← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 79

Sashe 36

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin wannan yanayin ta jiyo sautin muryar hadimar ta, wacce ta kasance tamkar Uwa ga Ƴaƴan ta, kuma ta zamto aminiya agare ta, tana mai kwaɗo sallama abakin ƙofar ɗakin ta, kasancewar aduk lokacin da take da ciki dama haka Hadimar tata mai suna Larai take ziyarta ta duk dare, dan taga halin da take ciki, domin kuwa wani lokacin ma idan ta shigo sai dai ta juya ba tare da ta same ta ba, idan har ranar ta kasance tana turakar mai Martaba kenan, sannan kuma da zarar ta haihu to kula da yaron da komai nasa yake komawa wurin ta, haka duk ta raini yaran tun daga kan Babban yaya har zuwa Nafisat auta.
Babu yarce magauta basuyi ba su janyo ta ajikin su, domin su samu damar kassara rayuwar Babban yaya cikin sauƙi, amma kwata-kwata taƙi, hakan ne yasa gaba ɗaya itama sukabi suka tsane ta, sannan kuma suke jin haushin ta, sai dai kuma babu yadda zasuyi da ita, domin kuwa Gimbiya Fulani ta daɗe da ƴanta ta.
Macece mai kimanin shekaru arba'in da ƴan kai aduniya, Ƴaƴa huɗu duka ta haifa, daga nan kuma mahaifin su ya rasu. Tun bayan rasuwar sa bata sake yin wani auren ba, ataƙaice ma tana zaune ne anan ɓangaren Gimbiya Fulani itama data bata ɗaki.

Da matuƙar sauri, sannan kuma cikin tsantsar tashin hankali ta ƙarasa wurin ta tana mai faɗin. "Subhanallahi haihuwar ce tazo kenan Mamy'n Yara." Ta ƙarasa maganar tana mai dafata, hankalin ta atsantsar tashe.
Yayin da ita kuma Gimbiya Fulani take ta cigaba da cizon yatsa, ba tare da tace mata komai ba.

Dasauri ta juya tana mai shirin tafiya, bakin ta na faɗin. "Bara naje na sanarwa Jakadiya ta sanarwa mai Martaba, in yaso ko asibiti ne sai ataf... Caraf taji Gimbiya Fulani ta riƙo yatsun hannun ta, hakan ne yasata juyowa ɓarin da take tana mai kai idanuwna ta kanta.
Ido huɗu sukai da junan su alokacin da ta juyo ɗin, tukun daga bisani Gimbiya Fulani ta buɗe baki cikin muryar ta da take nuni da halin da take ciki na tsantsar ciwo tana mai faɗin. "Kar kisanar masa, bana san wani mutum yaji labarin haihuwar nan ayanzu, domin kuwa kin san yarce wasu daga cikin mutanen gidan nan suke, dan haka ki barshi har zuwa nan da asuba muga yarce Allah zaiyi." Ta ƙarasa maganar da ƙyar tana mai cizon leɓe.

"Tom shikenan, amma bara naje É—akina na É—auko wasu magun-guna dana tanade su sabo ds zuwan wannan ranar."
Umma Larai ta faÉ—a ba tare data tsaya ja da maganar shugabar tata ba, domin kuwa sai dai ta bada labarin magautan cikin gidan nan, ba dai wani ya bata ba, tukun ta juya cikin sauri tana mai fucewa daga cikin É—akin.

*ƘASAR MALIN, CIKIN JIRGIN RUWA.*

Dare ya tsala sosai, yayin da gari ya kasance baƙiƙƙirin da duhu, amma duk da haka jirgin nan bai tsaya ba, kasancewar ɗauke yake da futulu masu matuƙar haske tako ina ajikin sa, hakan yasa duk tsayin dare bai sanyawa direbobin su tsaya daga tuƙi, muddin ba abinci aka tsaya siya ba ko sallah.
Tini suka daÉ—e da futa daga cikin Jahar Ruman, dan har sun shiga Jahar Karfuz ma.

