← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 79

Sashe 32

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗakin iccina ne mai ɗan girma dai dai misali, zagaye yake da bakin ƙyalle wanda aka buga tambarim Baƙar Masarauta tako ina na jikin sa da farin fenti, ga kuma kaskwayen wuta da suke ajiye a kowace kusurwa ta cikin ɗakin suna ci da huta, sai kuma wasu uban kayan kari-kitai kala kala marasa kyan gani da suke ako wane wuri dake cikin ɗakin.
Yayin da daga can jikin bango kuma akayi wani ƙaton daɓe mai matuƙar tudu, domin kuwa harda matattakalar hawa manne ajikin sa.
Daga saman daɓen kuma Sassaƙen gunkin nan wanda suke kira da abun bautar su ne kafe awuri ɗaya, ɗauke yake da kayan ado kala kala manne ajikin sa, sai daga can gefen sa kuma aka ajiye wata shimfiɗar fata tafkekiya, yayin da kowacce kusurwa dake kan shimfiɗar kuma ta kasance ɗauke da kaskwayen Huta waƴan da suke matuƙar ci da huta, sai dai kuma kamar yacce Boka ya faɗa gaba ɗaya hutar suna futar da jan hayaƙi ne, yayin da kalar hutar kuma ta kasance baƙa!
Acan kuwa tsakiyar shimfiÉ—ar mazaunin Boka mai hutar kasko ne awurin.
Gaba ɗaya layayoyi ne da ƙulluka kala-kala zagaye da mazaunin nasa, yayin da daga gaban sa kuma aka ajiye wata randa da take faman ci da huta itama, sai akusa da ita kuma aka ajiye wani ƙaton faranti da yake ɗauke da farin yashi acikin sa mai matuƙar yawa.

"Shin yanzu ka fahimci abun da nake sanar da kai ko, kaga yadda kalar Hutar kasko ta koma, abun da bai taɓa faruwa ba tun kafuwar mu duniya, wato canzawar Hutar kasko." Boka mai hutar kasko ya faɗa afirgice yana mai kallon Sarki Barbaru.

"Tabbas ko al'amari nada matuƙar ruɗarwa, dan haka na roƙe ka da abun Bauta Gargabilu kayi gaggawar fara aikin nan, tun kafin ƙwaƙwalwar kaina ta tarwatse, domin kuwa al'amarin baƙaramun ruɗar dani yayi ba." Cewar Sarki Barbaru awani irin hargitse.

Dasauri Boka mai hutar kasko ya cigaba da tafiya yana mai nufar kan daɓen nan.
Take masa baya shima Sarki Barbaru yayi cikin sauri.

Cikin hanzari yasa hannu yana mai fara fincikar wasu layoyi daga cikin layoyin da suke awurin da matuƙar yawa, adai dai lokacin da ya zauna awurin.
Yayin da Sarki Barbaru ma ya samu wuri akan shimfiÉ—ar ya zauna, yana mai cigaba da bin hutar kasko da idanuwa.

Wasu manya- manyan layoyi ya ɗauko har guda ukku yana mai ajesu agefe, tukun daga bisani ya juya ɓangaren da wasu karikitai suke yana mai sa hannu ya ɗauki wani ƙaton ƙullin tsumma ya a jesa agefe, sannan ya juya yana mai kai idanuwan sa tare da yatsun sa zuwa cikin farantin dake agaban sa.
Akan yashin dake cikin farantin ya ɗora yatsun sa biyu, tukun ya fara wasu zane zane akan yashin yana mai furta wasu kalmomi da ƙarfi, bayan ya rumtse idanuwan sa.
Ya ɗauki kimanin daƙiƙa kusan ukku ahaka, tukun ya buɗe idanuwan sa yana mai kaisu kan zanen da yayi.

Jijjiga kansa yayi, sabo da ganin da yay abun ya masa kamar yacce yake so, tukun daga bisani ya juya ɓarin da ya ajiye wannan ƙullin tsuman yana mai ɗaukar sa, tare da layoyin da ya aje agefe, tukun ya miƙe tsaye cak yana mai tsayawa agaban hutar dake ci acikin kasko.

