Sashe 79
Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta k'arasa maganar tana mai durk'ushewa akan guiwoyin ta ta cigaba da sakin kukan ta har da su shash-sheka.
Yayin da fuskar Yarima Asad kuma tak'i b'acewa daga cikin idanuwan ta, wanda harda hakan yasa take k'arajin tsanar sa fiye da wacce take yiwa Yariman Yamma, sabo da ada fuskar Gid'ad'on ta kawai ce ke mata gizo acikin idanuwan ta, amma sai gashi yau fuskokin sun zama biyu, wato ta gid'ad'o'n ta da kuma ta waccan mutumin mai siffa da 'yan iska da suka had'u.
*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*
Sosai hawaye suke kwaranya daga cikin idanuwan Gimbiya Tasmir tana tafiya.
Wani irin rad'ad'i da suya take jin zuciyar ta nayi mata, idan ta tuna yadda wancan k'ask'antaccen bawan ya had'a jikin sa da nata.
Ji take inama ace Ubangiji Gargabilu ya d'auki rayuwar ta tun kafin zuwan wannan ranar, ji take inama ace baya na komowa, tabbas da babu abun da zai sa tayi gigin cewa zata dake sa a yau, ballan tana har azo ga wannan d'anyen iskancin da fitsarar daya aikata a mata.
Wai ace kamar ita, kamar ita Gimbiya Tasmir, yarinya mai tsantsar kwarjin da Izza, aka samu bawan da ya iya tsayawa a gaban ta ya kalli cikin idanuwan ta, sannan kuma bai ma tsaya a iya kar kallon cikin idanuwan nata ba har sai da ya dangana da had'a jikin sa da nata wuri d'aya.
"Inaa! Wallahi hakan bazai yuwu ba!
Nayi rantsuwa da Ubangiji Gargabilu sai naga bayan ka, sai dai duk abun da zai faru ya faru, domin kuwa bazan tab'a barin ka ba kaci banza."
Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji, tana mai durk'ushewa a kasa akan guiwoyin ta, yayin da ruwan hawaye kuma suke cigaba ambaliya daga cikin idanuwan ta tamkar an bud'e famfo.
"Shi me yasa rayuwa zakiyi mun haka? Me yasa duniya zaki juyamun a lokaci guda? Me yasa izza ta, kwajini na tare da k'arfin ikona zasu nemi tarwatsewa a lokaci guda? Shin wane laifi na aikata maka Ubangiji Gargabilu da har zaka hukunta ni ta hanyar turo k'ask'antacce bawa gare ni? Me yasa, me yasa zaka hanani hukun tasa Baba?
Me yasa hakan zata faru dani?"
Ta k'ara fad'a cikin k'araji, hawaye na cigaba da tsiyayowa daga cikin idanuwan ta, abun da ita kanta bazata ce tasan lokacin da ta d'auka rabon ta da kuka ba, sai gashi yau tana yin sa har da k'araji ta sanadin Bawa, Bawan ma kuma k'ask'ancce wanda ko shi kansa bai san suwaye iyayensa ba, Bawan ma d'an tsuntuwa.
Kafin daga bisani kuma ta sake mik'ar da takobinta tana mai fad'in.
"Shairamaaa!!!"
Ta fad'a da wani irin k'araji bayan ta rumtse idanuwan ta.
Take kuwa wannan dank'areriyar macijiyar tata ta bayyana tana mai karkad'a harshen ta.
Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta k'arasa gaban ta da sauri, tana mai durk'usawa k'asa ta damk'i kanta da matuk'ar k'arfi.
Tukun daga bisani ta bud'e baki cikin tsantsar kuka tana mai fad'in.
"Shin ina taimakon da akace zaki yimun a rayuwa Shairama? Ina Garkuwar da akace zaki zame mun a gidan duniya Shairama? Kana ina hasken da akace zakina haskan gaba na da shi Shairama?
Shin wai meye amfanin ki ma agare ni Shairma, bayan gashi nan kina gani ana hulak'anta ni ana take izza ta da kwarjini na akan idanuwan ki ba tare da kin iya komai ba?
Shin taya ya zansan dalilin da yasa Baba ya hanani hukunta wancan matsiyacin Bawan, wane irin k'ulli ne yake ak'asa da har hakan zata kasance? Wata irin alak'a ce take a tsakanin su da har take shirin ta ture wacce take tsakani na da shi?
Tabbas zan binciko, kuma kome yene amsar muddin na gano sa to sai na tarwatsa sa!"
