← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 117

Sashe 103

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuru ne ya ratsa dakin bayan sun gama duba komai shi da daddy,sai system din da suka sanya a gaba suna kalla

"Inaji a raina dama akwai babban qalubalen daya tunkaromu......kabi komai a hankali.......mu qara kaifin addu'ar da mukeyi.....karka nuna maganar ta tada maka hankali,kaci gaba da rayuwarka kamar ko yaushe,bincike kuma ya gudana ta qarqashin qasa" ajiyar zuciya mai nauyi ya saukar,ya samu fiye da rabin nutsuwa cikin ruhinsa,lalllai kudi aka fitar musu maqudai,kusan fiye da rabin jarin kamfanin,amma shi wannan ba shine damuwarsa ba,tunda cikin abinda Allah yayi masa zai iya maida gurbin kudin cikin tashi lalitar,abinda yake tsoro.....irin fahimtar da daddy xaiyi masa,kada wannan ya jawo yarda da amincin da ya fara samu daga gareshi,saiya rufe idonsa kadan,qwaqwalwarsa na lissafa masa mutanen da xasu iya kasancewa suspect.

A rikice mummy ta koma da baya,ta kuma fara laluben hayar dakinta,ba shakka ko tantama babu najwa nada masaniyar wannan al'amari,wacce irin yarinya ce wannan takeson xame mata 'yar fata?,sai data fara biyawa ta dakinsu,ta tabbatar mata ta sameta yanzu a dakinta sannan ta wuce can uwar dakanta.

Kasa zama tayi,sai kai kawo da take daga can zuwa nan,har zuwa sanda najwa ta turo qofa ta shigo dakin,idanun mummy dake cike da zallar bacin rai da tashin hankali ta xuba mata har ta qaraso

"Me kika sani dangane da fitar kudi daga azare company?" Yanayin reaction na najwan kadai ya isa gaya ma mutum gaskiyar abinda ke faruwa,tun asali najwa irin mutanen nan ne da basa iya boye abinda ke ransu da zuciyarsu,saita sauke headphone din kanta,ta jingina da mudubin mummy bayan ta ajjiye wayarta saman madubin ta goye hannuwanta a qirji

"Ni da fawwaz muka fitar dasu,saboda ni gaskiya it's high time to get the money nima,na gina kaina na gina rayuwarta,saboda gaba daya ke na fuskanci ki fara sanyi,dukkan wasu plan naki sun daina aiki.....bazan zauna na qare a haka ba, Daddy ya mutu nida jawahir a bamu kason saraki ace mu raba ba,ke kuma a baki one over eight,kinga mu asara ta hau b......." Wani lafiyayyen mari ra zabgawa najwa,marin da yasa wuta ya dauke mata na wasu sakanni kafin ta dawo dai dai ta zubawa mummy idanu,zuciyarta tana tafarfasa,tunda aka haifeta ba'a taba marinta irin na yau ba,ko duka ba zata iya tuna sanda akayi mata shi ba,sai yau?,kamar ita da girmanta da shekarunta?,tana da matakin karatu mai zurfi,tana jin kamar ta maida hannu ta rama marin ne ko mummyn xataji irin yadda taji......

"Shashashar banza da wofi,wadda bata komai da hankali,fawwaz dai fawwaz dai?,qanin ubanki ne shi din?,da har zaki fara aiwatar da abubuwa bada shawarata ko masaniyata ba?,inda ta haka na tara duk abinda na tara da yanxu nakai warhaka ina al'amurana?,abun ba iya taku bane?,yanzu wannan kinsan matsalar da zata haifar?,kinsan dimbin masifun da xai tono?,to xanyi maganinku daga ke har fawwaz din" qarar wayar najwan dake gefe ya sanyasu maida hankalinsu,gaba daya suka kai hannunsu a tare,mummyn ta riga warcewa saboda ganin sunan fawwaz din,dama nemansa take ido rufe ya dawo da takardun nan,ga kuma wannan ta sake faruwa

"Kana jina da kyau?,ka saurara kaji abinda xan gaya maka,bisa kakkausar murya da kuma gargadi,baka da gadon najwa koda mutuwa tayi.....bare gadon ubanta.....saboda haka.....na baka awa ashirin da hudu,duk wani abu nata data baka da wanda ka karba,ka tattaromin shi ka kawomin cikin girma da arziqi,duk wani abu namu dake hannunku kaida uwarka,don na tabbatar akwai masaniyarta cikin komai,ida ma kun shirya wani zagon qasa ne to haqarku bata cimma ruwa ba,amma na baku awa ashirin da hudu,daga yamzu zuwa gobe,tunda baku san abun arziqi ba" daga haka ta datse kiran,tama kashe wayar gaba daya

