← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 117

Sashe 19

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tagumin ya cire,yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,kafin ya soma magana
"wato malam tanimu takaka ya shiga uku a wannan zamanin......ka ganni nan na rasa inda zan dora raina,bikin yarinyata ne ake ta saka rana amma abu ya gagara,sau uku ana saka rana ana dagawa saboda babu kudin da zan mata kayan daki,yanzu mijin yace idan aka qara dagawa ana hudu to ya fasa,abu na biyu yarona bashir da na sanya raina da burina akan zai taimaka min idan ya qare karatunsa......shima yanzu saura kwana uku a rufe registration amma ban masa ba,saboda bani da kudin yi masan,munje neman taimako gidanjen 'ya siyasan nan har mutum biyu amma saidai suce za'a kiramu har yanzu shiru,mutanen nan malam tanimu nasa tsoron Allah,sun gina manyan gidaje,suna hawa manyan motoci,sutura ta alfarma amma sun kasa taimakawa talaka dake nemam tsira da rayuwarsa koda da iya abincin da zai sanya a bakin salatinsa ne,kudin da bai gagaresu ba amma suna qyashi da baqincikin su dauka su taimaka maka,bayan duk wata qafafa tasu da suke da ita kudinka ne,da bazarka suke rawa,sai daka zabesu sannan suka zama abinda suka zama,sai da ka zabesu sannan suka je inda suke a yau,naje na yiwa murtala magana,ya taimaka min cikin albashina ya bani,ko katifa na samu da asiya mata da labulaye amma yace sam,ai wata sai yanzu yayi rabi ma,baza bani ba,na haqura waina jira har watan ya qare a soma albashi,ya ilahi ina mutum xai tsoma rayuwarsa ne?" .

wani abu ne yaja hankalinsa kan hirar da sukeyi din,saidai kafin yayi tunanin komai wayarsa ta shaida masa cikar sauran lokacin da ya rage masa,dole ya miqe ya dauki rigarsa ta sama daya cire ya cukuikuyeta ya taka a hankali ba tare da sun lura da shi ba ya fice.

ajiyar zuciya ya sauke,yana tsara abubuwa masu yawa cikin ransa,ran nashi yaji ya dan baci game da murtala,tun ba yau ba yana dan ji da samun qorafe qorafe a kansa game da ma'aikatan, akwai abubuwan da suka sanya yake daga masa qafa ne,banda haka da tuni ya dade da yanke masa hukunci,saboda shi din bai da wasa ka irin wadan nan al'amuran,dalilin da yasa kamfaninsa ya zama daban da sauran.

sai da ya zauna sosai kan mazauninsa sannan aka sake sabuwar gaisuwa,dakin ya dauki shuru,kowa ya nutsu yana jiran yaji daga bakin shugaban nasu.

fawwaz ya hanga cikin jerin ma'aikatan,ya masa kallon da bai wuce na sakanni uku ba saiya dauke kansa,cikin muryarsa Mai cike da kwarjini da wani nauyi dake cika kunnuwa,wanda ke nuna nutsuwa da confidence ya soma magana cikin harshen nasara,duk da yana jefa hausa lokaci zuwa lokaci a ciki
"abu na farko da zan soma bude taronnan dashi albishir ne....."take fuskar duk wani ma'aikaci dake wajen ta washe da fara'a da kuma farinciki,tun basu ji ke zaya ce ba,sunsanshi tun ba yau ba,duk sanda yazo da albishir to kowa saiya dara
"akwai qarin albashi ga ma'aikata"take wajen ya hautsine da farinciki,duk da cewa m.s construction company yana daya daga cikin kamfanunuwan dake bada albashin da babu kamarsa a gadin Nigeria
"amma ga wadanda suja dace....akwai tantancewa da zamu aiwatar kafin faruwar hakan"farincikin sai ya dan ja baya daga fuskokin wasu,yayin da kowa ya cika da fata da burin ya zamana cikin wadanda suka cancanta.

