Sashe 37
Dabiar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da tayi bismillah sannan ta saka qafarta soron,a hankali take tafiya cikin sanda kamar wadda ke taoron fadawa wani wawakeken rami,gabanta yayi wani mugun faduwa sanda taxo tsakiyar soron,hancinta ya fara jiyo qamshin wani abu me kama da ganyan taba.
Wani wawan ihu ta saki sanda taji an cafki hijabinta ta baya,ba tare da wani jinkiri ba ta fara kokawar qwace kanta,jin motsin tahowar mutane ya saketa ya koma lokon daya lafe,hakan ya bata damar fellawa da mugun gudu zuwa cikin gidan.
Karo sukayi da ummanta data fito da sassarfa,inna haule dake sashensa itama ta fito saboda ihun dataji din,jikin umman nata ta fada jikinta na wani irin rawa,hannu biyu umman tasa ta riqeta tana tambayarta lafiya?,muryarta na rawa kamar wadda aka watsawa ruwan qanqara ta hada kalmar
"Au....walu ne"
"Wanne auwalun?" Inna laure ta fada bayan ta gama daura zaninta wanda tayi daurin qirji dashi,wanda kusan aikinta kenam,a haka take kwana ta kuma wuni,shi yasa dukka zannuwanta suka kode suka nar rigunanta,ta kuma koma tana gyara daurin dankwalinta dake barazanar suncewa ya bayyana diddigeggen gashinta da kaltum ce dama marufar asirinsa,tunda kowa ta dauki gana dasu bayan karan tsanar data jima da dora musu tabar barin kaltum din tayi mata kitso.
"Auwalu nawa kika sani a gidan nan?"umma ta amsa mata cikin wani irin fushi dakr tashi saman fuskarta,ita kanta inna kauren sai data kalli inna sanda taji ta tofa tata,abinda batasanta dashi ba,duk da kuwa irun cin kashin da take mata cikin gidan
"Ke zuwaira,banason sharri,haka kawai 'yarki taga wani abun daban za'a laqawa auwalu na,koma wanne dan jakar uban ta rakito bari na leqa na ganshi don ubashi zai jawa yarona bacin suna ba gaira babu dalili,baya duk sanya idanun da jama'ar qauyen nan suka masa" daga haka tayi hanyar soron bakadan bakadan,bata ko damu da yanayin suturar jikinta ba.
Umman na tsaye anan tabi laure da kallo,tana zuwa dai dai sanda auwalun ke zuqe sauran abun mayen dake hannunsa,salati tahau rafkawa
"Yanzu dama auwalu baka daina zuqe zuqen nan ba?,to don ubanka zoka wuce ka fice daga gidan nan,ba zaka jawomin magana ba bakin magauta,tattarawa zakayi ka koma inda ka fito,matuqar ba zaka daina abinda kakeyi ba"
"Habba....laure....yawa kike,nifa inason yarinyar nan,tayimin wallahi.....tun....ba yau ba,kuma keda iliya......duka kun sani"
"La'ilaha ilallahu....muhammadu ya rasaulullahi,to wallahi haihata haihata,maza ka fita"ta fada tana tankadashi zuwa waje da hannu bibbiyu har sai data tabbatar ya fice sannan ta dawo ciki.
Babu kunya babu tsoron Allah data dawo ta iskesu a wajen sai tayi mursisi,cikin muxuran borin kunya ta fara magana
"Ajawa yarinya kunya ehe.....banason aikin banza da wofi,shi yana qoqarin yakiceta amma ita tana liqe masa ina dalili?,to wallahi auwalu na dan gata kuma dan asali gaba da baya yafi qarfinta,babu abinda zaiyi da ita"
"Ke laure" inna ta kirata cikin kakkausar murya,cak ta tsaya tana mamakin yadda umman ta kirata
"Idan har ke kin manta abinda ya faru a baya ni din ban manta ba,duk wannan soki burutsun da tabarmar kunyar ba abinda ya shafeni dashi,abu daya nakeso shine,ki jawa danki kune,ki jawa danki kunne,ki jawa danki kunne,bazan dauki duk wani ganganci nasa tsageranci ko rashin kunya akan diyata ba,maganar gata da asali indai kaltume bata dashi to ita da auwalu duka sammakal suke,gata kuma babu gatan daya wuce na ubangiji,duk wani dan adam da zai baka gata to koma bayan gatan ubangiji ne,ki tilastashi yayi qoqarin kiyaye shiga hurumin diyata" ta dakata a nan,sannan ta kama hannun kaltum zuwa ciki ba tare da tabi takan inna laure kota damu da gyadar da tuni kaltum din ta watsar da ita ba cikin qasar dake wajen.
