Sashe 24
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba tare da sun gama shigowa ba suma bayi maza suka fara shigowa da baya da baya akuma kan layi, su kuma ɗauke da damin iccina masu matuƙar yawa akan kafaɗun su, suna ta faman rawa tare da faɗar kalmar. "Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!" Da tsantsar ƙarfi yarce kasan zasu tsaga wurin, ga kuma uban sautin kiɗan ganguna da suke tashi awurin mai matuƙar dadi.
Sanye suke su kuma da fararen wandina na yadi masu matuƙar faɗi iyakar guiwoyin su, yayin da gaba ɗaya jikin wandinan kuma suka kasance ɗauke da zanen tambarin masarautar tasu da akayi sa da baƙin fenti, sai fuskar su da fatar jikin su da ta kasance zane da tambarin masarautar tako ina, kasancewar babu wanda yake sanye da riga acikin su.
Gaba ɗaya suma nufar hanyar wurin da abun bauta Gargabilu yake sukayi da baya da baya, hannuwan su ɗauke da iccina suna faman aikin dilliƙar rawa, yayin da gumi kuma ke yanko musu ta koce kafar gashi dake jikin su sabo da wahala.
ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.
Acikin masarautar wasai kuwa tun kafin gwamna da tawagar sa su ƙarasa fada masu tarbar su suka ƙaraso inda suke, kasancewar an riga ansan da zuwan su tun jiya.
Cikin girmamawa wasu daga cikin fadawan mai martaba Sarki Abdallah suka da aka turo su tarbar mai girma gwamna suka durƙusar da kai agaban su suna masu miƙa gaisuwar su gare sa.
Yayin da shi kuma gwamna da yake zaune agidan baya cikin azababbar motar da suke ke ciki ya sanya drivern sa ya sauke masa glass ɗin motar ƙasa, tukun shima ya ɗagawa dakarun hannu yana mai sakar musu murmushi alamar amsawa kenan, sannan suka juya suna masu dosar hanyar da zata sada su da fada aƙafafuwan su, yayin da suma motocin su gwamna da escort ɗin sa suka bisu abaya, bayan driver'n shi ya mai da glass ɗin motar ya rufe.
Ko da suka ɗauki hanyar fada amai-makon su shiga cikin ta sai suka ɗauke hanya suna masu yin wata hanyar wacce zata kai su zuwa ga gidan da mai martaba Sarki Abdallah yake ganawa da manyan baƙin sa, kasancewar tun jiyan da mai girma gwamna ya aiko da saƙon zuwan sa sai da yasa sanarwa da mai martaba cewar babbar magana ce zata kawo su wurin su, sai dai amma ba wacce ta shafi Jaha bace, magana ce wacce ta kasance family issue.
Hakan yasa mai mairataba Sarki Abdallah bai sa akai su fada ba sai yace awuce dasu zuwa masaukin baƙin sa direct.
Gaban wani haÉ—É—aÉ—en plat building fadawan sarki suka tsaya, sannan suma motocin su gwamna akayi parking É—in su awani wuri da yake ajikin gidan, wanda anyisa ne sa domin aje motocin dama.
Dasauri escort ɗin da suke acikin motocin waƴan da suke sanye da uniform kala kala ajikin su suka buɗe murafan motocin su su suna masu furfutowa waje, tukun suka fara ɗaga ƙafafuwan su suna masu dosar wurin motar da mai girma gwamna tare da aminin sa suke aciki, cikin takun su dake nuni da su ɗin cikakkun jarumai ne, yayin da hannuwan su kuma suka kasance riƙe da manya-manyan bindigu.
Mutum biyu suka matsa jikin ƙofofin motar suna masu sanya hannu suka buɗe su, yayin da suran escort ɗin kuma sukayi tsai-tsaiye abakin motar cirko-cirko.
Ƙafar sa da take sanye da wani azababben cover shoe mai matuƙar kyau da tsada ya fara zurowa waje, tukun daga bisani ya sanyo gangar jikin sa waje yana mai futowa duka.
