← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 117

Sashe 73

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nutsuwa yake takowa zuwa cikin gidan,sanye da wasu blazers ruwan sararin samaniya,sunyi matuqar haskashi da qara masa kwarjini,jikinsa na fidda qamshin turarensa da koda yaushe,zatinsa na tsaho da murjajjen jiki ya fito sosai,hannunsa daya dauke da wasu takardu dake qunshe cikin files dinsu.

Cikin lallausar muryarsa yayi sallama cikin falon,daga can inda take tsaye gaban katafaren teburin cin abincinsu da taje dinan kofunan da biban tace ta kawo ta jiyo kamar muryarsa,duk da bata tantanceta sosai ba,saita waiwaya a hankali tana amsawa.

Amsawarta yaja hankalinsa yakai duba inda take,saita tako a hankali riqe da kofunan,ta iso gabansa ta durqusa qasa tana gaidashi,cikin yanayin kulawa yace

"Lpy alhmdlh,ya karatun?" Dan murmusawa tayi kadan,karon farko da yaga fara'arta tunda yake ganinta

"Alhamdulillahi" ta amsa masa

"Ina jawahir" sai data kalla sashen dakinsu sannan tace

"Tana ciki"

"Kiramin ita" ya fada yana dan zama hannun kujera,tace to tana miqewa da hanzari.

Da sallama ta tura qofar dakin,tsaye ta samu jawahir gaban tarin kayan shafarta,hannunta riqe da wata zungureriyar roba,ta amsa tana ajjiye robar.

Tun kafin tace wani abu jawahir din ta soma magana

"Fada kawai kikeso muyi dake kaltum,kayan nan har yanzu banga kina amfani dasu bafa,yanzu man wanke kan nan banga alamar kin taba amfani dashi ba" dan murmushi tayi,batasan me yasa ta damu da lamuranta da yawa haka ba

"Kiyi haquri jawa,ki fara zuwa wajen....."sai kuma tayi shuru,don batasan da wanne suna zata kirashi ba,daga bisani ta yanke tayi kiransa da yaya kawai

"Ok,ina zuwa" ta fada tana juyawa ta nufi qofa da sauri.

Sai data fice itama tabi bayanta don kaiwa biba kofunan.

Kamar ko yaushe ta gaida samir din cikin girmamawa,ya amsa mata shima cikin kulawa

"Idan baki komai ki shiga ki gyaramin sashe na"

"To yaya" ta amsa tana masar muqullin bangaren nasa,shi kuma ya wuce zuwa sassan daddy.

Kitchen ta duba bata samu biba ba,saita wuce zuwa dakinta don ta gaya mata takai.

A nutse ta daga labulen dakin,idanuwanta suka fara sauka kan biba dake tsaye riqe da wani dan qaramin hoto a hannunta,wanda bata iya hango wanda ke ciki saboda da kadan ya wuce girman passport.

Sallamar kaltum yasa ta soma qoqarin boye hoton,a hankali ta qarasan gaban biban tana cewa

"Nakai kofunan kitchen,amma saina taras bakya nan,nama wanke na mayar dasu inda suke" kai ta gyada mata ba tare da tace komai ba,sai kaltum ta lura da hawayen dake idanun biban da take qoqarin gogesu,cikin mutuwar jiki tace

"Baki da lafiya ne?"kai ta gyada mata

"Kaina ne yake dan ciwo kadan,shi yasa na taho na huta" duka sai kaltum taji babu dadi

"Ayyah,sannu,Allah ya sawwaqe,gwara ki huta kam,Allah yasa kaffara"

"Amin"ta amsa tana sake goge idanunta da kyau,tayi kamar zata zauna tare da ita,amma biban tace babu komai taje,itama yanzu zata fito,tunda ciwon ba sosai bane,bai matsa mata ba.

