Sashe 50
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tamfatse-tsen office ne mai matuƙar girma da kyan tsari.
Jere yake da wasu haÉ—aÉ—É—un kejeru masu tsanin kyau da taushi acikin sa, yayin da daga can gefe É—aya na cikin office É—in kuma wani haÉ—aÉ—É—en table yake kafe a wurin, sai daga bayan table É—in kuma kujera ce mai tsantsar kyau irin wacce ke juyawa da mutum idan yana kai, yayin da saman teburin kuma yake É—auke da takaddu tare da system akan sa.
Direct doctor muhammad ya huce zuwa kan table É—in, yayin da su kuma su Mai Martaba suka zazzauna akan kujerun nan suna masu fuskantar sa.
Gyaran murya yayi yana mai sa yatsun hannun sa ya cire maɓalli ɗaya daga cikin maɓallayan dake jikin gaban rigar sa.
Kana daga bisani ya buÉ—e baki cikin sanyi yana mai faÉ—in.
"Haƙiƙanin gaskiya dai shi ne, munyi iyakar yin mu, sannan kuma munyi amfani da duk abun a ya kamata muyi, domin mugano abun da ke damun sa, amma sai dai kuma gaba ɗaya binciken da mukayi babu wanda yay mana nuni da wata matsala da take tattare da shi, asalima duka result ɗin suna nuna negative ne na duka tests ɗin da mukayi masa, sai dai kuma munyi nasarar dai-dai ta numfashin sa tare da bugun zuciyar sa, but yanayin zafin jikin nasa ne har yanzu babu abun da ya ragu, sannan kuma shima ɗin bai farfaɗo ba."
Doctor Muhammad ya ƙarasa maganar cikin sanyi, domin kuwa ya yi iyakar yin sa amatsayin sa na cikakken Medical Doctor, amma bai gano komai na dan gane da abun da ke damun yaron ba, kuma baya tinanin ko sun bar nan sunje wani wurin za adace ɗin, domin kuwa gaba ɗaya kayan ai'yukan da yake amfanni da su a cikin asibitin nasa duk irin na ƙasashen turawa ne, wato irin waƴan da ake amfanni dasu acan ɗin ma idan an kai mutum, kasancewar sa mutum wanda yake da kuɗi, sannan kuma ya taso cikin ruwan kuɗi a gidan su, domin kuwa shi kansa duka karatun nasa ba a Ƙasar Hausa yayi sa ba, hatta da primary kuwa.
Wani irin zazzafan numfashi Mai Martaba ya fesar, yana mai jin kansa na sara masa, ga kuma idanuwan sa da sukayi jajajir, alamun ba ƙaramun tashin hankali yake ciki ba.
Galadima ne ya buÉ—e baki cikin sanyi yana mai faÉ—in.
"To yanzu mene abunyi kuma a gaba Doctor, bi ma'ana me kake ganin zaku iya sake yi masa, ko kuma wane wurin kake tinanin zamuje bayan nan wanda suke da kayan aikin da sukafi naku?"
Girgiza kai Doctor Muhammad yayi yana mau É—an yin shiru, tukun daga bisani ya buÉ—e baki bayan ya É—ago ya kalle su, yana mai faÉ—in.
"Haƙiƙa bazance kuma ga wurin dana sani ba wanda nake da tabbacin yafi nan, domin kuwa a duk faɗin Jahar Wasai babu wani Asibiti da ya kai namu, sabo da mu kaɗai ne muke amfani da kayan aiki irin waƴan da ake afanni da su a Asibitocin mu na ƙasashen waje, amma sai dai kuma ni atawa shawarar sai nake ganin mai zai hana a gwada na Islamic chemist, wato na musulunci ko Allah zai sa adace."
Ya faÉ—a yana mai kallon su.
Yayin da su kuma dukan su sukayi shiru ba tare da wani ya iya furta komai ba.
Sun É—auki tsayin mintina biyar a hakan, tukun daga bisani mai martaba ya buÉ—e bakin sa bayan yasa yatsun hannuwan sa ya sharce gumin dake tsats-tsafowa akan goshin sa, yana mai faÉ—in.
"Ina ganin shawarar taka ita zamubi Doctor, dan haka tun yanzu nake tinanin zamu shirya tafiyar, domin kuwa akwai wani Babban malami na da yake zaune a London, malami ne masanin Al'qur'ani tare da litattafai, da kuma magun-guna irin na Islamic, domin kuwa a wurin sa nayi karatu na a lokacin da nayi zaman Saudiyya, to daga baya ne yanayin ai'ki ya mayar dashi can ƙasar London, dan haka ayau-yau ɗin nan zamubi Private Jet mu tafi."
Ya ƙarasa maganar yana mai miƙewa tsaye.
Hakan da suka ganine ya sanya su suma dukan su suka miƙe tsayen har doctor, tukun suka juya suna masu fucewa aga cikin ɗakin.
Tamkar gawa haka Mai Martaba ya sake ɗakko Asad a hannun sa bayan anyi dischargen nasu, domin kuwa kwata-kwata yaƙi ya bari aɗora sa akan gadon marasa lafiya, shi da kansa yake ɗaukar abun sa.
A haka duk suka shige cikin motocin su da dogarawa suka yi musu ƙawanya, tukun matuƙan ciki suka jasu suna masu fucewa daga cikin hospital ɗin.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka fara cuku-cukun tafiyar su Mai Martaba Kasar London.
