← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 79

Sashe 73

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka nan kawai yaji bata da wata sauran k'ima ko kad'an a cikin idanuwansa, domin kuwa ada da farko yayi mata kallon wacce bata san komai ba dan gane da wannan harkar, amma kuma a yanzu da suka buga wasan da ita ya tabbatar da ba wannan ne karon ta na farko ba, domin kuwa ba k'aramun k'warewa ta nuna masa ba.
Wannan dalilin ne yasa yaji gaba d'aya babu wata sauran k'imar ta acikin idanuwan sa, sai dai kuma yana ganin zai cigaba da rakawa da ita a hakan, sabo da lura da yayi data san kanta ba laifi, domin kuwa bai ga wani abu na aibu ba tattare da ita tunda suka fara abun su, asalima sai zallar k'amshin turare da yake tashi ta ko ina a jikin ta, shi kuwa dama a wannan fagen yafi auki, wato tsafta da k'amshi.
Tabbas duk mai yin su to fa suna shiryawa da ita.

_K'alubale gareku 'Yammata, domin kuwa ba a iya novel hakan ke faruwa ba, ko azahiri ma hakane, muddin kikayi gangancin barin saurayin ki ya fara mu'amala da wani sassa na jikinki, to daga wannan ranar duk wani mutunci da yake ganin ki da shi ada zai zube. Zubewa kuma irin warwas d'in nan, ko da kuwa ace shine ya fara nuna miki hakan, kana kuma duk irin mugun son da yake miki, to wallahi daga wannan ranar da kika fara barin sa yana tab'a wani sassa na jikin ki ba tare da kin tsawatar masa ba, to gaba d'aya darajarki ta k'are a cikin idanuwan sa, ta yadda har ba zai ji shakkar fad'a miki ko wane irin kalami ba, kai a k'arshe ma maybe ya bud'e baki ya kiraki da ballagaza a gaban ki._
_Dan haka ku sani babu wata aba soyayyar minti face zallar lalacewa da zubda mutunci, ko da kuwa iya 'yan yastun ki ne zallah saurayin ki ke rik'ewa, to tabbas ki sani fa wani pacentage na daga cikin mutuncinki na raguwa a idanuwansa._
_Allah ka kiyashe mu kasa mufi k'arfin zukatan mu. Rabbi ka shiyar da mu baki d'aya al'ummar musulmi albarkacin Annabi da Al'qur ani. Amin!_

Dan tab'e baki Yarima Asad yayi yana mai ganin yadda take wani irin abu tamkar mai jin bacci, babu ruwan ta da lokacin sallah da ya gabato ma.
Kana daga bisani ya juya yana mai dosar hanyar bathroom.
Yayin da ya fara watsi da kayan jikin sa tun anan cikin falon.

Ita kuwa Billy gaba d'aya wani irin farin ciki ne mara misaltuwa taji yana juyawa da ita.
Tana jin lokacin da ya janye jikin sa daga nata, amma ta kasa yin ko da k'wak'k'waran motsi, sabo da yadda take jin wata irin kasala na sauka a jikin ta.
Hakan yasa ta cigaba da zama a wurin tana mai cigaba da lumshe idanuwan ta.

Acan b'angaren Yarima Asad kuwa cikin sauri yayi wanka, kana a k'arshe ya d'ora da na tsarki.
Tukun ya wuce wurin da bathrobe d'in sa take yana mai d'aukar ta ya sanya ta a jikin sa.
Kana ya kamo hanyar da zata sadasa da cikin bedroom d'in nasa.

Direct ya doshi gaban wardrobe d'in sa.
Wasu tausasan kaya ya d'auko masu matuk'ar santsi ya aje a gefen sa.

