← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 79

Sashe 46

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki Barbaru ne atsakiya kamar yacce suka saba tawowa idan suna taro, sai dai wannan karan kuma hannun sa ɗauke yake da Ƴar jaririyar da aka haifa.
Yayin da gafe da gafen sa kuma matan sa biyu Gimbiya Haiwa da kuma Gimbiya Salwa mai jego suka kasance, gaba ɗayan su suma sunci uban ado mai matuƙar ɗaukar hankali da tsada a jikin su, a gefen su kuma yaran su ne maza suke biye da su, yayin da bayan yaran kuma da gefe da gefen su kuma duk dakaru ne, hannuwan su riƙe da bulalai tare da makamai soke a jikin su.

Sanye sarki Barbaru yake da wasu irin kaya masu matuƙar kyau da tsada a jikin sa, yayin da jinjirar dake riƙe a hannun sa kuma aka sanya mata wata doguwar riga mai tsananin kywu da tayi mata dai dai a jikin ta, sai wasu ƴan takalma masu tsananin kyau da suke sanye a ƙafar ta.

Kai tsaye suka doshi gaban kaskon hutar da yake a tsakiyar fili dukan su.
Zagaye kaskon sukayi a dai dai lokacin da suka ƙarasa gaban sa, tukun Sarki Barbaru ya yaye showel ɗin da yake ƙudun-dune jikin jinjirar yana mai cillasa cikin hutar kaskon nan, sannan ya ɗaga ta sama yana mai tsayar da ita asaitin kaskon hutar nan, tukun ya buɗe baki cikin sauti yana mai faɗin. "Gargabilu! Garbailu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi.

Take kuwa jama'ar dake wurin suma suka ɗaga murya da matuƙar ƙarfi suna masu faɗin hakan, yayin da ita kuma jinjirar na ta tsanyare da kuka.

Ƙara gyara riƙon Ƴar Sarki Barbaru yayi a hannun sa, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Jama'a ina son ku shaida, ni Sarki Barbaru na sanyawa Ƴata mafi soyuwa a raina suna TASMIR, a yau bayan shafewar kwana bakwai da zuwan ta duniya.
Na raɗa mata suna Tasmir akan darajar shanu ɗai-ɗai ɗai-ɗai har kimanin guda Goma shabiyu mafiya girma daga cikin shanun da nake da su, sannan kuma nayi Al'ƙwarin bata kariya a yanzu, irin kariyar da babu wata ɗiya mace a duniya da take da kamar ta."

"Huuuuuuuuuuu!!!"

Ɗakacin Jama'ar dake cikin filin suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani Boka mai wutar kasko ya taso daga kan shimfiɗar da yake zaune yana mai yowa wurin da su Sarki Barbaru suke.

Hannu ya miƙa yana mai amasar ƴar a hannun Sarki Barbaru a lokacin da yazo, bayan ya gama shirya kayan tsafin sa duka, sannan ya fara saɓulewa jinjirar kayan da suke sanye a jikin ta a bainar jama'a, har ya cire mata su tas, tukun ya rumtse idanuwan sa yana mai kai ta gaban kaskon wuta ya fara sakin wasu irin surutai da matuƙar ƙarfi.

Ya jima yana surutan yadda kasan bazai dena ba, tukun daga bisani ya tsaya da surutan da yake yin yana mai buɗe idanuwan sa, sannan ya sake miƙa hannun sa ya ɗauko wani ruwan tsumin magani da yake a cikin kofi, yana mai wanke ƴar tas da shi, tukun ya sake miƙewa tsaye yana mai ɗaga ƴar sama a hannun sa, kana ya buɗe bakin sa bayan yakai ƙwayar idanuwan sa kan jama'a yana mai faɗin.

