Sashe 63
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye tayi daga bayan sa a lokacin da ta k'arasa wurin da yake, tana mai lumshe kyawawan idanuwan ta.
Tukun daga bisani ta wara su a hankali akan farar-fatar gadon bayan sa da take a bud'e, kana ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in.
"Tabbas rayuwar da babu kai tamkar mutuwa take a wurin Haddiyal Gid'ad'o am, domin ko zuciya da ruhi sun dad'e da yin nunk'aya a kogin k'aunarka.
Ina maka so irin son da ban tab'a yiwa wani mahaluk'i makamancinsa ba a duniya.
Kai ne na fara sani a duniyar soyayya, da kai zuciya tayi sabo, duk da a kullum rashin jin sautin muryar ka na matuk'ar rikitamun lissafi, kallon ka gare ni shi ne ya zamto farin ciki na.
Shin har sai zuwa wane lokaci ne zaka bud'e baki kayi mun kwatan-kwacin irin kalaman da nake maka Gid'ad'o am? Domin kuwa zuciya ta tana gab da yin bindiga muddin za'a cigaba da tafiya a haka."
Ta k'arasa maganar cikin sanyi, tana mai jin wani irin yanayi tattare da ita.
Yayin da shi kuma ya fara juyowa a hankali, har juyo b'arin da take gaba d'ayan sa yana mai fuskantar ta, fuskarsa d'auke da tsantsar annuri.
Sassanyan murmushin sa na ko da yaushe yake jifan ta da shi, yana mai d'an lumshe idanuwan sa, kana ya sake bud'e su akan ta.
"Hak'ik'a ina sonka, kuma zan cigaba da sanka daga nan har zuwa ranar da numfashi na zai tsaya, sannan kuma har zuwa lokacin da zaka bayyana a gareni a zahiri, saboda ni d'in an halliceni ne domin ka, kamar yadda aka hallice ka domin ni."
Ta k'arasa maganar itama tana mai jifan sa da nata kyakkyawan murmushin.
Kana tana mai jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ilahirin sassan jikin ta, yana kwanciya a cikin b'argon ta.
*JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Komai ya sauya a cikin masarautar wasai, tamkar yadda rayuwa take sauyasa ako da yaushe.
Tini Gimbiya Fulani ta aurar da 'ya'yanta mata dukan su sai Baby auta kawai da tayi saura.
A fannin Babban Yaya shima yayi aure tun yana da shekara ashirin da tara, ta yadda har ya ajiye 'ya'ya ukku yanzu, domin kuwa a yanzu haka shekarun sa sun kai talatin da tara zuwa arbai'n a duniya.
A yanzu haka daga shi har mahaifiyar su Gimbiya Fulani basu da wata damuwa face ta hallayar Asad, a kullum basu da aikin yi wanda ya huce addu'oin da suke masa, suna masa fatan Allah ya shirye sa, domin kuwa ba k'aramun sosuwa ransu yake yi ba aduk lokacin da Asad yake gida.
A b'angaren Mai Martaba kuwa shima sosai hallayar Asad d'in ke damun sa, domin kuwa bak'aramun d'aci ransa yake masa ba, idan ya tuna yadda suke yin shiga iri d'aya, tare da zama a wuri d'aya da shi da d'an nasa ada, suna hira a koda yaushe tare, amma yanzu gaba d'aya ya canza yak'i komai na baya, babu irin lallab'in da ba yayi masa akan yasa manyan kaya ya kumaje fada amma gaba d'aya a banza, domin kuwa babu abun da Asad ya tsana a halin yanzu irin Fada, yayin da su kuma manyan kaya yake musu kallon barguna.
Godiyar sa d'aya ga Allah shine da yariga yasan duk iskancin Asad d'in baya shaye-shaye, sannan kuma baya wasa da Sallah ko kad'an, sai dai kuma bayan ita kuma babu wani abu da ya dame sa na addini.