"Ya haka mummy,tunda kin gama fada ai sai ki bani wayata kuma ko?" Najwa ta fada cikin fada da qunar rai

"Idan kuma na hanaki fa?" Bata ankara ba najwan cikin fushi ta kaiwa wayar wafta,ta samu nasarar finciko abarta kuwa ta kuma qara gaba babu ko waiwaye,saidai kuma hakan yayi sanadiyyar faduwar mummyn,kwankwasonta ya bugu da gado.

Wajen ta dafe tana ringse idanu,saidai kuma ta bangare guda tsoro ne da firgici fal zuciyarta,tsoron sauyawar najwan zuwa wasu halaye da dabi'u data jima da saninsu a wani muhalli na daban.

********Tsaye take a gaban madubin tana nada dankwalin rigar jikinta,gabanta ne keci gaba da faduwa,a ranar yau nasara ce ko kuma faduwa a garesu,tuni bibi ta fita zata samesu bakin titi,a yanzu ita da samir da amiru ne suka rage cikin gidan,cikin wata qatotuwar sa'a kuma......mummy ta fita tun sassafe,dama kuma basa son ta gane ko ta fahimci fitarsu zuwa dawowarsu.

Tana fitowa daga daki taga giftawar hajiya qarama,sai ta lumshe idanunta tana qiyasta yadda Hajiya qarama zataji duk sanda labarin raihananta tana raye yakai kunnenta,zataso ace da ita za'ayi tafiyar nan.....saidai dole a dakata da xuwa da itan saboda wasu dalilai,komai zai kasa yiwuwa yadda sukeso matsawar ya zamana anje ne da hajiya qaraman.

Tun kafin ta qaraso ta ya hangota ta madubin gaban motar,tsaida idanunsa cikin madubin yana binta da kallo,tana sake matsowa inda suke suffarta na sake bayyana,tayi kyau sosai cikin orange atamfa me adon dark brown,madaidaicin medium mayafi brown,fuskarta fayau,sai wani kwantaccen kyau da fuskarta ke fitarwa,qawatacciyar brown skin dinta ta sake kyau wadda laushinta da santsinta a idanu kawai ya bayyana,lips dinta babu komai akai,saidai yanayin yadda Allah ya tsara mata lips dinta gwanin sha'awa ne game kallo.

Kamar walqiya yaga juyawar madubin da yake kallo zuwa robar dake bayan madubin,ya juya a nutse zuwa gefansa,sai yaga amiru na dubansa,da alama shine ya juyar da mudubin.

Ido daya ya kashe masa
"How far bro?" Kansa samir ya dauke sannan yace

"Me ya hana bude gate din nan ne?" Yayi maganar dai dai sanda yake tada motar,dariya amiru ya bushe da ita

"To ai driver din motar bai shirya ban....." Daidai lokacin kaltum ta bude murfin motar ta shigo.

Cikin sassanyar muryarta ta gaidasu,suka amsa samir ya fara motsa motar suna ficewa daga cikin gidan,yana jin amiru nadan tsokanarta,bata amsa ba,saidan sautin murmushinta kawai,kafin daga bisani shuru ya ratsa motar,har suka cimma bibi suka dauketa sannan ya qara speed na motar.

"Ina muka nufa bibi?" Amiru ya waiwaya kadan ya tambayeta

"Kaltum ce jagorar tafiyar,zata dinga muku kwatance har mu kai" dukkansu sun danji mamakin furucinta,to amma ba wanda ya tanka,samir yaci gaba da sauraron kwatancen da take masa cikin sassanyar muryarta,har suka kawo qofar wajen.

"Nan ne?" Samir ya nuna qofar gidan da yatsan hannunsa cikin kokwanto
"Nan ne" bibi ta amsa masa a maimakon kaltum,kamar zaiyi magana kuma saiya fasa,ya gangara da motar a hankali xuwa ina aka tanada saboda ajiyar motoci ya tsaidata,sannan ya faka,kowa ya kama murfin motar suka fito.