sauyawar tasu bai hanashi kiran sunan murtala ba
"murtala"
"yes sir"ya fada yana miqewa tsaye, hannunsa dauke da wani littafi mai manyan shafuka,da rubutu birjik a cikinsa,yadan rusuna masa sannan ya miqe
"daga yau....."ya dakata yana kallonsa,yayin da dakin ya dauki amsa amon na muryarsa
"daga yau......duk wani ma'aikaci,kama daga babba zuwa qarami,duk wanda yazo maka da buqatar albashinsa kafin lokacin bada salary yayi,a dauka a bashi"kallon kallo suka soma yi a junansu,kalamansa na yiwa wasu daga cikinsu dadi,yau kam zaman na musamman ne a wajensu,yazo musu da abubuwa masu dadi.

Duban fuskar murtalan yake yana jiran yaji abinda zai fada,muryar fawwaz ta maue gurbin muryar murtala da samir yake kira yaji yace wani abu akai
"amma samir.....hakan sai nakega baiyi tsari ba,ya ace tun ba'a ga performance na mutum ba a cikin watan sai a dauka salary dinsa kawai a bashi,bugu da qari kuma ma.....kowa ya sani cewa,akan iya samun asara a kamfani ko riba,duka ba zakayi duba da wannan ba zaka zaka yanke wannan hukuncin,idan asara ta samu kuma kenan kamfani shi kadai zai dauka bazai shafi ma'aikata da albashinsu ba"kallo.ya zubawa fawwaz na wasu sakanni,yana mamakin yadda fawwaz ke masa shishshigi haka cikin lamuransa,yana sane dashi,ya dage masa qafa ne saboda albarkacin wasu mutane guda biyu,saiya janye idonsa daga kan fawwaz din ba tare da yace masa komai ba,ya maida dubansa ga murtala
"this is an order"ya fada kai tsaye cikin salo na bada umarni,kai murtala ya gyada
"in sha Allah sir"ci gaba yayi da kallonsa yana jefa masa tambaya ta biyu, analysis ne na wasu abubuwa da suka shafi kudin dake shiga da fita a kamfani,murtalan da team dinsa suka soma bayani,tsahon wani lokaci da samir ya tabbatar komai yayi dai dai, bayani kuma ya kammala yadda ya kamata,murtala ya miqa masa takardun ya karba,da zummar idan yaje gida zai sake dubawa,ya kuma sanya hannu,saiya miqawa umar dake zaune daga gefansa,sannan ya sallami wasu daga cikin ma'aikatan,yabar wadanda suke cikin gaba ta biyu da zasuyi magana akanta.

"umar....ina da ina aka binciko bayan qauyen dan sarari?"samir ya fada yana shafa kansa da hannunsa,saboda gajiya da ya farayi da zaman,uwa uba kansa ya dauki chargy sosai,miqewa umar yayi a nutse shima da wasu takardun a hannunsa
"sir....akwai qauyuka guda biyu,qauyen ɗinya da kuma qaunyen me saje,dukkaninsu suna buqatar makaranta da masallaci,koda na kamsus salawati ne"kai ya jinjina idanunsa qur kan file din dake gefansa
"cikin biyun wanne qauye ne sukafi buqatar hakan"bubbuda shafukan takardun hannunsa umar yayi sannan ya dago ya dubi samir
"qauyen dinya,don makarantar dake kaf qauyen guda daya ce,an ginata shekara talatin da suka gabata,kuma tun wancan lokacin ba'a ake sabuntata ko bi ta kanta ba,sannan qauyen basu da masallacin kamsus salawatin ma,suna salla ne qarqashin bishiya"kansa yake qara jinjinawa,ransa na baci,idan ya tuna shuwagabanninmu,me sukeyi?,meye amfaninsu?, duk wani abu da aka zabesu don su yiwa talaka shi bashi suke yi ba,yanzu wadan nan mutanen abinda sukafi buqatar ayi musu ba'a musun ba,kuma baya raba dayan biyun,suna iya shiga har can neman quri'unsu idan lokacin zabe yazo,amma a yanzun tamkar basusan akwai wata al'umma dake rayuwa a wajen ba
"i hate it"ya furta can qasan ransa,kamar yadda yake dukkan wannan tunanin cikin ransa.