A fannin magautan su kuwa har kawo yau basu fasa jifan su da mugayen abubuwa ba, mussaman ma Babban yaya a yanzu, domin kuwa shi Asad suna ganin sun riga da sun gama da babin sa tun da ya kauce hanyar zama Sarki har abada.
Hakan ne yasa suka duk'ufa akan Babban yaya ba dare ba rana, amma sai dai kullum yi suke tamkar basayi, domin kuwa har yau basu tab'a jin ance musu ko ciwon kai yayi ba, gashi har ya fara tara iyali shima, wanda hakan kuwa ba k'aramun k'ona musu rai yake yi ba.
Tini Baby autar Gimbiya Fulani ta girma, dan ko a yanzu haka ma karatun degree d'in ta takeyi a cikin d'aya daga cikin k'asashen turawa, ita da 'yar gidan Waziri mai suna Fa'iza, domin kuwa a yanzu haka suna da shekaru goma shatara zuwa ashirin ne a duniya.
Sosai Fa'iza take mutuwar san Yarima Asad tamkar ranta, amma sai dai kuma abun takaicin shi ko kallo bata ishesa ba, dan kuwa ko gaisuwar ta ma bako da yaushe yake amsawa ba, sai dai idan suna tare da Baby ne tun daga ranar da ya gane take-taken ta, domim kuwa a cewar sa Allah ya kiyaye ya kula wata daga cikin yaran gidan da sunan soyayya.
Haka kuma ba ita kad'ai bace take son sa a cikin 'yammatan gidan nasu, sun kai su kusan Biyar, amma gaba d'ayan su babu wacce take samun darajar kallon arzik'i ma balle ya kulata.
*UNGUWAR 'DAN TANKI.*
Rayuwa ta canzawa su Aishatu da Iyalanta, ta sanadin aikin da Sheikh Ahmad ya samu na koyarwa a cikin jami'ar su a shekarar da ya gama.
Kasancewar ya futa ne da first class, shiyasa makarantar tasu ta rik'e sa amatsayin malami, wato lecture, kana kuma suka basa damar k'aro karatu ta hanyar nauyin sa da duk suka d'auka, hakan ne yasa acikin shekarar da result d'in nasa ya futo ya sake neman gurbin karatun gaba anan cikin jami'ar tasu, wato masters, inda ya d'auki fannin Tauhid.
Hakan kuwa ba k'aramun dad'i yayiwa mahaifan sa ba dama duk wani masoyan sa ma.
Shekarar sa biyu da fara aikin kacal yayi musu sabon gida na gani na fad'a acikin wata unguwa da take a gaban unguwar su, wacce ta kasance ta masu kud'i, mai suna Babban Zaure Locus, duk da dai gidan nasu ba wai irin tank'ashe-shen nan bane, sai dai kuma a hakan ba k'aramar had'uwa yayi.
Part biyu ne a gidan babba da k'arami, babban part d'in mai d'auke da d'akuna sama da k'asa da kuma k'atoton falo shi ya bawa iyayen nasa, yayin da k'aramin kuma da ya kasance plat building shi kuma ya zauna a cikin sa.
Kasancewar shekara d'aya kawai su kai da komawa gidan shima yayi aure, inda ya auri d'aya daga cikin d'aliban sa na makarantar islamiyyar sa.
A yanzu haka 'ya'yan su biyu shi da ita mace da namiji.
Ishak' mai sunan baban sa shine babba, yayin da suke kiran sa da Dady, sai kuma Aishatu mai sunan maman sa da tazo ata biyu, bayan haihuwar Dady da shekara biyu da rabi, ita kuma suna kiran ta da Amira.
Sosai sunan Sheikh Ahmad yayi matuk'ar shahara a cikin garin Wasai, domin kuwa a yanzu haka shine limamin juma'a na babban masallacin da yake a cikin garin wasai, idan aka cire na gidan sarki.