*_SHIN KINSAN CEWA AKWAI RAMUWAR SALLA A KANKI ME JININ AL'ADA?_*

________________________________

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

43

Tsahon wasu mintuna yana duqe gaban daddyn bayan ya gaidashi ba tare daya maido masa amsar gaisuwarsa ba,kamar bazai amsa din ba,har sai daya gama kurbe baqin ruwan shayinsa sannan ya dubeshi

"Sai yanzu ka damu dani daka ganni?,sai yanzu ka damu kasan lafiyata?"

Ƙas yayi da kansa,don baisan da wanne yare zai wanke kansa ba,iya yinsa dukka yayi ya sameshi a waya amma abun yaci tura,baisan me yasa hakan ba

"Duk dai tsiya baka da mahaifi sama dani,kuma ba'a cazawa tuwo suna ko?"

"Tuba nake" ya fada cikin ladabtacciyar murya,yana zaune har daddyn ya qarashi fadansa yadda ransa yayi masa,duk da qoqarin dakatar dashi da mummy keta yi,saiya hada harda itama cikin fadan.

Sai daya tabbatar ya gama sannan ya sake gaidashin,ya amsa sama sama,sai ya miqe ya lalubi kujera ya zauna bayan ya aje masa file din hannunsa a gabansa

"Wannan file din dukka lissafinmu na qarshen shekara ne da dukka bayanan komai da komai,zaka sanya hannu ne asanya cikin documents na kamfani".

Baiko daga kai ya duba file din ba,yana zuba wani ruwan tea din a kofi yace

"Ka dauka ka baiwa fawwaz ya duba ya sanya hannu"

Banbarakwai yaji lamarin,ta yaya fawwaz zai shiga cikin lamari irin wannan?,ta yaya babban sirri irin wannan zaice a baiwa fawwaz din ya saka hannu?,bayan abune daya shafi daddyn?,share dinsu ne shi dashi,me ya shafi fawwaz banda yayi aiki a biyasa kowanne wata kamar kowanne ma'aikaci,ya zaci zaiji mummy tace wani abu,amma baiji tace komai ba,saiya dauke idanunsa daga kan file din zuwa fuskar daddyn

"Amma kamar ba hurumin fawwaz bane,wannan abune daya shafi masu share a kamfani"

"Kudin waye?" Daddyn ya fada kansa tsaye yana duban qwayar idanun samir

"Naka ne,Allah ya huci zuciyarka" saiya miqe ya qarasa inda ya ajjiye file din ya dauke

"A huta lafiya" ya fada yana nufar qofa

"Son,yau da wuri haka?,abincin fa?"

"Zanci a waje mummy"

"Jirani,ko wani abun sassauqa a hada maka ka tafi dashi" ta fada tana miqewa da hanzari.

Hannu tasa ta amshi packaging da tasa aka yiwa samir din tana miqa masa

"Kaga bance komai ba kan batun bawa fawwaz file ya saka hannu ba ko?" Tayi tambayar tana miqa masa,yasa hannu ya karba ba tare da yace komai ba,tasan kuma zaiyi wuya yace din,don ta karanci fushinsa da bacin ransa fiye da kowa

"Kayi haquri son,daddynka ya fara zargar goya maka baya akan komai,banason wannan rashin jituwar dake tsakaninku taci gaba da dorewa,gudun kada takai har kan 'ya'yanka,shi yasa na yanke shawarar yin shuru kan wasu abubuwan,badon inason hakan ba,sai don babu yadda zanyi" kai kawai ya gyada mata yana lumshe ido,tare da qoqarin hadiye bacin ransa,saiya juya zai soma barin wajen,tayi hanzarin sake tsaidashi,tana ganin wannan wata dama ce gareta daya kamata tayi amfani da ita.

"Son" ta sake kiransa,saiya dakata ya kuma waiwayo,takawa tayi zuwa inda yake tsayen da kanta,fuskarta na nuna russuna da kuma alhini.

