← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 79

Sashe 34

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To amma Boka babu wata hanya wacce zamubi mu hana wannan mummunan abun faruwa?" Ya faÉ—a ahaukace, sabo da yarce duka magan-ganun Boka mai hutar kasko suka sake haukatar da shi.

"Akwai abun da za'ayi wanda zai sa agano sa, wannan abun kuma ba komai bane face binciko hanyar da zai bi ya huce ta ita, sannan akarɓe duk wani jariri da aka samu akan hanyar daga hannun uwarsa, bayan an karɓe sa kuma sai akai sa gaban kaskon huta a ajiye sa, daga nan kuma sai aɗaga kibiya ayi kamar za'a caka masa ita aciki, to muddin shine jinjirin zai sanya ƙafafuwan sa ya ture kaskon hutar nan, tayarce har sai ya rabe gida biyu, idan kuma har bashi bane ba, to bazai iya ture sa ba, dan haka sai kawai acaka masa mashin akashe sa duka, idan kuma shine bayan ya ture kaskon, sai aɗauke sa atafi da shi ya zamto Bawa acikin masarautar mu, hakan da za'ayi itace kawai mafuta garemu, domin shine zai zama aƙarƙashin ikon mu, muddin kuma akai kuskuren barin shi ya futa daga cikin masarautar nan, to wajibi ne zai dawo bayan shuɗewar wasu shekaru ya kuma yaƙe mu, sannan yaci galaba akan mu, haka kuma kashe sa ko ba ayanzu ba shima yana dai dai da tashin duniyar mu ne, domin kuwa bani bama, hatta da abun bauta Gargabilu faɗan yafi ƙarfin sa."
Boka mai hutar kasko ya faÉ—a idanuwan sa akan Sarki Barbaru.

"To ta wace hanyace shi jinjirin zaibi ya huce ne yakai Boka?" Cewar Sarki Barbaru cikin tashin hankali.

"Abun da nima ban sani ba kenan, sai dai kuma bawai zamu zauna bane, a yanzu tashi zamuyi mubi wata hanyar domin mu gano ta sashin da shi jinjirin zai huce, idan kuma har aka kai gobe bamu gano ba, to kawai zamu sanya dakaru su zagaye mana kowace ƙofa ta shigowa garin nan." Boka mai hutar kasko ya faɗa yana mai yin gaba, tukun shima Sarki Barbaru ya bisa abaya, domin suje su cigaba da binciken hanyar da zasu gano ta inda Jaririn zai huce.

Kwana sukai cir suna abu É—aya amma abanza, babu kalar tsafin da Boka mai hutar kasko baiyi ba dan ya gano ta hanyar da Jaririn zai wuce amma baiyi ba.

Har sun yanke hukuncin zasu hakura su subi waccan hanyar ta toshe ko wace ƙofar garin, sai kuma boka mai hutar kasko ya tuno da wata hanya da baibi ba acikin duka tsafin da yay.
Hakan yasa cikin sauri ya juya ɓarin da Sarki Barbaru yake yana mai faɗin. "Akwai wata hanyar bayan waƴan da mukabi da muka manta bamu yita ba, dan haka yanzu muyi sauri zuwa gaban ƙaramin rafi, domin kuwa anan ne kawai wurin da zanyi aikin."

Dasauri Sarki Barbaru ya bisa abaya hankali atsantsar tashe.
Gaban ɗan ƙaramin rafin da yake ɗauke da farin ruwa acikin sa Boka mai hutar kasko ya tsaya.
Wasu irin abubuwa ya watsa acikin ruwan, tukun ya fara wasu irin mahaukatan surutai yana mai zagaye rafin.
Lokaci ɗaya ruwan ya dinga wata irin hautsinawa da matuƙar sauri, tukun aƙarshe wani irin hoton tafkeken ruwa mai matuƙar girma ya bayyana acikin sa.

Dasauri Boka mai hutar kasko ya tsaya da surutan da yake yana mai faÉ—in. "Tabbas munyi nasara ayanzu, domin kuwa ga hoton hanyar nan tazo.
Jiniirin zai biyo ne ta tsakanin hanyar data ratso daga Ƙasar Hausa zuwa jahar ruman, dan haka sai muyi maza-maza yanzu mu koma cikin masarauta, domin ahaɗo kan dakaru da kayan aiki mutafi gaban ruwan, tunda babu wanda yasan lokacin hucewar sa." Ya faɗa suna masu juyawa cikin sauri suka tafi.