Tun daga farfajiyar wajen bibi ta soma sharar hawaye,babu abinda take tunawa illa tsahon shekarun da hajiya raihana ta share cikin wadan nan mutanen,tsahon shekarun data share tana rayuwa irin tasu,wahala data fuskanta tsauri da tsanani.

Kai tsaye office din shugaban gidan aka kaisu,ya karbesu hannu bibbiyu,basu shaida masa ainihin su su waye ba,don kusan ma bibi ce tayi masa bayanin cewa,sunzo ziyartar marasa lafiyanne.

Sosai ya nuna jin dadinsa,saboda yanayinsu kadai ya bayyana masa cewa lallai yau gidan akwai samuwa,don haka ya tashi da kansa suka fara zagayawa gurare gurare.

Dukka gaba dayansu ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba,lallai lafiya babbar ni'ima ce,duk wanda Allah ya bashi kyauta da baiwar lafiyar hankali ji da gami da gani ba qaramin abu bane.

"Alhamdulillah" saraki yake furtawa a fili,saidai qasa qasa,kana duban qwayar idanunsa zaka gane cewa yanayin da ya bayin Allah ya taba zuciyarsa.

Minti kusan arba'in suka diba,wani abun ya basu tausayi,wasu a cikinsu su basu dariya,sosai saraki yayi rabon kudi,kudi sosai ya raba musu,musamman wadanda hankali ya fara samuwa a garesu,sannan suka dinguma sukayo hanyar barin wajen.

Sosai ta riqe hannun bibi sanda sukayi kusa da wajen,bibin najin hakan ta fahimci abu na gaba dake shirin faruwa,don haka kaltum na sauka daga hanyar tabi bayanta.

Kyauro shine mutum na farko daya fara ankara dasu,tun shigowarsu wajen dama yaji sam hankalinsa bai kwanta ba,musamman lokacin da yayi idanu hudu da yarinyar,ya shaidata sarai,ya kira hajiya jidda kuma yafi sau hamsin daga shigowarsu kawo yanzu amma wayar taqi shiga,har ya fara murna sanda yaga sun kammala ziyarar lafiya,sai ya hangi kaltum na nufar wajen da yake tamkar rayuwarsu ne a wajen.

"Ke.....ina kuma zakuyi?,baga hanya nan ba?" Ya fada da wata irin rudewa data gaza boyuwa

"A'ah,akwai sauran baiwar Allah da ba'a dubata ba ita,kuma ta cancanci a dubata din" kaltum ta fada cikin wata dakiya tana duban qwayar idanun kyauro.

"Ba kowa ta nan bangaren,dukkansu kun gansu a inda ake fito dasu ai hajiya" ya fada fuskarsa na fitar da wani busashen murmushi,bushewar data zarce har maqogwaronsa cikin sakanni 'yan kadan

"Akwai saura,akwai wadda ni ban ganta ba,bayan wanacan karon na ganta" wani gumi ne ya zartowa kyauro,yaga alamar akwai wani gagarumin tashin hankali da yarinyar ke son ballo musu,don haka ya fara takawa zuwa inda suke tsayen yana kafe kaltum da ido

"Hajiya kiyi haquri,kowa da kowa yana waccar farfajiyar da kuka baro,lokacin ziyara ma ya kusa fita".

"Babu inda zani sai na ganta" ta amsa masa kanta tsaye babu wani tsoro ko dar,don ta riga ta shiryawa koma meye

"Kaga sani.....qyaleta,aiba wani abu bane" yaji umarnin shugabansa daga bayansa,adan rude ya juyo ya dubeshi,sannan ya maida dubansa ga kaltum

"Shikenan,ki shiga ki fito sab......"

"Bani kadai ba.....gaba dayanmu muke da buqatar shiga" sosa samir dake tsaye daga baya yake karantar fuskarta,fuskar da bai taba ganin makamancin abinda yake gani a yanzu cikin qwayar idanunta ba,tabbas akwai wani abu,tun ba yau ba,ya jima da sanin halinta,bata kafiya akan rashin gaskiya.....taurin kanta akan gaskiyarta ne....tun ganinsa da ita na farko.

Fusata yayi sosai daa datsar numfashinsa da tayi,abin yayi matuqar fusata shi,dama abunka da maras gaskiya cikin fada ya fara magana

"Ke wacce irin matace?,to ba zaki shiga din ba,kece qarama amma kinfi kowa musu da taurin kai?"
Chapter 103 · 0% Book details