← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 117

Sashe 75

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudun zuciyarta ne ya qaru sosai,ta zubawa biba idanu tana kallonta tare da son gano abinda take fada,kawai don ta fadi cewa ta ganta tana kuka hakan saiya zama barazana ga rayuwarta,ta buda baki a hankali da niyyar yin magana biban ta rigata

"Kada kice zaki tambayeni komai,domin yin hakan shima qarin hadarine ga rayuwar dukkaninmu,kiyi haquri kattume,ba daga ni bane,na daga gareni bane" daga haka ta saka kanta waje da sauri,da alama wani abun ya sake taba zuciyarta ya kuma raunatata.

Kusan a kidime ta shiga daki,amma saita taras da jawahir tana rolling mayafinta a ka gaban mudubi,bata juyo ta dubeta ba tace

"Ki shirya zamu raka ya saraki gidan hajiya qarama,dama baki taba zuwa ba" a salube ta isa bakin gado ta zauna idanuwanta akan jawahir,saidai tunaninta yayi nisa da nan

"Anya ko jawa?,kice dai ina gaisheta idan kunje,wataran saiki rakani naje na gaisheta" barin abinda tayi ta juyo tana duban kaltum

"Hajiya qarama fa?,maman ya Aamiru?,qanwar daddy,bashi da 'yar uwa a duniya sama da ita" yanayin yadda ta mata bayanin ya nuna tana son nuna mata muhimmancin hajiyan a wajensu ne,saboda haka saita miqe kawai ta jaqo hijabinta ta zura

"Dakata,wallahi kaltum kina da maida bara bana" fa fada tana zaro mata kaya cikin kayan sawarta,ta feshe da turare da kyau sannan ta miqa mata su

"Saka wadan nan,ni bakiga sai dana canza ba" kanta a cake yake,don haka bata ce mata komai ba ta saka din.

A tamface mai manyan zane da kaloli masu kyau a jiki,wanda suka haska baqar fatarta,wadda a hankali ta soma rikidewa zuwa kalar wankan tarwada,kala mai bala'in kyau da daukan hankali,batasan kalae fatar nata na canzawa ba saida taji daga bakin jawahir,don ita din ba kallon mudubi ta cikayi ba,takance me zata kalla a fuskar tata?.

Dukka idanunta mummy ta zuba mata sanda take shaida mata zasu gidan hajiya qarama,ta jinjina kanta a hankali

"Saikun dawo,kice ina gaisheta da kyau" ta fada tana miqa mata wani kwalin turare mai guda uku a ciki,mai tsadar gaske ne sosai,zuwanta dubai ta siyoshi,ta karba tana juyawa ta fice da sauri,da alama tafiyar tana mata dadi.

"Kin tsani zaman front seat,yau kam a nan zaki zauna" jawahir ta fada tana mata dariya bayan ta bude mata gidan gaban,kwanyarta cike take da kalamai da tunanin maganganun biba,don haka komai akace kawai yi take,saita shige a hankali ba tare data cewa jawahir komai ba,ta kwashe qafafunta zuwa cikin motar tana shirin jan qofar,qamshin lalausan turarensa tare da sanyin ac yana shige mata hanci.

A hankali ta waiwaya ta dubeshi sanda yake qoqarin aje wayar hannunsa da sauran tarkacensa a tsakiyarsu,wani irin takura da nauyinsa takeji,kusancin dake tsakaninsu takejin kamar yayi yawa,tana jinsu very close da juna

"Ina yini?" Ta gaidashi tana dan rusunar da kanta saboda nuna girmamawa,sabida yau gaba daya basu hadu ba.

Kansa ya dago da niyyar amsa gaisuwar,sai idanunsa suka fada fada cikin nata,ya janye qwayar idon nasa a hakali,fuskaraa kadaram kadaham kamar yadda suka saba ya amsa mata tare da dora fadin

"Kina lpy?" Sanda yake yunqurin daura seat belt dinsa

"Alhamdulillah" ta amsa masa itama kamar kullum,tana jin lallausan muryarsa mai dauke da wani heaviness irin na mazantaka can cikin kunnenta sanda ya furta bismillah ya kuma tayar da motar.

Lafewa tayi sosai cikin kujera sanda suke tafiyar,rabin hankalinta naga tunani,yayin da lokaci lokaci kuma hankalinta ke kaiwa ga hirarsu,musamman idan jawahir din ta sanyota a ciki.

