← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 79

Sashe 44

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Agefen ta kuwa wasu dattijan matane tsaye akan ta, É—aya na aikin yi mata firfita da furta kalmar sannu gare ta, yayin da É—aya kuma take dafe da bayan ta tana mai faman faÉ—in.
"Yi nishi sosai Gimbiya kin kusa da yardar Ubangiji Gargabilu, yi nishi da ƙarfi kin kusa sannu kinji."
Ta faɗa tana mai shafa mata bayan ta, yayin da ita kuma take ta ƙoƙarin yin nishin tana girgiza kanta.

Wani irin nishi tayi mai matuƙar ƙarfi, tukun daga bisani kuma sai ga kukan jariri nan ya cika ɗakin da matuƙar sauti ba ƙaƙƙautawa.

"Godiya muke abun bauta Gargabilu."
Matan nan biyu suka faɗa cikin tsantsar farin ciki, ɗaya daga cikin su na durƙusawa wurin ƴa macen da idanuwan ta suka gane mata kwance tana cilla ƴan ƙafafuwanta sama tare da sakin kuka...

*ƘASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FULƊE.*

Yau jama'ar cikin Masarautar Fulɗe suka tashi da tsantsar farin ciki, ta sanadin haihuwar da Gimbiya Kaɓel tayi da asuba, kuma abun farincikin shine 'Ya Macen da suke fata a wannan karan ita Allah ya basu.
Zo kuga kuwa farin ciki da murna wurin jama'ar gidan tun daga kan LamiÉ—o har zuwa kan Bayi da hadiman gidan mazan su da matan su.

Kakar su mahaifiyar Lamiɗo kuwa labarin haihuwar na isa kunnen ta ta taso ta tawo daga ɓangaren ta zuwa ɓangaren Gimbiya Kaɓle cikin matuƙar farin ciki.

Sosai tayi matuƙar ruɗewa alokacin da idanuwan ta suka yi mata arba da kyakkyawar Ƴar da aka haifo ƙatotuwa da ita fara tas, cikin kayan fulani na jarirai da aka shirya ta.

Cikin tsantsar farin ciki ta miƙa hannu tana mai amsar ta ahannun Hadimar Gimbiya Kaɓel, bakin ta na furta kalmar.
"Tubarakallah Masha Allah."
Tukun daga bisani ta fara rawa a cikin É—akin É—auke da Æ´ar ahannun ta, kana ta É—ora da faÉ—in.
"Amma akan me za'a sanya mata kaya bayan ba a riga an bata kariya ba, dan haka amshe ta nan ayi maza-maza a cire mata kayan nan afuto mun da ita zuwa ɓangarena, ni kuma yanzu zanje na fara haɗa kayan tsafi, domin kuwa ku da kanku kun sani a ranar da yaro yazo duniya muke bashi makari acikin gidan nan."
Ta ƙarasa maganar tana mai miƙawa Hadimar nan ƴar.
Tukun ita kuma ta juya cikin sauri tana mai gyara ɗaurin zanin da yake a haɓar ta, tare da kama hanyar waje.
Yayin da ita kuma wannan Hadimar ta fara cirewa kyakkyawar jinjirar kayan da suke sanye a jikin ta, tukun daga bisani ta miƙe tsaye hannun ta ɗauke da ƴar ba kaya a jikin ta, sai ɗan showel ɗin da ta naɗe ta a cikin sa tana mai kama hanyar waje.
Yayin da suma sauran matan da suke a cikin ɗakin duk suka miƙe suka bi bayan ta, sabo da suyi kallon shagalin da za'ayi a ɓangaren tsohuwar mahaifiyar Lamiɗo.

Tafkeken wuri ne mai matuƙar kyau da girma. Zagaye yake da ɗakuna irin na fulani a cikin sa.

Gaban wata bukka Kaka ta ƙarasa tana mai sa hannu ta buɗe murfin karar da yake a jikinta, tukun ta danna kanta zuwa cikin bukkar.

