← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 79

Sashe 66

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me yaja maka Jarumi na? Akan me zaka shiga harkar Gimbiya bayan kasan ita É—in ba tsaran ka bace ba?
Wayo ni, wayyo ni na shiga ukku na lalace."
Iyar bayi ta sake faɗa a tsantsar ruɗe tana mai jijjiga Bir, gaba ɗaya hankalin ta idan yayi dubu sai da duka ya tashi, domin kuwa tana yiwa Bir wata irin soyayya, fiye da wacce ta kewa duka sauran yaran data raina, tana mai jin sa a cikin ranta tamkar ita ta tsugunna ta haife sa, ita kanta wasu lokutan har mamakin kalar soyayya da take yiwa Bir ɗin take, amma idan ta tuna da itace ta riƙe sa tun ranar da yazo duniya, ta kula da cinsa shan sa wankan sa da komai nasa, sai taga ai dole ne ta jisa a ranta.
Shi yasa duk wata damuwarsa take zamtowa tata damuwar itama.

Da matuƙar sauri ta jayue kan Bir daga cinyar ta tana mai a jesa a ƙasa, tukun ta miƙe cikin tsantsar ruɗu tana mai kama hanyar ɗakinta.

Ko minti biyar ba tayi ba da shiga ɗakin sai gata nan ta futo hannun ta ɗauke da ƙwarya, tana mai sake yowa inda suke.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta zuba duka ƙullikan magun-gunan data ɗauko na ciwukan a cikin ruwan da yake a cikin ƙwaryar.
Sannan ta fara É—ibar ruwan da hannun ta tana mai watsawa Bir shi a jiki.
Yayin da gaba É—aya wurin kuma ya kasance zagaye da Æ´an uwan su Bayi suna ta kallon su.

Shi kuwa Bir lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin yadda ruwan ke ratsa duka ciwukan jikin sa.

Amma ko kaÉ—an ba sune damuwar sa ba, asalima babu abun da yake gani a cikin idanuwansa face kyakkyawar fuskar Gimbiya Tasmir.
Yayin da yake ganin ɗan ƙaramin bakin ta a cikin idanuwan sa a lokacin da take motsa sa tana tambayar sa waye shi.

Lokaci ɗaya wani irin murmushi ya suɓuce masa ta gefen baki, sabo da tino yadda ranta yayi tsantsar ɓaci da yayi, domin kuwa ba ƙaramun kyau yaga ta sake yi masa ba a hakan.

Ji yake inama ace yanzu ma idan yayi wurin zai sake ganin ta, tabbas da babu abun da zai hana sa sake tsayawa a wurin, domin ya ƙara arba da kyakkyawar hallitar ta.

Sosai Iyar Bayi ta shafewa Bir duka jikin sa da maganin nan.
Kana bayan ta gama ta É—ago kansa tana mai buÉ—e baki tace.
"Shin ma mene ya kai ki shiga sabgar Gimbiya Jarumi na?
Yanzu duba fa kaga irin illar data sanya aka yi maka."

Ta ƙarasa maganar cikin sanyi, idanuwan ta a kan fuskar Bir da take ganin yana ta sakin murmushi lokaci bayan lokaci.

A hankali Bir ya fara buÉ—e idanuwan sa har ya buÉ—e su duka akan fuskar Iyar Bayi.
Tukun ya saki wani irin murmushin gefen baki yana kallon ta, kana ya buɗe baki cikin yin ƙasa da murya, ta yadda ita kaɗai zataji abun da zaice mata, yana mai faɗin.

"Rabo ne Iya ta."

"Rabo kuma Jarumi, wannan wana irin rabo ne haka mai tafe da tsantsar tsautsayi?"

Iya ta faÉ—a tana mai kallon Bir, tare da mamakin jin furucin da ya futo daga cikin bakin sa.

