Sashe 36
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jawahir itace ta soma serving din kowa, mummy ta dubi najwa
"Tayata mana saboda kufi sauri" hakanan taji kawai kaman mummy ta rage mata qima wajen jauhar,tasan yarinyar sarai,yar hutu ce kuma 'yar gata ta qarshe,komai yi mata ake,cewa tayi serving nasu kamar wani ragin qima ne a wajenta,haka dai ta miqe saboda babu damar musu saboda idanu ta soma zuzzuba abincin a yangance,tanayi kamar ba zata kai ba,yayin a jawahir ke komai bisa karasashi da walwala.
Cikin mintuna qalilan kowa abincinsa ya isa gabansa,kowa ya soma qoqarin kaiwa cikinsa,banda samir da yaji sam zaman wajen bai wani yi masa ba,karo kusan na uku kenan suna hada idanu da yarinyar,saita sake masa murmushi,yana qoqarin maida mata koda shi nashi murmushin baikai zuci ba,yana ganin kawai idan ya maida matan kamar ya girmama baqin daddyn ne.
Game dinsa daya saba yi lokaci bayan lokaci idan kansa ya dauki zafi musamman wajen aiki ita yake bugawa,duk abinda ke faruwa hankalin mutum biyu na tare dasu,daddy shi da mummy,duk suna ankare da samir din,tsayin mintuna kusan goma
"Am son" muryar mummy ta ratsa kunnensa,saiya cira kansa a hankali
"Ko zaku koma cikin parlour kaida jauhar.......kaman sai tafi sakewa a can taci abincin sosai ko?" Maganar mommyn ita ta sanyashi maida qwayar idanunsa kan yarinyar da suke kira da jauhar din,tana cin abincinta yadda ya kamata,duk da batayi nisa a cin ba,so baiga wani abu da zaisa su kebe ba kuma,saidai kuma bazai iya musawa mummyn ba,don haka muryarsa can qasan maqoshi ya furta
"Ok" dai dai sanda murmushi ya kubcewa jauhar din,da idanu tace da mummyn
"Thank you" saita gyada kai kawainta dubi jawahir
"Jawahir saukar musu da abincin qasa" da murmushi ta miqe tana dan boye dariyarta
"Ok mummy" idonta kan yayan nata,suna hada idanu saita waske,hakan ya gaya masa da wata a qasa,shima basarwa yayi yana miqewa,cikin takunsa mai cike da wata nutsuwa data cakuda da qasaitar data gadar masa da sunan saraki ya sauka daga wajen.
Kujera daya mai cin mutum biyu ya zaba ya zauna,dai dai sanda itama ta qaraso tiqe da cups guda biyu data cika da lemon inibi,gabansa ta qaraso idanuwanta a kansa tana yana kamewarsa da ginshira irin tashi ta miqa masa cup din,sai daya kalleta ta jefeshi da murmushi,yasa hannu ya karba,qasa qasa ya furta
"Thanks" saiya aje cup din gefansa hannun kujerar da yake kai,ita kuma ta koma a hankali ta zauna kam kujerar dake fuskantar tasa,har yanzu idanuwanta a kansa,tana qoqarin karantarsa.
Komai najwa ta jere musu,daga qarshe ta tsiyaya coffee mai zafi data dafa saboda yayan,kuma taga baisha ba ta miqa masa tana murmushin dai,harara ya jefe mata data sanyata kintsa bakinta,ya miqa hannu ya amsa cup din,ta juya tabar wajen,sanda shi kuma ya gyara zansa sosai saman kujerar ya aje wayarsa gefe ya fara surbar coffee din a hankali.