"Haƙiƙa kariya ta tabbata a jikin Gimbiya Tasmir irin kariyar da babu mai kamar ta, kamar yacce ubanta ya buƙaci ta samu, sannan kuma Jarumta da ƙarfin zuciya zasu dawamma a gare ta ta sanadin irin ai'kin da aka yi mata."
Ya faɗa yana mai miƙawa Sarki Barbaru ita, yayin da su kuma jama'ar dake wurin suka sake buɗe baki suna masu faɗin.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Da tsananin k'arfi suna masu É—aga hannuwansu sama.

Amsar ƴar sarki Barbaru yayi, tukun ya juya yana mai kaita kan shimfiɗar fatar da take shimfiɗe a gaban su ya kwantar da ita, tukun ya miƙe tsaye yana mai kai hannun sa zuwa kan ƙugun sa, bayan ya shigar da shi cikin al'kyabbar dake sanye a jikin sa, ya zaro wata irin Takobi mai matuƙar tsawo da ƙyalli.

Juyawa yayi gaban mutane yana mai kallon su, bayan ya É—aga Takobin tasa sama, tukun daga bisani ya buÉ—e baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti yana mai faÉ—in.
"Ni Sarki Barbaru, a yau nayi kyautar Takobin tsafi na tare da macijiya ta wacce Kaka na ya bani su zuwa ga ƴata abar ƙaunata Tasmir, domin su zame mata kariya a rayuwar ta."

Ya ƙarasa maganar cikin ƙaraji, yana mai juyawa ya kalli inda ƴar tasa take, tukun daga bisani ya rumtse idanuwan sa da matuƙar ƙarfi, bayan ya ɗaga Takobin tasa ya nuna gefen wurun da jinjirar take a kwance da ita, sannan ya buɗe baki cikin muryar sa mai matuƙar amo yana mai faɗin.
"Rai Rai Rai Rai Buuuu Hoooo Reeeeee!" Da tsananin ƙarfi, take kuwa a wurin Takobin nan tayi wani irin kawo farin haske a jikin ta yana walwali.

Buɗe idanuwan sa yayi a kan Takobin yana mai girgiza kai, tukun daga bisani ya sake buɗe baki yana mai kallon gefen wurin da Jinjirar take a kwanc,e tare da faɗin. "Shairamaaa!" Da tsananin ƙarfi.

Take kuwa wata irin danƙare-riyar macijiya ta bayyana tana mai karkaɗa harshe ta, idanuwan ta ƙur a kan fuskar Sarki Barbaru.
Yayin da shima ɗin yake kallon ta da nasa idanuwan ba ƙiftawa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar mai amo yana faɗin.

"Shairama ga Ƴata nan Mace ɗaya ƙwal a duniya, ina son daga yau ki koma gare ta, sannan kuma ki zamto mata kariya a bokiyar shawara agare ta kamar yacce kika zamto agare ni, ki kasance mai bayyana a duk lokacin da ta buƙace ki, sannan kuma ki share mata hawayen ta a duk lokacin da takawo miki kukan ta, kamar yacce kikai mun, domin kuwa wannan jinjirar da kike gani a gefen ki itace farin ciki na, ina sonta tamkar yacce nake son rayuwa ta, ina sonta irin soyayyar da nake yiwa abun Bauta Gargabilu, wannan dalilin shine ya sanya na bar mata ke ni kuna na haƙura, domin kuwa ni na sani zata fini buƙatar ki, dan haka gata nan kusa dake daga yau itace shugabar ki ba ni ba."
Ya faÉ—a yana mai matsawa kusa da wurin da jinjirar take kwance ya cake Takobin a gefen ta.
Yayin da ita kuma Macijiyar nan tayi wata irin juyawa, tukun ta fara tafiya tana mai zuwa ta fara hawa kan jinjirar ta dinga kanan-naÉ—e ta, sai da ta gama kanan-naÉ—e ta tas, tukun ta zaro harshen ta tana mai lasar fuskar jinjirar da shi, sannan daga bisani ta fara barin jinkin jinirar tana mai yin wurin da Takobin nan take a cake.
Kanan-naɗe Takobin tayi tas, tukun daga bisani kuma ta ɓace ɓat yarce ƙasan ba a taɓa yin ɗuriyar taba a wurin.

