← Book details Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 117

Sashe 35

Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna hada ido da samir din ta saki murmushi cikin nuna zallar farinciki
"Sannu da zuwa son" gefanta ya qaraso
"Yauwa mommy,na sameku lafiya?"
"Lafiya qalau alhmdlh,ya hanya?"
"Alhmdlh mommy" fitowar jawahir dauke da wani babban tray ya dakatar da gaisuwar da sukeyi,tuntuni daddy ya wuce sashensa
"Yayaaaaa" ta fada a shagwabe cikin farinciki,sannan da hanzari ta dora farantin saman dining ta dawo inda yake tsaye
"Yaya sannu da zuwa,i missed you yaya" murmushi yayi yana duban jawahir din,she cares so much,tana masa qauna ta 'yan uwantaka na haqiqa,shi yasa shima yake ji da ita
"Me too our auta,ya makarantar?" Sai data dan sosa kanta kadan tana tabe fuska,don ita sam ba wani son makaranta take sosai ba,tun daga yarinta izuwa girma,abun mamaki wani irin so da sha'awar sana'a da kuma kasuwanci Allah ya sanya mata,ba kamar najwa ba,abinda ke hadasu fada kenan ko yaushe da mummyn,saboda ita tafi son suyi karatu,tace koma meye daga baya ayishi idan an gama karatun
"Makaranta ba dadi yaya?" Qaramin murmushi ya saki yana girgiza kai
"Ba zaki canza ba auta" saita saki dariya shima ya tayata da murmushi
"Gafara.....kin cikashi da surutu,kuma ke baki kawo masa komai ba" cewar mommy tana dan jefa mata harara
"No mummy,ta manta ne,amma banda haka saina ce ya isa haka,i need to take bath ma before I eat something"
"Ba damuwa,hakan yayi,daddynku ma yace na shaida maka tare za'aci abinci"
"Ohkey" ya amsa yana duba lokaci a agogon hannunsa,ya daga kansa dai dai sanda jawahir ke cewa
"Mommy,i have finished....nima wanka zanje nayi"
"Good,hakan yayi......idan kin shiga ki turomin waccar uwar bokon tazo" dariya jawahir tayi kamar kowanne lokaci kafin ta juya zuwa ciki.

Tun daga dan medium falonsa ya soma rage agogon hannunsa zuwa suit din jikinsa,ko ina neat kamar yadda yakeso,bai taba dawowa daga tafiya ya sami bangaren nasa ba dai dai ba,wanda wannan kusan dukka aikin mommy ne,ta kula da duk wani buqatu nashi tun kafin yakai ga furtawa.

Kai tsaue toilet dinsa dake bedroom dinsa ya shiga ya hada ruwa me zafi yayi wanka,sannan ya dawo dakin don ya shirya,a sannan ya lura da wayarsa tana haske,koda ya duba screen din missed call din Aamir ya samu,ba tare da bata lokaci ba yabi bayan kiran.

"the giant saraki" shine abinda Aamirun ya fara fadi,wanda yasa murmushi subucewa daga fuskar sarakin,indai yaji amirun ya fadi hakan yanason shafe laifinsa daga wajensa
"Zaka fara kamun qafar ne?,malami idan zaka yanki ticket ka dawo tun ban biyoka ba gwara ka dawo"
"I almost done guy, don't worry,am on my way very soon.....meye labari?" Murmushi ya kubce masa daya tuna waccan qauyen da irin abubuwan da suka faru
"Labarai zaka ce....but babu ko daya da zan baka a yanzu,idan na samu chance may be zan kiraka,but not now" dariya Aamiru yayi,yasan samir din duk yayi haka ne saboda yana jin haushin rashin dawowar tashi,kafin ya ankara ma ya kashe wayarsa abunsa,sai yabi wayar da kallo yana jinjina kai kawai.

Gaban yalwatacciyar ma'ajiyar kayan sawarsa ya nufa,yafi ta'ammali da qananun kaya fiye da manya,saiya fidda wata shirt light ash da baqin jeans.

Yana tsaka da shiryawar ya soma jin shigowar baqin motoci cikin gidan nasu,yaja dan qaramin tsaki,saiya koma shiryawa slowly,koda ya kammala shirin ma zama yayi ya buda safe dinsa yana ajjiye wasu muhimman takardu.

Kira ne a jejjere ya dinga shigowa wayarsa,wanda ya tilasta masa barin abinda yake din,ya nufi wayar ya daga yana duba me kiran.

