← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 117

Sashe 62

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Qaraso ciki" ya bata umarni kai tsaye,yana kausasa muryarsa,hada idanun da sukayi bayan umarnin daya bata shiya hanata komawa a guje kamar yadda tayi niyya,ta qaraso daura dashi kadan,ta zame a hankali ta zauna saman lallausan carfet din dake gaban kujerun,tana jin kamar zata nutse saboda tsananin laushi,sai a sannan idanun jawahir yakai ga kaltume,ta zuba mata idanu sosai tana yamutse fuska,ita kuma wannan daga ina?,daga ina yayansu ya debota?,ta yiwa kanta tambayar,saidai babu ikon tambayarsa,saboda tasanshi sarai ba sanin shanu ba.

A nutse momy ta koma ta zauna,saidai har yanzu hankalinta yana kan kaltume,duk da cewa idanunta ba'a kanta yake ba.

Najwa ce ta gaisheshi bisa dole kamar yadda takeji a kullum har cikin zuciyarsa,ya amsa ba tare daya bawa yanayinta muhimmanci ba,ya maida hankalinsa ga momy,ya gaidata ta amsa tana bada umarnin a kawo masa abun tabawa cike da nuna tsantsar kulawa kamar yadda ta saba nuna masa a ko da yaushe,ya tsaida hakan ta hanyar cewa sai zuwa anjima.

"Wannan fa son?" Ta tambaya tana nuna kaltum da baki

36

Hkan ya baiwa najwa damar juyawa zuwa sashen da kaltume ke zaune a rakube,kamar zakace kyat ta zura da mugun gudu

"Mai aiki na qaro muku" ya fada kansa tsaye yana relaxing saman kujerar da yake zaune,yana jin yadda gaba daya ya gaji.

"Me aiki yaya?"jawahir ta fada cikin wani salo me kama da gatsali

"Jawahir......" Momy ta kira sunanta da qarfi
"Na'am" ta amsa tana duban momyn,da idanu ta gaya mata kada ta sake magana,sai taja bakinta ta tsuke,haushi da takaici na cikata,ta taya zai dauko kucakar ya kawo musu gida da sunan mai aiki,gidan ma irin nasu,gidan professor rashid guda,wanda mutane da yawa ke kwadayin yin aiki qarqashinsu,koda an tashi daukar mai aiki momyn nasu saita zaba,ta kuma jarraba mutum ta aminta dashi take dauka,ma'aikatan daba ita ta daukesu ba cikin gidan batajin basu wuce uku ba,shine kawai zai wani kwaso musu kalar qyanqyami,saboda yana taqama da ikon da yake dashi a gidan,qwafa taja can qasan ranta,tana jin sauran qiris ta rushe komai,ta maye gurbinsa,wannan shine babban buri da muradinta,wanda dashi take kwana take kuma tashi.

Da murmushi saman fuskar momyn,tana qoqarin dai daita komai ta dubi samir din

"Banda abinka son....ai kasan tsarin daukan ma'aikata a gidan nan,ko baya ga haka ma professor kasan baya bari a dauki qananun yara kamar haka,banason wannan ya jawo wani sabuwar matsalar tsakaninku fa?".

Numfashi ya fidda
"Babu komai momy,a bata wajen zama,zanyi magana da dadyn"

"Shikenan....."ta fada tana mutstsuka hannaye ta,tana jin wani abu nason kutsawa cikin zuciyarta amma tayi gefe dashi,ta dubi jawahir

"Kuje da ita ki bata daki"

"Kaman zuwaira ke kaisu boys quarters din" jawahir ta fada,sai momyn ta tsuke fuska sosai

"Ba cikinsu zata zauna ba,a bata daki nata na daban" idanu jawahir din ta fiddo,kamar zatayi magana sai kuma ta fasa,mamakin abinda momy ke nufi ya kamata,kamar wata 'yar gida za'a bata daki guda?,miqewa tayi da hanzari ranta a bace ta soma yin gaba

"Tashi ki bita.....meye sunanki ne?" A hankali samir ya bude baki zai amsawa mommyn,sassanyar qaramar muryarsa ta maye gurbin tata
"Kaltume" ta fada da qaramin sauti mara amo.

"Tashi kije ta baki masauki" kamar wadda ciwon paralyze ya kamawa qafafu haka ta dinga ji sanda ta miqe,tsoro baqunta rauni da kuma firgici sukayi mata qawanya gaba daya,tana riqe da qullin kayanta taci gana da bin gurbin da jawahir kebi har suka isa wani kebantaccen corridor me dauke da dakuna manya guda hudu.

