← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 79

Sashe 8

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsantsar ruɗu da firgici Gimbiya Tasmir ta buɗe baki tana mai faɗin. "Tuba nake yakai mahaifina, tuba nake ranka ya daɗe, labarin ka yazo mun atayarce bazan taɓa fahimtar me yake nufi ba, karatun ka ya girmi ƙwa-ƙwalwar Gimbiya Tasmir tayarce har yake shirin tarwatsa ta, nazari na da hangen nesa na bakai wurin da kake son yaje ba!
Na roƙeka da abun bauta Gargabilu katai maka kamun yarce zan ɗauka!" Ta ƙarashe maganar cikin wata irin murya tana mai girgiza kai, yayin da manya manyan idanuwan ta kuma suka sake rikiɗewa suna masu komawa kamar garwashi dan firgici.

Juya mata baya yay ba tare da ya tanka mata ba, tukun yayi taku ɗaya, biyu, zuwa ukku daga wurin da yake, kana ya sake juyowa yana mai kafe ta da jajayen idanuwan sa, tukun ya sake ɗaga laɓɓa cikin kakkausar muryar sa yana mai faɗin. "Na same sa ta tsaura-rarriyar hanya ce ba sauƙaƙƙa ba, na same sa alokacin dana futar da tsammanin samun sa, na same sa ta hanyar taimakon abun bauta Gargabili, ba da ban haka ba dako ke ba asamu wanzuwar ki aduniya ba balle har akawo yau." Ya ƙarashe maganar yana mai fara ɗaga ƙafafuwan sa ya doso inda take.

Tsaye ya sake yi a'inda ya tsaya tun farko, wato gab da ita, tukun ya sake saita idanuwan sa cikin nata, sannan ya buɗe baki cikin kaushi yana mai faɗin. "Umarni ne nake baki ba shawara ba, ki gaggauta zuwa ki kwance yaron nan tun kafin komai nawa ya lalace, domin ko wannan yaron da kike gani shine gaba ɗaya duniya ta, sannan kuma shine duniyar ki! Wannan yaron dai da kike hukuntawa bada ban samuwar sa ba da tuni babu sauran tarihin BAƘAR MASARAUTA ayanzu, da tuni kafaffen tarihin mu ya rushe, da tini labarin mu ya shafe, dan haka na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura ki bari sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance saba, muddin kuwa kika watsar da magana ta to ina mai tabbatar miki dake kan ki ƙarshen ki yazo, sannan kuma babin mu ya shafe, domin ko faɗan bani kaɗai yafi ƙarfi ba, hatta da abun bauta Gargabilu yafi ƙarfin sa, cewar boka mai HUTAR KASKO!"
Ya ƙarashe maganar da ƙarfi, tukun ya janye kansa daga saitin fuskar ta, kana ya juya cikin takun sa wanda yake nuni da tsantsar jarumtakar sa ya futa.
SARKI BARBARU kenan, shugaban BAƁAR MASARAUTA wanda yake akan karagar mulkin tsawon shekaru arba'in baya kenan har kawo yanzu. Sarki mai tsantsar girman jiki da kauri, sarkin da sautin tafiyar sa kawai ke razana zuciyoyin Al'ummar da suke ƙarƙashin mulkin sa!

Wani irin tashin hankaki Gimbiya Tasmir ta samu kanta aciki irin wanda tunda tazo duniya bata taɓa riskar kanta aciki ba.
Ɗaga ƙafafuwan ta ta farayi tana mai zaga tanƙashe-shen falon da yakasan ce tsit da shi, kanta asama tana kallon rufin falon, so take ta gano inda zantukan mahaifin ta suka dosa da kuma abun da suke nufi amma gaba ɗaya ta kasa, ko kaɗan bata fahimci inda tsauraran kalaman sa suka dosa ba, abu ɗaya kawai da ta sani shine ransa yayi matuƙar ɓaci irin ɓacin da bata taɓa ganin sa acikin sa ba, tun da take da shi bai taɓa yi mata ko da tsawa ba, sabo da irin mugun ƙaunar da yake mata, amma sai gashi yau har ihu ya mata acikin kunnuwan ta akan wani ƙas-ƙantaccen bawa mara galihu.