Da fari daddy ne,sai kuma ya koma number mommy, lastly kuma jawahir,sai ya zabi ya fara da kiran number jawahir din
"Yaaya,ka fito inji daddy,baqin suna gab da shigowa" yaji jawahir din ta fada,muryarta qasa qasa,
"Ok" ya amsa can qasan maqoshinsa,fuskarsa da alamun gazawa da rashin walwala ya janyo wani tattausan baqin takalminsa da yafi zubi da slippers ya sanya,kana ya miqe ya sale feshe jikinsa da turare,hannunsa riqe sa wayarsa ya fice zuwa ainihin cikin gidan nasu.

Da sallama ya shiga falon nasu,saiya samesu dukka a zaune saman kujera,banda daddy dake tsaye hannunsa daya riqe da wayarsa,daya hannun nasa kuma na a cikin aljihun rigar shaddar jikinsa dinkin tazarce.

Da daddyn suka fara hada idanu,ya jefa masa wani kallo me kama da harara,wanda ya sanya samir din yin qas da nasa idanuwan,kafin ya tako a hankali ya giftashi
"Duk wani qoqari da nake mafi yawancin lokuta saboda kai nake yinsa,amma kuma kowanne lokaci baka da wani qoqari kuma babban farincikin da ya wuce ka bula min qasa a idanuna......" Ya fadi cike da kamalar dake muna tsahon lokuttan daya shafe a duniya,daga haka ya juya a hankali ya nufi qofar barin falon,najwa ta miqe da hanzari ta rufa masa baya.

Shima hannunsa na cikin aljihun wandonsa,ya dunqule su waje guda cike da zuzzurfan tunanin abinda ya aikatawa daddyn daya cancanci qorafi,amma tunaninsa kaf ya gaza gano hakan,saiya maoda idanuwansa kan mommy cike da fatan ta warware masa abinda yayin?,saidai kamar kowanne lokaci taqi basi damar karantar komai,hakanan batace dashi komai din ba,saiya sauke ajiyar zuciya yana yiwa damuwar tasa mazauni na daban,ya maida idanunsa kan teburin dake shaqe da kaya sannan daga bisani ya dubi jawahir daketa buga game
"Hope kowa ya samu abinci a gidan nan?" Earpiece din kunnenta ta zame guda daga ciki sannan ta dubeshi
"A'ah yaya,abincin baqi ne gaba daya,zuwa anjima zasu dora nasu ya nasu" shuru yayi na sakannin da basu wuce biyar ba,still idanuwansa akanta,saiya fara takawa zuwa gaban tebur din,ya ciro hannunsa daya daga aljihu ya dafe teburin yana irga adadin yawan nau'ikam abincin da aka tara,wanda yana da yaqinin ko baqo ashirin ne zasu zo a yau din ya musu yawa
"Taso ki duba wasu daga cikin wadan nan ki zuba musu suci" ya furta kansa tsaye yana duban jawahir daga inda take zaune,idanuwansa da jikinsa na nuna zallar zararrasa da kuma cikar kwarjini.

Daga kai mummy tayi cikin murmushi
"Yanzu zansa zuwaira ta dora musu wani abun,wannan na baqim daddynka ne,ai ba'a taba ba son" kai ya girgiza alamun a'ah
"Indai zamu farantawa wasu daga waje.....na cikin gida da suke tare damu koda yaushe suke qoqarin hidimta mana,su yafi cancanta su fara cin gajiyarmu.....taso ki dauke waccar golden warmer din" ya sake baiwa jawahir umarni.kai tsaye,idanuwan mummy saman fuskarsa tana dubansa,tana son nuna masa tata zararra amma wani abu daga fitowa daga gareshi ya taso ya danneta,ta tsani wannan raunin nata daya jima yana cutarta,duk kuwa da yadda take yaqi dashi babu dare babu rana,rauni ne wanda ada batasan dashi cikin halittarta ba sai yanzu.

Kamar yadda yace haka jawahir ta aiwatar yana tsaye har komai ya kammala,saiya samu daya daga cikin kujerun falon shima ya zauna bayan ya fidda wayarsa yana duba wasu sabbin tractors da aka tura masa da zasu qara cikin kamfaninsu, bulldozer ce da sauran wasu kayan aikin.

Miryoyine a cakude cike da hirarraki dake nuna farinciki da walwala suka doso qofar falon,cikin sakannin da basu wuce biyar ba suka bayyana daga qofar falon zuwa cikinsa.