Sanye yake da wata arniyar getzner shadda ash color da take matuƙar ƙyalli da ɗaukar ido, ɗinkin babbar riga ajikin sa.
Aɓangaren abokin nasa shima futowa yay yana mai dawowa ɓarin da mai girma gwamna yake, shi ɗin ma sanye yake da shiga ta alfarma ɗinkin babbar riga ajikin sa.
Tukun suka fara takawa suna masu dosar ƙofar dake manne jikin haɗaɗɗen building ɗin nan, yayin da suma escort ɗin suka bisu abaya suna ta faman bubbuɗawa.
Cak fadawan nan suka tsaya daga bakin ƙofar suna masu komawa gefe suka buɗawa mai girma gwamna wuri.
Suna zuwa bakin ƙofa ya ɗagawa escort ɗin dake binsu hannu ba tare da yace musu komai ba.
Cak sukai tsaye awurin daga bakin ƙofar suna masu gyara riƙon bindigun dake hannuwan su.
Yayin da su kuma su gwamna suka danna kawunan su zuwa cikin ƙofar.
Tamfatse-tsen fallo ne wanda ya gaji da haɗuwa da kayan ƙawa da alatu yarce kasan babu mutuwa.
Tsit fallon yake babu kowa cikin sa sai sautin futar ac kawai dake tashi acikin sa, tare da wani irin ni'imtacce ƙamshi.
Kan wata mayyar royal chair dake zagaye da fallon mai girma gwamna da aminin sa suka samu wuri suka zauna.
Yayin da daga gaban kujerar kuma wani tamfatse-tsen center table yake cike maƙil da kayan ciya-ciye, irin su ruwa, fruits, naman kaji, dana rago wanda aka sarrafa sa kala-kala jere akan wani ƙaton tray.
Basu jima da zama awurin ba sai ga Waziri da Galadima nan sun futo ta wata ƙofa da take acikin fallon bakunan su ɗauke da sallama.
Ƙarasawa sukayi zuwa kan kujerar da take facing ɗin wacce su mai girma gwamna suke akai, tukun suka zauna suna masu fara gaisawa cikin mutunta juna da girmamawa.
Zaman su baifi da minti biyar ba sai ga mai martaba Sarki Abdallah nan ya futo ta cikin ƙofar dasu galadima suka futo bakin sa ɗauke da sallama shima.
"Wa'alaikumu salam." Gaba É—ayan su suka amsa masa suna masu kai idanuwan su kansa.
Sanye yake da shigar sa irin ta koda yaushe, wato manyan kaya tare da alkyabba mai azabar kyau da rawani É—auke akan sa.
Ƙarasawa yayi zuwa gaban kujerar da su mai girma gwamna suke yana mai miƙa musu hannu sukayi musabaha cikin mutunci da girmamawa, kana ya juya yana mai komawa kan kujerar da take agefen wacce su Waziri suke akai ya zauna, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Bismillah ga abinci nan ku taɓa mana." Ya ƙarasa maganar yana mai musu nuni da tray'n dake cike da kayan abinci kala kala akan sa da yatsar sa manuniya.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah wallahi!!" Suka haÉ—a baki wurin fadÉ—e suma fuskar su É—auke da murmushi.
Shiru ne ya biyo baya ba tare da wani ya ƙara cewa komai ba acikin su. Tukun daga bisani aminin mai girma gwamna mai suna Alhaji Saleh yayi gyaran murya yana mai ɗago kai ya fuskanci su mai martaba, tukun daga bisani ya fara ɗaga laɓɓan sa yana mai faɗin. "To ataƙaice dai ba komai ne yasan ya mu muka buƙaci zama daku ba sai akan wani muhimmin abu da yake atsakanin yaran mu duka, wanda afannin mu mu muke masa kallon abun alkhairi tare da alfahari garemu gaba ɗaya idan har muka samu ya tabbata." Ya faɗa yana mai gyara zaman sa akan kujera, yayin da su kuma su mai martaba suka zuba masa ido suna masu kallon su tare da sauraran sa fuskar su ɗauke da murmushi, ba tare da sunce komai ba.