Take a wurin kuwa É—aukacin jama'ar dake wurin harda su Sarki Barbaru da iyalan sa suka sanya ihu, suna masu faÉ—in.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Yayinda shi kuma sarki Barbaru ya ƙarasa wurin da huƙar nan take a cake yana mai funcike ta daga cikin ƙasa, sannan yasa hannu ya ɗauki jinjirar tasa, tukun ya juya yana mai kaita wurin Mahaifiyar sa da take tsaye duk a kusa da su.

Amsar ta tayi tana mai sanya mata wasu sababbin kayan da wata Hadima ta miƙo mata su yanzu, ba wayan da aka cire mata ba, tukun ta mayarwa Sarki Barbaru ita.

Gaba ɗayan su ɗaga ƙafafuwan su suka farayi suna masu dosar wurin da kujerun nan suke a ajiye.
Yayin da makaɗa kuma suka cigaba da sakin kiɗi da matuƙar ƙarfi, maraya na ai'kin ɗirkar rawa.

Su kuwa Bayi mata Iyaye hucewa sukayi zuwa wurin da tukwanen nan suke, suna masu buɗe su suka fara ɗibar abinci suna zubawa a manya-manyan farantai, yayin da su kuma Ƴammatan Bayi ke ai'kin ɗaukar abincin suna kaiwa mutane su.

A ɓangaren Bayi Maza manya kuwa, su hurin da shanun nan suke a saƙale suka huce suna masu ciro su, aka zuba musu kayan haɗi akan su, kana aka kwarara musu mai mai matuƙar yawa, tukun suka matsa da su jikin huta suna masu fara babbake su.

Haka dai akai ta shagali a ranar, ana yankan nama anaci tare da kaɗaɗe, maraya na ai'kin dillaƙar rawa kowa cikin tsantsar farin ciki.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Ko ina ka kalla cikin Masarautar jama'a ne suke giftawa ta ko ina, kowa da kalar shigar dake sanye a jikin sa, kasancewar yau ne sunan jinjirar da Gimbiya Fulani ta haifa.

Tun safiya a kayi raɗin suna yarinya taci suna Bilkisu, wato sunan mahaifiya Gimbiya Fulani, hakan yasa Gimbiya Fulani tayi mata laƙabi da BABY.
Sosai a keta shagali tun safe, har zuwa yanzu da a kayi sallah la'asar ana shirin yin hawan suna, kamar yacce aka saba ako wace haihuwa da akeyi a cikin Masarautar.

Yau Yarima Asad jin ta yake tamkar sallah a wurin sa, koma ace fiye da sallah, kasancewar yau ɗin itace rana ta farko da zai fara yin hawa akan doki ba tare da wani ya riƙe masa dokin sa ba, daga shi har Al'amin.

Ana idar Sallahr la'asar a cikin masallacin Masarauta Yarima Asad da al'amin suka futo cikin sauri.
Sanye suke da wasu azababbar shadda ɗin kin doguwar riga tare da wando a jikin su, da sukayi matuƙar yi musu kyau iri ɗaya a jikin su.

Cikin sauri suka kama hanyar part É—in mai Martaba, kasancewar anan kayan su da zasu sanya yanzun suke, domin kuwa gaba É—aya yau É—in kaya iri É—aya suka sanya da su da Mai Martaba, duk da dama shi Asad kusan kullum hakan ne yanzu, dan kuwa rabon da Mai Martaba yayi É—inki shi kaÉ—ai ba tare da an masa ba tun kafun a yaye sa.

Suna shiga cikin part ɗin suka ci karo da Jakadiya zaune a kan kujera daga bakin ƙofar ɗakin Mai Martaba, yayin da hannuwan ta kuma suke riƙe da hula da rawanin su tana mai jujjuya su.
Chapter 46 · 0% Book details