Dogon wando ne tare da rigar sa wacce take da dogon hannu ita.
Boxer ya fara sanyawa da farko, tukun ya d'ora dogon wandon a sama.
Kana ya cire bathrobe d'in dake sanye ajikin sa yana mai yin hulli da ita, sannan ya kamo hanyar da zata sadasa da fallo, hannun sa rik'e da rigar wandon jikin sa yana mai b'alle mab'allen ta, sabo da saurin da yake na kar atayar da sallah kafun ya k'arasa masallacin nasu da suke sallah.

Da sauri Billy ta bud'e idanuwanta akan faffad'an k'irjin sa da yake cike da yalwar bak'in gashi sid'ik, ga wata irin k'ira data gansa da ita irin wacce bata tab'a cin karo da namijin da yake da kamar ta ba.
Wani irin yam-yam taji k'wak'walwar ta nayi mata, ga kuma tsigar jikinta da ta fara mimmik'ewa lokaci guda.

Da sauri ta lumshe idanuwanta tana mai fesar da numfashi, sabo da ganin da tayi Asad ya d'ora rigar ajikin sa, wanda ko kad'an ba taji dad'in hakan ba, ita taso ace zai zauna a haka ne gaban tai ta kallon sa, sabo da ba k'aramun kyau yayi mata ba a idanuwan ta.
Tabbas yanzu ta k'ara tabbatarwa da kanta cewar Asad na daban ne a cikin maza, kana kuma ta gane dalilin da yasa yake juya mata duk yadda ransa yaso, kuma suke binsa a hakan.

"Ki tabbatar kin cire k'azantar dake jikin ki, ko kuma kisan inda dare ya miki before na dawo daga masallaci."

Taji sautin muryar Yarima Asad acan k'asa-k'asa yana mai fad'in hakan.
Hakan ne yasa ta juyawa b'arin da yake da sauri, amma sai taga har ya k'arasa fucewa daga cikin d'akin, kuma da alamun dama yana tafiyar ya watso zancen ba wai tsayawa yayi ya kalle ta ba.

Amaimakon taji haushin kalaman da ya gasa mata, sai kawai ta saki murmushi tana mai mik'ewa tsaye.
Kana ta bud'e baki tana mai cewa.

"Kome zakayi ba zanga laifin ka ba my Prince, domin kuwa ka kai kayi ne guy."
Ta k'arasa maganar tana mai dosar hanyar bedroom d'in sa da taga ya futo daga ciki.

Sosai tayi kallo tare da jinjina tsafta da kuma gayun Yarima Asad a lokacin da ta shiga cikin bathroom d'in sa, bayan ta gama kalle abubuwan da suke a bedroom d'in nasa.
Ji tayi inama ace yace ta dawo wurin sa da zama gaba d'aya, tabbas da tasan ta gama dacewa a rayuwa, kana kuma sunan ta zaiyi k'aura a cikin school d'in tasu, tamkar yadda nasa yayi k'aura.

Cikin wani k'aton dustbin ta watsa kayan da ta cire, kamar yadda taga nasa kayan aciki har na jiya data gansa da su, kuma dama ta riga da taji labarin sa na cewar baya tab'a mai-maita kaya idan ya cire, wannan dalilin ne ya sanya itama bata fara gigin adana natan ba.

Sosai tayi wanka mai rai da lafiya, tana mai jin wani irin nishad'i na lullub'e ta ta ko ina.
Tukun a k'arshe bayan ta gama ta janyo sabuwar bathrobe data gani, tana mai sanya ta ajikin ta ba tare da tasa komai daga k'asanta ba.

'Yan igiyoyin jikin rigar ta kama ta d'aure su, sannan ta d'aura alwala, kana ta juyo tana mai futowa daga cikin bathroom d'in.

Gaban dressing mirrow ta huce tana mai shafa had'ad'd'un mayukan da ta gani akan sa, kana a k'arshe ta sake gyara zaman bathrobe d'in da take sanya a jikin ta.
Sannan ta mik'e daga kan kujerar tana mai dosar hanyar da zata sadata da falon.
A kuma dai dai lokacin shima Yarima Asad ya danno kansa cikin fallon.

