← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 117

Sashe 15

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau sakanni yana hado maganar kafin yace

"Dama Abba akan maganar Fatima ne."

"Uhum ina jinka. Ya akayi?"

"Dama... Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin gidan nan yake."

Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace

"Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku albarka."

" Amin Abba." Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi,

" Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga an zama daya ai in sha Allah babu wata matsala."

" Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma."

" Amin." Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din yayi kafin ya mike

" A huta lafiya Abba."

" Yawwa Ibrahim."

Yana fita ya daka tsalle a wajen yace

"Yes!!"

Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan gida yafi bare.

***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500 din nan ne, a rayuwar sa be taba hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu.

"Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin ka?"

"Wait and see." Yace yana kawo wata leda a kusa dashi, ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a mudubi

"Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya sai mu karasa."

"Na saka me?" Musaddik yace da sauri yana bud'e ledar.

"Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan."

"Mu nawa ne a dakin nan?"

"You must be kidding me, haba haba an fad'a ma kowa ma irin ka ne."

"Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci I'm dying to see my love."

"Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani ba."

"Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare. Allah dai ya taimake ka wallahi."

" Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan son, the whole you, Captain Muhammad Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba, musamman idan allurar ku ta motsa."

Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi

" Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na Muhammad ba."

Dariya maganar ta bawa Musaddik,

" Ni zaka saka frog jump?"

" Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga."

Tashi Musaddik yayi ya sake daga kayan, kafin ya fara sawa yana cigaba da mita.

" Kanka akeji wallahi." Moh yace yana cire agogon hannun sa.

" Ka cire watch dinka please, anything da zai sa ta zama suspicious, I don't care idan kowa na gidan su yasan ni waye, amma ita? Da marikiyarta will be the last da zasu sani, surprise ne me kyau nake son basu dukka, sai dai kowanne da yadda surprise din zai zo masa."

" Wicked soul." Musaddik yace yana jefar ta watch dinsa akan mirrow

" What ever!" Yace yana yin gaba yabi bayan sa yana jin dadin kayan jikin sa, babu nauyi shawai shawai amma kuma ba zai yarda Moh din yasan ya ji dadin kayan ba.

A daidai shagon aka daajiye su, yace su je chan in da suka saba jiran sa su jirashi zai kirasu. Duk da basu so ba amma haka suka tafi suka barsu, Musaddik ya dinga jan tsaki suna tafiya a k'asa har suka isa kofar gidan. Wayar sa ya ciro ya kira ta, tayi ta ringing bata daga ba,

" Bata daga ba."

" Da ka kirata tun kafin muzo ai."

" Wannan ba matsala bace, bari kaga."

Ya kwankwasa gate din kafin ya dan tura shi suka shiga, dai-dai lokacin Khalil ya taho zai fita sukayi kichibis, wani kallo ya bisu dashi irin na sama da k'asan nan, kafin ya tuntsure da dariya sosai, hakan yayi bala'in bata ran Musaddik da dama chan baya daukar nonsense.

" Malam lafiya zaka kalle mu kayi dariya?"

" Lafiyar kenan, sai dai kun makara, dan gida ya shiga ya fita ya gama tabbatar da komai akansa, sai abi wani sarkin dan an riga an gama magana kuma su din ba kananan mutane bane da zasu sauya maganar su."

" Kana nufin?" Musaddik yace a zafafe

" Ina nufin kamar yadda na fada mishi ne a baya, Iman matata ce an riga an gama magana rana kawai ake jira a saka mana."

Wani kallo Moh yayi masa da ya saka Khalil shan jinin jikin sa, amma sai ya dake ya cigaba da gaggayawa musu magana. Muhammad be ce komai ba har ya gama, ya juya ya fice ya barsu a tsaye kamar mutum mutumi.

" I have no option than to show him my real identify, idan yaso duk abinda ya biyo baya yayi kuka da kansa ba da kowa ba, karfe nawa ne appointment dinsa?"

" Da safe ne, goma kamar."

" Owk Allah ya kaimu."

" Amin." Musaddik ya amsa ransa na sake baci akan abinda Khalil din yayi musu

HALIN GIRMA

Hafsat Rano

WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .

