← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 79

Sashe 30

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu damu da sai sunyi karatun boko ba, domin kuwa ada kwata-kwata ma basu yarda da ita bokon ba, sai daga baya ne abayan haihuwar Buba da Harisu aka samu wasu turawa tare da haɗin goyon bayan gwamnati sukazo har cikin Masarautar suka ƙarayi musu bayani akan boko tare da muhimmancin sa, kuma Alhamdulillahi alokacin sunyi sa'a, Lamiɗo ya aminta da zancen su duk da kasancewar sa mutum mai kafiya da tsayawa akan magana ɗaya.
Hakan yasa koda Habu da Harisu sukai wayo aka ɗauke su aka kaisu wata makarantar kwana, wacce ake biyan maƙudan kuɗaɗe suka fara tun daga farko anan.

SHEKARA TALATIN BAYA.
1991..........✍

*SHARHI DA TURAWA NAKE BUƘATA DAGA GAREKU FANS, HAKAN SHI ZAI BANI ƘWARIN GWIWAR CIGABA DA RUBUTO MUKU.*

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 12*

*1991*
ƘASAR MALIN, YANKIN JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.

Gudu suke tun ƙarfin su yadda kasan waƴan da sukai gamo da mutuwa, banda faman sakin haki babu abun da suke yi, ga kuma wani irin gumi dake yanko musu ta kowace ƙafar gashi dake jikin su.

Ƴammata ne guda biyu da suke ɗaure da wani ɗan guntun baƙin ƙyalle tare da ƴar ƙaramar riga ajikin su, wato dai sanye suke da shigar su irin ta bayi ajikin su.
Gudu suke sosai tun ƙarfin su suna yi suna kallon sama, ahaka har suka ƙarasa cikin Masarautar tasu, amma duk da haka basu dakata da gudun da suke ba sai da har suka sada kansu da cikin fada.

Da matuƙar sauri fadawan Sarki Barbaru da yake zaune akan wata arniyar kujera, sanye da wasu irin manyan kaya ajikin sa suka miƙe tsaye suna masu dakawa ƴammatan nan da suka faɗo cikin fadar arikice wata irin gigitattar tsawa.
Amma sai dai ko inda suke Ƴammatan nan basu kalla ba sai da har suka dan gana kansu da gaban kujerar da sarki Barbaru yake zaune akai, tukun suka durƙushe aƙasa suna masu sakin haki da tari.

Dasauri Fadawan nan suka sake yowa kansu gadan-gadan cikin tsantsar ɓacin rai, amma sai dai tun kafin su ƙaraso wurin kowanne daga cikin su ya ƙame awurin da yake cak, sabo da yarce Sarki Barbaru ya ɗaga musu hannu sama ba tare da yace ƙala ba, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance ƙur akan Ƴamnatan bayin nan, yana mai mamakin abun da ya kawo su cikin fadar sa a irin wannan yanayin.

Tafukan hannun su suka sanya suna masu dafe ƙirjin su da shi, tukun daga bisani suka sake sunkuyar da kansu ƙasa idanuwan su akan shimfiɗar kafet ɗin da take awurin, kana suka buɗe baki cikin muryar su wacce take ɗauke da tsantsar tashin hankali suna masu faɗin. "Tuba muke ranka ya daɗe, tuba muke da labarin da bakin mu zai furta, domin kuwa mu kan mu mun san bamai daɗin ji bane." Suka faɗa jikin su na tsantsar rawa.

Yayin da wani bafade da yake tsaye agefe ya buga musu wata gigitacciyar tsawa yana mai faɗin. "Ku ƙaz....."
Tsit yay da bakin sa ba tare da ya ƙarasa furucin nasa ba, sabo da yarce Sarki Barbaru ya sake dakatar da shi ta hanyar hannun da ya sake ɗaga masa.