Ta k'arasa maganar tana mai sakin kan macijiyar da ta damk'a tare da sake mik'ewa tsaye zumbur.
Kana ta d'ora da fad'in.
"Baki da amfani a gareni Shairma, ba kiyi mun komai ba a rayuwa, kana ban ga amfanin zaman ki a tare da ni ba tun da har kin kasa bani kariya akan wancan dak'ik'in Bawan!
Tabbas baki da amfani, ki tafi bana bukark'i bana buk'atar ki tattare dani yanzu Shairama."
Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji tana mai shurin macijiyar nan da k'afa.
Take kuwa a wurin ta b'ace b'at tamkar ba'a tab'a yin ta.
Yayin da ita kuma Gimbiya Tasmir ta fara d'aga k'afafuwan ta tana mai dosar hanyar da zata sadata da part d'in su ta baya, ba tare da ta koma filin bikin nan ba.
Acan cikin filin biki kuma sosai hankalin Iyar Bayi yayi bala'in tashi, jikin ta ya dinga wata irin karkarwa, gumi na yanko mata daga can wurin da take a tsaye, domin kuwa akan idanuwanta komai ya faru na abun da Gimbiya Tasmir tayiwa Bir, har binsa abaya da tayi bayan ya bar filin kuwa.
Hawaye ne keta tawo mata tana mayar da su, tare da danne kukan nata tana mai hanasa bayyana afili, domin kuwa muddin aka ganta tana kuka a irin wannan ranar kashin ta ya bushe, sabo da za'ayi zato ko tausayin matasan bayin nan take ji, wanda kuma a k'a'idar Bak'ar Masarauta babu tausayi ga wanda ake yiwa hukunci, ballantana kuma su da ba hukunci ake musu ba duk hakan yana daga cikin murna ne.
Sai dai kuma ayau ta k'udirtawa ranta cewar muddin Bir ya tambayeta labarin sa zata fad'a masa, ko da hakan ko zai zamto silar futar numfashi ta da ga gangar jikin ta ne, wato futar rai daga cikin ruhinta.
Sabo da tasan tausayin sa ba zai tab'a bari ta sake b'oye masa ba muddin ya tambaye tan, kasancewar tana da matuk'ar rauni akan Bir, asalima shine ya zamto raunin ta a yanzu.
A cikin filin Biki kuwa ko kad'an babu wanda ya lura da Gimbiya Tasmir bata wurin hatta da iyayen ta kuwa, hakan ne yasa aka cigaba da d'ibar shagali hankali kwance, ana kid'i da rawa tare da ihun kiran sunan Gargabilu.
A b'angaren su Bir kuwa cikin duwarwastun nan dakarun nan suka dinga jansa da matuk'ar k'arfi.
Sosai jini ke kwaranya daga jikin sa yana zuba aduk wurin da suka huce tamkar an yanka rago.
Amma a hakan ko kad'an ba tasu yake ba, asalima babu abun da yake gani a cikin idanuwan sa face kyakkyawar fuskar Gimbiya Tasmir.
Yayinda taushin jajayen lab'b'an ta kuma suka zauna daram akan nasa lab'b'an, k'wayoyin idanuwansa kuwa babu abun da suke hasko masa face k'yallin da lab'b'an nata suke yi tare da dogon karan hancin ta.
Yayin da k'ofofin hancinsa kuma suka rik'e k'amshin mayen turaren da yake sanye a jikin ta, ta yadda har yake jin tamkar har yanzu suna tsaye a wuri d'aya ne.