"Ba zaki taɓa fahimta ba a yanzu Iyata, amma tabbas akwai lokacin yana nan zuwa, wanda ba iya ke kaɗai ba kowa ma zai fahimta."
Ya ƙarasa maganar yana mai sake lumshe idanuwan sa, tare da gyara kwanciyar kansa akan cinyar Iyar Bayi.

Yayin da ita kuma tayi sakato tana mai binsa da idanuwa, fargaba da tsoron abun da yake shirin aikatawa na cika zuciya da ruhinta, domin kuwa tasan halin É—an nata, duk abun da yace zaiyi to fa zaiyi san da gaske bada wasa ba.

"Koma dai mene ne Jarumi, na roƙeka daga yau akan karka ƙara cewa zaka tsaya akan hanyar Gimbiya tamkar yadda kayi yau, domin kuwa ban shirya yin kukan rashin ka ba anan kusa."
Cewar Iyar bayi tana mai cigaba da shafa kansa.

*ENGLAND*
Cikin tsantsar farin ciki Billy ta koma mazaunin su.

Ko da ta koma zaune ta samu Zee a gefen bed tana kwalliya, da alamar futa zatayi itama.

Inda take bata kalla ba ballan tana har ta bata labarin abun da ya faru, domin kuwa tun da ta ga Zee bata bata karfin guiwa ba akan son da take yiwa Yarima Asad gaba ɗaya ta dena bata labarin sa, sannan kuma ta kudurta a ranta cewar sai ta bata mamaki, sai ta tabbatar mata da cewa ita Billy'n da ban take da sauran matan, haka kuma tun da ta zo duniya bata taɓa neman abu ta rasa -sa ba.

Yayin da Zee kuma ta juyo ɓarin da Billy take fuskar ta ɗauke da far'a, tana mai faɗin.
"To ya dai Beb, ina fatan dai yau an dace ko?"
Ta ƙarasa maganar tana mai gumtse dariya a cikin bakin ta.
Yayin da ita kuma Billy ta kalle ta tana mai faÉ—in.
"Uhm!" Kawai.
Kana tayi shiru tana mai É—aukar wayar ta ta fara shafata.

Miƙewa Zee tayi tana mai fucewa daga cikin room ɗin gumtse da dariya a cikin bakin ta, yayin da cikin zuciyar ta kuma takewa Billy kallon ƴar wahala.

*WASHEGARI*

Da mafarkin YarimaAsad Billy ta kwana, kamar yadda ta kwanta da tinanin sa a ranta.
Hakan yasa yau tana ta shi da safe ta shirya shaf-shaf cikin shigar doguwar riga tare da ɗan ƙaramin mayafi akan ta, tana mai fucewa daga cikin room ɗin su ba tare da ta yiwa Zee ko sallama ba.

Direct ta huce wani haÉ—aÉ—É—en wuri da akayi sa domin gyaran gashi, tun daga kan na maza har zuwa na maza.
Sosai wuri yayi bala'in haÉ—uwa, domin kuwa gaba É—ayan sa anyi sa ne da glass.

Ba tare da ɓata lokaci ba aka fara yi mata gyaran gashin tare da wankin ƙafafu, kasancewar wuri ne babba da yake cike da wadatattun ma'aikata, shi yasa ba afiya haɗa dogon layi ba ana jira kafin azo kan mutum.

Cikin lokacin da bai zarce awa ɗaya ba aka gama yi mata gyaran gashin nata tare da wankin ƙafafuwan, tukun ta zauna wata baturiya ta fara tsantsara mata wasu irin ƴan mitsi-mistin kitso da gashin dokin da jelolin sa suke saukowa har zuwa gadon bayan ta.

Sai da suka ɗauki kimanin awa huɗu suna abu ɗaya tukun aka gama, kuma wai a hakan ma sabo da an yiwa kan nata rubdugu ne, domin kuwa bayan waccan da ta fara yi mata har da wasu matan guda biyu ne suka ƙaru akan ta, wato dai mutum ukku ne suakyi mata kitson.

Misalin ƙarfe ukkk na rana ta dawo mazaunin su.