Muqullin jiki ta murza ya bude ta soma shiga,tayi tsaye sanda kaltume ke takowa sannu a hankali,kamar wanda ke shiga wuta

"Dalla malama ki shigo,nan ba bukka bace ko rumbu" ta fada cikij tsawa,tsawar data razana kaltume din,saboda haduwa da tayi da tsoro da kuma ganin yanayin dakin da bata taba katarin ganinsa ba,hakan ya sanya qullin hannunta faduwa saman qafafunta,jawahir ta bisu da kalllo kana ta tabe baki

"Ga daki nan,amma ki sani,ba qyaleki za'ayi ba,duk abinda kika barnatar saikin biya,don haka kibi a hankali" ta qarasa maganar tana galla mata harara,sannan ta kewayeta ta fice,ta bita da kallo har zuwa sanda taja mata qofar.

Zafafan hawaye suka sauko mata,wannan rayuwar kuma itace yanzu zata fuskanta,su waye wadan nan da zata rayu cikinsu ne?,me zata tarar,shi kansa wanda aka kira da sunan mijinta wayeshi?,bata da tabbas a kansa bata da tartibin wata amsa guda daya gamsashshiya game dashi,ta juya ta kalli gabas da yamma kudu da arewa na dakin,ta yaya ma zata iya rayuwa a wannan wajen me kama da gidan aljanu?,ko ina glass,da wani abu mai santsi da qyalli,shiba daben sumunti ba,hakanan ba ledar tsakar daki ba,saita zame taja da baya a hankali ta zauna a qasan da batasan na meye ba,kuka na balle mata.

A zafafe jawahir ta koma falon,ta tadda saraki ya fice sai mommyn

"Mommy,ta yaya......" Bata kai ga qarasawa ba mommyn ta daga mata hannu

"Babu abinda kika sani ko kima kika iya sai shirme,wadansu lokutan ina raina hankali da wayonki....." Daga wannan bata sake cewa sa ita komai ba, taci gaba da kankare farcenta data taras tana yi,saita juya ta kwashe wayarta da headphone dinta ta yi dakinta fuuu,mommyn ta bita da kallo,daga bisani ta dauke kanta tana girgiza kai,nan da wasu mintuna tasan zata dawo da kanta,don haka taci gaba da gyaran farcenta.

Sai daya gama sharce kansa sannan ya lalubi undies ya feshesu da turare ya fara sakawa,sai daya gama sawa ya dubi Aamir

"Zamu leqa wajen hajiya qarama,amma sai zuwa anjima,zan leqa company yanzu kafin lokacin tashi yayi,akwai abubuwan da zan dudduba"

"Ba damuwa,inason na leqa mutuniyar" ya fada yana dan kashingida

"Saika nema kuma abokin rakiya,badai muhammad samir ba" ya amsa masa yana qoqarin bude katafaren ma'adanar kayanshi.

Qaramin murmushi kawai Aamir ya saki,yasan halin kayanshi dama,abu daya da bai yarda dashi ba yayi rakiyar zance,yace shiba yaron kowa bane,baiyi,kuma shima ba wanda zai nema yayi masa,kowa ya iya allonsa ya wanke,rakiyar zance ko gulma.

Cikin kayansa ya dudduba,ya fitar da wani lallausan yadi butter color ya sanya,a nan yabar Aamir yayi ɗai ɗai,shi ala dole ya gaji,ba yadda samir din baiyi ya tashi su fita tare ba yaqiya.

Tun tana kasa kunne ko zataji motsi ko gilmawar wani,harta saddaqar da cewa an kawota qare kukanka,inda babu wanda zata ji,babu kuma wanda zai jita.

Duk sanda agogo ya kada saita daga kai ta kalleshi,duk da cewa batasan qarfe nawa yake bayarwa ba,yanayin shigowar hasken rana dakin kuwa bashi da banbanci daga shigowarta zuwa yanzun da take zaune a jikin bago kamar wata qadangaruwa,ya kamata ace taji yunwa,amma tunanuka dake cunkushe cunkushe cikin kanta ya hanata taji yunwar arziqi,sannu a hankali lokaci ya dunga motsawa zuwa gaba,cikin jikinta ta dinga jin yakamata ace tayi salla,koda lokacinta baiyi ba,bare tana ji a ranta ma lokacin yayi qila ma har ya gota,saidai batasan inane zata nufa don daura alwala ba.

