← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 79

Sashe 4

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kallon sa Yarima Asad bai ba ya ƙara sa bakin bed ɗin yana mai bin kayan da ya gani ajiye akai da idanuwa.
Tattausan farin yadi ne ƙal mai matuƙar kyau, wanda yake ɗauke da irin aikin da ake yiwa rigunan sarakai da baƙin zare mai matuƙar kyau, kai ko baka san kaya ba idan ka kalli wannan yadin tare da aikin dake manne ajikin gaban rigar sa zaka san ba ƙananan kuɗi aka ɓatar ba kafun asamar da shi, agefen yadin kuma wata azababbar alkyabba ce fara mai matukar kyau da ɗaukar idanu, sai baƙin takalmi sandal tare da baƙar hula wacce take ɗauke da sirkin farin zare ajikin ta, waƴan da suma basai an faɗa maka ba kana kallon su zaka san bana ƙananan mutane bane, bayan su kuma sai farin rawani da yake ajiye agefe gaba ɗayan su anjere su akan gadon ne gwanin sha'awa da su.

Wani irin matsiyacin kallo Yarima Asad ya dinga bin kayan da shi yana mai yaƙuna fuska yarce kasan wanda yaga kashi, tukun daga baya ya ɗago kai yana mai watsa idanuwan sa ɓarin da Al'amin yake zaune, wanda shima ɗin shi yake kallo yana mai addu'a Allah yasa ya sanya kayan nan acikin ransa.

Danna lower lips ɗin sa yayi cikin baki yana mai taune sa da haƙora tare da lumshe idanuwa, tukun daga bisani ya wara su akan fuskar Al'amin yana mai buɗe baki yace. "Ina fatan dai ba wai ka ajiye waƴan nan shirgin bane anan wurin, da nufin nine zan sanya su ajiki na ko?"
Ya faÉ—a yana mai sake yamutsa fuska tare da mai da idanuwan sa ya sake lumashe su.

"Dan Allah Yarima Asad ka daure yau kaÉ—ai ka taimaka kasanya kayan nan muje fada please." Al'amin ya faÉ—a yana mai haÉ—e tafukan hannuwan sa wuri É—aya tare da kallon fuskar Yarima Asad a marai-raice.

"Uhm! Amma gaskiya ina ganin da alamu kafara samun taɓin hankali ne guy, imagin ni Asad kake cewa in sanya waƴan nan kayan, ni, ni Asad zan sanya waƴan nan blankets ɗin ajiki na. Tirr god forbid." Ya faɗa yana mai sake juyawa ɓarin da kayan suke ya watsa musu wani matsiyacin kallo.

"Haba Asad, koda baka son irin waƴan nan kayan bai kamata ace a irin rana tayau da ake bikin naɗa babban Yaya Ciroman gida ka ƙisu, domin ko kasan duk masarautar nan babu mai maka irin son da yake ma ko? Dan haka ni a gani na ya kama ta ace wannan ce irin shigar da zakayi ayau kaɗai domin ka taya masoyin ka farin ciki."
Al'amin ya fada cikin sanyi yana mai fatan Allah yasa Yarima Asad ya fahimce sa yasan ya kayan nan acikin ransa.

Mtswww!!! Yarima Asad yaja dogon tsaki yana mai wucewa gaban wadrobe ba tare da ya sake tankawa Al'amin ba.

Buɗe wadrobe ɗin yayi yana mai zaro wani black creazy jeans, tare da farar long sleev t shirt sababbi gadagal ya aje akan bed ɗin, tukun ya sake sa hannu ya zaro wani farin ƙyalle mai kama da hirami yana mai diresa akan bed ɗin shima, kana ya rufe nan yana mai juyawa zuwa inda wata ƴar ƙaramar loka take manne ajikin bango ya buɗe ta.
Wasu irin azababbun agoguna ne masu matuƙar kyau da sarƙoƙin huya suka bayyan aciki, hannu ya sanya ya ɗakko wani baƙin agogo tare da sarƙa mai matuƙar ƙyalli aciki, tukun ya mai da lokar ya rufe ta, kana ya juya zuwa inda kayan suke ba tare da ya sake ɗaga kai ya kalli Al'amin ba yana mai ware su ya fara sanya su ajikin sa.