Kwance ƙullin tsuman nan yayi yana mai riƙe sa da hannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun nasa kuma ya danƙule layoyin da ya riƙe acikin sa da matukar Ƙarfi, sannan ya kuma ya rumtse idanuwan sa da ƙarfi, kana ya buɗe baki yana mai fara yin wasu irin surutai, tare da fara tsiyaya wannan garin da yake cikin tsumman sa acikin hutar kasko.

Yana fara tsiyayawar gaba É—aya hutar cikin kaskwayen dake cikin É—akin duka suka mutu atare!
Wata irin gigitattar ƙara Sarki Barbaru ya saki da ganin hakan, wacce tayi sanadin da yasa Boka mai hutar kasko ya buɗe idanuwan sa da tsantsar sauri.

Da matuƙar sauri shima yaja baya yana mai sakin tsumman da layoyin da suke riƙe ahannun sa, sabo da yarce yaga gaba ɗaya hutar dake cikin kaskwayen sun mace, aƙoƙarin sa na ganin yayi abun da zai yi sanadin saduwar su da Gargabilu, abun da bai taɓa faruwa ba kenan tun wanzuwar su aduniya, wato mutuwar Hutar kasko, domin kuwa kullum cikin ƙara izata ake yi.

"Shin meke shirin faruwa da mune haka, mai ya sanya Hutar kasko zasu mutu ne Boka? Shin wane irin bala'ine yake shirin riskar mu, domin kuwa ko atarihi ban taɓa jin ance hutar kasko ta mutu ba, sai yanzu da abun ya faru agaba na."
Sarki Barbaru ya faɗa cikin tsantsar ruɗu da matuƙar tashin hankali, yana mai matsawa kusa da boka mai hutar kasko, da yake ta aikin zare idanuwa shima.

"Tabbas ba kai kaɗai ba, koni dana fika shekaru ban taɓa ganin hakan ya faru ba, sannan kuma ko atarihi ban taɓa jin ance akwai ranar da hutar kasko ta taɓa mutuwa ba sai yanzu, wanda hakan kuma shike nufi da cewar wannan abun yafi ƙarfin har abun bauta Gargabilu, domin kuwa ta wannan hanyar ce kawai muke da ikon saduwa da shi harya bamu mafuta, amma sai gashinan gaba ɗaya ta toshe hany...."

Sautin ihun da suka jiyo awaje da matuƙar ƙarfi ne ya sanya Boka mai hutar kasko tsayawa da maganar da yake, ba tare da yakai ƙarshen ta ba, tukun daga bisani suka fara ɗaga ƙafa suna masu dosar hanyar futa daga cikin ɗakin cikin sauri, dan suga abun da ke shirin faruwa.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN UNGUWAR ƊAN TANKI.*

_WASHEGARI_

Yadda Aishatu taga dare haka taga rana bata iya rumtsawa ba ko kaɗan, sosai mutuwar mahaifin nata ta girgiza ta, sannan kuma tayi matuƙar gigitata, tayi kuka iya kuka yadda kasan ranta zai futa, bata taɓa sanin haka zafin mutuwar iyaye yake da tsantsar raɗaɗi ba, sai ajiya da abun ya risketa.
Kwana sukai cir Ishaƙ na aikin rarrashin ta, aƙarshe ma da yaga takasa yin shiru sai ya sanya ta taje ta ɗauro alwala, tazo tai ta sallolin nafula tana mai roƙawarwa mahaifin ta rahama awurin Ubangiji.