Acan ɓangaren Jirgin su Ishaƙ da Aishatu kuwa, adai-dai wannan lokacin ya.............✍

*BAƘAR MASARAUTA*

*NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 14*

Ya huce ta ta cikin Baƙar Masatauta aguje, yana mai ɗaukar hanyar da zata kaisa Jahar Ruman kai tsaye.
Yayin da su Sarki Barbaru kuma tare da boka mai wutar kasko suka ƙarasa cikin Masarautar a matuƙar ruɗe.

Cikin daƙiƙun da basu zarta goma shabiyar ba duka aka haɗa kan dakarun.
Wasu irin jibga jibgan baƙaƙen mutane ne da suke sanye da ƴan gajerun baƙaƙen wandina babu ko roga ajikin su, yayin da idanuwan sa kuma suka kasance jajahur babu kyan gani, ɗauke suke da wasu irin makamai tun daga kan takubba, kibiyoyi da dai sauran dangunan su, kallon su kawai ya isa ya sanya mutum firgici, muddin bai saba ganin suba.

Gaba É—ayan su suka juya suna masu dosar bakin ruwan nan.

Zagaye sa sukayi ta kowane fanni, ya zamto duk ta inda mutum zai ɓullo sai yaci karo da su kafun ya huce, gaba ɗayan su riƙe suke da mugayen makamai.
Tsayuwar su keda wuya awurin wani ƙatoton jirgin ruwa ya tawo zai huce, cikin sauri suka hulla wata igiya mai tsantsar girma, wacce take maƙale da wasu iccina ajikin ta, tayarce jirgin bazai taɓa iya hucewa ba sai ya tsaya.
Ai kuwa kamar yacce sukai zato, jirgin yana hangar igiyar ya tsaya cak awurin da yake, yayin da mutanen cikin jirgin kuma hankulan su yayi bala'in tashi, sabo da abun da suka gani, ga kuma wasu irin mutane da basu da kyan gani da suke tun karo su gadan gadan acikin nasu jirgin ruwan.
Wasu daga cikin dakarun nan ne suka shige cikin jirgin ruwan Baƙar Masarauta, wanda yake zane da tambbarin ta tako ina ajikin sa, hannuwan su riƙe da makamai.
Suna ƙarasawa wurin da jirgin ruwan nan yake suka zare makaman su, suna masu nunawa matuƙan jirgin hanyar da zasu bi.

Cikin tsantsar ruÉ—u, tare da firgici, direbobin jirgin ruwan da suka kasance mutum ukku suka juya kan jirgin nasu, suna masu dosar bakin ruwan nan inda su sarki Barbaru suke atsaye.
Suna isa bakin ruwan Sarki Barbaru ya buɗe murya cikin ƙarfi yan mai faɗin. "Ina son kuyi maza maza ku shiga cikin jirgin nan, abincika mun ko ina na cikin sa lungu da saƙo, tare da jikin kowace mata da take cikin sa, muddin aka samu jinjirin yaro namiji, to akarɓo sa akawo mun shi nan, idan kuma har uwarsa tayi gardama wurin badashi, ku caka mata kibiya, sannan ku tawo mun da ɗan nata." Ya faɗa cikin wata irin muraya mai matuƙar amo da firgitarwa, yayin da su kuma mutanen cikin jirgin nan hankulan su ya sake bala'in tashi, tayarce har wasu daga cikIn su suka fara sakin ihu, yayin da wasu kuma suka sassaki fitsari awuraren da suke, musamman ma mata.

"Duk matar da taƙara gigin barin amon sautin ihun ta ya daki kunne na, to ta sani tabbas ƙarshen rayuwar tane yazo." Sarki Barbaru ya faɗa cikin tsawa, yana mai kai idanuwan sa kan mutanen da suke acikin jirgjn nan.
Take kuwa duka wurin ya É—auki tsit, sai faman muzurai kawai da mata sukeyi.
Yayin da su kuna dakarun nan suka afka cikin jirgin suna masu miƙar da duk matar da suka gani tsaye su duba jikin ta.