"Hi"ya kuma ji ta ambata,saiya dora idanuwansa saman fuskarta,hakan ya sanyata sauke nannauyar ajiyar zuciya a boye sannan tace
"Am jauhar,daughter of honorable bukhari mustapha...... Muhammad samir isn't it?" Kansa yadan kada yana dubanta,saita saki murmushi,sannan ta kurbi lemon hannunta
"Nice meeting you"
"Me too" yayi qoqarin fada,kai ta sake jinjinawa,shuru ya sake ratsa tsani,kafin daga bisani ta gyara zamanta,ta dora qafarta daya saman daya
"Kasan dalilin da yasa mummy tace mu sauko nan.......?" Kafadunshi ya dage kafin ya girgiza kai,duk da cewa ya jima da fuskantar komai,saita sake gyara zamanta sosai tana fuskantarsa,bayannta hade tafukan hannayenta waje daya
"Dukkaninmu iyayenmu manyan mutane ne,munyi ilimu me zurfi.....mun samu gata da kulawa daga garesu,kasantuwar mu yaran farko a wajensu nida kai gaba daya....inaga abun zaiyi kyau idan muka fuskanci juna,muka kuma qulla alaqar auratayya,kamar yadda yake buri da mafarkin iyayenmu"
D/Z
20
*_littafin kudi ne,kiji tsoron Allah kada ki mana sharing dinsa,ki guji cin haqqin wani,yadda bamu cutar da ke ba kada ki cutar damu,ki biya naki ta wadan nan numbers din ki karanta cikin aminci_*
08184017082
Ko kuma
09134848107
*SHIGA LINK DINMU NA WATPAD KIYI FOLLOWING DINMU DOMIN SUMUN TSOFAFFIN LITATTAFAN ZAFAFA*
@ *ZAFAFABIYAR*
_______________________________
........tako ina mun dace da juna" takai qarshen maganar tasa ne hadi da fitar bugun zuciyarta,kaf tsayin rayuwarta wannan shine karo na farko data taba magana irin wannan da wani da namiji,kowanne lokaci suke qoqarin kawo kansu zuwa gareta,da furta kalaman da zasu sanya ta aminta dasu,sai gashi a wannan karon reshe ya juye da mujiya,dan mutan azare ya wargatsa mata record.
Murmushin gefen baki ya fitar,tako ina ta kuma kowacce fuska baiga dacewar da take magana a kanta ba,tana da wasu siffofi daya zuwa biyu da yake ra'ayin matar da zai aura ta mallaka,amma akwai kuma tarin abubuwa da nauyinsu ya haura muradin siffofin da suke tare da itan
"Bamu dace da juna ba" yayi maganar kanshi tsaye yana ajjiye mug din hannunsa idanuwansa a kanta
"Like how?"ta fada cike da mamakin yadda ya iya kallonta kanshi tsaye ya gaya mata hakan,babu wani kwane kwane ko kara
"Babu ta inda na hangi dacewarmu dake,alaqarmu ba zata taba bada wani abu me armashi ko kuma sakamako mai kyau ba.....dan taqadirin misali da nake ganin zaki fi fahimta dashi shine....ni dake din tamkar wasu halittu ne dake rayuwa bisa duniyoyi mababanta....."saiya miqe tsaye yana duban agogonsa,akwai sauran mintunda suka kusa ashirin kafin akirayi sallar magariba
"Wannan itace tattaciyar gaskiya mara algus.....am sorry if i hurt you" daga haka ya soma takawa ya nufaci qafa fita,saita bishi da kallo ba tare da tasan meye abu na gaba daya dace ta aiwatar ba.
Cikin qididdigaggun sakannni ya bacewa ganinta,ta sauke jiyar zuciya tana janye idanunta,duk da cewa martani ta samu mara dadi daga gareshi,amma sai taji zuciyarta bataji haushinsa ba,saima burgeta da yayi,saita maida bayanta tana mai jingina da kujerar tana fitar da iska daga bakinta.
Koda ya fito din bai tsaya cikin gidan ba sai daya isa waje,hakanan ya samu kansa da yin tattaki cikin layukan unguwar tasu,iskar dake tafe da duhun magariba tana kadashi,duk shaqa daya da zai mata sai yaki ta fita ne da sauram guntuwar damuwa ko matsewar zuciya daya samu kansa a ciki,ya fahimci wannan duka plan din daddy ne,saidai babban abun tambayar,kamar mummy ma wannan karon tana goya masa baya.
Bukar mustapha,idan ya tuna dai dai,kamar shine mutumin da daddy ya shaida masa zaya bawa kamfaninsa babbar kwangilar da kamfanoni da dama suke farautar samunta,hakan na nufin zaiyine saboda diyarsa?,ko daddy nason ya amshi diyarsa a matsayin tukuici na kwangilar da zai sama masa?,wannan tunanin ya sanyashi ciro wayarsa da sauri,ya fara laluben number ezikwe.