Dunƙule tafin hannun ta tayi da ƙarfi bayan ta rumtse idanuwan ta, sabo da yarce sautin muryar mahaifin nata take ta mata amsa kuwwa acikin kunnuwa yana faɗin.
_"Na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance sa ba!"_

"Inaaaa!! Tayaya ma!! Shin me hakan ke nufi kenan?" Ta faɗa da mugun ƙaraji idanuwan ta na furfutowa waje, yayin da jijiyoyin kanta suka futo sukai raɗa raɗa akan goshin ta, tukun daga bisani ta fara ɗaga ƙafafuwan ta cikin sauri tana mai dosar hanyar da zata sada ta da waje takobin ta damƙe acikin tafin hannun ta, har kuma lokacin kalaman mahaifin na basu dena mata amsa kuwwa acikin kunnan ta ba.

Tana futa gaba ɗaya bayi da dakarun da suke acikin harabar wurin suka zube wanwar aƙasa suna masuyin ribda ciki, amma sai dai ko inda suke bata kalla ba balle har ta tsaya cak kamar yacce ta saba, tai shigewar ta gaba cikin sauri kamar ta kifa ƙasa.

Cikin tsantsar sauri dakarun nan nata suka mimmiƙe tsaye, sabo da ganin da sukayi ta shige ba tare da tsaya sun gama gaishe ta ba, balle har ta bawa mariƙi takobin ta suyi gaba.
Dasauri suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar inda tayi, sai dai tun kafin su ƙaraso wurin da take tayi saurin ɗaga musu tafin hannun ta sama tana mai dakatar da su ba tare da tace ƙala ba, tukun ta cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar inda wani garken dokuna suke.

Bata dakata ba har sai da taccima gaban wani ɗirkeken baƙin doki da yake atsaye yana cin ciyawa.

Wani irin mugun tsalle ta buga tana mai ɗanewa kansa, tukun tasanya hannun ta na hagu tana mai damƙar linzamin dake rataye awuyan sa da shi, kana tasa dunduniyar ƙafar ta tana mai dukan cikin sa da matuƙar ƙarfi da ita.

Wata irin haniniya dokin ya saki da matuƙar ƙarfi, tukun ya zabura da mugun gudu yana mai dosar yamma.
Gudu yake ba gudun wasa ba, yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta kasance zaune asaman sa jajayen idanuwan ta kafe akan hanya, yayin da iska ke kaɗa mayawaicin baƙin gashin dake kanta yana tashi sama, ga kuma jibgegiyar rigar ta da ƴammatan bayi keta aikin riƙewa ɗazu da take ta faman tashi sama itama, sabo da irin tsantsar gudun da dokin yake yi.

Cikin lokacin da bai huce daƙiƙa ukku ba duka suka bayyana adai-dai bakin ƙofar ɗakin azaba.
Cak dokin ya tsaya awurin sabo da yarce ta matse linzamin dake jikin sa da hannu.
Sakin linzamin dokin tayi, sannan ta durko daga kansa zuwa ƙasa.
Kana ta miƙar da takobin dake ɗauke ahannun ta tana mai nuna ƙofar nan da ita, sannan ta buɗe baki cikin tsantsar sauti tana mai faɗin. "Gargabiluuuuuuu!"

Take awurin ko ƙofar nan ta fara ɗagawa sama har ta buɗe duka.
Wani irin baƙin hayaƙi ne ke futo daga cikin ta da matuƙar gudu.
Sauke takobin tata ƙasa tayi tana mai cake tsinin ta acikin ƙasa, tukun ta sake rumtse idanuwan ta tana mai yin wasu irin surutai, sannan daga bisani ta buɗe su tana mai buɗe tafin hannun nata ta watsa abubuwan da suka bayyana acikin sa zuwa cikin ɗakin.