Zaune ta tadda Zee akan kujera tana cin abinci.

Da sallama É—auke abakin ta-ta shigo É—akin.
Kana ta huce zuwa kan dining table É—in da ta hangi food flask ajiye a kansa, tana mai zuwa ta fara zuba abincin da yake É—auke a cikin su.
Yayin da Zee kuma ta juyo gare ta tana mai faÉ—in.
"Ke ko Billy wannan wane irin gyaran kai ne aka miki haka mai jan mugun lokaci."
Ta ƙarasa maganar tana mai ture plate ɗin dake kan cinyar ta, tukun ta tashi tana mai dosar wurin da Billy take.
Yayin da ita kuma Billy ta buÉ—e baki daga wurin da take tana mai faÉ—in.
"Da yake ba iya gyaran kan kawai akayi ba, har kisto sai da aka yi."
Ta ƙarasa maganar tana mai zame mayafin kanta kitson ya bayyana.

"Kai masha Allah, kinga yadda kitson yayi bala'in haÉ—uwa kuwa Beb.
Kai tukunna ma, wai meke faruwa ne haka da na ganki tun jiya kina ta wasu gyara-gyare?"
Zee ta faɗa daga wurin da take tsaye idanuwan ta akan kitson Billy, da yayi matuƙar tafiya da ita.

"Ba zaki gane bane Beb ko nace zan miki bayani I know, but just wait and see, ina mai tabbatar miki da sai na baki mamaki a yau -yau É—in nan."
Billy ta faÉ—a in serious toungue, tana mai sakarwa Zee murmushi.

Yayin da Zee kuma ta jijjiga kai daga wurin da take tsaye, sabo da fahimtar inda kalaman Billy suka dosa da tayi.
Kana daga bisani ta buÉ—e baki tana mai faÉ—in.
"Can't wait to see, but firstly ina miki fatan Al'khairi."
Ta ƙarasa maganar tana mai komawa kan kujerar da ta tashi ta zauna, tare da mayar da idanuwan ta kan tv'n da take kallo.

Misalin ƙarfe huɗu na yamma dai-dai Billy ta futo daga cikin bathroom.
ÆŠaure take da wani lallausan farin towel a jikin ta.
Yayin da hannun ta kuma yake riƙe da wani ɗan ƙarami tana mai tsane ruwan jikin ta da shi.

Direct ta huce gaban dressing mirrow ɗin da yake cike danƙam da kayan kwalliya kala-kala.

Kujerar da take ƙarƙashin sa ta janyo tana mai zama akan ta, tukun tayi wurgi da ɗan ƙaramin towel ɗin da yake riƙe a hannun ta a ƙasa.
Kana ta janyo mayukan da take shafawa tana mai fara matso su a cikin tafin hannun ta, tukun ta murza su, kana ta shafe sa akan lallausar fatar jikin ta da take ta faman glowing, alamun ba ƙaramun daɗi ake jiyar da ita ba.

Cikin ƙan-ƙanin lokaci ta gama mutsika mayukan, tare da tura-rirrikan jikin da take amfani da su a jikin ta, kasancewar lokacin zaman Asad ya kusa, shi yasa take komai cikin sauri.

Ba tayi wata kwalliya ba mai yawa akan fuskar ta, domin kuwa powder kawai ta shafa tare da lips bam akan laɓɓan ta, sai kwallin da ta sanya acikin idanuwan ta, sabo da jin labarin da tayi na cewar kwalliyar cika fuska bata birge Asad ko kaɗan a binciken da tayi akan sa.

Mayar da duk abubuwan da tayi amfani da su tayi zuwa mazaunin su, tukun ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take akai, tana mai juyawa ta doshi wurin da wadrobe ɗin su take.

A gaban haɗaɗɗiyar wadrobe ɗin ta tsaya tana mai ɗora hannun akan murfin ta ta buɗe sa, sannan ta fara bin sababbin ƙananan kayan da suke saƙale a cikin ta da idanuwa.
Chapter 66 · 0% Book details