Tun da suka shigo jahar karfuz Aishatu taji jikin ta ya ƙara matuƙar yin sanyi, ga bugun zuciyar ta kuma da yayi matuƙar ƙaruwa, tayarce har take jin tamkar zata faso ƙirjin ta ta futo, tun tana addu'a acikin zuciyar ta har sai da ta dawo yin ta abayyane, sabo da yarce take jin yanayin na sake hau-hawa fiye da da, tayarce har Ɗan cikin ta shima keta motsi fiye da yarce ya saba yi.

Ta fannin Ishaƙ shima sosai yake jin zuciyar sa na cigaba da dukan tara-tara, ga wani irin tsoro da fargaba da suka lulluɓe zuciya da ruhin sa, irin wanda bai taɓa tsintar kansa a makamancin su ba.
Hakan ne yasa sa damƙe hannun Aishatu cikin nasa da matuƙar ƙarfi, yana mai karanto duk addu'ar da tazo zuciyar sa azuciyar sa shima.

Misalin ƙarfe huɗu da ar'ba'in dai-dai na dare jirgin su ya danna kansa zuwa yankin da ya ratso ta cikin BAƘAR MASARAUTA, wanda shigar tasa kuma tayi dai dai da bugawar da ƙirjin Aishatu yayi da matuƙar tsanani fiye da da, yayin da zuciyar ta kuma ta cigaba da tsinkewa da matuƙar sauri.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Rabi da kwatan mutanen dake cikin jirgin suka furta cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali, sabo da yarce suka hango h.............✍

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 15*

Hasken futulu masu matuƙar ƙarfi an dallo idanuwan su tun daga can nesa da su.
Take a wurin Aishatu ta sake matuƙar rikicewa, jikin ta na tsanstsar rawa da karkarwa, hakan da Ishaƙ ya gani ne ya Sanya sa sake damƙar hannun ta da matuƙar ƙarfi, bakin sa na furta duk addu'oin da suka zo cikin zuciyar sa cikin tsantsar tashin hankali, kamar yadda sauran ɗaukacin mutanen da suke a cikin jirgin suke.
Yayinda tawagar mutanne Baƙar Masaruata kuma suka afka cikin jirgin ruwan su da matuƙar sauri, tukun suka doso inda suka hango jirgin su Aishatu, suna masu cigaba da dallewa direbobin tare da mutanen ciki idanuwa da hasken futulun su, bakin su kuma na aikin furta kalmar. "Gargabilu!" Da tsantsar ƙarfi.

Cikin daƙiƙun da basu zarta huɗu ba suka ƙaraso wurin da jirgin da su Aishatu suke ciki yake.
Ba tare da sun tsaya jan lokaci ba suka zare makaman su daga cikin jikin su, suna masu É—aga su sama, tukun suka yiwa direbobin jirgin nuni da hanyar da zasu bi.

Cikin tsantsar ruɗu kuwa matuƙarn jirgin suka nufi wurin da suke nuna musu hankulan su abala'in tashe, domin kuwa ba iya makaman su bane abun tsoro, su kansu mutanen da suke a cikin jirgin abubuwan firgici ne ga mutumim da bai saba ganin su ba.
Yayin da jama'ar dake cikin jirgin kuma suka sanya ihu da matuƙar ƙarfi, suna masu faɗin sun shiga ukku cikin tsantsar tashin hankali.
Afannin Aishatu kuwa kallo ɗaya tayiwa mutanen taji cikin ta yayi wata irin murɗawa, sabo da firgita, tukun daga bisani Ɗan cikin nata ya fara wani irin hutsul-hutsul da matuƙar sauri, tayarce har na kusa da ita zai iya lura da motsin sa muddin ya kalli cikin nata.

Da matuƙar ƙarfi ta rumtse idanuwan ta, tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe cikin ta da shi, zuciyar ta na tsantsar bugawa, yayin da bakinta kuma ke ai'kin furta duk wasu addu'oi da sukazo cikin sa, ba tare da tasan tana yin suba ma.