Wasu irin kayan karikitai ta ta futo da su riƙe a hannun ta cikin wani baƙin kasko, tana mai zuwa ta ajiye su a bakin ƙofar bukkar, tukun ta koma ciki-cikin sauri, kana daga bisani sai gata nan ta sake dawowa hannun ta riƙe da wani kaskon, wanda yake ɗauke da ruwa a cikin sa, sannan ta sake juyawa still tana mai komawa cikin bukkar.

Bata jima a ciki ba ta k'ara futowa É—auke da wata Sanda irin ta Fulani a hannunta, tana mai zuwa ta a jiye ta kusa da waÆ´an can kayan.
Tukun ta juya bayan ta tana mai kai idanuwan ta zuwa inda wasu maza suke, da alamun dai Hadimai ne su É—in, duba da irin suturar dake sanye a jikin su da ta zamto kalar ta Hadiman.

Daga nan wurin da take ta buɗe murya cikin ƙarfi tana mai faɗin.
"Kai kuyi maza maza kuje gaban rafin gabas, zakuga turamen tsafi na tarihi gaban bishiyar É—orawa ku É—auko mun su."

Da tom suka amsa mata su duka huÉ—un, suna masu juyawa cikin sauri suka tafi.

Dawowar su daga wurin da ta aike sun tayi dai-dai da lokacin da Hadimar Gimbiya kaɓel tare da tawagar ta suka ɓullo wurin, hannun ta riƙe da jaririyar.
Yayin da su kuma Hadiman nan maza suka tawo ɗauke suke da wasu irin manya-manyan turame masu matuƙar girma akafaɗun su.
Ƙarasowa wurin da Kaka take sukayi suna masu a jiye su a gaban ta, wurin da kayan nan suke.
Yayin da ita kuma ta duƙusa ƙasa da sauri tana mai fara futo da abubuwan da suke a cikin kaskon nan.

Wasu irin ƙullikan tsummokarai ta zaro masu matuƙar yawa, tukun ta fara kwance su da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, kana ta ɗibu wasu iccina daga cikin ƙulli ɗaya tana mai zuba su acikin ruwan nan da ya kasance shi ba na zafi ba, sannan kuma shi bamai sanyi ƙarara ba, tukun ta sake ɗibar wani ta zuba sa shima a cikin ruwan.
Haka ta dinga É—ibar su tana zubawa a cikin ruwan É—aya bayan É—aya har tasa duka, yayin da kalar ruwan kuma duka ta sauya lokaci guda, tana mai komawa ruwan É—orawa.

Miƙewa tsaye tayi bayan ta ɗauki wasu layoyi masu matuƙar yawa ta riƙe su a hannun ta, sannan ta juya ɓarin da mazan nan suke riƙe da abubuwan nan da ta ɗauko su yanzu, tana mai faɗin.
"Kuyi maza ku gyara mun turamen nan yanzu, ya zamto sun zagaye wannan kaskon ruwan."
Tayi maganar cikin harshen fulatanci, tukun ta juya ɓarin da Hadimar Gimbiya Kaɓel take tana mai sa hannu ta ɗauki jinjirar nan tsirara, ba tare da ta haɗa da showel ɗin ba.
Yayin da su kuma Hadiman nan maza suka yiwa turamen kamar yacce tace suyi musu.

Layoyin da suke riƙe a hannun ta ta ɗaurawa yarinyar a kan ƙaurin ta duka biyu, kana ta kama damtsen hannuwan ta suma ta sanya musu wasu layoyin, sannan ta durƙusa ƙasa tana mai matsawa gaban kaskon nan, tukun ta rumtse idanuwan ta da ƙarfi tana mai fara yin wasu irin surutai.
Take a wurin wani kalar hayaƙi ya fara futa daga cikin ruwan, yana mai wani irin juyawa, tukun ita kuma ta tsunduma ƴar jinjirar nan acikin ruwan tana mai sanya tafin hannunta ɗaya, ta fara ɗebo sa tana zubasa ajikin ƴar tun daga kan gashin kanta.