Tun daga nesa idanuwanta da zuciyarta ke gaya mata shine,bata samu yaqinin haka ba sai da suka sake matsowa kusa dashi,samun kanta tayi da jan mayafin basma,wanda saura kadan ya zame daga kanta,tayi hanzarin dafeshi,ta kuma juyo a fusace cikin fada tace
"Bakya gani ne hala mubina zaki ciremin mayafi tsakiyar hanya"
"Sorry..... sorry don Allah,duba can da Allah,kamar me sanyi nake hangowa,mutumin afra" dubanta ta mayar wajen,ta koma ta kalli mubina
"Shine mana"
"Oh god" mubina ta fadi,duk yabi ta rude
"Meye kike haka mubina,kinyi hauka ne?"ta fada ganin yadda mubinan ke mazari,ta kuma tafi kanta tsaye,dakatawa tayi sanda taji abinda basma ta fada
"Sorry,wallahi rudewa nayi,kinsan tun ranar zuciyata bata huta da tunaninsa ba,duk sanda na fita kuma zuba ido nake ko zan dace"
"Hakane,amma kuma saiki sanya nutsuwa ko?"
"Yes" mubina ta fada tana daidaita numfashinta
"Muje to" ta fadi cikin dakiya da qwarin gwiwa,fatanta idan sunje wucewa ta gabansa ya ganta,har yayi qoqarin mata magana ma.
"A shirya dukka takaddun da suka dace,gobe zan shigo da sassafe,banason kowa yasan da shigowata,zan zauna mu rubuta takardar nema kwangilar nan"
"Amma sir.....ina cewa kana da hanya mai kyau da aka tabbatar maka da samun contract din.....akwai kamfanoni da yawa da suke a buqata,ko dazu munyi hirar da daniel,babbar kwangila ce,hakan yasa masu so sukayi yawa fiye da yadda ake buqata" ya fada da gurbataccen turancinsa,iska samir ya furzar
"Na sani,kawai kayi yadda nace din" yakai qarshen jimlar idanunsa na sauka akanta,bugun zuciyarta taji ya qaru fiye da dazu,sai tayi qoqarin aika masa da murmushi,saidai bisa rashin sa'a kansa taga ya dauke,babu wata alama data nuna ya taba sanin fuskarta a rayuwarsa,duk kuwa da cewa sun hada idanu dashi,har kuma suka gota bai waiwayi sashen da suke ba,bare ta sanya ran ya ganeta.
Kamar zata saki kuka sanda suka giftashin saita dakata tana duban basma
"Wannan wanne irin bad luck ne basma,kinga fa,kamar bai taba ganinmu ba"
"Komawa zakiyi kenan kiyi masa bayanin kanki?"kai ta kada alamun a'ah,tayi gaba zuciyarta na gaya mata abinda ya dace tayi,tunda dai har ta ganshi cikin unguwar,zuciyarta dama gangar jikinta na bata lallai tabbas nan ne unguwarsu,indai ko hakane to ta kwana gidan sauqi.
Bai dawo gidan ba sai wajen tara na dare,zuwa sannan baiga kiran kowa ba,wala'alla saboda kashe wayarshi da yayi ne,koda ya dawo sashensa ya wuce kai tsaye ba tare da ya nemi kowa ba,yayi relax saman sofa yana maida numfashi yaji an tura qofar dakin an shigo,yana daga kwancen ya wulga idanunsa bakin qofa,wanda yaga yana shogowar ciki ne yasa ya miqe sosai ya zauna,shigowar daddy bangarensa wani baqon al'amari ne,wanda baifi a qirge adadin lokutan daya taba shigowar ba.
"Barka da warhaka daddy" hannu ya daga masa,fuskarsa a dinke tsaf tamkar bai taba dariya ba
"Kai za'a yiwa barka da kuma sannu gaba daya,samir.....kayi qoqari kaga ka watsa min qasa a idanu,ka kuma nuna rashin muhimmancina kaji" daga haka bai qara ba ya juya abinsa ya fice,maganar data sanya samir din cikin tunani,ko meye dole yayi qoqari yabi dukka abinda daddyn yace har baqin su gama zamansu a rabu lafiya,indai har abinda jauhar ta fada daxun haka yake......to shine abu guda daya da baiga hanyar bullewarsa ko dai daituwarsa ba.
Hutawar da yayi niyyar yi ya fasa,saiya fidda kayan jikinsa ya shige toilet don ya watsa ruwa,ya wuce zuwa cikin gidan daddyn yaga gilmawarsa ko hakan zai sassauta zuciyarsa.
**********Sake riqe gyada me gishirin data siyo tayi da kyau sanda take tunkaro saronsu gabanta na dan faduwa,daga sanda auwalu ya dawo gifansu gaba daya ya zamana bata da wani sauran nutsuwa,duk sanda zata fita da dare koda yammaci cike da fargaba zata shiga,hakanan cikin fargaba zata fita.