Zagaye ta dinga da idanunta harta hangi qofar toilet,ta miqe zuwa qofar sannu a hankali ba tare da tana da tabbacin wane waje bane nan,sai a sannan tasan lallai tana buqatar abinci,saboda jinta da tayi fayau iska na dibarta,ga sanyin wajen da taketa jin ya mata yawa.

Tsaye tayi a bakin qofar,ta jima tana qiyasta ta yadda zata budeta,kafin daga bisani tayi shahada ta soma gwada budewar na wasu mintuna kafin ta samu nasarar turata ta bude.

Bin bandakin tayi da kallo,wanda yafi mata kama da daki,don kaf karkararsu bata taba ganin mai kya makwanci kwatankwacin nan wajen ba,take ranta ya bata cewa wani dakinne mai zaman kansa,kenan babu wajen zub da ruwa bare ta daura alwala?,idan kuma tace zata fita ina ta nufa?,ba zata iya maida kanta inda ta baro dazu ba bare ta koma wajensu ta tambayesu.

Sake qudundunewa tayi a yadda take zaunen,sanyin tiles dana ac na ratsata,wanda batasan sanyin meye ba,sai dan banzan takura matan da sukayi,zuwa wani lokaci cikinta ya sake buqatuwa qwarai zuwa ga abinda zai sarrafa ya bawa jikinta kuzari.

Mamaki qwarai ya mamayeta,wadanne irin nau'in mutanene wadan nan?,masu qarancin karamci?,iya rayuwarta da yadda suka ga ummansu nayi akan baqi sam ba haka bane,duk da kasancewarta mai qaramin qarfi,wadda itama idan aka bata da farincikinta zata karba,amma duk sanda baqo ya shigo gidan,nata ko ba nata ba,saita zuba ta miqa mishi,koda bangaren kawu iliya yazo ba nasu ba,ta riga ta saba da ganin hakan,sai gashi yau ta fada hannun wasu mutane,an yasar da ita a wani daki dake mata kama da qiyama.

Qarfe shida da mintina ashirin ta shigo gidan a gajiye daga makaranta,mintuna goma kenan a gaba suka rage a kirayi sallar magariba,duk da cewa kaita ake a daukota amma hakan bai hanata jin gajiya a jikinta ba,tayi mita tayi qorafi kan a bata mota,amma saraki yace ba yanzu ba,yasan yadda jawahir keda tarin qawaye,kasancewarta mai faran faran da son jama'a,ta haqura da tsarin yayan nata,saboda tasan cewa kome ya tsara a gareta baiyi don ya cutar da ita ba,sai don amfanin kanta,bata kuma damu da kalar motar da najwa ke hawa ba,ta tattara ta barwa lokacin da yayan nata ya zaba mata.

A falo ta zube tana ajjiye takardunta,mommy dake shirin shigewa shiyyarta don shiga wakan tarbar mai gidan da bai mata tsufa ta dubeta

"Yanzu nake shirin daga waya na kiraku,yau dadewar tayi yawa"

"Wallahi momy,yunwa da gajiya,bamu zaci muma zamu kai hakan ba"

"To barkanku tunda kun dawo,saiki shiga ki saka a kawo miki abinci"

"Sai nayi sallah momy,saura 'yan mintuna a tayar,idan naci yanzu kasa tashi zanyi nayi sallar akan lokaci" ta amsa mata tana qoqarin miqewa saman doguwar kujera abinta.

Ganin falon babu kowa saita dauka remote tana canza channel din dake aiki saman screen din tvn dake falon,tare da maida hankalinta ga channel din data sauya.

Sosai program din da take kallo ya dauki hankalinta,har aka tayar da sallar aka idar bata sani ba,motsin shigowar samir da fitowar mommy cikin shigar alfarma ya sanyata miqewa ta zauna,kamar ko yaushe fuskarta qunshe da murmushi takewa samir din murnar dawowa

"Yaya,bari naje nayi salla na dawo naji nasarar da aka samu wannan karon,bamuyi waya sosai ba tunda ka tafi"

"Au,dama bakiyi sallar ba tun daxun?" Tana zura takalminta cikin sauri tace

"Wallahi momy bansan an idar bama" ta hada da mayafinta tana yin bangaren dakunansu da hanzari.
Chapter 62 · 0% Book details