Kwayar idanunsa ya daga yana katse shurun ta hanyar cewa
"murtala....a dubamin putting smile account aga nawa muke dashi,idan kudin baikai ba a sanya dukka albashina a ciki,a soma shirin zuwa yi musu aiki,idan ina free zani wannan karon,idan kuma akwai aikin dake da buqatata cikin kamfani zan turaku ku aiwatar kamar yadda aka saba"
"an gama sir"ya fada cikin girmamawa.

Kafeshi da idau fawwaz yayi,yana jin wani abu na taso masa cikin ransa,sam samir baima ga kallon da yake masa ba,har sai daya tashi daga kashingiae da yayi yana soke yatsunsa cikin na juna yana kallonsu daya bayan daya
"akwa mai wata magana qorafi ko qarin haske?"haka yake,duk sanda akayi taro irin wannan yana baiwa kowa dama ya tofa albarkacin bakinsa,yakan gayawa kansa dakansa cewa
"kowa ma mutum ne kamar shi,nawai saboda Allah ya bashi jagorancinsu ba kuma ya zamana shi kadai yake da abun cewa,kowa ma baida abun fada".

Fawwaz ne yayi gyaran murya sannan ya zauna sosai yana duban samir
"akwai qorafin da zanyi"dubansa yayi na wasu sakanni sannan ya gyada kai alamun ya bashi dama
"amma ni a ganina mr samir kai ba gwamnati bane da zaka ce saika farantawa kowa,koda gwamanti bata iya aiwatar da komai da komai,kowanne lokaci kama kwashe kudaden kamfani kana zuwa kana wahaltawa wasu mutane da basu gama sanin dadin rayuwa ba bare susan ciwon kansu,ko wata biyu ba'ayi akaje wasu qauyukan aka musu aiki,kafin su ka yiwa wasu da dama da bansan iyakacinsu ba,hakan bai isa ba?",cike da mamakinuake duban fawwaz,yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,naisan aninda ke damun fawwaz din ba,amma ya soma gajiya a wasu baqin halayensa,kusan maganar fawwaz din taja hankalin yawa yawan wadanda ke wajen,murmushin gefan baki samir din yayi sannan yace
"kana da matsala da hakkanne?,ko kamfani na tauyeka da wani abun?" kai ya girgiza
"ko kadan....amma...."hannunsa ya daga masa
"bana son amma....matsalarka nakeson naji idan akwaita,idan kuma babu fine,zamuyi addu'a mu tashi"shurun da ya biyo baya shiya tabbatar masa da cewa.....dukka qorafin da zaiyin ba mai ma'ana bane,ba kuma muhallinsa bane......

10
*Zafafa biyar na kudine,siya ki karanta cikin aminci*
08184017082
Ko
09134848107

tun daga safiyar jiya zuwa yau din nan babu abinda ke yawo a ranta illa zallar farinciki da jin dadi,duk inda ta kalla cikin sassan nasu farinciki ne yake mamayeta,farincikin da take ciki ya sake ninkuwa a safiyar yau,bayan sunje gidan habiba sun mata dukkan jeren daya dace.

Jere ne da ya yiwa kaltum ba zata,don bata taba zaton habiban zata tsira da abinda ta tsira a yanzun dashi ba.

Sun isa gidan sun samu.mahaifiyar yusufa mai tarin kirki da karamci kamar yadda aka dinga gaya musu habiban ta dace da surukai,bangarenta na cikin gidansu yusufa ne,wanda babu kowa daga ita sai bangaren surukar tasu,sai sashen qanin yusufan da yake gini shima yana saka ran aure nan kusa,su biyu ne yara maza da babarsu ta haifa,sai hudu mata wadanda duka an aurar dasu,sai kuma wasu matan su biyu da babarsu ta rasu kafin a auro babar yusufa,babar yusufan ce ta riqesu harta aurar dasu.
Chapter 19 · 0% Book details