Komawa bafadan yayi zuwa wurin da yake yana mai tsayawa, yayin da su kuma waƴan nan Ƴammatan suka sake buɗe bakin cikin rawar murya suna masu faɗin. Haƙiƙa labarin ba zaiwa kunnuwa daɗin saurara ba, kamar yacce bai mana kyan gani a idanuwan mu muma ba, hakan yasa muke neman gafara gareka ya shugaban mu, domin kuwa ayau ɗin, akuma yanzu munyi mummunan gani ne, irin wanda bamu taɓa yin sa ba!" Suka ƙarasa maganar da sakin haki kansu durƙushe aƙasa, tukun daga bisani suka ɗora da faɗin.

"Munga sama ta juye daga fari zuwa wasu kalolin, giza-gizai na juyewa daga kalar su ta farare suna komawa zuwa jajaye da baƙaƙe, gari nayin duhu tayarce har ba'a iya hangen abun da ke agaba, yayin da ruw...." "Kaiiiii!" Sarki Barbaru ya faɗa da matuƙar ƙaraji yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar da yake cikin tsantsar firgici da ruɗu, yayin da su kuma jikin Ƴammatan Bayin nan ya ɗauki wata mahaukaciyar kyarma, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "Shin me hakan ke nufi kenan? Wane irin mummunan laifin aka aikata da har Ubangiji Gargabilu yake shirin yi mana hukunci ta hanyar juyar da mu?" Ya faɗa da wani irin ƙarfi idanuwan sa duk sun futo waje, tukun daga bisani ya sake buɗe baki cikin ƙaraji yana mai faɗin. "Daƙiƙa ukku kacal na baku, kar ku kus-kura ku bari takai huɗu ba tare da kun samo mun tabbacin labarin nan ba." Ya ƙarasa naganar yana mai watsa idanuwan sa akan fadawan sa da suke tsaye cirko-cirko suma duk arikece, tukun ya sake juyawa ɓarin da Ƴammatan nan suke yana mai faɗin. "Ku sani muddin labarin ya suya daga yarce kunnuwa na suka jiyo sa daga bakunan ku, to awannnan karan ni da hannu na zan luma takobi acikin cikkunan ku!" Ya faɗa cikin ƙaraji, tukun ya juya cikin tsantsar sauri yana mai fucewa daga cikin fadar duka, ya ɗauki hanyar da zata sadasa da wurin Boka mai hutar kasko, domin yaji ko yana da masaniya akan zancen, sabo da shi dai tunda yazo duniya bai taɓa jin wani labari makamancin wannan ba.
Yayin da su kuma Ƴammatan Bayin nan hankulan su ya sake bala'in tashi.
Da matuƙar ƙarfi suka ruƙun-ƙume junan su kamar zasu shige cikin jikin su, suna masu fashewa da wani irin gigitaccen kuka!

ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTA WASAI.

Tun bayan haihuwar Nafisat Gimbiya Fulani bata sake haihuwa ba, sai yanzu da take É—auke da tsohon ciki mai kimanin watanni takwas har da sati Biyu ajikin ta.
Sosai hankalin magautan ta ya sake matuƙar tashi, fargaba da tsoron karta sake haihuwar Ɗa namiji suka cika zuciya da ruhin su, domin kuwa yanzu hakama kullum ƙoƙarin su shine suga bayan Babban yaya, sai dai kuma har kawo yau da yake da kimanin shekara Goma cif aduniya Allah bai basu nasara ba, wanda hakan kuma ba ƙaramu firgita su yayi ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba, amma duk abanza bayaci, danko ataƙaice ma sai kyau da farin jini tare da tsantsar hankali yaron yake ƙarawa awurin jama'a.

Tun daga lokacin da cikin jikin Gimbiya Fulani ya bayyana gaba É—aya hankulan magautan su ya sake tashi, domin kuwa ko kaÉ—an babu wanda yasan da cikin sai dai kawai lokaci É—aya suka wayi gari suka gansa ya futo, hakan yasa suka sake bazawa wuraren Bokayen su, domin ganin sun lalata cikin tun kan yazo duniya, sabo da atsoron su kar suje namiji ne ba mace ba, sai dai kuma duk abun da sukayi abanza, ko kaÉ—an baici ba, domin kuwa gashi nan zuwa yanzu har an fara tsumayen ranar haihuwa.