Basu dakata ba har sai da suka turasu gefen ruwan nan, inda su sarki Barbaru da Boka mai hutar kasoko, tare da sauran jama'ar su suke.

Shimfiɗar fata ce ajiye daga gefen ruwan, wacce jikinta yake ɗauke da jini faca-faca, ɗauke take da kaskon wuta da yake matuƙar ci da wuta, yayin da gefen kaskon kuma aka aje wata irin kibiya mai matuƙar tsini, sai Boka mai wutar kasko da yake zaune daga gefen shimfiɗar, yayin da Sarki Barbaru kuma yake daga tsaye a bakin ruwan nan, gaba ɗayan sa a wani irin birkice, domin kuwa ko shigar da ke sanye jikin sa tun ta wancan satin ce, ranar da suka fara riskar tashin hankalin nan bai canza ta ba, asalima ko barin hurin kwata kwata baiyi ba har kawo yau, domin kuwa abinci ma a rana baifi sau ɗaya yake cinsa ba, shima sai yaji yunwa na shirin hanasa miƙewa tsaye.

Sosai mutanen cikin jirgin nan suka sake matuƙar firgita, suna masu sakin ihu da salati, sabo da irin mutanen da suke sake arba da su agafen ruwan da suka iso yanzu.

"Daƙiƙa ɗaya kawai na baku, ko wane mutum ya zamto ya kama bakin sa, muddin kuma kuka bari na sake jin ihun wani cikin kunnuwa na bayan giftawar daƙiƙun, to kusani sunan mutum gawa, ko waye ne shi kuwa."
Sarki Barbaru ya faɗa cikin muryar sa mai matuƙar amo, yana mai kallon mutanen cikin jirgin nan.

Take kuwa wurin ya ɗauki shiru gaba ɗaya, yarce kasan ba'a taɓa hallitar mutum ba, balle ayi zaton anan wurin ihun ya gama tashi.
Yayin da Aishatu kuma ta taune leɓen ta na ƙasa da ƙarfi, tana mai dafe cikin ta da hannu ɗaya, sabo da yadda taji marar ta tayi wani irin kartawa, ga kuma bayan ta da taji lokaci ɗaya ya riƙe gam!
Taune leɓenta ta cigaba dayi da ƙarfi, tana mai faman zare idanuwa tare da gumtse baki, gudun kar addu'ar da takeyi a zuciya ta suɓuce ta futo fili, Sarki Barbaru yaji, yayin da shi kuma Ishaƙ yake ta aikin shafa bayan ta a hankali, cikin tsantsar ruɗu shima.

"Ku shiga cikin jirgin nan yanzu, ku bincika mana ko ina da ina, lungu da saƙo, ku futo mana da duk wani jinjirin yaro namiji da kuka samu."
Sarki Barnaru ya faÉ—a cikin amo yana mai kallon wasu daga cikin dakarun nan nasu.
Yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, barin ma matan da suka san suna ɗauke da jariran Ƴaƴa.

Dasauri wata mata da take ɗauke da jinjirin ta a hannunta, ta sake danna sa cikin hijabin ta jikin ta na tsantsar rawa, sabo da yadda taga mutanen nan sun tunkaro inda take gadan-gadan, kasancewar sun riga da sun hango ɗan nata tun farko, sabo riƙesan da tayi a hannun ta.

Girgiza kanta ta farayi tana mai ja da baya daga zaunen da take, cikin tsantsar tashin hankali da firgici, yayin da su kuma waÆ´an nan dakarun suka cigaba da doso ta gadan-gadan.

Ganin da tayi suna daf da isowa inda take ne, ya sanya ta miƙewa da sauri tana mai shirin rugawa baya, amma sai dai tana ɗaga ƙafarta ɗaya taji ta- ta kife kif a ƙasa, kanta na dukan katakon dake jikin jirgin da matuƙar ƙarfi, sabo da yadda ɗaya daga cikin dakarun ya sanya ƙafarsa ya tatsiye ta da ita.
Chapter 36 · 0% Book details