← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 79

Sashe 76

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ta duk'ufa wurin binciken ganin ta gano mazaunin sa, amma a kullum abun baya yihuwa.
Tana da amintaccen Bawa wanda take kiran sa da Buba, wato amintacce ta kenan da fulatanci.
Shine kad'ai ya tabbatar da Gid'ad'on ta mutum ne ba aljan ba, sannan kuma ya duk'ufa wurin ganin ya taya ta cimma burin ta.

A yanzu haka tana da shekaru Ashirin da biyu ne aduniya, yayin da kyawun halittar ta kuma ako da yaushe yake k'ara bayyana, ta yadda babu mai iyayi mata kallo d'aya ya janye idanuwan sa ba tare da ya sake ba, tun daga kan mace kuwa har namiji.

Duk da secondry d'in da tayi batasa ta bar al'adun su na fulani ba da shigar su, kamar yadda ta taso ta ganta acikin ta.
Domin kuwa haka masarautar tasu take tafiya har kawo yau da al'adun ta, wannan dalilin ne ma ya sanya ko wasu kayan daban Gimbiya Haddiyal bata sanyawa sai nasu na fulani, duk da kuwa ba su d'in ne kad'ai suka zamto kayan ta ba, domin kuwa Habu da kansa yake siyo mata English wear tare kuma da atamfofi da leces, amma ko kallo basu isheta ba.
Iyakaci idan kaga tasa wasu kayan daban to lokacin bacci ne, shine take sanya sleeping dress a jikin ta.
Yayin da su kuma kayan nata na fulani suka zamto kala-kala, kana masu matuk'ar yawa, ta yadda har idan tasa wani sai ta shafe sama da wata ukku ba tare da ta zagayo kansa ba, kai wani lokacin ma har mantawa da wasu takeyi.

*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA*

Tun bayan karon da Gimbiya Tamir da Bir da sukayi na biyu da har yau basu sake gamuwa ba, tsawon watanni da yawa kenan, kuma hakan ya faru ne ta dalilin rok'on sa da iyar bayi tai-tayi har da su k'wallar ta akan kar ya k'ara shiga sabgar Gimbiya.
Amma sai dai kuma ba k'aramar cutuwa yayi ba da rashin ganin tan da bayayi, domin kuwa babu ranar da zata zo ta shige ba tare da yayi tinanin ta ba, haka kuma aduk daren duniya yana aikin mafarkin ta.
Sosai kuwa ya rame kana gaba d'ayan sa ya k'ara komawa shiru-shiru.

Haka kawai kwanan nan yaji aduk duniya babu abun da yake son gani sama da fuskar ta, ta yadda har yake jin baik'i ba ace ko kashe sane tasa ayi muddin ya riga ya ganta.
Wannan dalilin yasa sa k'udirtawa ransa cewar yau duk runtsi duk huya sai ya isa gare ta, sai dai duk abun da zai faru ya faru bayan ya gantan.

Ita kuwa gimbiya Tasmir a b'angaren ta sai da ta d'auki kusan wata tana jin bak'in cikin abun da yayi mata, kafun daga baya kuma komai ya huce.

Babu abun da yafi damun ta sai idan ta tuna da yadda bugun zuciyar ta ke sauyawa aduk lokacin da suka had'u.
Hakan yasa ta k'udiri aniyar cewa muddin suka k'ara yin gamo da shi sai yayi mata bayanin dalilin da yasa take jin fad'uwar gaba idan ta kasance a gaban sa, sabo da tana zargin ko wani asirin gare sa akan ta, sai dai kuma tun bayan waccan had'uwar tasu ba ta k'ara ganin sa ba.
Hakan yasa ta gane cewa ya bam-bance tsakanin ta da shi kenan, shiyasa bai k'ara biyo hanyar ta ba, wanda hakan kuma ba k'aramun dad'i yayi mata ba.