Cikin mintinan da basu huce biyar ba duka ya sanya creazy jens ɗin tare da farar rigar da tayi matuƙar kama jikin sa, tayarce har ta bayanna hallitar ƙarfin sa, domin kuwa ko singlet bai sanya aciki ba zallar rigar kawai ya ɗora.
Ɗaukar hiramin nan yayi yana mai ware sa ahannun sa, tukun daga bisani ya lanƙwasa sa yana mai nin kasa gida biyu, kana ya ɗago sa yana mai dire sa akan sa ya haɗa da kunnuwan sa ya ɗaure sumar tas, wato dai ya ɗaure kan yarce kasan ɗan kwali, kana ya sake buɗe wata loka yana mai janyo wasu sababbin fararen boot masu matuƙar kyau da girma ya sanya fararen ƙafafuwan sa acikin su, kana ya ɗago yana mai hucewa gaban mirrow hannun sa riƙe da silin sarƙar nan.
Buɗe bakin ta yayi, tukun ya ɗora ta akan huyan sa, kana ya maida bakin nata ya haɗe, sannan ya sake ɗaukar parforms ya feshe ko ina na jikin sa da su, tukun ya juya ɓarin da Al'amin yake zaune sake da baki yana mai karkace kai, tare da ƙanƙantar da idanuwa akan sa yana kallon sa.

Farine ƙal yarce kasan ataɓa sa jini ya ɓullo, faffaɗa ne mai matuƙar tsayi da kauri dai dai misali, yana da doguwar fuska wacce take ɗauke da siririn dogon hanci tare da ɗan ƙaramin baki akan ta, sai fararen idanuwan sa da suka kasan ce su ba manya can ba, sannan kuma su ba ƙanana ba, yayin da gefe da gefen fuskar tasa kuma take ɗauke da kwantaccen baƙin gashi da yabi har ta tsakan-kanin saman bakin sa zuwa haɓar sa, mai matuƙar taushi da yayi matuƙar ƙara haska ka fuskar tasa, sosai sajen nasa yasha gyara yay gwanin ban sha'awa, kai kana ganin sa kasan ba ƙaramun ji yake da sajen ba, sabo da yarce yake futar da wani irin walwali da sheƙi akan fuskar tasa.

Cikin tsantsar ɓacin rai Al'amin ya buɗe baki yana mai faɗin. "Am............✍

*FOLLOW ME ON WATPPAD @umarfaruqD pls.*

*#COMMENTS*
*#VOTE AND SHARE FISABILALLAH*

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎

👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹

_*NA*_

UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*PAGE 02*

"Amma kai da kanka kasan hakan da kai bai dace ba ko Asad, domin ko hatta mai martaba idan ya ganka acikin wannan shigar arana irin tayau wacce sarakunan garuruwa da dama suka halarci gidan nan kasan ransa ba ƙaramun ɓaci zai yi ba ko, ina ma laifin ace kasanya iyakar manyan kayan basai kasa alkyabbar ba, in yaso bayan an gama shagali sai kazo kacire su ka maida irin wanda kake so ko."
Al'amin ya ƙarashe maganar cikin sanyi kamar bashi ne ya fara ta cikin fushi ba, domin ko yasan har dai bata lallami yabi Abokin nasa ba to ko kallo ma bai ishesa ba balle har yayi amfani da abun da yake faɗe .

Kallon sa Yarin Asad ya cigaba dayi har sai da ya bari ya kai ƙarshen maganar sa, tukun ya ɗan taɓe baki yana mai juyawa ya doshi bakin bed ba tare da ya tanka masa ba.