Take haske ya bayyana acikin sa, sai dai kuma duk da haka hayaƙin nan dake futowa bai fasa futowa ba da matuƙar tururi.
Ɗaga ƙafafuwan ta ta farayi tana mai matsawa jikin ƙofar. Sake rumtse idanuwan ta tayi tana mai dunƙule tafin hannun ta, sannan ta sake buɗe baki tana mai faɗin. "Rai Rai Rai Buuu Hooo Reeee!!!" Da tsantsar ƙarfi.

Take awurin hayaƙin nan duka ya ɓace ɓat, tukun ta juya baya tana mai zuwa ta funciki takobin ta daga jikin ƙasar da ta cake ta, sannan ta juya tana mai sake nufar cikin ɗakin gadan-gadan.

Tsaye yake ajikin ƙarafan nan da yake ɗaure jikin sa nata faman kar-karwa, yayin da gumi ya jiƙa sa yay masa sharkaf yarce kasan wanda aka tsamo daga cikin ruwa, banda layi da girgiza kai babu abun da yake iya yi, sai kuma buɗe baki da yake ta aikin yi gaba ɗaya leɓun kasa sun bushe sun yi baƙiƙƙirin dasu! Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ba ƙaramun jigatuwa yayi ba, sabo da yarce duka yana yin hallitar sa ta sauya.

Cigaba da taka ƙafafuwan ta tayi tana mai dosar wurin da yake.
Sai da taje har gab da shi tukun taja ta tsaya tana mai ƙare masa kallo, yayin da shi kuma har lokacin kansa ke ɗage asama yana ta faman aikin girgiza sa.

Shiru tai ba tare da tace komai ba, sai kawai idanuwa da take binsa da su tana mai jin tamkar ta shaƙe masa huya ya faɗi ya mutu, ko taji sassaucin baƙin cikin da take ji acikin ranta ta sanadin sa.

Sauke kansa ya farayi ƙasa -ƙasa har ya sauke idanuwan sa duka acikin nata.
Wani irin murmushi ya ƙaƙalo yana mai jifan ta da shi duk da irin wahalar da yake ciki, kana daga bisani ya buɗe baki cikin muryar sa da take tsantsar rawa, sabo da azabar dake sauka ajikin sa yana mai faɗin. "Gimbiyar mu Gimbiyar BAƘAR MASARAUTA... Ya da dawowa yanzu kuma?" Ya ƙarashe maganar yana mai sake jifan ta da murmushi, yayin da har lokacin kuma gumi ke cigaba da tsats-tsafowa ta kowace kafar gashi dake jikin sa.

"Kai ɗin wane ne? Wane ubanka? Wace kuma uwarka acikin BAƘAR MASARAUTA da har kake ja da iko na?" Ta faɗa cikin ƙaraji tana mai sanya idanuwan ta acikin nasa ita ma.

Murmushi ya sake yi yana kallon ta, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Abun da na daɗe ina son sani kenan tsahon shekara da shekaru acikin baƙar masarauta, amma ba damuwa, tunda har kema kin buƙaci ki sani yanzu, shikenan na barki da aikin neman, in yaso duk randa kika gano ko suwaye sai inzo ki faɗamun su nima!" Ya ƙarashe maganar yana mai zaro harshe ya lashi busassun laɓɓan sa, har kuma lokacin bai fasa jifan ta da murmushin da yake aikin yi ba.

"Wat...!
_"Na baki daƙiƙa daga ɗaya zuwa biyar, karki kuskura sukai shida balle har su tsallaka goma ba tare da kin kwance sa ba!"
Muryar mahaifin ta ta sake dukan kunnen ta da matuƙar ƙarfi, tayarce har tai sanadin tsinkewar maganar da take kanyi ba tare da ta kai ba.
Chapter 8 · 0% Book details