← Book details Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 79

Sashe 22

Bakar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa tsaye tayi cikin tsantsar farin ciki tana mai sakin dariya, tukun daga bisani ta buɗe baki tana mai faɗin. "Barkan ku da zuwa Birbillo am masoya na." Ta faɗa tana mai cigaba da sakin dariya, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Shin ta wata hanyar kuke ganin zanbi domin na tsallake ruwan nan?" Ta ƙarasa maganar tana mai tsayawa awuri ɗaya tare da zuba idanuwan ta akan su.

Rufe bakin ta keda wuya gaba ɗayan su suka tashi daga kan tafukan hannuwan nata suna masu komawa kan sandar ta da take ajiye agefe, tukun suka ƙara tashi daga kan sandar suna masu tafiya zuwa saitin ruwan nan sukayi kamar zasu nutsa cikin sa, sannan suka sake juyawa suna masu sake hayewa kan tafukan hannuwan ta.

"Godiya nake masoya na, bada ban kuba da bansan yacce zanyi in tsallaka ruwan nan ba." Ta faɗa tana mai sakin murmushi, tukun ta daga bisani ɗora da cewar. "To sai da anjiman ku masoya na, ni zan ƙarasa wurin Gidado am."

Tashi sukayi dukan su suna masu komawa cikin ciyayin nan, yayin da ita kuma ta durƙusa ƙasa tana mai sa hannu ta ɗauki sandar ta dake ajiye aƙasa, tukun ta ɗago ta tana mai riƙe ta ahannun ta, ta miƙar da ita tare da zuba mata idanuwan ta, kana daga bisani kuma ta buɗe baki tana mai faɗin. "Na dogara dake sandar gado ta, dan haka ina fatan bazaki bani kunya ba, kamar yacce akace ba zaki taɓa bani kunya ba arayuwa, zaki kaini zuwa ga Giɗaɗo am." Sannan ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar bakin ruwan nan gada-gadan.

Tana zuwa gaban sa ta sake dunƙule sandar nan tata da matuƙar ƙarfi acikin tafin hannun ta, tukun ta ɗaga ta tana mai buga ta acikin ruwan nan da matuƙar ƙarfi.
Take kuwa ruwan ya dare gida biyu gaba ɗayan sa. Yayin da ta sake jiyo sautin busar nan da matuƙar ƙarfi na cigaba da dukan kunnen ta.
Ba tare da ta tsaya wata -wata ba ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da take atsakiyar ruwa kai tsaye.

Sai da tai tafiya mai É—an tsawo, tukun ta fuce daga cikin ruwan, kana hanyar ta koma ta haÉ—e gaba É—ayan ta ta zama ruwa kamar da.
Yayin da ita kuma Gimbiya Haddiyal tayi tsaye a'inda take tare da buÉ—e kunnuwa tana mai sauraran sautin busar nan, dan ta fahimci ta inda yake futowa.
Murmushi ta saki tana mai lumshe idanuwan ta, tukun daga bisani ta warasu tana mai fara ɗaga ƙafafuwan ta ta doshi hanyar da take tinanin anan zata tarar da mai busar nan.

Miƙaƙƙar hanyace mai ɗauke da farin yashi mai matuƙar laushi akan ta, cigaba da tafiya tayi har ta ɓulla zuwa wani ƙaton fili mai ɗauke da duwar-watsu tare da da ƙananan ruwaye zagaye da shi.

Zagaye ta farayi aÉ—an rukunin wurin da take tana mai wara idanuwan ta, domin ta hango ta inda mai busar yake.

Tsaye ta hange sa acan bayan wani dutse ya juya baya yana mai karkaÉ—a kai, tare da cigaba da sakin busar sa da take jin daÉ—in ta na ratsa har cikin kwanyar ta.

Lumshe idanuwan ta tayi awurin da take tana mai sakin murmushi, tukun daga bisani ta sake buɗe su akan bayan sa, kana ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar wurin da yake.

Tsaye tayi abayan sa tana mai jin wani irin shauƙi na ɗibar ta. Yayin da shi kuma yake cigaba da sakin busar sa hankali kwance ba tare da yasan da tsayuwar ta ba awurin ma.

Gyara tsayuwar ta ta sake yi awurin tana mai ɗora sandar ta akan kafaɗar ta, tukun daga bisani ta buɗe baki cikin daddaɗar muryar ta tana mai faɗin. "Yau dai gani gaban ka Giɗaɗo am, ubangijin shanu da mutane ya yayin sanadin haɗuwar mu da juna yau. Ta ƙarasa furucin cikin wani irin shauƙi wanda bata taɓa tsintar kanta amakamancin sa ba, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "Tabbas yau ɗin ta kasance rana ta musamman gareni ni Gimbiya Haddiyal, yau ɗin ta zamto rana ta daban daga cikin ranakun da nayi arayuwa ta, dan haka juyo ka ganni na ganka Giɗaɗo am, juyo gani masoyi na, juyo kayi arba da wacce aka hallita domin kai, juyo kaga kyakkyawar hallitar da ta daɗe tana tsumayin ganin ka." Ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai tsayawa da yayi da busar da yake yi.

Sake gyara tsayuwa tayi tana mai ɗorawa da faɗin. "Ka sani na soka fiye da kowa da komai dake cikin duniyar nan, na soka kuma ina kan sonka fiye da yarce nake son kaina Giɗaɗo am! Ka sani kai ɗin nawa ne ni kaɗai kamar yacce na kasance taka kai kaɗai kaima, dan haka juyo ka ganni na ganka masoyi na!" Ta ƙarasa maganar still fuskarta ɗauke da tsantsar murmushi.