Nannauyar ajiyar zuciya Al'amin ya sauke yana mai sakin murmushi, sabo da yarce yaga Yarima Asad ya nufi inda waÆ´an can kayan suke, amma sai dai ko gama murmushin nasa bai ba ya koma ya É—inke fuska yana mai bin Asad da ido, sabo da yarce yaga ya huce ta gaban kayan ko kallon su baiyi ba balle ya dauka ya sanya.

Direct yayi saitin inda pillow'n sa yaka yana mai zuwa ya ɗauki makullin motar sa tare da wayar sa ƙirar iphone 13 pro max ya riƙe, tukun daga bisani ya juya yana mai dosar ƙofar da zata sadasa da waje ba tare da ya sake kallon inda Al'amin yake ba, yayin da shi kuma Al'amin har lokacin yake binsa da kallo yana mai jin-jina girman rainin hankalin Asad acikin ransa.

Sai da yaje har bakin ƙofa tukun ya tsaya yana mai juyowa ya sake jifan kayan nan da kallon ƙas-ƙanci, tukun daga bisani ya janye ƙwayoyin idanuwan sa daga kansu yana mai -mai dasu kan kujerar da Al'amin yake zaune yana kallon sa baki sake shima.

"Katabbatar ka kwashe waƴannan shirgin banzan naka kafun na dawo, and then idan ka gama abun da kake kana iya rufe mun ɗaki ka ƙara gaba." Ya faɗa yana mai juyawa ya sanya kai ya fuce ba tare da ya tsaya jin abun da Al'amin zai ce ba.

"Kuttt, Amma wallahi sai kaci ubanka Asad, yanzu duk awannin dana ɓata ina jiran ka kagama shiryawa mutafi tare shine har zaka huce ka barni, to dan uwarka baza a kwashe kayan ba kayi duk abun da zakayi." Al'amin ya faɗa da ƙarfi yarce Asad ɗin zai jiyo sa yana mai miƙewa cikin jin haushin sa yabi bayan sa.

"Barka da futowa yaya." Wasu kyawawan ƴammata da suke zaune akan haɗaɗɗun kujerun da suke jere acikin tamfatse-tsen fallon suka faɗa, suna masu kallon Yarima Asad da ya futo daga ɓarin sa.

"Ina mamy take ne?" Ya faÉ—a idanuwan sa akan waya ba tare da ya amsa gaisuwar da sukai masa ba.
Da sauri ɗaya daga cikin su ta buɗe baki tana mai cewa. "Mamy na part ɗin ta, amma bari baby taje ta kira maka ita." Ta ƙarashe maganar cikin wani irin salo wanda yake nuni da tayi hakan ne domin ya ɗago ya kalle ta, amma sai dai ko motsi bai canza ba daga kalar wanda yake yi balle har ya kallo tan, yayin da ita kuma wacce aka kira da baby ta miƙe tsaye da sauri tana mai faɗin. "Ok bara nayi sauri."

"To yaya ga wuri kazauna mana, kafin mamy'n ta ƙaraso ko." Ta faɗa tana mai far-fara idanuwa tare da ɗan buɗa space akusa da inda take idanuwan ta akan fuskar sa.

Taune lips ɗin sa na ƙasa yayi yana mai yamutsa fuska ba tare da yace tak ba, domin kuwa ita bata sani ba ba ƙaramun takura masa tayi ba da surutun da take tayi ma.
Ba tare da ya ɗaga kai ya kalli ko kujerar da take zaune akai ba duk da yarce take ta faman gyara zama tana kwar-kwasa kala kala ya juya yana shirin fucewa daga cikin falon, akuma lokacin ne Al'amin ya ƙaraso falon yana ta faman masifa.

Baice ƙala ba duk da yaji abun da Al'amin ke faɗa, sai ma taɓe baki da yayi yana mai cigaba da tafiyar sa hankali kwance.
Chapter 4 · 0% Book details