Sashe 52
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu fah kamar ƙarami sai gashi yana shirin zamtowa Babba, domin kuwa har kawo yau da su Gimbiya Fulani suka cika sati ɗaya da zuwa kuma suke shirin juyawa a yau ɗin, Asad baiyi magana ba, wanda hakan kuma ba ƙaramun tayar musu da hankali yayi ba, domin kuwa iyakar su da shi kallo ne kawai.
A haka dai rai babu daɗi suka rabu, driver'n Sheikh Yaƙub ya kai su airport, domin su koma Ƙasar Hausa zuciya na zafi da ƙuna.
***
Kwanaki sunja watanni sun zo sun shuÉ—e, tun ana sa ran Yarima Asad zaiyi magana a cikin Æ´an satittika sai gashi har ya É—auki tsawon wata tara ba uhm ba uhm-uhm sai dai kallo da idanuwa kawai.
Gaba ɗaya sun fara futar da tsammanin zai sake magana, duk da har lokacin basu bar ƙasar London ba, kwatsam rana ɗaya kawai a daren ranar da zai cika wata goma da fara rashin lafiyar tasa, suna zaune tare da Mai Martaba da ya dawo daga Ƙasar Hausa aranar, kawai sai jin muryar Asad yayi tana dukan kunnen sa ahankali.
Da farko basarwa yayi ba tare da ya juyo ɓarin da yake ba, domin kuwa duk atinanin sa amsa kuwwa ne kunnen sa yake masa na muryar tasa kamar yadda ya saba yi masa a kusan kullum.
Amma sai yaji Asad ya sake faÉ—in.
"Abba na!"
Hakan ne yasa sa juyowa ɓarin da yake da matuƙar sauri, yana mai kallon sa baki buɗe.
Yayin da shi kuma Yarima Asad ya lumshe idanuwan sa a hankali, tukun daga bisani ya sake buÉ—e baki cikin sanyi yana mai faÉ—in.
"Abba na."
Zumubur Mai Martaba ya miƙe daga kan kujerar da yake, yana mai nufar wacce Asad yake a kai cikin tsantsar aljabi.
Yana ƙarasowa gaban kujerar da yake ya durƙushe a ƙasa yana mai zama akan guiwoyin sa, tukun daga bisani ya buɗe baki cikin rawar murya idanuwan sa akan fuskar Asad, yana mai faɗin.
"Shin da gaske ne abun da kunnuwa na suka jiyo mun, kai É—in ne kake magana da kanka Baba na?"
Mai Martaba ya faɗi haka cikin sauri, yana mai kamo tafukan hannayen Yarima Asad duka biyu ya riƙe su da nasa.
Yayin da shi kuma Asad ya sake mayar da idanuwan sa yana mai lumshe su, tukun daga bisani ya jin-jinawa Mai Martaba kai alamar Eh.
Girgiza kai Mai Martaba ya fara yi yana mai faÉ—in.
"A'a Baba na ba da kai nake son ka amsa mun ba, muryar taka nake son sake ji tamkar yacce naji ta yanzu."
"Abba na!"
Yarima Asad ya sake faÉ—e yana mai kallon mahaifin nasa.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya buÉ—e baki cikin tsantsar farin ciki yana mai faÉ—in.
"Shin tun yaushe ne ka fara magana Baba na ban sani ba, ko kuwa dama can kanayi-yin ne baka yi Baba na?" Ya faɗi maganar cikin rawar murya, yana mai shafa lallausar sumar da take kwance sunƙum akan Asad.
"Yanzu nima naji nayi maganar."
Asad É—in ya faÉ—a yana mai sake yin shiru.
Da wani irin sauri Mai Martaba ya janyo sa jikin sa yana mai rungume sa ƙam-ƙam a ƙirjin sa yarce kasan zai mayar da shi ciki.
Tukun daga bisani ya buɗe baki cikin muryar tsantsar farin ciki, hawaye na tsiyayowa daga cikin idanuwan sa, ya fara faɗin kalmar. "Alhamdulillah." Ba ƙaƙƙautawa.
Suna a wannan yana yin ne Sheikh Yaƙub ya danno kansa cikin ɗakin, bakin sa ɗauke da Sallama.