Ahankali shima ya fara juyowa gare ta fuskar sa ɗauke da tsadadden murmushin sa da yayi matuƙar ƙara masa kyau.
Kallon ta ya farayi yana mai jifan ta da murmushin sa ba tare da yace mata komai ba.
Yayin da ita kuma ta lumshe kyawawan idanuwan ta tana mai cigaba da sakin murmushi, tukun daga bisani ta fara buÉ—esu ahankali-ahankali, tana mai jin sun nata wani irin nauyi, sai dai kuma suna gama buÉ—uwa amai-makon taga GiÉ—aÉ—o am É—in ta sai kawai tayi arba da fillown da ta É—ora kanta akan sa tun kafin tayi bacci!

Zumbur ta miƙe zaune daga kwancen da ta ka tana mai ɗaukar tafin hannun ta ta dafe goshin ta da shi cikin tsantsar takaici da haushi, sabo da fahimtar da tayi na duk abun da ya faru ba gaske bane ba mafarki ne irin wanda ta saba yin sa akoda yaushe tayi.

Ta ɗauki kimanin mintina biyar ahaka tana mai cizon leɓen ta na ƙasa, tukun daga bisani ta janye hanun nata daga kan goshin ta tana mai matsawa bakin gadon tare da zura ƙafafuwan ta ƙasa.
Sannan ta miƙe tsaya tana mai yin taku biyu daga inda take, tukun taja ta tsaya tana mai rumtse idanuwan ta da ƙarfi, kana daga bisani ta buɗe su tana mai faɗin. "Wato idan na fahimci dai dai, wannan mafarkin na nufin sandar tsafi na ta gado ce zata nuna mu hanyar da zanbi in gano ka Giɗaɗo am kenan." Ta ƙarasa maganar tana mai girgza kanta tare da sakin murmushi, tukun ta cigaba da ɗaga ƙafafuwan ta cikin kuzari tana mai dosar wani ɗan ƙaramin ɗaki da yake acikin ɗakin baccin nata.
Hannu tasa tana mai janyo ƙofar dake wurin, tukun ta danna kanta zuwa cikin ɗakin.

Ɗan ƙaramin ɗaki ne sosai, domin ko ko mutum ɗaya bazai ɗauka ba da sunan kwanciya acikin sa.
Ɗauke yake da wasu kayan kari-kitai kala kala acikin sa, sai kuma wata doguwar sanda irin ta fulani da take jingine ajikin bango an yafa mata wani farin ƙyalle akan ta.

Hannu tasa tana mai janye ƙyallen dake kan sandar, sannan ta damƙe ta cikin tafin hannun ta na hagu da matuƙar ƙarfi, tukun ta ɗago ta tana mai juyowa tayo waje da ita.

Hannun daman ta ta sanya ta rufe ƙofar ɗakin da shi, tukun ta juyo tana mai dosar wata ƙofa dake manne jikin bangon ɗakin gadan -gadan.

Buɗe ƙofar tayi itama, kana ta zura kanta tana mai dosar cikin wurin.

Tafkeken filine mai matuƙar girma da faɗi ya bayyana, ashe wai nan ɗin ma hanya ce wacce take sadar da mutum wani shashi na daga cikin sashikan dake cikin gidan cikin sauƙi.

Ɗaukar sandar nan tayi tana mai rataye ta akan kafaɗar ta, tukun ta fara ɗaga ƙafa cikin sauri tana mai dosar wata hanya.
Sai da tayi tafiya mai ɗan nisa daga cikin ɗakin ta data futo, kana ta bayyana gaban wani tafkeken farin ruwa wanda ko ƙarshen sa ba ahange.
Tsaye tayi agaban sa tana mai rumtse idanuwan ta da matuƙar ƙarfi, tukun ta fara ɗaga laɓɓan ta cikin kakkausar murya wacce batai kama da tata ba tana mai faɗin. Zaibaaaa!!!" Tukun ta ɗaga sandar nan tana mai bugata acikin ruwan da matuƙar ƙarfi, kana ta sake rumtse idanuwan tana mai sake faɗar kalmar Zaiba da matuƙar ƙaraji, tukun ta wara idanuwan nata tana mai kaisu kan ruwan nan gaba ɗaya, sai dai kuma me, take awurin taga gaba ɗaya kalar ruwa na sauya daga farin da yake zuwa baƙiƙƙirin yana wani irin tsalle.

Dasauri taja baya tana mai girgiza kai tare da sakin sandar ta aƙasa, tukun daga bisani wasu irin hawaye masu matuƙar gudu suka ɓalle daga cikin idanuwan ta suna dira akan kuncin ta.

Ba ta ita ta tsaya da ja da bayan da take ba har sai da ta jita jikin wata tafkekiyar bishiyar É—orawa, tukun ta jingina da ita tana mai buÉ—e baki cikin kuka tace. "Shin me yasa irin hakan ke faruwa akowa ne lokaci ne? Shin ita É—in Æ´ar gidan uban wace da har take mun katanga da ganin ka GiÉ—aÉ—o am?
Nayi iya yina, nayi duk abun da zanyi domin na sameka amma duk abanza. Shin wane dalili ne ya sanya akowane lokaci ruwan ke canzawa daga kalar sa zuwa Baƙar kala." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jikin bishiyar da ta jngina, tukun ta farayin taku daga inda take tana mai komawa wurin ruwan nan da taga yana juyawa yana komawa asalin kalar sa.
Chapter 22 · 0% Book details