Misalin Æ™arfe goma na dare dai-dai Private Jet É—in da suka kama wanda ya zamto su biyun ne kawai acikin sa, wato daga Mai Martaba sai Asad É—in, ya É—aga zuwa sararin samaniya.............âœ
_Kadanba na gaji haka_ 😟
*BAƘAR MASARAUTA*
*NA*
UMAR FARUQ*D*
*PAGE 20*
Sosai Gimbiya Fulani da duk wani makusancin ta masoyin ta kuma suka shiga cikin matsanan ciyar damuwa, jin abun take tamkar Al'mara, domin kuwa lafiya ƙalau Asad ya bar wurin ta alokacin da aka kira sallahr la'asar, suka tafi masallaci tare da Al'amin, ba tare da yace mata yana ko ciwon kai ba.
Kusan duk jama'ar dake cikin masarautar sun shigo sun mata jaje, sai ƙalilan ne kawai basu shigo ba, irin su Gimbiya Huwaila da kuma Gimbiya Amina kishiyoyin ta.
Sai dai kuma ko kaɗan abun bai dama ta ba da rashin zuwan nasu, sannan kuma bai bata mamaki ba, domin kuwa tariga da ta daɗe da sanin babu wata mai ƙaunar ƴaƴan nata a cikin su,.
Hakan yasa ta duƙufa kaiwa Allah kukan ta, tana mai roƙon sa akan ya tada kafaɗun Ɗan nata.
_LONDON_
Sai a washe garin ranar da suka isa, tukun mai martaba ya fara bincikar gidan Sheikh Yaƙub, wato malamin nasa, bai wani sha wata wahala ba wurin neman gidan ya gano sa, sabo da dama ba wannan bane zuwan sa na farko.
Cikin girmamawa tare da mutun-tawa sheikh Yaƙub ya tarbi Mai Martaba da hannu bibbiyu a cikin falon sa da yake sauke baƙin sa cikin sa.
Bayan sun gama gaisawa ne Sheikh Yaƙub ya buɗe baki idanuwan sa akan Asad da yake kwance a kan cinyar Mai Martaba, tamkar yadda yake jiya yana mai faɗin. "Yaron ba lafiya ne, ko kuwa bacci yayi maka a hanya ne?"
Girgiza kai Mai Martaba yayi yana mai kai idanuwan sa kan fuskar Asad ɗin da yayi wata mahaukaciyar rama daga jiya zuwa yau a hakan da yake, tukun daga bisani ya ɗago kai idanuwan sa akan fuskar Sheikh Yaƙub, yana mai faɗin. "Lafiyar ce dai babu Ya Sheikh, domin kuwa tasanadin ta mukazo nan wurin naka ma." Mai Martaba ya faɗa murya asanyaye, cikin harshen larabci kamar yadda suke maganar da shi dama.
"Subahanallahi! Meke damun sane haka to?"
Shikh Yakub ya tambaya yana mai miƙewa tsaye daga kan kujerar da yake ya nufi wurin su mai martaba.
Gyaran murya mai martaba yayi, tukun ya fara bawa Sheikh Yaƙub labarin duk abun da yasan ya faru har zuwa asibitin da sukayi, da kuma shawarar da likitan su ya basu na cewa su haɗa da maganin addini.
Girgiza kai Sheikh Yaƙub yayi alokacin da ya gama jin bayanin Mai Martaba, hannun sa riƙe da ƴan yatsun Asad.
Tukun daga bisani ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in.
"Tabbas kuwa ba abun mamaki bane hakan ya kasance, domin kuwa mutum babu abun da bazai iya ba, amma in banda rashin imani ma duka-duka nawa wannan yaron yake, me yasa ni ne ma da har za'a cutar da shi irin haka, but ba damuwa insha Allah zai warke tas nan kusa bada jimawa ba."
Sheikh Yaƙub ya faɗa yana mai sa hannu ya ɗauki Asad daga kan cinyar mai martaba, tukun ya juya yana mai dosar wata ƙofa da take a cikin fallon, bayan ya cewa Mai Martaba ya biyosa zuwa ciki.
ÆŠan madai-daicin É—aki ne mai matsakaicin girma.
Ɗauke yake da magun-guna kala-kala irin na addini, tun daga kan na ruwa har zuwa na gari, da suke aje akan kantocin da suka yiwa ɗakin ƙawanya.
Yayin da daga ɓari ɗaya kuma aka ajiye wani ɗan gado irin na Asibiti.
Direct Sheikh Yaƙub ya huce da Asad zuwa gaban wannan gadon na cikin ɗakin, tukun ya ɗorsa akan sa, kana ya juyo ɓarin da mai martaba yake yana mai masa nuni da wata kujera da take ajiye a gefen gadon, yace ya zauna a kanta.
Hannu mai martaba yasa ya matsar da kujerar bakin gadon, tukun ya zauna akai, yana mai riƙo tafin hannun Asad cikin nasa yana murzawa.
Sosai yake jin tausayin ɗan nasa na ratsa ko wane lungu da saƙo na jikin sa, yana kwanciya a ɓargon sa.
Kana yana mai jin a ransa muddin abun nan ya zamto gaskiya, wato asirin akaiwa ɗan nasa, kuma ya zamto ya gano wanda ya ai'kata masa hakan, to kowaye shi sai yaga ƙarshen fushin sa, sai ya masa hukunci na dai-dai laifin da ya ai'kata masa.