Suna futowa daga masallacin asuba Ishaƙ yayo gida danniyar yazo ya shirya kayan sa, sannan suyi sallama da mutan gidan, domin kuwa jirgin dake tashi ƙarfe shida na Ƙasar Malin zasubi ayau ɗin, sai dai kuma me, yana shigowa cikin ɗakin yay tsaye awuri ɗaya yana mai bin Aishatu da idanuwa, sabo da yarce ya ganta zaune akan kujera sanye da hijab, ga kuma jakar kayan ta da nashi ajiye agefe, alamun shi kawai take jira ya ƙaraso su tafi, gashi shi kuma ko kaɗan bai tsara tafiyar da ita ba. To ta ina ma zai fara cewa zata bisa irin wannan doguwar tafiyar, wacce har sai an kwana kusan biyu ahanya, bayan ga halin da take ciki. Ya raya hakan acikin ransa daga bakin ƙofar da yake atsaye, tukun daga bisani ya fara takawa yana mai dosar wurin da take, idanuwan sa akan fuskar ta.
Yayin da ita kuma ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai wasa da farcen hannun ta.

Agafen ta ya zauna yana mai miƙa hannuwan sa duka biyu ya riƙo nata da su, tukun daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "Amma dai kin san ba tare zamu tafi ba kina cikin wannan yanayin ko Aishatu, naga kin haɗo jakun kuna har guda biyu."

Dasauri ta ɗago kanta tana mai kallon sa, kafin daga bisani kuma hawayen da tasamu ta tsayar da su tun ɗazu suka sake ɓallewa daga cikin idanuwan ta da matuƙar gudu, kana ta buɗe baki cikin dashash-shiyar muryar ta tana mai faɗin. "Dan Allah kar kace bazan bika ba Abban Ahmad, domin kuwa muddin banje ba to bazan taɓa samun natsuwa anan ɗin ba. Ina son naje naga su Dada tare da sauran ahalina, ina son naje nayi ta'aziyyar mahaifina, sannan kuma na karɓi gaisuwar sa.
Na roƙeƙa da sunayen Allah kyawawa tsarkaka kar kace bazan bika ba Abban Ahmad." Ta ƙarasa maganar cikin kuka.
Yayin da shi kuma ya lumshe idanuwan sa yana mai murza tafin hannun ta da suke a cikin nasa, ba tare da yace komai ba, tukun daga bisani ya buɗe idon sa yana mai faɗin. "In banda ke Ummin Ahmad, ke yanzu ahaka yarce kike ai ko nida kaina nace ki shirya kije ya kamata ki tausayawa kanki kice bazaki ba, dan haka ina son kiyi haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya, sai na ɗauke ku na kaiku dukan ku har yarama insha Allah, dan kuwa ke da kanki kin riga da kin sani wanda ya rasu ya riga da ya rasu, babu tayarce za'ayi ya dawo, sannan kuma koda bakije ba suma baza suji komai ba, sabo da sun san irin yanayin da kike ciki, sab...." "Assalamu alaikum." Muryar Kaka ta ratsa kunnuwan su daga bakin ƙofa, wacce ta sanya Ishaƙ dakatawa daga zancen da yake ba tare da ya ƙarasa ba, yana mai sakin hannuwan Aishatu.

"Wa'alaikumu salam." Ya amsa mata yana mai gyara zaman sa akan kujerar da yake.
Yayin da ita kuma kaka ta danno kanta zuwa cikin É—akin bakin ta na faÉ—in. "Me kuma ya zaunar da kaine har yanzu, bayan kasan irin tafiyar da zakuyi bata wasa bace ba, tun É—azu nake jiran naji futowar ka amma naji shiru, shi yasa ya nace bara nazo naga abun da ke faruwa." Kaka ta faÉ—a tana mai zama akan kujerar da take facing É—in wacce suke akai.

"Wai Aishatu har yanzu kia nufin kice baki dena kukan nan ba?" Kaka ta sake faÉ—a tana mai kallon ta, fuskar ta cike da tausayin ta.

Nannauyan numfashi IshaÆ™ ya sauke, tukun ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in. "Dalilin da ya hanani futowa kenan Umma, wai kin ganta nan ta dage sai mun tafi tare, gashi ma har da haÉ—a kayan ta tayi." Ya faÉ—a cikin sanyi yana mai kallon mahaifiyar tasa.
Chapter 32 · 0% Book details