Tukun shi kuma ya É—ora da faÉ—in. "Ba komai bane ba kuwa face soyayyar dake atsakanin yarinyar wurin mu, wato bilkisu Æ´ar wurin mai girma Gwamna, da kuma yaron wurin ku Yarima Asad."
"Asad kuma!" Suka haɗa baki su duka ukkun suna masu faɗin haka fuskar su cike da tsantsar mamaki, domin kuwa cikin su duka babu wanda bai san halin Asad ba na rashin son aure, dan kuwa babu yarce ba'ayi ba da shi akan su futar da matan aure amma shi yaƙi sai Al'amin ne kawai ya futar da tasa.
"Tabbas kuwa Asad naku da Bilkisu, dan kuwa ataƙaice sun ɗauki tsawon shekaru kusan huɗu suna atare, hakan yasa mukaga amai-makon su zauna suna ta abu ɗaya gwanda ace kawai anyi mai duka kowa ya huta, wannan shine dalilin da yasa muka buƙaci zama daku." Yaƙarasa maganar yana mai sakin murmushi.
"Masha Allah! Masha Allah!!" Galadima da Waziri suka faɗa gaba ɗayan su fuskar su ɗauke da murmushi, tukun daga bisani suka sake buɗe baki atare suna masu faɗin. "Haƙiƙa munyi matuƙar jin daɗin wannan labari daga bakin ku, kuma insha Allah abun bazai ɗauke mu ga dogon lokaci ba ba tare da anyi sa ba, tunda har su yaran sun samu fahimtar juna." Suka sake faɗe fuskar su ɗauke da murmushi.
Yayin da shi kuma mai martaba ya sake gyara zaman sa akan kujera, kana daga bisani yayi gyaran murya, tukun ya buɗe baki cikin yanayin sa wanda baka isa kace fariciki yake ba ko kuwa akasin sa, yana mai faɗin. "Masha Allah, naji duk abun da aka tattauna akai, kuma nayi farin ciki da jin hakan, dan haka yanzu sai muyi fatan Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya ƙarasa maganar da sakin murmushin yaƙe, domin kuwa haka kawai yaji bai wani amunta da zancen su mai girma Gwamna ba, na cewar Yarima Asad na san Bilkisu, gashi shi kuma aransa yana mai jin bazai taɓa iya yiwa ɗan nasa mafi soyuwa acikin ransa auren dole ba, sai dai kuma yasan tunda abun ya zamto ahaka to koda tinanin sa ya zamto gaskiya na Asad baya son yarinyar babu yarce zasuyi daga shi har Asad ɗin dole suyi haƙuri ayi, domin ko shi dai bazai iya buɗar baki yace bazai haɗa jini da mai girma Gwamna ba, hakan shine ya sanya gaba ɗaya yaji yana yin sa ya sauya, sannan kuma ya ƙudiri aniyar samun Asad da maganar dan yaji ta bakin sa ayau yau ba sai gobe ba.
Ta fannin Alhaji Saleh kuwa cikin farin ciki ya buÉ—e baki yana mai faÉ—in. "Amin Amin."
Yayin da shi kuma mai girma Gwamna yake ta sakin murmushi ba tare da yace komai ba, duk da yarce yake son tun ɗazu ya buɗe baki yayi wa mai martaba bayanin abun da Yarima Asad yake yiwa Bilkisu tare da kashedin ajamasa kunne, sabo da jin da yay Alhaji saleh baiyi magana akan hakan ba, sai dai kuma da zarar ya kalli mai martaba danniyar ya buɗe baki yay masa magana akan hakan sai yaga ya masa wani irin kwarjini acikin idanuwa, hakan yasa yake ta ruƙon maganar acikin sa tun ɗazu duk da yarce yake son ya furta ta ba tare da yayin ba.