Sun danyi nisa ya faka a store din daya saba yiwa hajiyan siyayya,ya dubi jawahir

"Muje ki rakani" ta amsa masa tana bude murfin motar,tare da cewa kaltum itama ta fito

"Zan zauna a nan kuje ku dawo" ta fada da wani irin sanyi da take jinsa har qashinta

"Ya kayi mata magana,ai tare zamu shiga ko?" Kai ya gyada yana duban kaltume din kadan kafin kuma ya soma yin gaba,dole ta zuro qafafunta ta fito tunda ta sakashi cikin maganar.

Waje ta samu ta jira jawahir ta gama daukan komai,don dama samir din daga can wajen biyan kudi yayi tsaye yana jiranta yana duba wasu roll on da deodorant.

Kwandon hannunta shaqe da kaya tace

"Muje kaltum" bayanta tabi,ta kuma yi tsaye dai a bayanta wajen biyan kudin,ba kowa saman seat din masu karbar kudin,sai sun dan jira kadan,saboda zagayawa da yayi bayan ya nema afuwarsu.

"Me zakiyi da wannan haka?" Tambayar da samir yayiwa jawahir,murya qasa qasa saidai ta yadda zaiji tace

"Kaltum na siyawa,waifa bata fara sawa ba yaya har yanzu" a hankali ya juya inda kaltume ke tsaye yana dubanta,ya tuna watannin baya,ganin da yai mata tsaye cikin dandali,tabbas bata isa fara sakawar ba,saiya sauke idanuwansa tun daga qasan qafafunta har zuwa muhallin da aka siyawa abar,zuwa yanzu bambancin kadanne da yadda ya gani a baya

"Kuma wallahi yaya ashe qarya takemin,nina gani kunyar sawa kawai take" maganar data dawo da kaltum hayyacinta kenan,takai dubanta kan kwandon da jawahir ta zuba siyayyar a ciki,me zata gani?.

Brassier ce kusan dozen guda,idanuwanta a warwaje taso maidasu ga jawahir sai suka hada ido da samir,kamar zata nutse a qasa haka taji sanda ta fuskanci kallonta yake saita jingina da kantar kusa da ita da sauri sanda shi kuma ya dauke idanunsa,yayi ma kamar babu abinda ya faru ya maida hankalinsa ga me karbar kudi sanda yake dawowa wajen.

Harara ta jefi jawahir dashi sanda take mata dariya qasa qasa,ita babu abinda ya shalleta da alama,mamakin jawahir din take,ta yadda batajin nauyi da kunyarsa take gaya masa wannan maganar,duk da tasan halinta dama faranse ce ita,amma ta sanyata jin wata iriyar kunya,wadda ta hanata sakewa har suka isa gidan hajiya qarama.

A falo suka taddata tana zaune tana kallon tafsirin sheik Dr Bashir Usman,gefanta lemo ne da cake a ajjiye,da alama ta fara ci ta ajene.

Da hanzari jawahir ta isa gareta ta zube a cinyoyinta,itama tana dariya ta dora tafin hannunta a gadon bayan jawahir din tana murmushi da murnar ganinta.

A nutse kaltum dake dauke da ledar siyayyar hajiyan tayi sallama a falon,sallamar data ja hankalin hajiyan,ta dago tana amsawa tare da zubawa kaltum idanu harta qaraso,ta zube ledojin a hankali sannan ta zauna ta soma gaida hajiyan.

A nutse cikin yanayi na karantar dan adam ta amsa,sannan ta sake maida kanta ga jawahir kafin samir ya shigo.

Yadda shima ta amsa sallamarsa zuwa gaisuwarsa zai tabbatar maka da cewa ba qaramar qauna bace tsakaninsu shida ita da jawahir din

"Ina waccar mai baqin halin?" Hajiyan ta fada sanda take miqewa zata kawo musu wani abun su taba,saidai da qyar ta miqe din saboda ciwon dake qafarta,kusan kuma shine silar zuwansu gidan su dubata.

"Tana gida hajiya,kema kinsan bazata zo ba"

"Nima bana gayyarta,randa duk taga dama tazo,bari na kawo muku abun sha" sai tayi hanyar kitchen,kaltum ta bita da kallo,wani abu na taba ranta,tana tuna mata da ummanta da nata ciwon dake qafarta,saita lumshe idanunta,tana sauke qaramae ajiyar zuciya.