UNGUGUWAR ÆŠAN TANKI.

Zaune Aishatu take akan kujera gaban murhu ɗauke da ƙaton ciki jikin ta tana tuƙin tuhu.
Yayin da daga can gefe kuma mu'allim da kakar sa mahaifiyar Ishak suke zaune akan tabarma suna hira tana yanke masa farce.
Ayanzu haka yana da shekara goma ne cif aduniya, yayin da ƙannen sa mata suma duka sukai girma tare da wayo sosai sosai, sai dai kuma tun daga kan ƴar ƙaramar su Ruƙayya, Aishatu bata sake haihuwa ba, sai yanzu da take ɗauke da ciki mai kimanin watanni takwas ajikin ta.

"Anya kuwa lafiya kike Aishatu, domin kuwa gaba É—aya tun daga jiya nake lura dake duk kin canza, shin ko dai haihuwar ce ta tawo ne?"

Kaka ta faɗa tana mai janye ƙafar Ahmad da take akan cinyar ta tana yanke masa farce daga jikin ta, tare da kai idanuwan ta kan Aishatu da take tuƙin tuwon amatuƙar sanyaye.

Murmushi Aishatu tayi tana mai cigaba da tuƙin tuwon ta, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Wata irin haihuwa kuma Baba, cikin da dukan sa yanzu ya shiga wata na takwas ma, kawai dai gaba ɗaya jikina ne nake jin sa ba daɗi tun jiya, ga kuma zuciya ta da take ta yawan tsinkewa." Ta ƙarasa maganar cikin sanyi sosai.

"To ai dama jin daɗin jiki ga mata irin ku sai ahankali, tun...." "Assalamu alaikum." Suka jiyo sautin sallamar Ishaƙ wacce ta sanya gaban Aishatu wata irin muguwar faɗuwa, tayarce har sai da ta rumtse ido, yayin da ita kuma kaka tayi shiru da abun da take faɗe ba tare da takai ƙarshe ba.

"Wa'alaikum Salam." Suka faÉ—a atare cikin sanyi, suna masu binsa da idanuwa, sabo da yarce suka gansa ya shigo ba'a irin yana yin da ya saba shigo musu ba.
Yayin da shi kuma Ahmad ya miƙe da sauri yana mai ƙarawa kusa da shi ya riƙe yatsun hannun sa, tare da faɗin. "Sannu da zuwa Abba na."

Damƙe tafin hannun Yaron Ishak yayi ba tare da ya amsa masa ba kamar yacce ya saba, sai jansa da ya cigaba dayi har zuwa kan tabarmar da Kaka take azaune da yayi.

Cire takalman sa yayi agefen tabarmar, tukun ya hau kai ya zauna yana mai lumshe idanuwan sa ba tare da yace komai ba, yayin da Aishatu kuma da kaka suka juyo ɓarin da yake suna masu zuba masa ido, gaba ɗayan su sun kasa yi masa koda sannu da zuwa, sabo da yarce sukaji wata irin fargaba ta lulluɓe su, sabo da ganin sa da sukayi ahaka.

Sai da ya ɗauki kimanin mintina biyu rufe da idanuwan nasa, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai juyawa ɓarin da Kaka take ya kalle ta, sannan daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Ina yini Umma ta."

"Shin meke faruwa ne É—an nan?" Kaka ta faÉ—a ba tare data amsa masa gaisuwar da yake mata ba.

Lumshe idanuwan sa ya sakeyi ahankali, tukun daga bisani ya buɗe su yana mai kaisu ɓarin da Aishatu take zaune, kana ya buɗe baki cikin sanyi ba tare da ya bari ya kalli idanuwan ta ba yana mai faɗin. "Tawo baro gaban murhun nan, ga huri kizo nan ki zauna Maman Ahmad." Ya ƙarasa maganar cikin sanyi yana mai ɗaga ido ya kalle ta.
Chapter 30 · 0% Book details