Yanzu haka zaune take akan d'irkeken bak'in dokin ta sanye da shigar ta-ta yau da kullum.
Yayin da hannun ta d'aya kuma yake r................✍

*AMIN AFUWA ZAKUGA SUNAN MAHAIFIN SHEIKH AHMAD YA CANZA DAGA ABDULKARIM DA NACE A PAGE NA UKKU ZUWA ISHAK', HAKAN YA FARUNE TA DALILIN MANTUWAR DA NAYI.*
SAI KUMA NA BIYU YAYAN GIMBIYA HADDIYAL HABU SUNAN SA, BUBA KUMA SUNAN AMINTACCEN BAWAN TANE, SHIMA ABAYA NAYI MISTAKE NA CEWA HABU BUBA, WANDA SAI DAGA BAYA NA FAHIMTA.*

UMAR FARUQ.✍

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
👑👑
🦋
🦅🕊🦆
🐍🎠🐄🏹

_*NA*_

UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*PAGE 30*

_END OF BOOK 1_

Rik'e da zureriyar takobin ta, d'ayan hannun ta kuwa rik'e yake da linzamin dokin ta.
A hankali dokin ya fara tafiya, yau da alamun ita kad'ai kawai take sha'awar yawon, duba da yadda babu wani da ya biyo ta a cikin dakarun nata.

Tafe suke a saman dokin fuskar ta d'auke da annuri, sab'anin sauran ranakun da ko da yaushe take a d'aure.
Yau tun da ta tashi daga bacci take jinta cikin wani irin farin ciki.

'Daga kanta tayi sama tana mai kallon yadda giza-gizai suke a ko ina, ga kuma yadda garin nasu yayi luf-luf tamkar koda yaushe, kana ga wata irin sassanyar iska mai matuk'ar dad'i da take busata ta ko ina, ta yadda har uban bak'in gashin kanta yake d'an d'agawa sama.
Ga kuma yadda iskar ke kad'a rigar da ke sanye a jikin ta, tana ta faman bud'ewa, wannan dalilin shine ya sake sanya ta cikin annashuwa sosai.

Acan wurin Bir kuwa cikin wani irin yanayi na tsantsar buk'atar ganin fuskar Gimbiya da yaji shi a cikin sa ya mik'e daga bakin bishiyar da yake zaune.

'Daga tafin hannun sa yayi yana mai shafa lallausar sumar dake d'auke akan sa mai matuk'ar yawa.
Kafin daga bisani kuma ya d'an saki murmushi, yana mai fatan ya had'u da itan idan ya tafi.
Kana ya fara d'aga k'afafuwan sa cikin wani irin kuzarin da yake ji a tattare da shi, yana mai dosar hanyar da yake tsammanin zai iya cin karo da Gimbiyar tasa acan.
Sosai yake jin wani irin farin ciki mara misaltuwa tattare da shi.

A lokaci d'aya gaba d'ayan su bugun zuciyar su ya sauya, suka fara jin tamkar yadda suke ji aduk lokacin da sukayi kusanci da junan su.

Cak Bir ya tsaya a wurin da yake yana mai lumshe idanuwan sa, kana daga bisani ya d'ago tafin hannun sa yana mai dafe saitin zuciyar sa da shi.
Yayin da yake jin wani irin farin ciki mara misaltuwa nayi masa bargo a gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar sa, sabo da fahimtar da yayi na tabbas Gimbiyar tasa tana kusa da k'arasowa wurin da yake d'in, wato dai yau yayi futowar sa'a.
Kana daga bisani ya cigaba da d'aga k'afafuwan sa yana mai cigaba da bin hanyar, kansa sun kuye a k'asa, acewar sa yana son ta fara kallon sa ne kafin shima ya kalle ta.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir lokaci d'aya yanayin ta ya sauya, gaba d'aya annurin dake akan fuskar ta ya gushe, ta yadda har launin idanuwan ta suka fara d'an sauyawa, ba dan komai ba kuwa sai sabo da jin da tayi bugun zuciyar ta gaba d'aya ya canza, k'irjin ta na wani irin bugun tara-tara, wanda hakan yasa ta fahimci abun da ke shirin faruwa, wato dai yau ma batayi futowar sa'a ba, tayi gamo da k'ask'antaccen Bawan ta.
'Dan rumtse idanuwan ta tayi da k'arfi, tana mai tinanin kalar hukuncin da zatayi masa idan har bai bata amsar tambayar da zatayi masa yau ba, domin kuwa ta k'udiri aniyar jin dalilin da ya sanya take samun fad'uwar gaba aduk lokacin da zai-zo gare ta.