Tsanyarewa da kuka jinjirar tayi da matuƙar ƙarfi, yayin da su kuma waƴan nan makaɗan suka fara buga kayan kiɗan su suna masu fara ɗirkar rawa, tare da zagaye turamun nan suna ɗaga hannuwan su sama cikin tsantsar farin ciki.
Ita kuwa kaka har yanzu idanuwan ta a rumtse suke tana aikin sakin wasu irin surutai daga cikin bakin ta, kana kuma tana cigaba da É—ebo ruwan tana zuba sa a jikin jinjirar.

Bata ita ta dena surutan ba har sai da taji ruwan nan ya dena juyawar da yake yi tas, sannan kuma ya dena futar da hayaƙin da yake futarwa, tukun ta buɗe idanuwan ta tana mai kaisu zuwa cikin ruwan.

Wani irin murmushi ne ya suɓuce mata, sabo da yarce taga ruwan ya koma fari kar, yacce take son yayin dama, domin kuwa komawar tasa farin shine yake nufin ai'kin yayi, wato an bawa yarinyar tsafin kenan itama.

Miƙewa tsaye tayi tana mai cilla ƴar jinjirar dake aikin tsala kuka sama, tukun tayi sauri ta caɓe ta, haka tai-tayi mata har kimanin sau ukku, sannan a ƙarshe ta zurata a cikin ɗaya daga cikin turaman nan bayan ta caɓe ta.
Tukun ta juya tana mai zuwa wurin da ta ajiye sandar nan da ta futo da ita.

Ɗaukar ta tayi a hannun ta tana mai riƙeta gagam, sannan ta buɗe baki cikin harshen fulatanci da ƙarfi bayan ta kalli jama'ar dake wurin, tana mai faɗin.
"To Jama'a ku shaida, ni Gimbiya Unau, matar Tsohon LamiÉ—on Masarautar FulÉ—e, nayi kyautar sandar tsafi na ta gado wacce nima na gaje ta a wurin Kakata ga kyakkyawar jika ta da aka haifomun ita yau halak malak, domin ta zamto mata kariya a rayuwar ta."
Ta ƙarasa maganar da sakin murmushi, tana mai matsawa gaban turaman nan.
Yayin da su kuma makaÉ—an nan suka canza salon kiÉ—i bayan jama'ar hurin sun saki ihu da tafi, a lokacin da Kaka ta gama bayanin ta.

Sosai wurin ya sake turnuƙewa da rawa da ihu, sabo da kiɗan da ke tashi mai tsantsar daɗi.
Yayin da ita kuma kaka ta ƙarasa zuwa gaban turmin da jinjirar nan take a ciki, sannan ta ɗaga sandar ta tana mai riƙe ta da hannu biyu, tukun ta fara zagaye turaman tana mai yin wasu irin kalamai da ƙarfi, kana daga bisani ta tsaya a gaban wanda jinjirar nan take a ciki, tukun ta ɗan zura sandar cikin turmin tana mai durƙusawa ta kamo hannun jinjirar da yake a dunƙule ta warasa, tukun ta ɗora sandar akan tafin hannun yarinyar.
Take kuwa ta ɗan riƙe jikin sandar a ƙoƙarin ta na ta sake rumtse hannun ta.
Hakan ya sanya Kaka rangaɗa wata irin buɗa da matuƙar ƙarfi, tukun ta janye sandar daga cikin turmin tana mai faɗin.
"Haƙiƙa kyauta ta karɓu, ke kika zamto ƴar gata gare ni, domin kuwa ke kaɗai ce kika samu kyauta mai daraja irin ta sanda ta a wuri na."
Ta ƙarasa maganar tana mai a jiye sandar a ƙasa, sannan ta koma ta ɗauko jinjirar a cikin turmin, tukun ta miƙa ta zuwa hannun Hadimar Gimbiya Kaɓel.
Amsar ta tayi tana mai sanya ta cikin showel ɗin ta lulluɓe ta da shi, tukun ta juya ita da tawagar ta da suka biyo ta suna masu komawa wurin da suka futo.
Yayin da ita kuma Kaka ta fara É—ibar kayan tsafinta tana mai mayar da su cikin bukkar nan, su kuma waÆ´an nan turamen Hadiman nan suka sake É—aukar su suna masu tafiya da su wurin da suka É—auko su.
Chapter 44 · 0% Book details