Sai da suka ɗauki kimanin daƙiƙa kusan arba'in suna abu guda, tukun suka gama da wannan jirgin ba tare da sun samu ko mai ciki acikin sa ba, sannan suka basa hanya ya wuce, kana suka koma kan na gaba da aka tsayar, kasancewar masu binciken daban suke, masu yawo acikin jirgin ruwan Baƙar Masarauta suna kaɗo jirgayen dake wucewa bakin ruwan, suma daban ne.

*JAHAR RUMAN*

Sai yamma liƙis Ishaƙ da Aishatu suka isa jahar ruman, cikin rugar da ahalin Aishatu suke rayuwa acikin ta, bayan kwana ɗaya da yini ɗaya da sukayi akan hanya.

Gari ne mai tsantsar daÉ—i da ni'ima.
Bukkoki ne tsalli-tsalli awurare daban daban da suke acikin rugar da suke.

Tun daga nesa suka hango mutane da yawa zaune akan tabarmu, ƙarƙashin inuwar bishiyar darbejiya.

Jiki asaɓule suka ƙarasa wurin, suna masu durƙusawa agaban tabarmun.
Sosai suka yiwa junan su gaisuwa, tukun suka tashi gaba É—ayan su zuwa cikin gidan.

_BAYAN SATI ÆŠAYA_

Yau ta kasance ranar Al'hamis, wacce tayi dai dai da cikar mahaifin Aishatu kwana goma da rasuwa.

Tun jiya suka fara haɗa kayan su, kasancewar yau Al'hamis itace ranar da suka tsara zasu koma, amma zasubi jirgin ƙarfe goma na safe ne.
Sosai dangin Aishatu suka haɗa musu tsaraba suka ƙulle ta wuri ɗaya.
Gaba É—aya kowa ka kalla dake cikin gidan jikin sa atsantsar sanyaye yake, domin kuwa har kawo yau mutuwar bata sake suba, jinta suke tamkar sabuwa, barin ma Aishatu da take jin jikinta na sake yin sanyi, wata irin kasala na rufe ta, tana mai jin tamkar su fasa tafiyar daga gobe, su bari sai wani lokacin, ga yarce gaban ta ke yawan faÉ—uwa tun bayan kwana biyu da suka huce, sai dai kuma babu wanda ta faÉ—awa kalar yanayin da take ciki, kamar yacce babu wanda ya tambayae tama, sabo da kowa na dan ganta sanyin nata ne da cewa mutuwar ce bata sake taba, yayin da ta fannin ta itama take ganin duk hakan ne.

Acan Ɓakar Masarauta kuwa yau kimanin sati ɗaya cir kenan da fara binciken jaririn da sukayi abakin ruwa, ba dare ba rana kullum abu ɗaya sukeyi, domin kuwa ko runtsawa harta da shi sarki Barbaru, sabo da gudun karsu kwanta jirgin da jinjirin yake aciki yazo ya huce basu sani ba.
Zuwa yanzu sun kashe jinjirayen mutane sama da ashirin da biyar, sabo da duk cikin yaran da suke samu har yau ba'a samu wanda ya tuntsirar da hutar kasko ba kamar yacce Boka mai hutar kasko yace jinjirin zaiyi.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Hadimai ne kawai ke giftawa ta ko ina acikin masarautar, wasu É—auke da abubuwa a hannayen su, yayinda wasu kuma suke share-share da goge-goge.

Aɓangaren sashin Gimbiya Huwaila, uwar gidan Sarki Abdallah kuma zaune take agefen gadon dake can cikin ƙuryar ɗakin ta.

Kallon matar dake zaune aƙasan gado daga gaban ta tayi ido cikin ido, tana mai miƙa mata wani ƙullin tsuma dake riƙe ahannun ta.
Miƙo tafin hannun ta matar mai kimanin shekaru hamsin tayi, itama ɗin idanuwan ta acikin na Gimbiya Huwaila.

"Ina son ki buÉ—e kunnuwan ki ki saurareni Jakadiya, domin kuwa awannan karan ba lallai ne na sake yarda dake ba, muddin kika cemun an samu matsala kamar na baya." Ta faÉ—a tana mai cigaba da kallon ta.
Chapter 34 · 0% Book details