Iya fushin da kaltum yau ta gani a idanun ummanta abune da bata taba ganun makamancinsa ba ko sau daya,tabbas rayuwar auwalu cikin gidan kar barazana ce ga tata rayuwar,sai da umman ta danganeta da dakinta,sun jima zaune shuru babu wanda yace wani abu,a qalla kusa awa guda sanda sukaji muryar babansu yana doka sallama da wannan fusatacciyar muryar tasa,wanda babu abinda yake sawa ta rusuna bare kalaman cikinta su fita da taushi
"Kici gaba da kulawa da kuma takatsantsan,ki yawaita addu'a,daga yau kuma kada ki sake kwanciya baki kulle qofar dakinki ba" saita juya ta fice a hankali jikinta cikin matuqar sanyi.......
*********Jikinta take kakkabewa bayan ta gama yiwa wasu mata su biyu kitso,ta sanya tsintsiyar laushi ta share wajen tas,duk da cewa dan sumunti ne daya fara farfashewa,wanda dama iyakacinsa qofar dakunanasu,inda sukanyi shimfida su zauna,sauran duka qasa ne da yashi.
'yar rumfar da suke dora abinci ta isa,ta shirya itace cikim qwarewa da gwanancewa ta kunna wuta,sannan ta cika tukunya da ruwa ta dora,kafin ta wuce ta daura alwalar sallar la'asar,yau cikin farinciki suke,saboda zuwan yakumbo indo,wadda ta taho musu da buhun shinkafa 'yar hausa,harda kwalin taliya sukutum da guda,taliyar da idan sukaga babansu ya basu ita to babu yadda zaiyi ne,a haka ma baifi cikin wata biyu suci sau daya ba,saidai 'yar murji ta hausa,itama idan ta samu. Ta hada musu da manja da man quli kowanne kwalba bibbiyu,haka take musu,lokaci baya lokaci takan yi musu irin wannan kyautar,ko ita ko kawu ado,ammafa saida su boye,su dinga diba da kadan da kadan suna dafawa,saboda matuqar babansu ya fahimci an kawo tofa babu sauran xaman lafiya a gidan,hakanan su da abincinsa sai bayan wani lokaci mai tsaho,koda wanda ta kawo.ya qare din,amma a yanxun da bai sani ba bakinsu alaikum,zai dauka buga bugar da suka saba sukayi suka dafa,idan yaga dama ya basu saisu tara zuwa lokacin da wanda suke dashi ya qare.
Sanda ta idar umman itama ta fito ta daura alwalar ta bada faralin sallah,lokacin kaltum na gaban tukunya tana sake iza wutar data hura,suna hira jifa jifa da umman,saidai ita umma har yau ranta babu dadi,tun daga lokacin da wancan abun ya faru,har yanzu ba'a sake take ba,tun daga ranar kullum tunaninta shine ta yaya zata baiwa diyarta tsaro da kariya har Allah ya kawo sanda zata bar gidan,tabbas da tana da inda zata kai kaltum din da zai zameta mata garkuwa daga barazanar gidan babu ko tantama zata haqura da zamanta a gabanta ta miqa ta can din.