Hango su da yayi a hakan ne yasan ya sa ƙarasawa ciki da matuƙar sauri, yana mai faɗin.
"Subahanallahi, meke faruwa ne yallaɓai na ganku a haka?"
Ya ƙarasa maganar yana mai ƙarasowa gaban su ya tsaya.
Yayin da shi kuma Mai Martaba ya saki Asad da sauri yana mai miƙewa tsaye ya rungume Sheikh Yaƙub.
Shi kuwa Asad mayar da idanuwan sa yayi ya lumshe su ba tare da yace komai ba, domin kuwa hakanan kawai yaji ko kaÉ—an baya son yin maganar, amai-makon ace yayi ta yin ta amatsayin sa na wanda ya daÉ—e bai furta koda kalmar A ba.
"Allah ya amshi addu'ar mu ya Sheikh, yau dai Asad É—ina yamun magana, ya kirani ba sau É—aya ba ba sau biyu ba."
Mai Martaba ya faÉ—a cikin matsanan ciyar murna.
Yayin da shi kuma Sheikh Yaƙub ya furta kalmar. "Alhamdulillah." Cikin tsantsar farin ciki, yana mai sake rungumar Mai Martaba shima, tukun daga bisani ya sake sa yana mai yin wurin da Asad yake, bakin sa ɗauke da tsantsar murna.
Zube guiwoyin sa shima yayi a gaban sa yana kallon sa.
Tukun daga bisani ya buÉ—e baki cikin tsantsar farin ciki yana mai faÉ—in.
"Asad! Shin da gaske na kayi magana?"
Jin-jina masa kai Asad yayi, tukun daga bisani ya buÉ—e idanuwan sa da suke a lumshe yana mai faÉ—in.
"Eh nayi magana Ya Sheikh." Ya faÉ—i hakan cikin sanyi.
Yayin da Sheikh Yaƙub kuma yayi saurin janyo sa cikin jikin sa yana mai godiya ga Allah.
Haka dai sukai ta farin ciki suna sake sanya Asad yana magana, duk da yadda baya son yin nata shida ko kaÉ—an.
Aranar Mai Martaba ya farayi musu cuku-cukun juyawa Ƙasar Hausa a gobe shida Asad.
Ko da dare yayi sosai Mai Martaba yayi bacci har da munshari, irin wanda ya jima baiyi kamar saba, domin kuwa rabon sa da cikakken bacci tun ana gobe Asad zai kamu da ciwon nan, wato tsawon wata goma yanzu kenan.
Washe gari kuwa tun da sanyin safiya suka tafi airport.
Ƙarfe takwas na safe dai-dai na agogon ƙasar jirgin su ya ɗaga zuwa sararin samaniya.
Yayin da Sheikh Yaƙub kuma da Iyalan sa da suka yo musu rakiya suka juya cikin jin kewar tafiyar tasu, suna masu komawa gida.
*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*
Lokacin da labarin dawowar Mai Martaba a yau ya fasu a cikin Masarauta Wasai, ba ƙaramun mamakin abun da zai sanya sa dawowa yau bayan kuma kowa yasan jiya ya tafi bane ya lulluɓe su.
Take kuwa maganar ta bazu ako ina dake cikin Masarautar, yayin da jama'a da dama dake cikin Masarautar sukai tinanin ko Asad É—in ne ya rasu, dan kuwa babu wani wanda yay tinanin ko warkewa yayi ne.
Tini kuwa murna ta cika zukatan magautan su gaba É—aya da tinanin da sukeyi na ko Asad É—in ne ya rasu, kasancewar Mai Martaba bai sanar da kowa dawowar tasa ba har sai da ya sauka a cikin Wasai Internationl airport, tukun ya sanar musu domin azo atafi da su, amma bawai ya faÉ—a musu dalilin dawowar tasa bane, sabo da yadda yake son yayi suprising É—in su.
Acan ɓangaren Gimbiya Fulani kuwa tana zaune akan kujera sanye da hijabi a jikin ta tana taz'bihi, ɗaya daga cikin Hadiman ta da suke anan part ɗin nata ta faɗo cikin falon da sauri.