Mahaifinsa ne,gefansa wani dattijo ne kamarsa,wanda a qalla zasuyi shekaru kusan daya,baikai hasken mahaifinsa ba,saidai kusan tsahonsu daya,duk da cewa daddyn ya dan dara masa,daga bayansu wani matashin saurayine mai kama da mutumin dake gefan daddy,sanye da wani yadi na maza mai tsada da aka yiwa dinkin zamani dai dai jiki,duka duka bisa qiyasi bai wuce shekara sha bakwai ko sha shida ba. Daga can bayansu kuma matane su biyu,matashiyar budurwa da wadda ta data,kana gani kasan mahaifiyarta ce,cikin wani lace dake nuna alfarmar wadda ke sanye dashi,hakanan diyarta dake gefanta,itama lace dinne,saidai nata straight gown ce,tayiwa kanta wani irin dauri daya zauna das a goshinta,sai.mayafin da kwata kwata tsahonsa iyakacin wuyanta zuwa saman kanta ta nade dashi,hannayenta sunsha fixing na faratan kanti,wanda aka yiwa ado da nail polish kalar lace din dake jikinta.

Mommy najwa da jawahir dukkaninsu suka miqe tsaye don nuna farincikin ganinsu,yayin da budurwa tadan taho da sassarfa zuwa inda momy ke tsaye ta rungume kafadarta,itama mummy ta tarbeta fuskarta qunshe da fara'a madaukakiya,ta sanya hannunta a gadon bayanta tana bubbugawa tare da fadin
"Oyoyo daughter jauhar"
"Oyoyo mommy" wadda aka kira da jauhar din itama ta fada fuskarta dauke da fara'a.

Duk wannan abun da ake samir na zaune,hankalinsa saman wayarsa,qasa qasa yaji kamar an kirayi sunansa,daya daga kai kuwa sai yaga daddy ne,wani kallo yake masa da yafi kama da harara,tsam ya miqe tsaye,dai dai sanda baqon me suna honorable bukari mustapha yake duban samir din
"Ah....yarona kana nan ashe" qoqarin sakin fuskarsa yayi kana ya qara taku uku zuwa gabansu,ya miqa masa hannu gami da cewa
"Ina nan abba" qwaqwalwarsa tana tuna masa mutumin,duk da cewa ya dauki wasu shekaru rabon da ya ganshi,hannun ya miqa masa shima sukayi musabaha,yana jaddada yadda yaga samir din ya sake zama babban mutum,cikakken mai hankali fiye da shekarun baya,qaramin murmushi samir din ya saka yana dan ja baya.

Tunda ya miqe yaja dukkan wani hankali nata,ko na minti daya saita kasa janye idanun nata daga kanshi,abinda tunda aka fara zancan tahowarsu wasu kwanaki da suka shude bata taba kawowa zaya faru ba,dui tsahon lokacin da maama ta dauka tana mata bayani bata tsammaci haka ba,cikin dan qaramin taqin lokaci irin wannan.

"Hi"ta fada da zazzaqar muryarta ganin bai lura ma da wanzuwarta a bigiren ba,waiwayawa yayi a hankali,suka hada idanu,ta sakar masa murmushi,shima saiya maida mata martanin murmushinta,yadan daga hannunsa kadan ya maida mata amsa da
"Hi"
"Son......ga hajiya murjana" mummy ta fadi,ya sake juyawa zuwa sashe da take tsaye,cikin girmamawa ya gaidata,ta amsa fuskarta dauke da fara'a farinciki,gami da gamsuwa kan lamari da kusan shi yayi silar takowarsu zuwa cikin gidan,yayi jagoranci kan tafiyarsun,muryar jawahir ta ratsa falon sanda take fadin
"Daddy....... food is ready"
"Da kyau auta... honorable bismillah,mu fara da cin abinci kada lokacin sallar magariba ya shigo"
"To....to babu laifi"sune a gaba,suna takawa zuwa wajen yana jan samir dake gefansa da hirarraki,wanda hakan ya faranta ran daddy qwarai,yayin da mummy maama jauhar najwa da jawahir suka rufa musu baya.

Da kansa samir din ya jawa daddynsa kujera,sai ya bawa honorable damar zama,don haka ya sake ja masa wata,sannan shima yaja tasa ya zauna,su mummy suka qaraso suma kowa ya yiwa kansa wajen zama,duk da hira dake tashi tsakanin mummy da maama,sai kuma jauhar da najwa.
Chapter 35 · 0% Book details