Cikin wani irin yanayi na tsantsar b'acin rai ta sake damk'ar linzamin dokin.
Ai kuwa take a wurin ya k'ara gudun sa akan wanda yake yi na baya.

Ba zato ba tsamnani kawai sai ganin su sukayi a gaban juna.
Ita tana daga saman doki idanuwan ta akan sa.
Yayin da shi kuma yake daga k'asa gaban dokin idanuwan sa a cikin natan.

Kallon-kallo suka fara jifan junan su da shi daga wuraren da suke tamkar ko da yaushe.
Yayin da bugun zuciyoyin su kuna suke sake tsanan ta, ta yadda har suke jin tamkar zasu hudo k'irjin su su futo.

Cikin wani irin yanayi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwan ta, tana mai jin tabbas wannan bawan yana shirin zame mata masifa a rayuwa, kafin daga bisani kuma ta fara aikawa kanta da tambayoyi.

"Shin mene yasa bashi da tsoro ne ma shi, wato kenan yana nufin yace duk wahalar da yasha a wancan lokacin bai daddara ba, tun da gashi nan yau ma ya tsare ni agaba yana aiko mun kallo da wa'yan nan mayun idanuwan nasa, tabbas yau d'in kuwa dole ne na san dalilin da yasa kallon sa yake sanya mun fad'uwar gaba."
Ta fad'i haka a cikin ranta, kana daga bisani ta bud'e idanuwan nata akan fuskar Bir.
Sannan tayi wani irin durowa daga kan dokin, tana mai fara d'aga k'afafuwan ta-ta doshi wurin da yake takobin ta rik'e a hannun ta.

A hankali Bir ya d'an fara d'aga k'afafuwan sa yana mai ja baya daga wurin da yake, sabo da yadda yaga ta nufo kansa gadan-gadan.
Yayin da har lokacin kuma idanuwan su suke sark'e a cikin na juna.

Ba shi ya dakata da ja da bayan da yake ba kamar yadda itama d'in bata daina biyo sa ba, har sai da ya dan gana da jikin wata k'atuwar bishiya, kana ya jingina da ita yana mai lumshe idanuwan sa.
Yayin da ita ma ta tsaya cak a wurin, tana mai jin zuciyar ta na cigaba da gudu a d'ari, ga kuma wani irin b'acin rai da tsantsar tsanar wannan bawan na gaban ta da suke taso mata tun daga k'asan zuciyar ta.

A hankali Bir ya bud'e idanuwan sa yana mai watsa su akan fuskar ta, kana ya d'an saki murmushin sa mai matuk'ar kyau, ta yadda har sai da fararen hak'waran sa suka bayanna, tukun ya d'an d'aga lab'b'an sa cikin yin k'asa da murya, yana mai fad'in.

"Hak'ik'a idanuwa na sunyi kewar ganin wannan kyakkyarwa fuskar taki, mai cike da abubuwan kallon akan ta Gimbiyar mu.
Shin wai me...."
Maganar tasa ce ta yanke, sabo da yadda yaga lokacin d'aya jikin ta ya d'auki wata irin rawa, ga kuma idanuwanta da ta zuba su akan sa da suke k'ara rikid'ewa suna yin ja, jan ma irin jajahur d'in nan.
Yayin da jijiyon kanta kuma suka futo sukai rud'u-rud'u akan goshin ta.

"Zan tambaye ka, sai dai kuma kafun nan ina son kasani bana son k'arya, asalima na tsani duk wani mak'aryaci a rayuwata, dan haka amsar tambayata kawai nake buk'atar ji daga gare ka a yau d'in."
Chapter 76 · 0% Book details