Dukka nutsuwarta ta tattaro tana dubansa,irin duban da zai gaya masa cewa dukka zancan da zata furta na gaske ne,shima ita yake kallo,da alamu kuma ya tattara mata dukkan hankalinsa ita yake sauraro

"Akwai abu guda daya da mahaifinka yake ra'ayi da kuma buri,wanda aikatashi zai zama silar warwarewa,dama dawowar dukkan wata fahimta da jituwa a tsakaninku" shuru ta danyi kafin taci gaba

"Mahaifinka bashi da burin daya wuce ka auri jauhar 'yar abokinsa,me zai hana ka sadaukar da wannan farincikin zuwa gareshi?,ina da tabbacin hakan zai sake kawo qauna da jituwa tsakaninku.....amma kaje kayi tunani,burin kowanne da ya samu qauna da kulawa ta mahaifinsa,kana da wannan damar"

Zaman irin na dirshan tayi gaban professor,irin xaman da idan tayi shi yasan tabbas akwai babbar magana da takeson yi dashi,idanunta cikin nasa,cikin wani laushi ta soma magana dashi

"Ko kusa ko alama bana jin dadin irin wannan mu'amalar dake gudana tsakaninka da samir,raina baya min dadi sam,ko babu komai kusan nice a tsakaninku,kuma samir tamkar dan dana haifa nake jinsa,kaga kuwa ko meye zaya sameshi hakan bazai taba yimin dadi ba"

Sosai yake kallonta,yake kuma yaba kyan hali dana zuciya irin nata,tsahon shekarun ko sau daya bai taba ganin ra kwarewa samir baya ba,komai wuya kome dadi tana a gefansa,saiya zauna sosai ya gyara zamansa

"Babu abinda yake hadani da danki illa taurin kai da kafiya,da kuma ganin ko meye ta yankema rayuwarshi nashi shine dai dai,kome na yanke a rayuwarsa yana kallons a matsayin opposition na ra'ayinsa,ni kuma bazan zauna yana yankamin da gindayamin dukka sharudda da yaso ya kuma ga dama ba,don bashi ya haifeni ba,nine na haifeshi" shuru tayi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta dago ta kalli professor

"Babu abinda yake zama cikasa hankali da kamalar dan adam irin aure,koda kuwa nutsuwarsa ake da buqata,tofa la shakka aure shike gyara mutum....inajin option daya kuma hope daya muke dashi akan samir....shine aure,aure ya kamata kayi masa"

Hannuwansa ya wara kafin ya maida bayansa ya jinginar a jikin kujera

"Ya isa ya yiwa kansa aure ai,ni meye nawa a ciki?" Kai ta jinjina wani abu na taso mata tana danneshi,tana tuna wani abu daua faru shekarun baya da suka shude,wata magana shigen wannan data taba faruwa,ba shakka duk inda take tunanin nasararta bata kai ba tama shallake nan,saidai a yanzu kuma ba irin wannan amsar take buqata daga bakin daddyn ba,tana so ne ya shiga lamarin tsundum fiye da kowa.

Kanta take kada masa kafin ta sake cewa

"A'ah,daddy wannan sam ba kalmar data dace ta fito daga bakinka bace,kanason ka sake jawomin sabuwar tsana daga mutane ire iren hajiya qarama?,wannan aikinka ne,dole ka sanya hannu,koda kuwa shine abu na qarshe da zaka yiwa danka,ba'a sakarwa yaro garma" saita dakata tana karantar yanayin fuskarsa na wasu sakanni kafin yace

"Kin fiya damuwa da lamuran samir da yawa....."

"Wa nake dashi sama dashi?" Ta tari numfashinsa fuskarta dauke da murmushi,sai yayi shuru ya zuba mata idanu,tana sake burgeshi,tare da sake jinjina mata,yana ji a ransa lallai ta cika macen qwarai,duk da har yanzu yana jin wani emptiness can qasan zuciyarsa,wanda har yau wannan gurbin ya gaza cikuwa.
Chapter 73 · 0% Book details