"Sannu da zuwa honey."

Billy ta fad'a tana mai yin wurin da yake, tare da shirin rungumarsa tamkar ba yanzu tayo alwala ba.
Amma sai Yarima Asad ya kauce yana mai nufar hanyar bedroom d'in sa ba tare da ko kallon fuskar ta yayi ba.

Rumtse idanuwa Billy tayi tana mai jin wani irin a cikin ranta.
Kana daga k'arshe ta koma kan kujerar da take a kusa da ita ta zauna.

Zaman ta baifi da minti biyar ba sai gashi nan ya sake futowa hannun sa rik'e da kaya.

Hullowa Billy su yayi daga wurin da yake a tsaye, kana ya juya yana mai nufar gaban fridge d'in sa.
Bud'e sa yayi yana mai zaro robar ruwa d'aya a ciki.
Kana ya d'auko d'an glass cup d'in da yake kife a cikin fridge d'in.
Sannan ya bud'e murfin jarkar yana mai tsiyaya ruwan a cikin sa, tukun ya juyo yana mai dawowa kan kujera ya zauna hannun sa rik'e da cup d'in.
Yayin da yake aikin kallon Billy ta k'asan ido yana mai sake jin sa a cikin wani irin yanayi, sabo da 'yar shigar da ya gani sanye a jikin ta kawai.

Ita kuwa Billy cikin sanyi ta mik'a hannun ta zuwa kan ledar kayan da taga ya hullo mata akan jikin ta.
Bud'e ledar tayi tana mai zazzage kayan cikin ta akan kujerar.

Da matuk'ar sauri ta furta kalmar.
"Wow."
Tana mai d'an wara idanuwan ta, sabo da arba da tayi da wata had'ad'd'iyar arabian gown tare da iner wear's masu tsananin kyau sun fad'o.

Da sauri ta d'aga rigar sama bayan ta mik'e tsaye tana jin wani irin farin ciki na lullub'e ta, kafin daga bisani kuma ta ajiye ta a k'asa tana mai sa hannu ta d'auki pant d'in da ta gani ajiye a wurin.

Yayin da shi kuma Yarima Asad yake cigaba da kallon duk abun da take ta k'asan ido.

Cikin wani irin salo wanda take fatan yaja hankalin Yarima Asad suyi komai yanzu tayi wani irin cire bathrobe d'in dake sanye a jikin ta.
Take kuwa ta koma tik babu komai a jikin ta.
Yayin da Yarima Asad kuma ya lumshe idanuwan sa da matuk'ar sauri, yana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin sa.

Ita kuwa Billy d'an durk'usawa k'asa tayi bayan ta juyawa Yarima Asad bayan ta, tana mai wara k'afafuwan ta tafara sanya wandon a jikin ta.
Tukun ta d'ago ba tare da ta juya b'arin da Yarima Asad yake ba, tana mai sa hannu ta d'auki best d'in da ta kasance mahad'in wandon, sannan itama ta sanya ta a jikin ta.

Shi kuwa Yarima Asad cikin wani irin yanayi ya sake bud'e idanuwan sa yana mai dire su akan bayan ta.
Jinjina kansa yayi yana mai k'ara tabbatarwa da kansa cewar yarinyar oga ce itama.

Yana kallo ta janyo rigar tana mai zurata ajikinta bayan ta d'an jujjuya jiki kafin ta sata.

Sosai yayi wata irin mazewa yana mai janye idanuwansa daga kanta, ya mayar da su kan wayar sa yana shafawa.

Gaba d'aya ta riga da ta gama rikata sa, amma sai dai kuma ya k'udiri aniyar ba zai nuna mata yasan abun da takeyi ba kwata-kwata, asalima yanzu zai sallame ta, sabo da ta gane shi d'in fa sai ya buk'aci abu yake yi ba wani kesa sa yayi ba.
Chapter 73 · 0% Book details