Sallamar qaramar yarinyar da bata wuce shekara tara ba shi ya tsaida hirar tasu,daga umman har kaltum fuskarsu da fara'a suke kallon yarinyar,kaltum ce ta fara magana
"Hali dubu 'yar gidan gwaggo habiba,yau an tuna damu?,ko gwaggon taki ce ta aikoki?" Dariya yarinyar ta saki tana gaida kaltum,sannan ta qarasa tabarmar umman tana gaisheta
"Cewa tayi nazo na gaya muku batajin dadi,wai ida n yaya kaltume bata komai tazo dan Allah ko yau ko gobe" girgixa kai kaltum tayi
"Dake za'a hada baki ko dubu?,to kwa gama qage qage ciwonku ku haqura" murmushi kawai ummansu tayi,tasa dama za'a rina,saboda tun zuwan habiba gidan na qarshe taga wasu canje canje daga gareta,tasan babu jimawa dama ciwo zai bayyana,kusan kwanaki bakwai kenan tana kasa kunnen jin hakan.
Ga mamakin kaltum sai taji ummansu da kanta tana cewa
"Kice mata zata zo in sha Allahu kinji ko?"
"To ummanmu" dubu ta fada kamar yadda taji habiban tana fada,yarinyar nata dariyar jin dadi ta fice yiwa uwar dakinta albishir.
"Ummanmu....kinsan fa banason zuwa wallahi,ni kunya nakeji,gidan qanwata ne fa" dubanta umman take,tausayinta yana ratsata,banda haka Allah ya shirya ai da yanzun itace adakinta ba habiba ba,saidai tsarin Allah kuma shine dai dai,tasan cewa kaltum din na kunyar zuwa,kodon surutu irin na jama'ar qauyen,duk da cewa ahalin yusufa basu da matsala,mutane ne masu karamci da dattako,har cigiyar babar yusufa take idan taji shurun kaltumen yayi yawa
"Na sani,amma ni kikeso naje naji matsalarta banda abinki kaltume?,kece fa 'yar uwarta,ke kadai take da" shuru kaltum tayi tana gamsuwa da zancan umman,saboda hala bata sake cewa komai ba.
Bilal ne yayi sallama yana shigowa gidan,yayi futu futu da qasa kamar kullum,qoqari kawai yake ya cire gwabza gwabzan takalman qafarsa tare da neman wajen zama,kaltum ta dago taga firfita wutar da takeyi,idanunta ya kada yayi ja saboda hayaqi tana dubansa
"Sarkin nema,a ina ka sake samun wajen aiki kuma?" Sai daya kalli umma sannan ya sosa kansa
"Wajen aikin nan dai nawane?" Idanu kaltum ta zuba masa
"Wanne wajen aiki?,inda na hanaka zuwa?,bilalu bakajin magana?,baka tsoron mutanen nan su illataka?baka son lafiyarka ko?" Fuskarsa cike da alamun damuwa yace
"Ummanmu ce wallahi,ita tace na koma,ki tambayi xunnu,mutumin ne yayi cigiyata akace masa na daina zuwa,da kansa yazo Allah ranar bakya nan kin tafi tsangayar sarki yin kitso,yace na koma,yana da kirki mutumin,ya tambayeni amma nima dalibin makarantar ne ko?,da nace masa bana zuwa bakiga fadan daya ringa yimin ba,yace lallai idan aka gama gini dani za'a koma,zai siya min komai har uniform da litattafai,kuma nima daya yimin fadan sai naji yaya inason na koma,kullum saiya bani ragowar abincinsa,baki gani ba harda nama a ciki" idanu kaltum ta zuba masa,zuwa wani lokaci ta dauke idanunta ta maida kan ummansu,kallon data yi mata yasa ta gane umman tasan komai,kai ta jinjina mata,sannan ta soma magana
"Duk wani abu daka zama a duniya haquri shine jigo da yake maka jagora izuwa wannan matsayin,saurin fushi baya haifar da komai illa dana sani,sa'annan duk sanda wani yayi maka kuskure daga bisani ya dawo ya nuna maka cewa ya gane abinda ya aikata din ba dai dai bane,cikar dan adamtakar mutum shine ya yafe masa,gajen haquri....saurin fushi da saurin yanke hukunci basu da wani amfani arayuwarmu,ina fatan zaki dauki darasi" a hankali kaltum ta gyada kai,dukka maganganun ummansu tasan kan hanya suke,koda yaushe umman tasu burinta shine taga sun zama wasu nagartattun mutane.