← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 117

Sashe 14

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*

"Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin amincewa dani ba."

Zatayi magana wayar sa tayi kara

" Sorry." Yace mata kafin ya daga yana rage volume din wayar sosai

" Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan fita, wai ina ka tsaya ne?"

" Gani nan yanzu in sha Allah."

Ya kashe kiran ya ce

" Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya kinji?"

" Tam shikenan." Tace a sanyaye

" Yawwa ga sakon ki..." Ya bud'e murfin motar ya fiddo da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa.

***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud'e taga ice cream ne da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi. Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za'a yi.
   Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta ta cigaba da karatun ta kawai.

"Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?"

"Wacce irin magana ce wannan Zeenat?"

" Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake kika fad'a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad'a masa Bashir bashi da hali me kyau?"

Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin tace

" Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan maganganun, dan haka please bana son maganar."

" Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya."

Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!

***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad'an karya ko wasa ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon wandon nasa.
   Suna tsaye k'yam suna jiran fitowar sa, kowanne su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud'e masa motar akayi da sauri ya fad'a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa, in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.
   Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan kaya.
   A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle murfin tare da me bud'e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki. Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.
   Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe cikin farin cikin ganin shi yace

"Maraba da Yarima!"

"Sarkin dogarai..."

Muryar sa ta saka takawa d'agowa, ya gyara daga gishingid'ar da yayi, ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa. Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik'a masa ya matso kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa

" Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?"

" Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa."

" Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya akayi?"

" Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana."

" Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?"

Dariya ya saka sosai

" Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma, sai na fasa auren ma gaba daya."

" Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema."

Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace

" Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a nemi iyayenta."

" A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu wasu suje su nema min auren ta."

" Wasu?" Yace yana kallon sa

" Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai."

" A wanne dalili?"

" Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin su."

Girgiza kai Takawa yayi

" A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin tunani ne haka ya shiga kanka?"

Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska

"Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje."

"Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su san kai din daga gidan da ka fito."

Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra'ayin farko, amma yayi tunani zai fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din yace.

"Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda shiririta."

Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar tsari bikin Abidah guda daga cikin jikokin gidan.
   A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad'an domin suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi masa neman ma ya kula su suke amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d'aya d'aya.
  Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad'a masa yadda yake abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san ma yana yi ba ma.
   Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin sa.

***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban, a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud'e masa kofar mota.

"Sannu da zuwa Abba."

"Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan."

" Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?"

" Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?"

" Alhamdulillah." Yace yana tuna abinda ya faru dashi.

" Allah ya taimaka ya bada sa'a."

" Amin Abba." Yace yana bin sa rik'e da jakar sa a baya.

" Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji."

Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da Babba nan da nan ya gane akwai wani abu.

" Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?"

" Eh Abba." Yace yana sosa kansa

" Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?"

" Toh Abba Nagode." Girgiza kai Abban yayi ya wuce bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi

"Yawwa wai kazo in ji Abba."

Rik'e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin sa dauke da addu'a ya shiga falon ya tarar Abban ya chanja kaya yana zaune da alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya.

"Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?"
Chapter 14 · 0% Book details