Batafi minti daya ba ta dawo

"Yau ni nake ganin rayuwa a gidan nan,masu aiki biyu amma babu ko daya a ciki?,dambu fa nace ayi an hada komai amma ya gagara gasucan zube a kitchen?,ke jawahir duba store ki debo muku ruwa da lemo,na fridge dinma ya qare an rasa me zubawa,nikam qafa ta matsamin,bazan iya ba,inajin masu aikin da naqi dai su za'a qaromin din" ta fada tana zama,sai jawahir ta miqe tana cewa kaltum tazo suje,suka miqe dai dai sanda samir ke gyara zamansa yana tambayar hajiyan ina duka 'yan aikin,ya za'ayi a barta haka ita kadai a irin wannan yanayin.

"Baraka dama ta tafi gida tun sheran jiya,ita kuma hansai zata dora girkin kenan akayi kiranta surukarta nakan gwiwa"

Kitchen ne me kyau da tsari sosai,kai baka ce kitchen din babbar mace bane kamar hajiya qaraman.

Tsaye tayi daga kitchen din tana dan kallonsa kallo irin na baqunta,jawahir kuma ta shiga ciki tana debo lemukan

"Zo mu wuce,wadan nan ai sun isa" tace da kaltume

"Jeki kai musu mu dawo nan mu zauna,wala'alla magana zasuyi da ita mu basu waje"

"A nan kuma?,ai akwai wani parlour din,saimu koma ciki" kai ta kada

"Kije dai ki dawo" tunda ta fadi haka tasan da dalili,saboda haka bata sake musa mata ba ta fice,babu jimawa ta dawo

"Tana da couse couse?" Kaltum ta tambayi jawahir

"Eh ba za'a rasa ba" saita gyada kai

"Dauko ko guda dayane na gwada wani ganganci mu gani,naga yana kama da barjajjiyar shinkafa da kuma tsakin masara,ko zaiyi mata dambun"

"Yes,correct.....dama anyin dambun couse couse din ai" jawahir ta fada tana murmushi,sannan ta ake shiga store din hajiyan ta soma laluboshu,babu jimawa ta fito dauke dashi guda biyun ta miqawa kaltum,ta karba ra durfafi inda taga an ajjiye duka kayan hadin ta janyo roba ta fara aikin.

A hankali ta dinga aiki da hankalinta da kuma hasashe na yadda take musu dambu a gida,tanayi tana fagabar kada yaqiyi tunda wannan din ba tsakin masara bane,bayan ta hada komai sukayi tsaye a kitchen din jawahir na mata hira,saidai ita hankalinta duka nakan girkin,da kuma kasadar da tayi daga zuwanta baqon waje,yanzu idan ya lalace baiyi bafa me zatace?.

A hankali ya soma fidda qamshi sosai,qamshin daya cika kitchen din gaba daya,mintunan data bashi kuwa na cika ta duba,saita kira jawahir tazo ta dandana.

Lomar farko ta fiddo idanunta waje

"Wow...wow, you make it kaltum....."sai data sake kai hannu ta debo takai bakinta sannan ta sake cewa

"Kinji dan ubansun dadin da yayi kaltum,ya akayi kika iya har haka?" Murmushi kawai tayi mata tana zaro plate guda biyu,ta cikasu dashi,jawahir ta riqe hannunta

"Haba malama,ya zaki kwashe?,mu kuma fa?"

"Hajiya iya da saura ai,ba duka na debe ba" kaltum ta fada tana mata dariya

"Kikai musu saiki dawo kici" ta fada tana tura mata farantan.

"Wai nikam qamshin girki fa nakeji,ko hancina ne saboda yunwar da nakeji?" Hajiya qarama ra fada bayan ta dakata daga maganar da sukeyi

"Qamshin abinci ne,amma ina zaton iskar kitchen ke kadowa ko,bari na fita nan kusa daku akwai eatery na samo miki wani abun da zakici,kafin a san wadda za'a kawo miki ta zauna miki kafin masu aikin naki su dawo" yana fadin hakanne dai dai sanda jawahir ta fito da plates din a hannunta fuskarta fal fara'a.
Chapter 75 · 0% Book details