___________

08
*zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun naki copy din ki karanta cikin aminci*

08184017082
Ko
09134848107

*_follow us @ instagram_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb

Or facebook
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

___________________________

Dan kwantar da kujarar yayi kana ya miqe sosai Samanta yana jin yadda gajiya take bin jikinsa,don gaba daya wunin yau bai shirya fita ba,ya shirya zama ya huta sosai a gida,saboda satin gaba daya cikin aiki ya yisu,babu dare babu raba,har inda ma a tsarinsa babu schedule na zuwansa sai daya ratso masa a sannan din.

hannayensa saman kansa yayin da idanuwansa suke a rufe,yayi nisa a tunaninsa sosai,busy busy ne dashi irin wanda mutane da yawa ke mamakinsa,sam bai bawa kansa hutu ba.

a qalla ya kusa minti ashirin a zaune a haka,wanda hakanan yaji zaman yayi masa dadi,ko ba komai ya dan samu break na wasu mintuna.

Dan waiwayawa yayi gefansa,a sannan ya hango tahowar professor shi da wasu mutane hudu,saiya miqe ya gyara zamansa,ya kuma kunna motar yana jiran qarasowarsa.

yana jin sanda ya shiga yana sallama da mutanen,suka maida murfin motar suka rufe masa,don haka saiya tashi motar,dai dai sanda professor ya furta
"alhamdulillah"yana sauke ajiyar numfashi.

A nutse yake tuqin har suka fita daga airport din,a hankali professor rashid yace
"lawan....ko ka sake koyon sabon salon tuqi ne?"raba idanu samir yayi hagunsa da damansa,saiya lanqwashe murya yace
"eh alhaji"dan jim professor yayi sannan yace
"to yayi kyau"daga haka bai sake cewa komai ba,zaman shuru yaci gaba da ratsawa a tsakaninsu.

"Daka sani ai baka wahalar da kanka ba samir....."yaji abban nashi ya fada bayan tsahon wani lokaci,ya ganeshi kenan,qyaleshi yayi kamar bai gane ba,qaramin murmushi ya subuce a kuncinsa,jerarrun fararen haqoransa suka bayyan,har yayi kamar bazaice komai ba sai kuma ya tanka
"yau daya dai abba....ai nima na samu ladan yau din"wayar hannunsa professor ya ajjiye,ya tsurawa gaban motar idanu,kamar anan fuskar samir din take,baisan me yasa a kullum shi da tilon dan nasa komai nasu yasha banban ba,komai nasu ba iri daya bane,abinda yake sam ba cikin tsari da burinsa ba,ya jima da sanin cewa ba haka yakeso ya kasance ba,ba haka tsarinsa yaso ya zama ba,to amma duk ta inda yake tunanin zai gyarota babu wani sauran dama data rage masa,don haka a maimakon yayi magana,saiya buge da hade yatsunsa waje daya,yana maida tunaninsa wani waje daban.

Duk sanda yayi tafiya irin wannan ya dawo iyalansa dama ma'aikatan gidan kan cika da murna,kamar yanzun,da samir ke biye dashi dauke da wata qawatacciyar qaramar jaka mai zubin akwati,yana biye da professor har zuwa cikin qawataccen falon gidan,mai yalwa da kuma burgewa,wanda ya wadata da dukkan wani nau'in kayan alatun rayuwa.

mutum uku ne ke dakonsa zaune cikin falon,biyu daga cikinsun matasan yammata ne,daya tafi daya tsaho da haske,kamar yadda daya tafi daya shekaru da basu wani taka kara sun karya ba,don dukkansu ba zasu gaza shekara sha tara da ashirin ba.

Daga wata kujera kuma mai mazaunin mutum biyu,macace xaune itama wadda ta mallaki shekaru ɗai ɗai har shekara hamsin,saidai idan har kai mai kallo xa'a qyaleka kayi mata ƙiyasin shekaru,to ba shakka zaka ce dauka cewa bata wuce shekara talatin da biyar ba.

Tun a kallon farko xaka bata sunan HAMSHAQIYA saboda ta cancanci sunan,fara ce sol,shekarunta sam basu boye hasken fatarta ba,tana da matsakaicin kyau wanda ya cakuda da tarin ado da qawar da take qawata kanta dashi kullum kwanan duniya,kallon farko zai gaya maka ta saba da ado ya zame mata jiki,salon irin abun nan da hausawa suke cewa WANKA YABI JIKI,tun daba hannayenta zuwa wuyanta kayan ado ne na mata,fuskarta wadace take da murmushi kamar bakinta zai yage,idanunta qur bisa saman fuskar wadan nan halittu guda biyu,wato samir da professor,tana dubansu da wani irin kallo me nauyi da zurfi.
Chapter 15 · 0% Book details