Sosai girman sa da kwarjinin sa tare da haibar sa harma da kyawun sa suka k'ara futowa, kasancewar a yanzu haka yana da shekaru kusan arba'in ne a duniya.
Yana da motocin hawa har guda biyu 'yan madai-daita masu kyau.
Yayin da Mahaifin sa Ishak' ma yake da ita, wadda shine ya siya masa da kansa.
A yanzu haka matsalar su d'aya ce kawai a gidan duniya, wacce kuma take matuk'ar nuk'ur-k'usar zuciya da ruhikan su, wato Aishatu, domin kuwa har kawo yau bata bar sanya damuwa a ranta ba, ta yadda har ta kamu da ciwon hawan jini mai tsanani, wanda aduk lokacin da ya tashi baya mata da sauk'i ko kad'an.
Ako da yaushe sai tayi kamar ta dena tinane-tinanen, kwatsam rana d'aya kuma sai suga ta koma gidan jiya.
Wannan damuwar da take ciki itace kawai take hana su sukuni gaba d'ayan su, domin kuwa hatta da kaka da d'akin ta yake anan k'asan bene ba k'aramun damuwa take da yanayin Aishatu ba, haka zata zauna wataran tai ta masifa tana fad'in, ta kasa d'aukar dangana sai kace ba musulma ba, kafin daga k'arshe kuma ta koma tai-ta rarrashin ta, wani lokacin ma har k'walla zakaga tana zubarwa.
A fannin fad'an su da Sheikh Ahmad kuwa babu ranar banza da zata zo ta k'are ba tare da sunyi ba, barin ma da aka aurar da k'annen sa mata gaba d'ayan su, ya zamto su biyu ne kawai sukai ragowa shi da autan su mai shekar kusan ashirin da d'aya yanzu take gani, to kullum sai ta takali sheikk Ahmad sunyi ta, domin kuwa shi Auta tasu tazo d'aya da shi sosai, hakan yasa da wuya aji ta fad'i ai'bun sa.
Yayin da Sheikh Ahmad kuma abun ya shafi har matar sa, domin kuwa kullum sai ta ai'bata ta tana kushe hallitar jikin ta, duk da kasancewar ta kyakkyawa sosai kuwa tamkar shi.
Yanzu haka gaba d'aya Ishak' da Aishatu sun aurar da 'ya'yan su mata.
Haka kuma bata sake haihuwa ba tun bayan haihuwar Auta.
*ENGLAND*
Da matuƙar ƙarfi Billy ta rumtse idanuwan ta sabo da abun da ta gani, jikin ta na wata irin karkarwa!
Yayin da ita kuma wannan baturiyar ta k'ara bud'a tafukan hanneyan ta tana mai tallabo k'eyar Yarima Asad da su.
Kana ta farasa harshen ta tana mai lasar saman jajayen lips d'in sa da suke matuk'ar birge ta da shi, kafin daga bisani kuma ta fara k'ok'arin tura harshen nata cikin bakin sa.
A hankali ya d'ago tafukan hannayen sa duka biyu shima, yana mai dire su akan jan gashin dake kanta, kana ya tallabo k'eyar ta, yana mai zaro tongue d'in sa ya hard'o nata da shi, tukun sukayi wani irin had'e bakunan su wuri d'aya suna masu fara kissing d'in junan su da sauri da sauri.
A kuma dai-dai lokacin Billy ta sake bud'e idanuwan ta akan su.
Da matuk'ar sauri ta durk'ushe k'asa tana mai sa tafin hannun ta-ta toshe bakin ta da shi, sabo da wani irin azabbaben kuka mai cin rai da taji ya k'wace mata.
Wani irin k'una take jin ranta da zuciyar ta suna yi mata.
Lokaci d'aya idanuwan ta suka kad'a sukai jajajir yadda kasan gauta, yayin da jikin ta kuma ke wata irin karkarwa tamkar wacce aka sanya acikin ruwa.