A haka har suka k'arasa gaban wannan tafkeken ruwan, wanda aka haifi Bir acikin sa tun a wancan lokacin na baya, wato shekara talatin baya kenan a cikin jirgin ruwa, domin su fara cika umarnin uwargijiyar tasu akan sa anan, kafin kuma suje ga azaba ta gaba.âœ
_*RIGIJI GABJ! K'AKA K'ARA K'AK'A. TABBAS YANZU NE WASAN ZAI FARA, DOMIN KUWA ABAYA DUK BURGA CE, DAN HAKA SAI ASAKE GYARA ZAMA*_
_*SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI FATU A CIKIN BAK'AR MASARAUTA KASHI NA 2*_
*GA DAI YARIMA ASAD DA GIMBIYA HADDIYAL SUNCI KARO, HAR YAGA ABUN DA BAI TAB'A HANGE BA A JIKIN WATA 'YA MACE AKAN TA.*
*SHIN ME KUKE TINANIN ZAI FARU?*
*GA KUMA MAI GIRMA GWAMNA YAZO NEMAN AUREN YARIMA ASAD GA 'YARSA, SHIN YAYA YARIMA ASAD ZAI D'AUKI LABARIN IDAN AN FAD'A MASA?*
*SHIN ZAI YADDA DA BATUN KO KUWA?*
*IDAN KUMA BAI YADDA BA MAI KUKE TINANIN ZAI FARU?*
*YA BILLY ZATAYI DA DAKON SOYAYYAR SA DA TAKE TA FAMAN YI.*
*SHIN WAI WAYE MA GI'DA'DON NAN NA GIMBIYA HADDIYAL DA KO DA YAUSHE ZANCEN TA YA ZAMTO NASA?*
*GASHI DAI BINCIKEN TA YA TABBATR MATA DA SHI 'DIN MUTUM NE, SHIN TO ZATA HA'DU DA SHI D'IN A ZAHIRI TAMKAR YADDA TAKE MURADI?*
*IDAN KUMA TA HA'DU DA SHI 'DIN ME KUKE TINAIN ZAI FARU?*
*SHIN SHI 'DIN YASAN DA ITAMA TAMKAR YADDA TASAN DA SHI KO KUWA, ZAI SOTA KO KUWA, ZASUYI AURE KO KUWA?*
*YA KUMA BATUN YARIMAN YAMMA ZAI KASANCE?*
*SHIN IDAN GI'DA'DO YA BAYYANA KUNA TINANIN ZAI YADDA YA SHIGA GASAR SHA'DI KUWA, TAMKAR YADDA HAKAN YA ZAMTO DOLE A AL'ADAR SU?*
*TO WAI KUNA MA HANGEN ABUN DA NAKE HANGOWA AKAN GI'DA'DON GIMBIYA HADDIYAL 'DIN NAN KUWA? 😅*
*SHIN AISHATU ZATA HA'DU DA JINJIRIN TA DA TA RABU DA SHI TUN A WURIN DA TA HAIFE SA KAFUN TA KOMA GA MAHALLICIN TA KO KUWA?*
*SHIN WAYE NE WANNAN YARON DA TAKE YAWAN MAFARKIN SA KUWA?*
*SHIN YA K'ARSHEN FA'DAN GIMBIYA TASMIR DA BIR ZAI K'ARE?*
*SHIN BURIN BIR AKAN GIMBIYA TASMIR ZAI CIKA KO KUWA?*
*SHIN ITA 'DIN ZATA CIKA BURIN TA NA GANIN BAYAN SA?*
*GA DAI IYAR BAYI NAN TACE ZATA FA'DAWA BIR LABARIN SA*
*SHIN ME KUKE TINANIN ZAI FARU IDAN YAJI LABARIN NASA?*
*YANA DA RABON SADUWA DA IYAYEN SA KO KUWA?*
*SHIN MEYE ZAI FARU ADUK LOKACIN DA AKACE BIR YA BAR CIKIN BAK'AR MASARAUTA, YA KUKE TINANIN SARKI BARBARU ZAIYI?*
*SHIN BINCIKEN BOKA MAI HUTAR KASKO ZAI TABBATA KO KUWA?*
*MUTANE DA DAMA SUNA TINAIN ME YASA MASARAUTU SUKA ZAMA DA YAWA, ME YE HA'DIN MASARAUTAR FUL'DE DA KUMA MASARAUTAR WASAI KANA DA BAK'AR MASARAUTA.*
*TO KUSANI GABA 'DAYA LABARIN BAK'AR MASARAUTA LABARI NE GUDA 'DAYA, WATO DUNK'ULALLE.*
*HAKA KUMA GABA 'DAYA WAYAN NAN AMSOSHIN ZASU ZO MUKU NE A CIKIN LITTAFIN BAK'AR MASARAUTA KASHI NA 2.*
*HAKAN YASA NAKE BAKU TABBACIN AKAN DUK WANDA BAI KARANTA BAK'AR MASARAUTA BOOK 2 BA TO TABBAS AN BARSA ABAYA, DAN HAKA KU GAGGAUTA NEMAR NAKU DOMIN ADAMA DAKU.
_*ALHAMDULILLAH*
_*ANAN NA KAWO K'ARSHEN BAK'AR MASARAUTA BOOK 1*_
_*UMAR DAYYAN.âœ*_
_