsa" murmushi tayi mata itama tana gyara saqalen jakarta

"To ina jinki,ai wai don karki qureni ne" sukayi dariya gaba daya,sannan shuru ya biyo baya,kaltum din cikin ranta tana juya yadda zata gabatar mata da tambayar,tsahon wasu mintuna sannan tace

"Asa misali kece kika tashi cikin rayuwar rashin wadata,baki da ilimi kyau ko arziqi,kwatsam sai Allah ya kawo wani kyakkyawan matashi,wanda ya fiki kyau kudi ilimi dama wayewa nesa ba kusa ba,irin nesan nan can can can,kawai tausayinki yasa ya aureki,yazo ya ajjiyeki a gida,ba abinda ke hadaku,kuna zaune kamar yaya da qanwa......"

"Wai,wanann shi ake kira da tsintar dami a kala" husna ta katse kaltum na tare data bari kaltum din takai qarshen maganar ba,tana ta murmushi tare da sake bawa kaltum hankalinta.

,ganin yadda husnan ta bawa zancan muhimmanci hakan ya bata nutsuwar ci gaba da magana

"A hankali kuna zaune kika fahimci yadda mata ke rububin sonshi,da kika lura da kyau,sai kika gane bayan dukka wadancan siffofi.....yana da kyawawan dabi'u kuma"

Hannayenta sama husna ta daga

"Wallahi ta fadi gasassa.....wannan mata idan nice sai inda qarfina ya qare wajen janyo hankalinsa ta dukkan wata hanya data dace,duk namijin da ya hada wadan nan siffofin tabbas babu shakka ya isa,ya kuma cancanci a soshi,rasashi kuma babbar hasara ce" maganganun da suka sanya kaltum nazari kenan,tayi shuru tana sauraren yadda husna keta wassafa kanta cikin lamarin har suka qaraso titi.

Tsaki yaja a hankali yana rufe file din gaban nasa,tare da dora bironsa akai,ya maida bayansa ya jingina da kujerar yana relaxing a jikinta,kana ga furzar da iska me dumi daga bakinsa,a hankali kuma ya soma juya kujerar daga hagu zuwa dama,daga dama zuwa hagu.

Tun daga lokacin har kawo yanzu ya kasa jin qwarin jikinsa kwata kwata,yanajin kowacce jijiya ta jikinsa ta zama weak,ya dunqule hannunsa waje daya kamar wanda ya boye wani abun yana kallon hannun,jijiyoyin dake tsintsiyar hannun sun tashi rada rada,har yanzu yana iya tuno laushi da dumin fatar cikinta,tun a lokacin jikinsa ke shaida masa da matsala,amma burinsa na ta samu relief na pain din yasa yaci gaba da abinda yakeyi.

Idanunsa ya lumshe,saiya dinga gano fuskarta wadda bayan ta gama jigata bacci ya dauketa har sai da kanta ya karkace,shi ya gyara mata kwanciya amma har ya gama yabar dakin batasan anyi ba.

A hankali aka tura qofar, secretary dinsa ya bayyana yana shaida masa neman izinin shigowa da fawwaza keyi,shuru ya danyi,sam baison hayaniya yau din,a niyyarsa yace ya shaida mata yana da ayyukan da yake dubawa,kuma suna da muhimmanci da kuma buqatar nutsuwarsa,saidai kafin yakai ga furtawa har ya hangi fawwazan tsaye daga bayan secretary din,da alama a shirye take ta shigo koda bai bata dama ba,don haka yace

"Ok, let her" ya fada yana tura kujerarsa baya,sannan ya miqe tsaye yana zuba hannayensa a aljihun wandonsa kafin daga bisani ya fara takawa cikin nutsuwa zuwa sashen da fridge dinsa yake.

Tunda ta shigo ta kasa zama,ya bata baya amma kallo take qare masa,tako ina samir din yakai namiji,tana jin sonsa yakai mata ko ina cikin rai da rayuwarta,amma ta fuskanci har yau ya kasa gane hakan.

A duk sanda zata dauko maganar saiya sako wani abun da zai kauda gaskiya da kuma qarfin maganar a ranta,ta rasa me zata masa ya tabbatar masa da dukkan abinda take fada da nunawa a kansa gaskiya ne?,tun tana ja masa aji da kuma shan qamshi,har ta daina ta sauko,da a tunaninta baiwar kyan da Allah yayi mata da iya gayunta kawai sun isa suja mata ra'ayin saraki,saidai kuma a hankali ta gane cewa tayi bahagon tunani ta kuma canki kuskure.

"Have a set" ya furta bayan ya juyo dauke da kwalin lemo da kuma cup yana nuna mata empty kujerar dake gaban table dinsa,saita dauke kanta a hankali ta qarasa ta zauna.

Gaban kujerarsa ya tsaya ba tare daya zauna ba yace

"Allah yasa lafiya" yana dan kurbar lemon kamar wanda aka yiwa dole,fuskarta fal da damuwa ta girgiza kai

"Ba lafiya ba samir,kuma babu lafiyar sam a tattare dani?" Dukka girarsa ya dage bayan ya dakata da shan lemon,abinda yayi masa kyau sosai

"Me ya faru kuma?" Kai take kadawa tana hadiye wani abu
Chapter 85 · 0% Book details