Da idanuwa Gimbiya Fulani ta bita bayan ta amsa mata sallamar da tayo, har ta ƙaraso bakin kujerar da take zaune akai.
Durƙusar dai ƙasa Hadimar tayi bayan ta zauna akan ƙafafuwan ta, tana mai buɗe baki tace.
"Barka da hutawa ranki ya daÉ—e."
"Yawwa barkan ki dai Talatu."
Gimbiya Fulani ta faÉ—a tana mai cigaba da kallon ta.
Yayin da ita kuma ta É—an fara mustu-mutsu a wurin da take tana mai son buÉ—e baki tayi magana, amma tana tsoron tayarce Gimbiya Fulani zata É—au zancen, sabo da sun sani gaba É—ayan su bata son gulma, asalima babu abun da ta tsana face mutum ya jiyo wani labarin na wani a cikin gidan yazo yace zai sanar mata, hakan yasa gaba É—aya ta kasa buÉ—e baki tayi maganar kai tsaye.
"Alamun ki sun nuna akwai magana É—auke abakin ko, shin meke faruwa ne to?"
Gimbiya Fulani ta faÉ—a tana kallon ta, sabo da lura da tayi da ita tana son yin maganar amma kuma tana shakkar yi.
Jin da Hadima Talatu tayi Fulani ta bata dama ne, ya sanya ta É—ago kai cikin rawar murya tana mai faÉ—in.
"Dama wai yanzu ne muma mukejin labarin dawowar Mai Martaba ayau, domin kuwa ance har ya sauka ma an tafi É—akko sa"
Ta ƙarasa maganar da sosa ƙeya.
Yayin da ita kuma Fulani tayi suman zaune a wurin da take gaban ta nayin wata irin gigitacciyar faÉ—uwa, sabo da jin furucin Hadima Talatu da tayi na cewa Mai Martaba ya dawo, sabo da jiya kafun ya tafi ita da kanta ta tambaye sa sai kuma yaushe zai dawo, amma yace mata bai sani ba shima sai yadda hali yayi, sai dai kuma yana tinanin zai É—auki tsawon sati biyu zuwa ukku kafun ya dawo É—in, sai gashi kuma yanzu labarin isowar sa yazo kunnen ta.
Zumbur ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take jikin ta na rawa, yayin da ita kumavwannan hadimar tayi saurin ja da baya daga zaunen da take, sabo da a zaton ta tashi tayi ta make ta ne, duk da dai tasan hakan ba halin ta bane, amma sai taga ta kama hanyar waje cikin ɗimuwa, bakin ta na furta kalmar.
"Innalillahi wa'inna ilahir raj..."
Cak maganar ta tsaya daga cikin bakin ta tana mai ƙamewa wuri ɗaya, ƙirjin ta na cigaba da dukan tara-tara, sabo da yadda muryar mai martaba ta daki dodon kunnuwan ta yana mai doko sallama shima.
Tukun daga bisani sai gashi nan ya danno kansa cikin falon.
Kana sai ga Asad nan kuma ya tako masa baya sanye da ƙana nan kaya a jikin sa.
Take a wurin Gimbiya Fulani ta fara zare idanuwa jikin ta na cigaba da kar-karwa, yayin da idanuwan ta kuma suka kasance ƙur akan fuskar Asad da tayi arba da shi tana kallon sa.
Itama wannan Hadimar tare da su Babban Yaya da sauran ƴan uwan su gaba ɗayan su ƙamewa sukayi a wuri ɗaya suna kallon Asad cikin tsantsar mamaki, ba tare da an iya samun ɗaya daga cikin su ya matsa wurin da yake ba.
Yayin da Mai Marataba dake riƙe da hannun Asad kuma yayi tsaye yana kallon Gimbiya Fulani, fuskar ɗauke da wani irin yalwataccen murmushi.
Tukun daga bisani ya mayar da idanuwan sa kan fuskar Asad da yake ta faman naniƙe sa, tun lokacin da suka shigo Masarautar, domin kuwa sai da suka ƙaraso ɓangaren Gimbiya Fulani ne ma tukun ya ɗan ware.